← Book details    Hibbatullah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 23

Sashe 3

   Hibbatullah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   Jin yayi larabci ya saka wani pretty smile sub'uce Mata,atlast ta samu wanda ke jin larabci don ta dade tana zaga gari tana cigiyar dan'uwanta,tana yi tana hadawa da kuka,duk wa'enda tayi ta haduwa dasu ahanya suka kuma tambayeta dalilin kukanta?bata jin abinda suke fada,sai dai tayi musu bayani da larabci cewa dan'uwanta ne ya b'ata shine take nemansa,sai kaga mutum yaja tsoki yayi wucewarsa abinsa tunda bai gane abinda take fada ba balle yace bari ya taimaka mata.

    Bayanin iyayenta ta shiga yi masa da kuma Akhee (my brother) kamar yadda take k'iran dan'uwanta daya b'ata.Tana yi tana hadawa da kuka da kuma kwatance da hannu,mutane kuwa tuni suka soma yi musu chaa! aka,da hanxari dogarai suka taka musu birki,suka hana musu samun kusanci da inda mai martaba M.K bahago yake.Don haka daga nesa kawai suka tsaya suna kallon ikon Allah!.Shi dai mai martaba M.K babu abinda ya tsinta acikin labarinta don iliminsa ta larabci bata kai girman wannan ba,haka mah dogarawansa babu abinda suka tsinta illa mah yarinyar birgesu tayi yadda take ta fidda larabci dakyau abin gwanin ban shaawa,yanayinta ne kadai zai sa kasan cewar labari me cike da tausayi ne take badawa.Abinda kawai mai martaba ya tsinta acikin labarinta shine, _*'Waldi*_ wanda yana nufin 'mahaifina',sai kuma _*'Ummii'*_ wanda yana nufin 'mahaifiyata',sai _*'Akhee'*_ wanda 'dan'uwana' yake nufi,se kuma _*'Ukhti'*_ wanda yake nufin 'yar'uwata'.Toh abubuwa ukun nan ne kurum ya tsinta acikin labarinta.

     Ya dubi dogarawansa yace"Ina ganin kawai mu dauketa mu kaita gidan sarki tunda bamu tsinci komai acikin labarinta ba sannan kuma shi kadai yasan yadda zaiyi da ita tunda acikin garinsa ta fado,amma ni ina ji acikin jinin jikina cewar ba karamin zaluntar yarinyar nan akai ba..... "

Dukawa sukai alamun girmamawa,sukace"Hakan kuwa za'ayi ranka shi dade,kamata yayi kawai akaita gidan sarkin...... "

Ya kamo hannunta ta soma turjewa tana yakusarshi,tana hadawa da ihu da kuma kokarin son takai masa cizo,da hanxari dogarai suka fasa mata wani uban ihu wanda hakan ba karamin razanata yayi ba,at once ta shiga cikin taitayinta,dole tayi musu hakan don hakan ce ta faru da Akhee dinta,tana ji tana gani wasu sukai gaba dashi acikin mota,shiyasa take gani kamar itama din cutar da ita zasuyi.

   Mai martaba yadan murmusa yace"Ku rabu da ita don Allah don ko waye ne mah zeyi tunanin cutar dashi ake shirin yi balle ita da take yarinya karama mah kuma wacce ko kadan bata jin yarenmu,dole ne tayi tunanin kila cutar da ita muke shirin yi.... "

Daya daga cikin dogaran ne yaji kawai yarinyar ta bashi tausayi,cikin harshen turanci yace"My dear relax! We mean no harm,we juz want to help..... " (dayake acikinsu duka shi kadai ne ya dan taba boko,amintaccen mai martaba kenan kuma shine ya rikeshi har ya sakashi aboko,iyakacinsa ss3,daga nan kuma ya zama dogarinsa,shine translator din sarki aduk lokacin da wani yayi wa sarki turancin da bai ji ba,Jabir ne mai translating😀😂).

   Ita dai binsa kawai tayi da kallo don ko kadan ilimin turancinta bai kai nan ba,dake ita kanta batayi bokon ba,abinda kawai ta tsinta shine kalmar 'help' wanda hakan na nufin taimakonta zasuyi kenan.Shima kalmar 'Help' abakin mutane take jinta idan zaayi taimako kenan.

