← Book details Nida Patient Dina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 31

Sashe 11

Nida Patient Dina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiga falon tayi da sallama abakinta dukkansu afalo ta samesu Banda azaad Dake dakinshi Yana bacci, yaseer ma yazo Dan agidan yakwana gaidasu tayi kafin tamusu yame jiki amsawa sukayi dasauki alhamdulillah ummi ce tace " ki haura Yana ciki " to ummi haurawa upstairs tayi tashiga part dinsa afalo ta tsaya tana tunanin yatashine ko Yana baccin yankewa tayi baride inje induba ajiye jakanta tayi afalonshi tashiga dakin kwance tasameshi Yana bacci bubbuga filo tafarayi Mr azaad katashi ahankali yafara Bude idonshi dasuka Dan kumbura kadan gashi yayi ja idon shine yasauka akan fuskanta ahankali yamike yazauna abakin gado farar jallabiya ce ajikinshi tunda suka dawo daga masallaci be cire ba yakwanta babu Wanda yayi magana acikinsu tashi yayi yashige toilet zama tayi akan kujera tana jiranshi bayan kaman 30mint yafito sanye da towel direct gaban mirror yaje yagama duk wani abinda zeyi kafin yashige dressing room dinshi FANAN kuwa tunda tazauna tafara game awayarta bata Kara dagowa ba fitowa yayi sanye da Riga armless fari jikin rigan anyi manyan rubuta MAN IS BORN TO HUSTLE da dogon wando na jeans zama yayi akan gadonshi yafara latsa wayarsa sunfi 30mint ahaka gajiya tayi da zaman tace " kasa akawo maka breakfast kayi insamu inma alluranka" ko dago Kai beyiba balle yasan ana mishi magana gajiya tayi takira zeenat" zanma yayanku allura gashi be ci komai ba" to kawai zeenat tace ta katse Kiran 5mint latter tashigo da kayan abinci Yaya mezansa maka be mata magana ba ya mata nuni da ta Bude duka food flask din Bude su tayi kulan farko yam balls ne aciki nabiyu Kuma chips ne dasukaji egg SE na ukun farfesun naman rago ne yaji kayan hadi se tiriri yakeyi nuni yamata da farfesun zuba mishi tayi Ta ajiye mishi a table din Dake gabansa kafin tahada mishi tea tafita. Fanan kuwa tacika fam kamar zata fashe gaba Daya yagama bata mata lokaci sewani Jiji Dakai yakeyi mtsssw tsaki taja Wanda batasan yafito ba dagowa yayi ya kalleta hada ido sukayi takawar da kanta gefe taci gaba da game dinta seda yakwashe mintoci kafin yagama hamdala yayi cikin sexy voice dinshi yace" am done kizokiyi abinda zakiyi I have something to do" sake Baki FANAN tayi tana kallonshi wato shi yanada abinda zeyi nice banida abinyi lallai wannan yacika babban Dan renin hankali mikewa tayi tadau ruwan alluran taja a syringe 💉 da cotton hannunshi yamika mata ta daure tasamo jijiya kafin tamishi alluran tasamai cotton dustbin taje tayar da syringe din maganinshi taballa mishi tabashi da ruwa yakarba yasha sannan ta tambayeshi "yanzu Meye yake damunka" kamar bazeyi magana ba yace "nothing" fita tayi a dakin tadau jakanta tabar part din falo tadawo tasamesu sunata hira zama tayi kusa da anty Amina suna hira, shigowa tayi falon batare da tayi sallama ba Kai tsaye inda fawwaz yake taje tatsaya " Kai Ina baby yake " juyowa su ummi dasu FANAN sukayi Dan basusan da shigowanta ba sanye take da wando crazy Baki se wata yar ficikan Riga pink kan nan babu Dankwali yasha attachment two color kafarta sanye da takalmi Sau ciki Shima pink fuskan nan yasha uban makeup FANAN kam mamakine yakamata Amma wannan kam arniya ce fawwaz kuwa cigaba da kallon ball din dayakeyi yayi beko dago Kai ba ganin baze kulata bane yasa takarasa kusa dasu ummi "hi guys Ina baby yaje" zeenat ce ta iya " kulata kinbamu ajiyansa ne" to karamar mara kunya banyi Dake ba kikama kanki Dani tam duk abinda sukeyi ummi batace musu ci kanku ba haka anty Amina ma FANAN kam Takoma yar kallo " tunda bawanda ze iya fadamin inda yake zanje indubasa da kaina" takarasa maganar tana