← Book details Nida Patient Dina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 31

Sashe 22

Nida Patient Dina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abangaren gidan su fanan kuwa yanzu shirye_shiryen saukan fanan akeyi haka gidansu amira ma Dan makaranta daya sukayi DHARUL_HUDA. Dukansu suna zaune afalo harsu baba yau basu fita kasuwa ba saboda shirye_shiryen saukan gobe dazaayi, fanan nazaune itada suhaima atsakiyar falon hannunta dauke da jotter da pen tana rubuta list din mutanen dazasuzo tana sanye da wando falazo black me manyan fulawi fari tanason falazo sosai dan tafi sakewa acikinshi, se farar riga kanta da hula ita kuma suhaima list din abubuwan da ake bukata take rubutawa, Dago Kai fanan tayi tace "mama nagama rubutawa bansan ko akwai wayanda suka rage ba " suhaima ce tace " kin saka gidansu ummi a list kuwa " " ah ah bansa ba basuma san zanyi saukan ba shisa bansa ba" cewar fanan dake kokarin rubuta sunan nasu a jotter ta, mama ce tace " aikuwa de yakamata asa inyaso tunda basu saniba anjuma al ameen seya kaiku gidan kubasu kati " to shikenan, mikawa ya usman list suhaima tayi dan tagama rubutawa karba yayi yana dubawa can kuma yace " iyakacin abinda ake bukata kenan !? Naga kamar list din yayi guntu" Yana magana yana kallon list din Jin abinda yafada ne yasa mama tace " inga ni" tashi yayi yaje yabata yadawo yazauna , duddubawa takeyi pen tadauko ta kara rubuta abubuwan dabata gani aciki ba bayan tagamane tamikawa baba yakarba yace" shikenan ko " eh sukace, mikewa baba yayi yadauki car key dinshi yace " Usman tashi ka tada mashin dinka ka kaini indauko motar muje kasuwa kaikuma Al ameen seku shirya kuje ka kaisu " dukansu Mikewa sukayi mazan su ya al ameen sukayi waje sukabi baba , ya usman yatada mashin baba yahau suka fita daukan motar saboda gidan baze dau motar biyu ba shisa baba yake baro nashi a inda ake gadin motoci yacewa ya al ameen yadinga packing din nashin kawai, fitowa fanan sukayi harda auta itama zatabisu dogon hijab duka sukasa , suka sameshi a motar shiga sukayi yatada motar suka kama hanyar gidansu azaad, fanan kwatance tadinga yimishi harsuka iso fitowa baba me gadi yayi ganin bakuwar mota yasa yazo dubawa dan leko kai fanan tayi tagaisheshi washe fuska yayi ganin itace yakoma yawangale musu gate shiga cikin gidan yayi , bayan yayi packing suka fito, hango zeenat da fawwaz fanan tayi alamun fita zasuyi karasowa wajan su sukayi mikawa ya al ameen hannu fawwaz yayi sukayi musabaha idon fawwaz ne yasauka acikin na suhaima dake gaisheshi murmushi yayi ya amsa kafin ya amsa na fanan cike da farin ciki ganin fanan zeenat tace" Allah kawata gaskiya nayi missing dinki naso zuwa sekuma Abba suka dawo jiya yanzu kuma ya fawwaz ne zekaini shopping segaku nan tom muje ciki " dariya suhaima tayi tace " ummm nadauka nikadai akecewa inada surutu yau naga wanda tafini " dariya zeenat tayi cikin yauki tace " yanzu dan Allah ni inada surutu yar shuru_shuru dani" fanan de shuru tamusu dan wayan nan biyun intace zata biye musu suta hiran basu taba gajiya ba , kallon suhaima da auta tayi taga suna kama da fanan nan tagane yan uwanta ne riko hannun auta tayi tace " zo muyi gaba fine girl tunda antynki taki kulani yau " wucewa sukayi ya fawwaz sukabi bayansu afalon kasa suka samu duk yan