    Wani ne acikin jama'ar da suka taru yace"Toh ina kuma zasu kaita?kar dai ace fa saceta suke shirin yi.... "

Da sauri Jabir ya waiga yana duban dukkan ilahirin jama'ar,axuciye ya juya ya soma takawa xuwa garesu yana fadin"Ina wanda yayi wannan maganar yake?maza ya fito nan..... "

     "jabir rabu dasu kawai kazo mu tafi,idan mutum yace zai biye ta jama'a toh kuwa bazai taba tabuka abin kirki ba,gidan sarki zamu kaita tunda ku bakuyi tunanin kai baiwar Allahn nan can ba,ni ban san meyasa duniyar nan ta lalace ba,sam babu taimako kowa kansa kurum ya sani,Allah ya kyauta.

Haka suka bar wajen suka nufi gidan sarkin kano,mutane kuma suka soma watsewa kowanne cike da mataccen jiki don sosai maganganun mai martaba ya shigesu dakyau.

_*Note:pls don't b confused,shekarun baya fa muke tunawa ahalin yanxu,labarin tsohon emir muke badawa wato mahaifin mai martaba umar bahago,yana da matuqar muhimmanci kuji wannan labarin kafin mu koma kan ainihin labarin,wannan labarin shine mafarin komai*_

   _*Idan har na gamsu da sharhi sosai da sosai toh ina iya baku update anjima,Nagode*

     *ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💞*

       ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
          *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
           ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️

    *❄️(ƙ'վɑմԵɑ ժɑցɑ Aℓℓαн)❄️*

**ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑**

   *MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💞*

       *WATPADD:HAFNANCY*

**ՏɑժɑվƘɑɾաɑ ցɑ Dr.մʍɑɾ fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα**
______________________________________

   *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*

{օղաɑɾժ ԵօցҽԵнєɾ}
*{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HEART TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINGS 💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔

_*°•мy anтy нaυwa мarυвυcιyar 'laвarιn rayυwaтa' ĸιna ιna?тoн ιdan ĸιna ĸυѕa мaza ĸι мaтѕo don wannan ѕнaғιn мallaĸιnĸι ne,na вaĸι ѕнι нalaĸ-мalaĸ,gιrмanĸι da мυтυncιnĸι aн ιdona ya wυce yadda ĸιĸe тѕaммanι cυz υ are really ιndeed a ѕιѕтer,aм very нappy тo нave υ ιn мy lιғe,Allah yaвar qaυna da хυмυncι,нaғnan тana мιĸι ѕon qaυna anтy нaυwa•°*_

     💥

      *Թɑցҽ 5⃣*

Acan gidan sarkin Kano kuwa,sosai yayi mamakin dawowar mai martaba M.K Bahago na ganin rabuwarsu kenan da nufin komawa garin Minna,don ana gama daurin aure,bai wani tsaya ba yace yana da wani uzuri dake jiransa ah minna,sukayi sallama ya taso tare da masu tsaron lafiyarsa,dalilin daya sanya sarkin Kano shiga tsananin mamakin kenan na ganin dawowarsa.Amma jin abinda ke tafe da Mai martaba M.K,ya sanya jikin sarkin kano yin sanyi qalau,gashi shima din ba wai yana jin larabcin bane haka mah jama'ar dake cikin fadarsa babu wanda harshensa ta larabci ya nuna,tunawa yayi da cewar akwai wani d'an abokinsa wanda yake jin larabci sosai,hasalima ah qasar eygyt yayi karatunsa ah inda ya karanci 'Islamic studies' zallah,Malami ne sosai wanda garuruwa da dama mah sukan gayyaceshi yin wa'azizzika.

Nan da nan kuwa ya aika hadimansa da suje su taho masa da Mal.Zubair (sunan malamin kenan).Wani aiki yake amma sai ya ture yabi bayansu don kiran sarki kira ce wacce bazaka iya ƙin xuwa ba.

Koda yazo aka masa bayanin wannan yarinyar,takawa yayi har xuwa gabanta ya tsugunna tare da tsura mata ido,ita kuwa baiwar Allah tun shigowarsu fadar take ta rawar dari gami da zazzare idanuwa lokaci xuwa lokaci don ko kadan ta rasa gane abinda ake ciki.Ahankali ya furta _*Alaisatirkha Hakaa kisswatu... " ma'ana"Ki nutsu ki bamu labarinki."

Kamar dama jira take abata umarnin hakan,sai kawai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya da kuma ban tausayi,ta shiga yi masa bayani ayayin da shi kuma yake aikin gyada mata kai wanda hakan ke nuni da cewar sosai yake gane bayanun nata,sauran mutan fadar kuwa,babu abinda suke illa sharar hawaye duk da cewar basu jin abinda take fada,amma duk wani mai imani da kuma raunin xuciya idan ya kalleta sai ya tausaya mata sabida yanayin yadda take bada labarinta kadai mah ya isa kasan cewar labari ne mai cike da tausaya take badawa.