nufan part din Azaad ganin baya falo yasa tawuce dakinsa akwance tasameshi zuwa tayi takwanta akanshi tana fadin "baby wake up am here" Bude ido yayi yaganta kwance ajikinshi tashi yayi yadan tureta daga jikinsa Yana fadin "aneesa meyasa Baki da hankali ne wai yanzu haka Kika fito daga gida kamar wata arniya " kallon jikinta tayi tace "baby what's wrong with my dress tell me if there's something wrong on it " takaicine yakamasa wato ita bata masan shigar datayi be dace ba harwani tambaya take what's wrong with her dress unbelievable Kuma wai ahaka ita ze aura yafada duniyar tunani yaji tana fadin "baby when are we going back to US " ke bansaniba ko dole sedani Zaki koma please don't disturb me aneesa kukan shagwaba tafara mishi tashi yayi ya dauki wayarsa yafita falon kasa yadawo tana biye dashi abaya gaida ummi yayi da anty Amina suka amsa yajikin naka dasauki kawai yace pressing phone dinshi yafara karasowa aneesa tayi tazauna a kujeran dayake tamanne dashi tana mishi magana ko kulata beyi ba yaci gaba da abinda yakeyi yaseer ne yace aneesa nikam bakyajin kunyane ga surkanki akusa Amma kina irin wannan abun murguda mishi Baki tayi Ina ruwanka ummi de tashi tayi abunta tayi sama anty Amina ma bayanta tabi yarage su zeenat ne afalon kallo takunna musu a TV tashan MBC action suna kallo areef ne yace " zeenat kaimana tashan MBC 2 nasan yanzu suna day breaking" to tace Dan batama San wani film bane shiga tayi aikuwa sukaga anhasko inda wata horror takecin kayan cikin wani ihu suka fasa da ita da FANAN yaseer da fawwaz mezasuyi inbanda dariya harda rike ciki kallon su kawai azaad yayi yadaga musu tsawa "wani irin haukane wannan" shiga cikin rigan nutsuwar su sukayi gashi areef yace baze canza Tasha ba SE rokonsa sukeyi karshema cillawa fawwaz remote din yayi.ganin hakane yasa FANAN da zeenat suka rungume juna da anyi abin tsoro suyi ihu mazan Kuma SE dariya sukeyi Banda azaad da aneesa datayi bacci tana kwance akan kafadar azaad wani wajan dayafi ko Ina tsoro aka nuna wani mutum horrorin suka kwantar suka dauko katon guduma sukayi kaca_kaca da kanshi yatarwatse wani irin ihu suka buga hannu FANAN takai tana ihu tana nuna TV wani irin spark TV yakeyi Yana kawowa Yana daukewa duk Basu luraba still hannun nata nasetin TV duk motsine da zatayi se tv yayi spark tun Basu ankaraba harsuka dawo da hankalinsu wajan itakuwa batama San tanayi ba dungule hannunta tayi da karfi tsabar tsoro tana kokarin rungume zeenat fat!fat!fat! TV yatarwatse yayi condem SE hayaki yakeyi zaro ido sukayi suka kalli TV sesu kalli FANAN ganin suna kallonta ne yasa tace meyafaru ya yaseer nuna mata TV yayi zeyi mata maganan abinda tayi azaad yayi saurin mishi signal da ido akan yayi shuru domin daga gani batasan tayi hakan ba Amma gaba Dayansu sun tsorata da abinda yafaru karasawa tayi kusa da TV tayi tace "subhanallhi meyasameshi yayi haka" bata gama rufe Baki ba jiri yadibeta zata fadi cikin zafin nama azaad ya rungumota kafin ya Ankara harta Suma daukanta chak yayi kamar yar baby ya kwantar da ita akan kujera ana kwantar da ita su ummi suka fito tana fadin " nikam yaran nan lafiya kuke mana ihu " sauka idonta yayi akan FANAN Dake kwance akan sofa dasauri suka karaso meya sameta fawwaz ne yabasu labarin abinda yafaru dukkansu mamaki yacikasu anty Amina ce tace" to me hakan yake nufi shafa kan FANAN takeyi ahankali Kuban ruwa Mika mata ruwa zeenat tayi shafa mata tayi afuska ajiyar zuciya tayi ta tashi tana rike kanta Dake mata azaban ciwo murya narawa tace "wayyo kaina zefita ya Allah,ummi kaina " kwantar da ita ajikinta ummi tayi "sannu kinji bari Kisha magani zedena to aneesa data danyi baccine tafarka tazo gun azaad baby natafi gida okay kawai yace mata kafin ta tafi ......

