← Book details    Hibbatullah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 23

Sashe 8

   Hibbatullah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace"Maymunerh yanzu na gama yiwa danki fadar wannan furucin da kikayi,sai gashi kema kin maimaitashi,maymunerh yau meya shiga cikin kwakwalarki ne da har ya sanya kikayi irin wannan furucin?Ayau Najmiy ce ta zamo mara asali?azatona kin dauketa ne tamkar 'yar data fito daga cikin cikinki,ashe tunanina akan hakan ba gaskiya bane,tunda gashi ayau kin fito kin nuna min cewar baki haifi Najmiy ba,baki dauketa kamar yadda kika dauki Hayatu ba,Najmiyya bata da gata,haka kuma bata da cikakkiyar usulin da har zaki iya bari danki ya hada jini da ita,toh ina son kisha kuruminki,ni Muhammadu bazan ma taba baiwa Hayatu auren Najmiyya ba sabida ko kadan bai cancanci abashi ita ba,don haka ki rubuta ki ajje cewa nina fadi hakan,maza kowa ya tashi ya bani wuri.... "

   Haka kowa ya tashi ya fice jiki ah sabule,bayan sun fita kuwa haj.babba ta hau yi mata fada akan meyasa zatayi irin wannan furucin?meya shiga cikin kwakwalwarta ne?

Ko kala bata ce mata ba tayi b'angarenta.shi kuwa Faruq so yake ya baiwa Hayat haquri amma ko kadan bai samu damar hakan ba.

     ***
  *°•Ah gurguje pls•°*

    Mai martaba M.k bahago ya saka su dogarawa sanya ido sosai akan Hayat da Najmiy,har umarni ya bada akan cewa muddin aka ga sun keb'e toh ahukunta masa Hayat,don ya riga ya gargad'eshi akan kada ya kuskura ya sake keb'ancewa da ita,karatu ma yanzu idan har zasuyi tofa sanya dogarawa ake atsakaninsu,kwata-kwata babu maganar da take shiga tsakaninsu bayan na karatu.Hayat duk yabi ya rame ya kuma lalace,sam bashi da wani sukuni da walwala,kullum cikin kuka yake,gashi mahaifiyarsa ta juya masa baya don kawai yace yana son mara asali,Faruq ma tuni ya koma makaranta,haj.babba ce kawai take dan jansa ajiki sai kuma kannensa,itama tayi tayi da mai martaba akan ya gaya mata dalilinsa daya sanya yace bazai baiwa Hayat auran Najmiy ba amma fir! yaki don yasan zasuce ba wani dalili mai karfi bane,amma shi kadai yasan abinda yake hangowa nan gaba.itama Najmiy zuwa yanzu ta soma tausayin Hayat,gashi babu damar keb'ancewa dashi,kuma ita bata masan wainar da ake tauyawa ba acikin gidan,ko kadan bata san cewa mai martaba yace bazai taba baiwa Hayatun auranta bane,itafa duk wannan mutanen da aka sanya su dunga tsaronsu ita azatonta kawai bai dace suyi soyayya bane ashekarunsu,shiyasa aka sanya masu gadin da zasu dunga lura dasu aduk sanda suka k'ebance don karatu ko wani abin can daban.

   _*jan нanĸalι na ғarĸo agareĸυ ιyayen yanzυ da ĸυмa ιyayen goвe,ĸυ daιna ѕanya dogon вυrι aranĸυ don вaĸυ ѕan мaι goвe zaтa нaιғar вa,gaѕнι yanzυ мaι мarтaвa мĸ yana neмar тaғĸa вaввan ĸυѕĸυre,da'ace yaвι ѕon zυcιyar danѕa ne da ĸυwa ĸoмaι dazaι ғarυ вaι ғarυ вa,waтaĸιla мa вayan aυre yana ιya canzawa тυnda нar yana ѕon najмιy dιn da gaѕĸe,aммa dogon вυrιn da yaĸe daѕнι aĸan ғaranтawa najмιy ѕнι ya нaιғar da ĸoмaι*_  мυje zυwa🏃

   _*idan har na gamsu da comments toh kuwa kuna iya ganin update anjima kadan*_

      *TAKU*

    *ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕*
           ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
              *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
               ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️

          *°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*

*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*

     *MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*

         *WATTPAD:HAFNANCY*

*°ѕα∂αυкαяωα gα Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα°*

  _*°•wannan page dιn naĸι ne ĸe daya мy najaтee мarυвυcιyar 'yarιмa ѕυнaιl',нaqιqa lιттaғιn na nιѕнadanтar daмυ,υвangιjι Allaн ya ĸara вaѕιra da kuma zaĸιn нand,ιna ѕo ĸι ѕanι cewar нaғnan dιnĸι тana мιĸι ѕan ѕo💕💕💕•°*_

