← Book details Nida Patient Dina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 31

Sashe 2

Nida Patient Dina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe 7:00am ta tashi daga bacci brush tayi tayi wanka sanan tafito ta saka dogon hijab har kasa tafito taje dakin baba ta gaisheshi daga nan tayi wajan mama suka gaisa tambayar mama tayi Meye zaayi na karyawa , mama tace kiyi Dan wake da tea kawai amsawa tayi to tamike , kitchen tawuce tahada kayan wanke wanke tafito dasu kafin Takoma tana kokarin hada kayan karyawa. Wanke wanke takeyi cikin kwanciyar hankali hartagama taje tajera komai yanda yadace a kitchen sannan tayi shara da mopping komai da komai daga nan Takoma kitchen tacigaba da hada kayan karyawa. Bayan takammala ta juye tea a flask takai falo da food flask ta ajiye direct dakin mama taje tasameta tasanar da ita tagama murmushi mama tayi tace allah yamiki albarka ta amsa da Ameen bari inje inyi wanka to kawai mama tace mata.

Komawa daki tayi tacire hijab din wanka zata sakeyi sbd ta gaji tahada zufa, bayan 10mints tafito sanye da towel ajikinta Bude wardrobe tayi tafito da uniform nata da handbag da takalminta a tsanake take shiryawa gyara gashinta tayi tahadeshi waje daya tayi donot dashi. Uniform tasa ajikinta wayanda suka kasance white 🤍color tadaura dankwali Amma seda sajen gaban kanta yafito powder Tashafa sannan tasa kwalli a idonta tasa libs stick adan karamin bakinta yayi kamar tasa janbaki.tubarkallah Masha bakaramin kyau tayi ba agogo tadaura a hannunta tasa after dress Baki asaman uniform din hijab dinta Wanda bewuce cikiba tasa feshe jikinta tayi da perfume sannan tadau handbag 👜 dinta tafito falo tasamu harsun kammala breakfast, mama ce tasamata kayan karyawanta zama tayi tayi Bismillah taci badayawaba ta ce mama zantafi allah yabada saa mama tamata sannan tace kije babanku na daki wucewa tayi dakin baba tayi sallama yabata umarnin shigowa mamana harkin shirya eh baba nagama dauko Dari 500 yayi yabata sannan yamata adduah allah yabata saa Ameen babana sena dawo tamishi sallama tafito kenan taci karo da ya Usman yafito da machine dinsa,ya usman ina kwana lfy Lau kintashi lfy ta amsa lfy Lau alhmdllh zokihau in ajiyeki tace to hawa tayi suna tafiya suna hira har suka Isa bakin asibitin SPECIALIST ajiyeta yayi yajuya duba time a wayanta tayi taga 9:30 tafiya takeyi harta karasa addimission ward tana shiga tahango Amira nasawa wata patient drip karasawa tayi gaisawa tayi da Yan wajan cikin sakin fuska da murmushi dauke afuskanta tamusu ya jiki amsawa sukayi dasauki nurse. Karasawa tayi wajan patient's dinta Dake kwance gaisawa sukayi kafin tace mata yajikin naki fatan dasauki washe Baki tayi tace ahh dasauki sosai murmushi kawai FANAN tayi magungunanta taduba taga duk tashasu akan lokaci, nayaune kawai batasha ba dogo Kai FANAN tayi tace kin ci abinci ne amsa mata matar tayi da ah ah banciba Ina mijinki bedawo ba tukun mamakine Yakama fanan tashiga tunanin wannan wani irin mijine matarsa nagadon asibiti bata da lfy sannan ace tunjiya haryanzu bedawo ba balle yasan halin da take ciki allah yakyauta. Kallon matar tayi taga jikinta tayi sanyi cikin tausayawa tace ya sunanki ahankali tafurta sunana balki, murmushi tayi tace anty balki karki damu mijinki yakusa isowa.yanzu Meye yake miki ciwo ah ah nurse yanzu kam jiki alhamdulillah sedan ciwon Kai da rashin karfin jiki ne kawai okay to Allah yakara sauki suna cikin haka mijinta ya karaso wajan Yana wani bata rai yagaida FANAN amsawa tayi tana kallon iKon Allah,cikin Shan kamshi yace ma balki ya jikin tace dasauki daga nan bekara cewa komai ba,FANAN ta lura kamar akwai Dan matsala kallonshi tayi tace inba damuwa inasan magana dakai okay badamuwa fitowa Bakin ward din sukayi . Cike da girmamawa da natsuwa tafara mishi mgn bawan allah ya nunanka sunana Abdul yabata amsa, murmushi tayi cikin tsigan zolaya tace kaikuma malam Abdul haka akeyi , katafi karba masoyiyar taka ita kadai bakowa nata balle naka Yan uwan bataci abinci ba gashi nazo zan bata magani ba abinci Anya ba kishiya kakeson mata ba kuwa takarasa tana Dan dariya shikuwa Abdul wata irin kunya ce takamashi Jin abinda nurse tafada mishi seyaji gaba Daya bekyautaba shuru yayi yarasa bakin magana itakuwa FANAN ganin tayi nasarane jikinshi yayi sanyi tacigaba da mgn malam Abdul kaga bata da lfy kadaure kadinga kula da ita koba komai itadin amanace awajanka aurenta kayi domin kunason juna sannan tace allah yabaku zaman lfy takarasa maganarta tana kallon idonshi, cikin sanyin jiki yace Ameen Ameen nurse nagode sosai da sosai murmushi tayi tawuce ciki tabarshi agun shikuwa daga nan abinci yaje yasiyowa matarshi yakawo mata taci dakanshi yabata maganinta se kallonshi takeyi tana Kara godewa allah dayakawo wannan sauyin dakuma nurse fanan Dan tasan harda taimakonta.