Tom semun hadu gobe in da Rai da lfy muhadu a comment section 😍😍😍😍😲

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story Written by (MRS 🌹 ISHAM 🌹)

Da sunan Allah me rahama mejinkai 🙏 Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen 🥰🥰

____________________________________________

Page 1️⃣6️⃣

Duka suna zaune cirko cirko sunyi shuru sunrasa abinyi ahaka har aka kira mangrib mazan duka masallaci suka tafi dakyar suka iya tashin FANAN da bacci yadauketa taimaka mata sukayi tamike tana rike da kanta dakin zeenat sukaje adaddafe tayi sallah tadawo tazauna shuru kanta akasa can Kuma kamar wacce aka mintsina ta tuna gida dawo Dede tayi aidasauri tafito dakin duk sundawo daga masallaci suna zaune afalo tafito gudu_gudu mikewa sukayi suma sun dauka wani abun ne yafaru ummi ce tariketa tana fadin" FANAN lafiya" arude tace " wayyo ummi yau nashiga uku Dama mangrib yayi innalillahi wainna ilaijiraji unnn yanzu mezan fada agida anhanani Kai dare awaje "takarasa magana idonta nazubo da hawaye yaseer ne yace "karki damu kizo sena kaiki inwa Yan gidanku bayani" kallonshi tayi tana girgiza Kai "ya yaseer bazaka gane bane daga zarran 5:40 yayi duk inda nake ana San ran dawowana wlh yau nasan mama da baba zasuyi matukar fushi Dani " tafashe da kuka dukkansu tabasu tausayi rungumeta anty Amina tayi tana rarrashinta, azaad da gaba Daya kukanta yadameshi tacika mishi kunne jiyake kamar zeyi hauka saboda ya tsani kukan mace kamar yarufeta da duka haka yakeji ummi tace" azaad daughter (anty Amina kasancewar itace yar farinta bata Kiran sunanta) yaseer Dani da zeenat zamuje gidansu fanan mukaita gida semu bawa iyayenta hakuri duka sunyarda da shawaranta .

Matukar tashin hankali da firgicine yabayyana akan fuskokin mama da baba gaba Dayansu babu Wanda yake cikin hayyacinsa duk sunfito compound din gidan suna jiran dawowar FANAN mama kam takasa jurewa inbanda hawaye ba abinda takeyi damin kuwa sukadai sukasan mezeje yadawo har inde tabiyo Daren nan tafito suhaima ce take rarrashin mama baba ne yace " nasan yata da gangan bazata tabayin abinda ze batamin rai ba da dawowarta awannan dare gwara ta Kwana aduk inda take domin nasan tana hannu nagari fitowarta awannan dare barazana ce ya Allah ka kawo mana sauki " ya al ameen,ya Usman, suhaima duk da hankalinsu atashe Amma kansu adaure yake meyene suke gudun faruwansa domin sun sasu aduhu shuru sukayi suka zubawa sarautar Allah ido.
Chapter 11 · 0% Book details