← Book details    Hibbatullah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 23

Sashe 2

   Hibbatullah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu b'ata lokaci sai ga mai martaba ya iso tare da dogarawansa biyu biye dashi abaya,wani uban sauri suke ta zabgawa kamar zasu tashi sama ah sa'ilin da suka soma tattaki bayan sun sauko daga cikin mota,jama'a kuwa sai kallonsu ake musamman Mai martaba Wanda kusan zan iya cewa ba'a cikin hayyacinsa yake ba.Straight ofishin Dr.Bature suka nufa wanda yake acikin ward din da aka kwantar da Prince Aryaan.

***
"Ikon Allah! your highness ashe ba ance min ka dade da tsufa ah airport ba? azatona ma jirginku ya dan jima da flying,sai kuma gaka anan,lafiya ka dawo da baya kuma?" Dr.Bature ne yayi wannan maganar ah sa'ilin da kallonsa ya sauka kan Mai martaba wanda ya shigo cikin ofishin dauke da sallama abakinsa.

Saida mai martaba ya samu wuri ya zauna tare da cire hularsa ta sarauta ya ajje saman tebirin dake tsakaninsu da Dr.Bature,kana ya budi baki yace"Ance kana son magana dani akan rashin lafiyar d'ana dalilin daya saka na dawo da baya kenan.... "

"Kashhhh! yanzu saida gimbiya ta saka ka dawo da baya?seda fa nace mata ta bari harka dawo sannan ayi maganar amma....... "

Da sauri mai martaba ya tari numfashinsa"Look Bature rayuwar d'ana yana da matukar muhimmanci agareni wanda bana jin zan iya yin sakacin rasashi saidai idan rabbi ne yayi ikonsa akansa,amma da lafiyata da komaina,ina ji kuma ina gani bazanyi wasa da rayuwarsa da gangan ba,don haka Dr.Bature Abu sadiq bazan iya haqura har sai na dawo kafin ayi maganar ba,so now tell me wat's the deal?meh kakeson gaya min agame da ciwon prince?"

Saukar da ajiyar xuciya Dr.Bature yayi,kana ya soma bayani"wato your royal higness amatsayinmu na kwararrun likitocin kasar india, munyi iya bakin kokarinmu wajen yakice cutar _*'Medulloblastoma brain tumor'*_ da danka keda shi,kuma munyi nasara,ayanxu sam bashi da wannan cutar,sai dai kuma komfutocinmu sun kasa detecting shock din dake kai masa attack ah kwakwalwarsa,munyi iya bakin kokarinmu wajen gano wannan matsalar amma abu daya har yanxun yake nuna mana wato _*'NOT DETECTED'*_,wannan shock din itace ta saka yake cikin coma,aduk lokacin daya yi yunkurin dawowa cikin rayuwa se kaga shock dinnan ta kai masa hari wanda hakan ke saka kwakwalwarsa baze iya juran shock dinnan ba se kaga ya koma cikin coman,am sorry to say idan har shock dinnan ya cigaba dakai masa attack continuosly toh kuwa watarana yana iya loosing memory dinsa,yaji kawai ya manta wasu abubuwa da suka faru dashi na shekarun baya can,idan har ze warken kenan,or probably lead to mental madness,infact it can also lead to the dead of the victim......"

Cike da zafin rai Mai Martaba Umar faruq Bahago ya mik'e tare da kaiwa table din dake atsakaninsu mugun bugu bana wasa ba,kana ya daga yar yatsa yana nuna Dr.Bature dashi,yace"Dr.Bature kalamanka suna neman yin tsauri da yawa don haka kayi gaggawan kiyaye harshenka,ni dana baze tab'a haukacewa ba kamar yadda kake masa fatar hakan,prince Aryaan insha Allahu nan bada jimawa ba ze tashi,ze dawo ya cigaba da rayuwarsa kamar kowani dan'adam,na baku nan da sati biyu cur! idan har banga wani changes ba,toh kuwa zan dauke d'ana xuwa wata k'asar don ba ku kadai ne kwararrun likitoci anan doron k'asar ba,aikin banza kawai....... "

Yaja tsoki tare da daukar hularsa ta sarauta daya ajje saman table,ya kafata akai,kana ya fice daga office din,Dr.Bature kuwa sae binsa yake da kallo baki sake,mai martaba ma bai tsaya yaji shawarar da zai bashi ba kawai ya dau magana da zafi,girgiza kai kurum Dr.Bature yayi tare da ayyanawa aransa cewar sannu ahankali zai fahimtar dashi abinda yakeson gaya masa agame da ciwon d'an nasa.