       *°•Intelligent writers Asso🖊•°*
__________________________________

                        💥

     *Թɑցҽ 1⃣0⃣*

    _*вayan waтannι υĸυ*_

      Zuwa yanzu Hayat ya soma fusata da gadin da ake musu,ba dama su zauna waje daya da Najmiy,sai gaka dogarawa nayiwa junansu signal alamun maza su matso kusa dasu,zancen soyayyar nan ne dai ba'a son suyita,shi yama fita harkan mahaifin nasa tunda harwa yau yaki sauraron maqigarsa(Mai martaba m.k Bahago wani irin mutum ne mai tsassauran ra'ayi,idan har yace haka yakeson abu,tofa babu wanda ya isa ya canza masa wannan tsarin,yana da kafiya akan abu sosai,Allah sarki duk fa akan baiwar Allah Najmiy yake kuntatawa dan cikinsa,don kawai ita ya faranta mata,ta samu tayi rayuwar farin ciki da kuma jindadi,(irinku sunyi karanci mai martaba m.k,Allah yaja da ran mutumin talakawa,amma ranka shi dade daka jaraba Hayat kila ya sauya halin saurin fushinsa dinnan da sauransu dai,dama ance sai kaga ta sanadin wani mutum ke canzawa daga wani halin da aka sanshi dashi.)

   Haka ma mahaifiyarsa Haj.karama tace babu ruwanta dashi muddin bai fita ahanyar Najmiy ba.kannensa Abida da kuma Hidaya suma sun dan ja baya da Najmiy don aganinsu itace ke nemar tarwatsa family dinsu.zuwa yanzu Najmiy tasan wainar da ake toyawa wanda ko kadan bata ji dadin hakan ba,tausayin Hayat da take ji ya sanya har ta soma developing sonsa acikin xuciyarta,amma babu damar gaya masa,kuma ko ta gaya masan ma tasan mai martaba ba yadda zaiyi ba.
Shi kuwa Faruq koda ya koma makaranta ya kasa samun kwanciyar hankali,gashi alokacin wani da wani ne ke rik'e wayar salula balle yace zai k'ira Hayat ya sake nemar gafararsa ko zaa dace wannan karon ya sauraresa.Allah-Allah yake semester tayi ta kare ya dawo gida.

   Watarana Hayat da Najmiy suna bitar karatunsu as usual,gefen haqunsu da kuma damarsu masu gadinsu ne,bayan sun kare karatun,hayat ya dubesu yace"Wallahi yau fa sai dai ku min duk abinda zakumin amma agaskiya sai na gana da Najmiy.... "

Kan suyi magana ya kalli Najmiy yace  _*"NAJMIYYA INA SONKI,SHIN KEMA KINA SONA?"*_

     Kan tayi magana kawai yaji saukar dorina agadon bayansa,wani dogari ne wanda dama ya dade yana jin haushin Hayatu,yanzu gani yake its an opportunity ya koyawa Hayat hankali,Hayat bai damu ba,Hawaye cike fal da idanuwansa yace da d'an k'arfi"Najmiy kiyi magana karki ji tsoro,shin kema kina sona?"

      Tuni Najmiy ta fashe da kuka ganin bulalar da aka sake tsula masa,wani dogari ne yayi mata alamu da ido wai ta tashi ta shige ciki,da sauri ta kwashi books dinta tayi ciki tana kuka.Hayat shima fashewa yayi da kuka mai tsuma xuciya bayan tafiyarta,ashe yanzu idan kace kana son wani ya zamo laifi?

Awannan ranar saida aka kaiwa mai martaba kararsa,ya kirashi ya tsassage masa yace ya fita aharkar Najmiy don ya riga da yayi mata miji ma amma bai fada masa cewar Faruq bane,ashe tun da dadewa suka kulla wannan zancen da sarkin kano,kan cewa Faruq zai baiwa auran Najmiy,toh shi ko kadan baya son canza magana arayuwarsa,shiyasa ya tsaya kan tsayin daka akan lallai fa Faruq zai baiwa ita.babu wanda yasan wannan kudirin nasa sai sarkin Kano.

     Yanzu ma sam sam an hanasu zama wuri daya suyi karatu,azahiri Hayat yayi kamar ya haqura ne amma shi kadai yasan famar da yakeyi da xuciyarsa akan soyayyar Najmiy,kullum kamar k'ara masa sonta ake acikin zuciyarsa.Rayuwar Hayat na tafiya ne ba yabo ba fallasa,idan kuna hira dashi kaji can yayi shiru,tofa tunanin Najmiy yake,idan ka tambayeshi abinda ke damunsa,toh kuwa next thing hawaye ne zai biyo baya,yanzu Ma ya daina concentrating kan karatunsa,CGPA dinsa ma yayi kasa da yawa,wanda har ya sanya saida level adviser dinsu ya kirashi yake tambayarsa abinda ke damunsa da har yayi sakaci CGPA dinsa yayi low da yawa.

