← Book details Nida Patient Dina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 31

Sashe 28

Nida Patient Dina Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ina godiya masuyin comment dakumin adduah nagode sosai Ina nan inata ganin wayanda sukemin comment, innaga comment dinki nada yawa zansaki a dayan group din.

Se munhadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy 👍🙏

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

https://chat.whatsapp.com/CwKPAkNXUGWFbqd8CIYeqe

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story & Written by (MRS 🌹 ISHAM 🌹)

Da sunan Allah me rahama mejinkai 🙏 Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen 🥰🤎

Alhamdulillah munzo karshen book 1 📚 se mun hadu a book 2 inda rai da lafiya zamu tafi hutu kamar 1week ko 2weeks,in andawone zaa daura da book 2 inme duka yakaimu da Rai da lfy.

A gaskiya Ina matukar alfahari daku sosai da sosai da yanda kuke bani ruwan comment Lodi lodi dakuma adduah nasara arayuwa Ina me matukar godiya sosai.

Musamman...!

Maman shurem
Sherteen gayu
Eysher raj
Maman junior
Maman yazeed
Umamah Abbas
Snacks craving
Pinky darling
Hauwa'u illiyasu
Oumu Maryam
jiddah
Nana farida
Maarufa Ahmad
Mum basma
Maman widad
Mami
Maman junior
Anty rukkaya
Fatima Hassan umar
Diamond sarah
Maman faruq
Yar mamanta
Ummu amal
Ummu suhaima
Mhizz deejerh
Zainab magarya
Anam
Anty ummi mulki
Maryam said
Khareema
Man munawwara
Etc Dade sauran ku

Yesterday you guys gave me unforgettable hot comments I really appreciate allah yabar kauna inasonku sosai🥰🥰🌹🎉

Wannan last page din sadaukarwa ne gareku🥰🥰🥰🥰.

Free book 📚📚📚📚

꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁

&_______________________________________&

Last page

Page 3️⃣0️⃣

Gaba daya garin gombe da ketare ta amsa da wannan labaran kowa se tofa albarkacin bakinsa yakeyi wasu sun yarda wasu basu yarda ba. TikTok, YouTube, Facebook, Twitter, Instagram, Vidmate, duk wani kafafen sada zumunta ta amsa social media kowa se Allah wadai da halin azaad da fanan yakeyi ko ina kashiga labarin dazakaji yana tashi kenan.

Su abba suna gidansu fanan har karfe 2 na rana dukkansu abin duniya yadamesu har wata har rama sukayi har izuwa wannan lokacin fanan na kunshe adaki bakaramin tausayi tabasu ba ba ruwa ba abinci gaba daya tafita a hayyacinta tawani rame kamar wacce tayi jinyar wata daya fuskan nan yayi fayau kamar ba jini ajikinta tana zaune akan dadduma gashin nan buzu_buzu takafe waje daya da ido.

Yan uwan ummi a dubai sekira sukeyi suna kwantar musu da hankali haka masarautar gombe kakansu azaad yakira abba awaya yake tambayarsa ina azaad yace "yana gida sukuma suna gidansu yarinyar" kafin yakatse kiran.

Jingine yake ajikin makeken gadon dakinshi da alamun sallah ya idar yau yasamu yatashi daga baccin yabiya duka sallolin da akebinshi gaba daya yatashi daga azaad din dana sani yakoma wani daban duk wanda yakalli fuskarshi seya mugun razana da firgita dan yau ne ainihin true color dinshi yabayyana komawa yayi kamar boss, waya yadaga yasa akunne kafin yace " spider inason kafin nan da 1hr kasamonin wayanda sukayi wannan hotunan " yana gama magana kitt yakashe wayarsa mikewa yayi yabude wani locker dake dakin yafito da bindiga piston yasa abayan trouser dinshi fitowa yayi falon kasa fawwaz da areef se zeenat ne afalon suna zaune suna jimami sukaga fitowarshi ganinshi awannan suffar yasa babu wanda yayi kwakwaran motsi haryakai bakin kofar falo zefita wayarshi kirar iPhone 16 tafara ringing dakatawa yayi yaciro wayar yasa akunne spider ne yakirashi yaname sanar dashi ankama daya daga cikin mutanen dasuke dasa hannu, budan bakin Mr azaad yace" beat the hell out of him before na iso " kittt yakashe yafita securities dinsa ne dukansu sukazo suna gaidashi ko kallonsu beyiba faisal ne jiki na rawa yayi saurin karban car keys din awajan driver yabude mishi murfin motar shiga azaad yayi yazauna tada motar faisal yayi gudu_gudu baba me gadi yabude musu gate suka fita duk yan aikin gidan susan abinda yake faruwa bakaramin tausayin me gidan nasu sukeyiba domin su ko aina zasu iyabada shaida akan Mr azaad baze taba aikata haka ba.