gidan harda su abba banda azaad dake can yana kwance shigowa sukayi da sallama abakinsu bismillah fawwaz yamusu basu zauna ba se suka tsunguna har kasa suna gaishe da Abba kafin suka gaida ummi da anty Amina bin mazan falon ya al ameen yayi yana basu hannu suka gaisa cikin mutuntawa kafin yazauna, ummi ce takalli fanan " su fanan tunda patient dinki yasamu lafiya aka guje mu ko !?" Cikin jin kunya ta sunkuyar dakai sannan tace " ah ah ummi bahaka bane shirye_shiryen sauka nane yasha min kai shisa kuka jini shuru " Abba tunda fanan tafara magana yake kallonta Jin yanda take magana cikin nutsuwa seta burgeshi sosai cikin barkwanci yace" ah ah umminsu kice wannan itace nurse din tamu kenan !" dariya suka danyi kafin ya cigaba " yaushene saukan naku ?" Cikin nutsuwa da kunya fanan tace " gobe ne yanzuma kati muka kawo muku " gyada kai abba yayi yace " Masha Allah awata makaranta ne!? Cikin zakin murya da yarinta auta tace" sunan makarantan Dharul_huda gobe da karfe 9 na safe zaafara atashi karfe 3 in akayi nasu anty semuma inmun je ajiya 6 muma zaayi namu yanzu ina aji uku ne" tagumi fanan da suhaima sukayi suna ganin iKon Allah yanda auta ke zaro zance sekace an tambayeta batasan mutane ba tazo tana musu surutu kamar wata parrot, ya al ameen de rike baki yayi , bakaramin dariya auta tabasu ba cikin dariya ummi tace" fanan kanwarki ce ko naga kuna kama sosai " karaff auta zatayi magana fanan tadaka mata harara aikuwa ba shiri tayi shuru harda sa hannu abakinta,nanma dariya suka karasawa dan sunga hararan da fanan tamata bakaramin nishadi auta tabasu ba mikewa fanan tayi tamikawa Abba katin karba yayi Yana karantawa kafin yace " fateema amma ya akayi makarantanku se yanzu takeyin nata saukan bayan yanzu wata biyu kenan da haddace Al qur'ani!?" " Eh Abba dama haka tsarin islamiyarmu take inmuka gama aji shida semunje hutu mundawo zaayi saukan " jinjina kai Abba yayi cikin gamsuwa da bayananta, ummi tace " in sha Allah zaki ganmu" mikewa zeenat tayi tace " kuzo muje daki " dukansu mikewa sukayi sukabi bayanta Abba ne yace " ohhh to zaku gudu dakin zeee kenan to ke zomuyi hira ko " yafada yana nuna auta da hannu zuwa tayi tazauna akusa dashi ya tambayeta sunanta aikuwa nantake tafara zuba zance se dariya sukeyi dan sun lura auta ita kanta comedy ce girgiza kai fanan tayi Jin yanda auta tacigaba da zuba kamar ba dazun ta hanata ba aranta tana cewa Allah yashiryeki auta, fitowa azaad yayi yawucesu afalon yatafi garden dan yaseer yafada mai yana wajan, mikewa Abba yayi yacema auta " karki je ko Ina kijirani anan indawo yanzu nan " gyada kai tayi shikuma yawuce yabi bayan azaad dan akwai abinda yakeson su tattauna harya kusa shiga garden din yaji kamar ana binshi abaya juyawa yayi yaga Abba ne tsayawa yayi abba yakaraso suka shiga garden din tare gaida Abba yaseer yayi Yana mishi ya hanya suka zauna akan kujerun wajan . hira suke tasha adakin zeenat tana basu labarin time din datayi graduate nata se kallon photos sukeyi awayarta can zeenat tace "kutashi muje garden muyi pics " " nide sekun dawo ba inda zani " fanan tayi maganar tana kokarin kwanciya, riko hannunta zeenat tayi tace " wlh Baki isaba sekinzo munje munyi pics din nan " mikewa tayi tace " nide bazaku taba barina inhuta ba koh semuje ai " tagama magana tana hararansu da