     "Babu komai sir" shine kawai abinda ya iya furtawa.Zuwa yanzu ya soma hulda da abokan banza,don sosai suke mantar dashi rayuwar kuncin da yake ciki,sigarin nan ma Hayat har ya soma d'an tabawa da kuma codein,idan yasha shi yakan jishi ontop of the whole world ne,yakan mantar dashi damuwar da yake aciki.sai dai wani abin birgewa,sam baya hulda da mata,mace daya yakeso kuma itace 'Najmiy Gaddafi'.Mutum na farko daya soma noticing canjin halayyar Hayatun shine wannan dogarin daya fi tsanarsa wato mamman.

   Watarana Hayat na dakinsa don zuwa yanzu ah boysquarters suke,tare yake da abokansa su hudu,'Spanzy', 'Roughcoin', 'Na babies','MD smart',sannan shi Hayat shine na cikon biyarsu wanda ake k'ira ayanzu da *'BADMAN'*😅.(chubby don't cry pls)

        Sun baje ak'asa suna buga chachaa wanda su Roughcoin ne suka kawoshi aboye.Mamman dogari wanda yazo yin fitsari ah boysquarters ya jiyo yar hayaniya adakin Hayat,cikin sanda yaje kusa da kofar dakin,lekawa ne yayi ta window ahankali,warin sigari ne ya daki hancinsa,ai kuwa da sauri ya fice yaje yakai rahoto wajen sarki,akunne ya gaya masa.cike da tashin hankali mai martaba ya nufi boysquarters,ai kuwa yana tura kofar dakin ta kuwa budu,ya afka ciki,dukkanninsu babu wanda yayi tunanin cewar akwai wanda zai iya shigowa har ya riskesu acikin wannan halin musamman ma mutum kamar mai martaba.

    Arud'e Hayat ya dubi roughcoin don shine ya shigo ak'arshe,yace"Kai banza dama baka rufe kofar bane?"

    "Allah ne dai ya shirya tona asirinku ayau... "acewar Mai martaba cike da dacin rai.

Can ya sake cewa  _*HAYATUDDEN*"_ nan da nan kuma sai ga hawaye ya zubo masa shaa! asaman kunci.Ya cigaba"Hayatu kaci amanata kuma kaci amanar tarbiyyyar dana baka,ashe haka abin yake?dan daka fiso shine ke sanyaka zubda hawaye?hayatu irin wannan kazamar rayuwar ne ka jefa kanka aciki?chacha acikin gidana?shan sigari?jibi sumar kanka ka canza masa Kala,haba shiyasa kodayaushe kake cikin saka hula,baka yadda ka fito waje ba tare da hula akanka ba,ashe dai kasan abinda ka aikata..... "

    Ya tsagaita jin numfashinsa dake haurawa sama sama sabida tsananin b'acin ran da bai taba experiencing irinsa ba.Shi kuwa Hayat fashewa da kuka yayi cike da nadamar irin sabuwar rayuwar daya jefa kansa wanda hakan ya sanya mahaifinsa zubda hawaye akansa ayau.Abokansa kuwa kowa jiki ba kwari suka kashe sauran karan sigarinsu tare da jefawa cikin aljihun wandunansu,Spanzy ne ya karbi ta hannun Hayat ya kashe don shi yama kasa motsawa daga inda yake tsaye.wannan wani style ne irin tasu da suka sabayi,idan har wani babba ya kamasu suna shanta,ko kuma wani yana musu fadar Shanta,sai suyi saurin kashewa atare kana su jefar da karan ah aljihun wandunansu.

    Roughcoin ya duka ya dauki kwalbar codein dake kasa,kana yayi wa sauran signal,ai kuwa da gudu suka rab'a gefen mai martaba,suna fita sukaci karo da dogarawan dake tsaye abakin kofa,wani irin dodging sukai musu suka arta aguje tamkar wasu karnuka.harsu dogarawan na shirin kwasa aguje su kamosu,suka ji mai martaba yayi sauri katse musu hanxari,yace"A'ah ku kyalesu sun tsira,yau ranarsu ce don haka babu hukunci,amma idan suka bari suka sake maimaita hakan acikin gidana tofa saina hukuntasu fiye da tsammaninsu,kai karma ku sake ku kara barin koda daya daga cikinsu ne ya tako cikin gidan nan,da fatar duk kunji abinda na fada ko?"

    Zub'ewa sukai akasa sukace"Allah ya taimaki mutumin talakawa insha Allahu hakan bazata sake faruwa ba."

     Yace"Dakyau kuma ina musu fatar shiriya.... "
Chapter 8 · 0% Book details