Bayan ta k'are labarin nata,Mal.Zubair ya juyo garesu,kwarmin idanuwansa cike suke da hawaye wanda dab suke da soma gangarowa saman kuncinsa,ta maza yayi ta hanyar kwafesu sannan ya soma fassara musu labarin data bashi cikin harshen hausa.

"Wato ita dai sunanta _*'Najmiyyah Gaddafi'*_,shekarunta na haihuwa bakwai,yar wani gari ne mai suna _*Baghdad*_ wanda shi din babban birni ne dake cikin ƙasar Iraq.Tana da yaya namiji mai suna *'Aryaan'* wanda take ƙira da 'Akhee',shekarunsa na haihuwa goma sha biyar,sai ƙanwarta mai suna *'Yumna'* wacce take ƙira da 'Ukhti',ita kuwa shekarunta na haihuwa biyar ne kacal.iyayensu talakawa ne liƙis wanda abincin da zasu ci mah sau uku arana daya gagararsu take,suma din sun tashi sun tsinci iyayen nasu ne acikin irin wannan rayuwar ta rashi,basu da kowa sai su ukun nan da suka haifa,Akhee shine kadai wanda aka saka amakaranta boko mai dan sassaucin kudi,su kuwa ba'a sakasu ba don iyayen basu da ƙarfin sakasu su duka,shima din don yana da namiji ne shiyasa aka sakashi dake yafi matan buqatar ƙaratun ko don gobe.makarantar islamiyya ce kurum suke zuwa.Wani abin birgewa wai shine,aduk sanda Akhee ya dawo daga makaranta toh duk wani abinda aka koya masa tofa zai hada kan kannen nasa ne suma ya koyar dasu,tofa anan ne suka soma tsintar kananu-kananun turanci.

Ah ƙasar Iraq suna zamansu lafiya qalau,fitintinu da kuma rigingimu awannan qasar da dan sauki musamman yankinsu Najmiy sam da wuya kaji ana tashin hankali anan.Kwatsam wata iftila'in ta kunno kai cikin wannan babban birnin,fada ta hada matasan Baghdad da kuma sojojinsu har takai ga kashe kashen rayuka,gida-gida ake bi ana kashe mutane,idan Allah yace da sauran kwananka agaba,sai kaga ka tsira,nasan kuna sane da wannan fadar da akayi awannan kasar don shekaranjiyan nan akayi news dashi,toh acikin rayukan da aka kashe,ciki kuwa hadda iyayen Najmiy da kuma 'yar qanwarta Yumna wato Ukhti.Cikin ikon Allah sai Najmiy da dan'uwanta Aryaan wato Akhee suka samu suka tsere,'yar karamar katangarsu suka haura suka sauka.Toh sai suka samu suka bi mutanen da suka tsere,tare da taimakon wani tsoho suka fad'o Nigeria kuma anan garin Kanon.Sunso bin wannan tsohon amma sai yace musu kowa yayi ta kansa,sauran ma haka sukace musu.

Tofa! Su Najmiy suka rasa madafa,gasu da kananun shekaru,shekarar Akhee goma sha hudu ayayin da ita kuma take da shekaru bakwai kacal aduniya,haka suka dunga yawo agari babu wanda ke son ya taimaka musu,wani gun ma wai korar kare ake musu,wasu kuma k'yamarsu ake balle anga farar fata (kun san dai yadda wasu ke k'yamar farar fata musamman irin fatar turawa ma wa'enda ba kabilarsu ba)😂.

Akarshe dai wasu samari dake cikin wata mota suka k'irawosu,toh turanci sukai da dan'uwan nata wanda ko kadan bata tsinci komai aciki ba,kalmar *'I will'* ne kawai ta gane,wanda hakan ke nuni da cewar wani abin suke son yayi musu shine yace zaiyi.

Can yayi mata bayanin cewar wani aiki zasu sakashi yi idan yaso sai su bashi abinci ya dawo suci tare,don haka ta zauna ak'arkashin gindin wata bishiya,bazai dade ba zai dawo.Tana ji tana gani akai gaba da Akhee dinta acikin mota,shi kuwa lek'owa yayi yana daga mata hannu yace _*"wada'an hataa naltaqi mujadadaan fi waqt lahiq Ya ukti😭"*_ ma'ana _*Goodbye till we meet again later my dear sister😭*_ (Ashe sallama ta har abada ne sukayi basu sani ba).
Chapter 3 · 0% Book details