Duk nurses din wajan sunata kula da patient dinsu wani babban mutum ne yashigo wajan yanda ake ta gaisheshi ze tabbatar maka da shine in charge na asibitin. Hango Amira yayi yakirata ta karaso bayan sungaisa ya tmby ta Ina fanan ko yauma batazo ba ah ah tazo bari inkirata Yana tsaye agun Amira suka jero tare da FANAN Yana ganinta yawashe Baki Yana kare mata kallo kamar wani maye ciki ciki FANAN tace mishi Ina kwana amsawa yayi yata washe baki kamar gonar auduga, tafiya yafarayi yajuyo yacewa FANAN kibiyoni office Dina. Tsaki FANAN taja saboda yanzu inda Wanda tatsana bewuce in charge nasu ba sbd yanda yasata agaba da maganar banza. FANAN kije kiji Meye damuwarshi Kuma yau hmmm kawai fanan tace tawuce office nashi.......

To zamuji yanda FANAN zata kare itada in charge nasu

Please kudingayin comment 😍😍😍🙏

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

🧑‍⚕️🧑‍⚕️NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story written by ( MRS 🌹 ISHAM 🌹)
Da sunan allah me rahama mejinkai 🙏 Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy Ameen 🙏🌹

Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci 🥰🥰🥰

____________________________________________

Page 4️⃣

Cikin bata fuska ta Murda handle din office din tashigo da sallama abakinta,atsaye tasameshi Yana faman jiranta cikin daddadar muryanta tace doctor gani wani irin malalacin murmushi yayi sannan yafara kare mata kallo daga sama harkasa idonshi kurr akan kirjinta yakafesu da ido lura da hakan datayine rai abaci tace zan iya tfy, karasowa yayi kusa da ita Yana kokarin rungumeta taja baya,ya rungumi iska , uhmm haba mekyau bekamata kinamin haka ba bakisan irin yanda nake mugun shaawarki da kaunarki ba burina kullum nakasance kusa Dake dazaki bani dama dakinga irin gata da kulawan dazanbaki sekinfi ko wace ya mace karasa maganar yayi Yana kashe mata ido Daya cikin salo irin na cikkakun Yan bariki, wani irin takaicine da bakin ciki Yakama fanan jitake tamkar tashaqeshi kozata huta, tsaki taja tare da wurga mishi mugun harara kafin tafara fadin.. kaikam wlh bakaji dadin rayuwa ba nasan idan baka da yar data kaini kakai ka haifeni Amma katsaya kana fadamin maganganun banza to bari kaji infada maka in sha Allah, allah bazetaba baka saa akaina ba. Kuma inawa kowace yarinyar fatan allah yakiyayesu daga sharrinka na neman aikata zina dasu allah yafika , bakaken magana take gaya mishi Amma shi wani irin Kara burgesa takeyi se kallon Dan karamin bakinta yakeyi kamar yaje yayi kissing nata juyawa tayi tafita a office tana Dana sanin fara aiki anan. Shikuwa gogan naku Yana tsaye Ayanda ta tafi tabarshi wani irin wutan shaawarta ne yake Kara wuruwa mishi afili yafara magana Yana fadin FANAN in sha Allah sena aureki domin in kawar da abinda nakeji akanki idankuma kinki kota halin Yaya sena sami abinda nakeso.

