← Book details Nida Patient Dina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 31

Sashe 21

Nida Patient Dina Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

" Sir wannan sune list din kayan da muka fitar awannan shekaran Kuma alhamdulillah duk sun kare komai yatafi smoothly, a motoci kwaya Dari shida na company duka sun kare saura guda gomane suka rage range Rovers , sekuma company shinkafa nanma abuhu million biyar da aka fitar duk sun kare,haka company sauran kayan abincin Suma komai yatafi yanda yakamata kuma ansayar da komai akan farashin daka fada, sekuma azaad unlimited company (inda ake sarrafa kowani irin nau in kayan sawa) nanma duk kayan ciki sun kare anzuba wasu, se manyan super market dinka dakuma manyan shagunanka na furniture Suma haka komai na wannan shekaran yakare anzuba wasu , se gidajen da akeyin renting ( gidan haya) Suma kowa yabada payment dinsa, masu napep masu taxi 🚕 kowa yakawo nashi balance din, se gidan gona Shima anzuba wasu kayan aciki , shopping mall dinkama haka, bayan hakama Muna bukatar sabbin ma aikata akalla guda dari ko sama da hakan wannan shine list din wannan shekaran sir" Faisal yagama magana yana juyawa azaad dake kwance akan lallausan gadonshi laptop din dan yagani , mikewa yayi yace " good job faisal karka damu base kanuna min ba kamanta komai inde abinda yashafi system dinka dana duk sauran ma aikatana ninake juyashi bane, you did a great job, yanzu abu nagaba shine kafadawa marketing manager yakaro sabbin ma aikata sannan kuma kaje kasamu accounter kowani employee dina akara masa salary akalla 50k each employee, sannan kayi arranging din ziyaran daza mukai gidajen marayu in this week" yana magana yana bata fuska kamar wanda akawa dole seyayi maganar, faisal kam ko ajikinshi inda sabo yasaba da halin ogan nashi shekara 10 bawasa ba , cigaba da magana faisal yayi " sir kanada meeting jibi misalin karfe biyu da kautal Jude company, sekuma jiri brothers and son's sunyi request din appointment dakai zaayi accepting dinsu neko Kuma!?" dan daga kai sama yayi kamar wani me tunani can kuma yace "okay I will think about it" okay sir suna cikin haka me aiki takawo musu abincin ta ajiye a dinning area na falonshi kafin tadan daga murya tace" sir your food is ready" tana gama fadin haka ta tafi ko motsawa azaad beyiba ,tashi Faisal yayi yaje dinning din yaga food flask sunkai takwas ajere bude nafarkon yayi yaga fried rice taji nama zuku_zuku plate yadauka yayi serving kanshi yazauna yafaracin abinci yaci yakoshi yasha drinks dinshi tukun yakoma gun azaad yace " sir cikina yadauka nizan wuce se anjuma" yadauki system dinshi dan dama beyi tsammanin amsa ba yatafi.

Safa da marwa mommy takeyi afalonta fuskanta ahade kamar anmata sako da mutuwa ita kadai se sambatu takeyi " ni Muhammad zeyi kokarin tozartawa wlh be isaba karyanshi yasha karya itakuma aysha senayi maganinta munafukar banza da wofi mtsssw" gaba Daya yaranta tagumi sukayi suka zuba mata ido ganin yanda take maganganu kamar wacce ta zauce anty shayida ce tace " please calm down mommy meyasa kike yawan tayar da hankalinki akan abinda betaka kara yakarya ba wannan aibawani abu bane nide nasan wallahi ummi nasonki tsakani da Allah " wani irin uwar harara mommy ta wurga mata " nide kam banji dadin rayuwata ba Allah yaban yara marasa kishin uwarsu Yan iska marasa zuciya,barinma ke tanuna anty shayida da yatsa nayi dana sanin haihuwarki saboda bazeyu ace nahaifi yarda bata kaunata ba banza laa'nanniya shisa kika kasa samun ci gaba arayuwa keda yara Kuma sede kiga ana haihuwa " ( iyaye yakamata musan irin kalman da zamu dinga furtawa yayanmu domin bakin uwa nada matukar kaifi akan danta walau adduah'ta walau mumunar Baki, Koda yakasance dah namaka laifi duk muninsa karkiwa danki baki domin rayuwarsa ne zetabbare Kuma daga karshe kema kizo kina danasani to miye riban haka, yaro tun Yana dan karami dashi Zaki tankwarashi takan farki mekyau yanda kinsan nan gaba inya girma baza kisha wahala ba, in laifi yayi kimishi fada sosai sannan kijashi ajiki kimai fada yanda nan gaba bazeyi shaawar Kara aikata hakan ba , sannan duka wasu iyayen suna ganin idan yaro yayi laifi akamashi amishi dan bazan duka shine dede to nanma bako wani laifi bane ake bugun yaro, saboda idan jikin yaro yasaba da duka nan gaba koya ganki da bulala wallahi baze gudu ba kokuma kiga alamar tsoro akan fuskanshi ba saboda yariga daya saba da dukan ahakane zakiga yaro yataso marajin magana da rashin ji,.)
Jin irin mugayen kalaman da mommy take binta dasune yasa kukanta da take dannewa yafito Fili, tashi tayi tahaura upstairs dakinsu dasuke ciki time din yanmatancin su ta cigaba da kukanta bin bayanta anty Zainab tayi tana rarrashinta "kiyi hakuri shayida komai lokacine wata rana se lbr yakamata yanzu inda sabo kisaba da halin mommy Kuma kidinga sata a adduah Allah yasa tagane gaskiya " cikin muryan kuka anty shayida tace" anty Zainab irin abinda mommy take mana kamar ba ita tahaifemu ba narasa dalilin dayasa bata kaunar mu tadauki Karan tsana tadaura mana barinma ni tafi tsanata shisa yanzu inbadan Abba da ummi ba wlh se infi watan ni banzo gidan nan ba, anty Zainab ninasan bakin cikine ze kasheni acikin Wanda sukemin gorin haihuwa ace harda uwata wacce yakamata itace zatana rarrashina amma harda baki take
min wai bazan taba haihuwa ba innalillahi wainna ilaijiraji unnn ya Allah kakawomin mafita " tagama magana tana Kara rushewa da marayan kuka rungumeta anty Zainab tayi tana bubbuga bayanta "is okay kinji kokin manta haihuwa na Allah ne shiyake bayarwa alokacin da yagadama in lokacin dazaki samu ciki yayi babu wani mahalukin daze hanaki samu kuma kici gaba da kai kukanki wajan Allah , kidena sawa kanki damuwa kokin manta munada ummi da abba ne ga kannanmu duk suna sonmu ga Amina ma " haka taci gaba da kwantar mata da hankali hartasamu tayi shuru.
Chapter 21 · 0% Book details