Driving faisal yakeyi amma besan inazasuje ba gashi yana tsoron tambayar ogan nashi, ganin shuru baze kaisu ko inaba yasa murya nadan rawa yace " sir inazamuje" ciki_ciki azaad yace " my jungle" okay faisal yace dan yasan wajan nan ne azaad yakeda bosawan yaranshi sannan anan ne duk wanda yamishi laifi yakesa adauko shi yamishi mugun hukunci daga bisani yamikashi hannun yan sanda. dajine daya amsa sunanshi daji bazaka taba tunanin akwai bil adama aciki ba wani tankamemen gidane nahango daga nesa ga wasu Yan daba se buge buge sukeyi kamar wani abu suke hadawa ga wasu agefe se gasa rago sukeyi dukkansu duk wanda kika kalla kinsan ainihin cikekken dan dabane agun kirar jikinsu ma kadai zebaka labari , tunkafin motar takaraso sukayi cincirindo suna jira isowar boss dinsu motar na tsayawa wani daga cikinsu yabude mishi kofa wani yazo da lema yana rike mishi dashi dan kar rana yatabashi wani ne yazo kamar wani basamude yazo yatsaya agaban azaad kansa akasa yace " boss can I help you with the shirt" gyada mishi kai yayi nan take yasa hannu yaballe mishi botiran riganshi yakoma gefe yatsaya cire rigan azaad yayi gaba daya nan take wannan kirar nasa yabayyana ga tattoo dake jikinshi tafiya yakeyi cike da izza yashiga ciki, sekwasan gaisuwa sukeyi wani bangare yanufa daga nesa babu abinda nakeji daya wuce ihu da kururuwa shiga wajan yayi wani matashine wanda akalla zekai shekara 27 zaune akan kujeran karfe anmishi daurin goro sunmishi mugun duka jikinshi se fitar da jini yakeyi ihu yakeyi kamar wanda ake zarewa rai juyawa azaad yayi yakalli spider nan take yakawo mishi kujera asetin matashin zama azaad yayi yasa hannu yadago fuskanshi agalabaice yake kallonshi dakyar ya iya furta "dan Allah ranka yadade kamin rai kayi hakuri" wani miskilin murmushi azaad yayi kafin yace" waya saka wannan aikin" shuru yayi bece komai ba alamar baze fada ba , dungule hannun azaad yayi nan take jijiyoyin hannunsa suka fito yakai mishi naushi afuska seda hakwaranshi guda shida suka zube hanci da baki suka fashe se jini suke zubarwa juyawa yayi ga spider yace " ban wuka" dasauri spider yaciro wuka a kugunshi yabashi yana karba beyi wata_ wata ba ya caka mishi acinya razanenne ihu yasa seda gidan ya amsa,daga wukan yayi zesake caka masa yayi saurin fadin" kamin rai wayyo zan fada ! Zan fada maka wayanda suka sani " shafa kanshi azaad yayi yace " good boy maza fada inajinka" yana hakin wahala yace " Alh Ibrahim tijjani ne yasani ! Nafada maka dan Allah kabarni intafi " tunda ya ambaci sunan alh Ibrahim tijjani azaad yaketa girgiza kai dan yasan babu wanda zasu mishi haka sesu amma yafison ya tabbatar tukun nan, lallai alh Ibrahim yatabo ruwan dafa kansa amma yanzu yasan kafin gaskiya tafito seyadau lokaci yana cikin wannan tunanin wayarshi tayi ringing dubawa yayi yaga abba ne ke kiransa kamar baze daga ba can kuma yadaga yasa akunne yace " hello" ajiyar zuciya abba yayi jin yadawo normal dan dama faisal ne yace mishi yafarka, cikeda bada umarni abba yace mishi " duk abinda kakeyi kabari kazo gidansu fatima" tofa tunani yafarayi wacece kuma fatima kamar baze tambayi abba ba can Kuma murya ashake kamar wanda akawa dole yace " wacece kuma fatima" rike baki abba yayi kamar wanda yake gabanshi daga karshe yanisa yace " to nurse dinka yanzu base anjuma ba kazo gidansu" seyanzu yatuna da ita tare aka musu qazafi tausayinta yaji ganin ita macece sun bata mata suna gwarashi namijine amma itafa sun cuci rayuwarta tabbas bazetaba barinsu susha iska medadi ba sesunyi danasani aikata hakan mikewa yayi su spider suka bishi abaya.
Chapter 28 · 0% Book details