Fitowa tayi tana tunani kala kala aranta nayanda yanzu manyan mutane suka zubar da girmansu kowa yazama Dan Iska azuciyarta tace to Allah yashiga tsakanin nagari da mugu nikuma dake bayanta na amsa da ameen 😜. Komawa tayi ward din sukaci gaba da aikinsu lura da mood dinta da Amira tayine tace mata bestie na meyafaru ne naganki wani iri ajiyar zuciya tayi tafara bawa Amira lbrn yanda sukayi da doctor Ib girgiza Kai kawai Amira tayi tace wannan mutumin baze taba canjawa ba allah yakyauta suka amsa da Ameen.

6:00pm Dede suka fito tare suna rike da hannun juna har suka tsallaka titi suka tare adedeta sahu amira ce takemishi kwatancen anguwar tasu me napep Dubai quarters zaka ajiyemu shiga sukayi suna yar hira harsuka iso suka sallameshi sallama sukayi kowa hanyan gida tanufa. Cike da gajiya FANAN tayi sallama dagudu auta tazo tana mata oyoyo, oyoyo autar mama anty sannu da dawowa yauwa auta Ina mama tana falo ok kawai tace tawuce falon anan tasamu mama tagaisheta amsawa tayi zama FANAN tayi akan cusion tana cewa wlh mama yau nagaji sosai murmushi mama tayi tace to sakaliya bakin dawo ba Zaki fara narkemin kamar wata man gyada 🤣🤣 dariya FANAN tayi tace Kai mama komai mutum yayi sekin sace mishi gwuiwa dariya suka sa tare tom sannu sekije kiyi wanka kizo kici abinci tom mama dakinta tawuce, samun guri tayi tazauna abakin gado ahankali tafara cire Dan kwalin kanta Sannan tasa hannu ta warware gashinta yasauko yarufe mata fuska zib din riganta taja kasa tacire rigan kallon kanta tatsaya takeyi a mirror 🪞 kome ta nuna naga tasaki wannan murmushin nata mekara mata kyau karasa cire kayan jikinta tayi tashiga toilet ta watsa ruwa tafito zafi takeji ko Mai bata tsayawa shafawa ba Bude wardrobe tayi tazaro wata dogon riga mara nauyi ja me Igiya tasa tadauki hula Baki tasa tafito abinci tasamu afalo tasan mama ce ta ajiye mata zama tayi tafaracin abincin seda taji takoshi tukun Tasha ruwa takwashi kwanukan takai kitchen anan tasamu mama na girki taimaka mata tayi har suka gama suka Kai komai falo.

Bayan sallah mangrib baba da ya Usman suka dawo abinci sukaci suna hira cikin nishadi kafin sukayi sallama FANAN Takoma dakinta kwanciya tayi kafin tajawo wayarta WhatsApp tashiga tafara Bude sakon ni wata group tagani ansata mesuna manyan yara tsaki tayi sbd ta tsani irin wayan nan group din left tayi ta ajiye wayar Dan yau agajiye take adduah bacci tayi ta kwanta.
Chapter 2 · 0% Book details