dara_daran idanunta, ta corridor suka bi yakaisu bangaren azaad daga nan suka gangaro kasa sukabi ta kitchen suka shiga garden din basuma lura da su azaad ba da Abba se yaseer dasuke zaune suna magana ba, suhaima da zeenat suna gaba seda suka shiga tukun suka lura dasu Abba dake zaune zeenat ce tace " laaaaah Abba ashe kuna nan Kuma " juyowa sukayi suna kallonsu " eh gamu nan munadan magana ne " cewar abba, murmushi yaseer yayi yace " ku karaso mana kuka tsaya agun" shide azaad ko tanka musu beyi ba suka karaso wajan, shigowa garden din fanan tayi cikin tafiyanta me kama dana mahauniya tana kallon flowers 🌺 din bakaramin burgeta sukayi ba hartazo zata wuce taga wani kyakyawan bunch of flowers din masu kaloli daban daban tafiya sukayi da hankalinta tanufi wajansu duk abinda takeyi batasan su Abba na garden din ba suna hiransu suna kallonta, gaban flowers din taje ta tsaya can Kuma tasa hannunta tafara shafa su cikin nishadi tafi 5mint agun kafin ta juya zata tafi,cikin rada taji ance " muna godiya sosai agareki da kika tabamu da hannunki me cike da karfin ikon jaaazana " asukwane tajuyo Dan taga wayeke magana gani tayi bakowa awajan dan duk tunaninta bekawo mata akan maganar daga gun flowers din bane ganin bakowa ne yasa aranta tace" kila kawai gizo ne kunne na kemin" tafiya taci gaba dayi abunta sannu ahankali flowers din data taba suka fara girma sunayin tsayi harsuka fi tsayinta duk batasaniba tafiyanta kawai takeyi amatukar razane su Abba suka mike dan duk wani motsinta suna lura dashi ganin flowers din sunzo dabb da itane kamar zasu tabata suhaima tafasa ihu tana fadin " wayyo fanan bayanki" jin ihun da suhaima tayine yasa azaad dagowa yana kallonsu ganin sun kafe waje daya da ido ne yasa yakai idonsa direction din dasuke kallo " ohhh shit " yafurta lokacin da yake kokarin tashi itakuwa fanan jin abinda suhaima tafada ne yasata zurawa aguje dan tamaki juyawa taga meye abayan nata, taku hudu zuwa biyar azaad yayi yakaishi inda take yarikota, rungumeshi tayi kam_kam kamar wacce zata koma jikinshi karasowa su yaseer sukayi inda suke suna ganin iKon Allah, azaad kallonshi yamayar kan flowers din dasuka girma suka zama kamar wasu bishiyoyi yayi ganin har time din basu koma ba suna tsaye kiqam yatsaya yayi wani tunani bakinshi yakawo dede kunnenta yace mata" kibude idonki sannan kijuya kikalli abinda ke gabanki " lokaci daya taji duk wani tsoron datakeji ya yaye ahankali tabude manyan idanunta tadaurashi akan cute face nashi dashima kallontan yake runtse idonta tayi dan bazata iya kallon cikin idonshi ba danji take kamar lantarki najanta, su Abba de suna ta kallonsu ,juyawa tayi kafin tadanyi step kadan tanufi flowers din tafuskance su, nan take yayi wani irin girgiza kamar ze fado kasa furanni ne suka fara zubowa akanta suna zubewe akasa ga dadin kamshi seda suka zubo duka flowers din gaba daya seda suka kare ajikinta yanda suke zuban abun burgewa kamar a India ,seda yazamana wajan bakomai kasa kuwa kamar anyi ruwan fure tsaban yanda suka zuba, wani irin juyowa tayi kamar wata robot seda sukadan ja baya da irin juyin datayin kamar ba lafiya ba banda azaad dako motsawa beyiba, kanta akasa kafin slowly tadago fuskanta idonta arufe eyelashes dinta yayi zara_zara kamar wanda ruwa yataba shi , Abba
Chapter 22 · 0% Book details