← Book details Nida Patient Dina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 31

Sashe 23

Nida Patient Dina Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

de tunda yake arayuwarshi betaba ganin irin wannan Al amarin ba se a film yau gashi yafaru agidanshi mamaki kamar yakasheshi, haka suhaima da yaseer suma mamakin sukeyi banda zeenat da azaad dansu abinda suka gani ranan ma yarufe komai tunda TV yatarwatse wannan ai kadan ne, ganin dasukayi komatsawa batayi ne yasa Abba yace " azaad jeka daukota " zuwa yayi yakai hannunshi kan kafadarta yadan tabata , slowly tafado jikinshi ganin tasake nauyintane yagane ta suma cakk yadagata kamar yar baby yayi falo da ita su abba sukabi bayanshi, ganin azaad yashigo da fanan ahannu ne yasa duk suka mike kwantar da ita yayi akan kujera yadauko bottle water yabude goran yashafa mata afuska , da mamaki ummi take tambayar abba meya sameta bece mata bakomai ba yadauko wani zancen Yana cewa zeenat tamiko mishi agogonshi ,sauke ajiyar zuciya tayi kafin taware idonta ganin mutane atsaye akantane yasa tamike tanabin falon da kallo tunawa tayi da abinda yafaru a garden kokarin tashi takeyi anty Amina ta taimaka mata tazauna ya al ameen ne yakaraso kusa da ita yarike hannunta yace" yar kanwa dama bakida lafiyane!?" Yagama maganar yana jiran amsarta girgiza mishi kai tayi alamar ah ah " to mutafi gida kinji " nanma still gyada mishi kai tayi, azaad nazaune yana binsu da kallo musamman fanan din Aransa yake magana "tabbas wannan yarinyar akwai wani boyeyyen al amari atare da ita wanda iyayenta sunsan da haka suke boyewa , wani zuciyar tace kila ba mutum bace ita din kila aljanace amma ita bata saniba Kara kallonta yayi dakyau yaga de babu wani alaman daze nuna aljan ce, can wata zuciyar tacemai ko kuma rabinta mutum rabinta aljana ce, can kuma yayi tsaki jin shirmen da zuciyarsa kefada " jin tsakin dayayi ne yasa suka juya Suna kallonshi ganin sunzuba mishi idone yasa yadaure fuska , gyaran murya Abba yayi yace " al ameen zaku tafi amma sedan anjuma kaji" shikenan to Abba cewar ya al ameen. Hira suka zauna sunayi babu wanda yadauko maganar abinda yafaru balle fanan taji, kallon time abba yayi yace kuntashi mutafi masallaci duka mazan mikewa sukayi suka tafi masallaci, sukuma suka haura sama danyin sallah bayan sun idarne suka fara shirin tafiya gida, saukowa sukayi sukaga kowa na falon harsun dawo mikewa ya al ameen yayi yace to mutafi ko sallama suka musu Abba yace " auta yanzu tafiya zakiyi baraki tsaya kimana hira ba haba auta " cikin dariyarta tarufe fuska tace " to ai abba zanzo kawo muku katin saukana nima " dariya akayi jinwai zata kawo musu katin saukanta saukan daba nan kusa ba , fanan de girgiza kai kawai tayi manyancen auta har tsoro yake bata kamar wata babbar mace, shikanshi azaad seda yaji yarinyar ta burgeshi dukda bayason yawan surutu, fitowa ummi tayi Abu me aiki nabiye da ita rike da ledoji niki_niki tace " yauwa autana ga chocolate " zaro ido tayi takalli fuskar fanan taga ya reaction dinta yake karta kabar tayi laifi ganin murmushi akan fuskantar ne yasa ta kalli ummi tace" angode sosai ummi Allah yasaka miki da alkhari yakara budi " amsawa sukayi dukansu da Ameen Ameen suna jinjina irin tarbiyan da yaran suka samu dan kallon azaad tayi dukda dazun bata ganshi ba dasukazo, kamar zata tafi kuma setace "bye_bye Yaya balarabe" kallonta yayi kafin cikin daddadar muryanshi yace " bye bye " bakaramin mamaki sukasha ba dan dukansu basuyi tunanin zebata amsa ba, seda tabi kowa na falon tana musu bye_bye , seda sukaji kamar karsu tafi dan dukkansu sunada saurin sabo barinma auta data dinga basu comedy yau, fawwaz da areef se zeenat da yaran anty amina ne suka fito rakasu suka shiga motar suna musu bye_bye fawwaz se satan kallon suhaima yakeyi (in yeeeh su fawwaz kenan love at first sight) seda suka tafi tukun suka koma cikin gida duk suna shiga falon suka tadda abba na waya da wani abokinshi bayan yagama ne yacewa ummi" Amma wannan yarinyar aina kuka samota" bashi labarin yanda takula da azaad dakuma abubuwan dasuka faru na tv dakaita gidansu dasukayi ummi tayi , jinjina kai Abba yayi sannan yaci gaba " wannan yarinyar akwai wani abu atare da ita tabbas amma koma menene Allah yakawo musu shi dasauki dan yarinyar takwanta min arai yanayin nutsuwarta dakuma irin tarbiyan dasuka samu agidansu abune na ayabawa iyayensu" anty Amina ce takarbi dacewa " abbana nifa anawa ganin yarinyar nan akwai wani abu ajikinta ne" azaad dayamike zewuce part dinshi kamar Wanda akawa dole seyayi magana yace " babu abinda yake jikinta itadince dakanta " ya haura stairs abunshi , cike da Al ajabi sukebin bayanshi da kallo dan yasasu aduhu meyake nufi da itadince dakanta.
Chapter 23 · 0% Book details