Mai martaba na fita,straight ya nufi room din da aka kwantar da prince ayayin da dogaransa suka take masa baya.Yana shiga dakin ya tarar da Gimbiya zaune kusa da Prince,hannayenta sarke cikin nashi as usual,sam baya son ya kara mata wani damuwar akan wanda take ciki shiyasa yayi saurin shanye bakin cikin daya kunso awurin Dr.Bature.

Hawaye ne ya soma kwaranyowa asaman kuncinta ah sa'ilin data hada idanuwa dashi,kansa ya shiga girgiza mata yana fadin"A'ah my Najmiy karki soma,mu cigaba da yiwa Aryaan addu'a insha Allahu zaya tashi da izinin Allah ta'ala,oya maza wipe up ur tears and put a smile on ur face for ur dear King.... "

Wani irin pretty smile ne ya sub'uce mata wanda har hakan ya sanya ta dan manta da kuncin da take ciki na yan dakiku,ai kuwa da hanzari tayi kamar yadda yace.

Matsowa yayi kusa ya bata labarin yadda ta kaya tskaninsu da Dr.Bature,tasha kuka sosai ayayin da mai martaba ya dunga bata baki,akarshe ta saduda ta fawwalawa Allah komai,yayi mata sallama ya tafi akan cewa bayan anyi sadakar uku zai dawo sai susan nayi da prince,idan har babu wani changes tofa zasu daukeshi zuwa qasar Germany.

_*How far Hafnan's freaking fans? How was the first page?is it okay?and if yes should I move on?*_

_*will prince Aryaan survive at all?*_

_*sannan wannan wani irin shock ne da har kwararrun likitoci kamar na k'asar India suka kasa ganowa?*_

_*Sannan kuma ku biyoni don jin irin tsuntuwar da Mai martaba umar Faruq Bahago zaiyi akan hanyarsa bayan ya sauka qasar Nigeria*_

*I*
*STILL*

*REMAIN*

*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ*
     ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
        *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
           ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️

      *❄️(ƘվɑմԵɑ ժɑցɑ Aℓℓαн)❄️*

          **ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє 💏**

        *MALLAKAR:HAFNAN*

       *WATPADD:HAFNANCY*
___________________________________

**ՏɑժɑմƘɑɾաɑ ցɑ Dr.մʍɑɾ fαяυq вαнαgσ,eмιr oғ nιger ѕтaтe,мιnna**

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-1194933670662901/

      *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*

            {ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ}
*{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HEART TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINGS 💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔

_*°•gaιѕυwar вan gιrмa gareĸa мaι мarтaвa Dr.υмar ғarυq вaнago,нaqιqa ĸa cιĸa ѕнυgaвan ĸwaraι wanda вυrιnѕa aĸodayaυѕнe ѕнιne ya ĸyaυтaтawa тalaĸwanѕa,мυ'aмalarĸa da мυтane ιѕ jυz perғecтly oĸay,ιna neмar gaғararĸa,вanyι wannan lιттaғιn don тѕoĸacι agareĸa вa,ĸιrĸιnĸa ga al'υммa ya ѕanya nayι aмғanι da ѕυnanĸa dιrecт вa тare dana canza вa,υвangιjι Allah yaѕa ĸa wanye da dυnιya laғιya,can'т love yoυ leѕѕ мy ĸaĸυѕ😀•°*_

_*°•wannan ѕнaғιn мallaĸιnĸι ne ĸe daya мy ѕaнιвa jaмeelaн janaғ,ĸιrĸιnĸι agarenι ιѕ jυz ĸιnda мaѕнa Allah,нaĸa мa ѕoyayyarĸι agarenι ι jυz нave тo alнaмdυlιllaнι ĸaѕeeran,ιna ѕon ĸι ѕanι cewar nι нaғnan ιna мιĸι ѕo мaι cιĸe da dυмвιn qaυna💕,don Allaн ѕaнιвa ĸι cιмιn υwarĸυ нaj. ĸarι da ѕaĸιna😂, мaĸe deм ѕυғғer & regreт ιn lιғe😁, ĸι ѕaѕѕaιтa мιn ĸawυnanѕυ dυĸ plѕ😊,ĸυ neмa ĸυ ĸaranтa lιттaғιn ѕaнιвa мaι ѕυna 'TA TAFKA KUSKURE•°'*_

                        💥

    *Թɑցҽ4⃣*

_*SHIN WANENE MAI MARTABA UMAR FARUQ BAHAGO?*_

      Mai Martaba Umar Faruq Bahago ∂a ne ga tsohon sarkin Minna wanda ake kira da _*'мaι мarтaвa мυнaммad ĸнaмιѕ вaнago'*_.Matan auran Mai martaba m.k bahago biyu,Gimbiya Khadeejah wacce aka fi sani da Haj.Babba itace uwargidansa,ita dinma 'ya ce ga sarkin gombe _*мaι мarтaвa мυнaммad υмar zayyan*_.Ya'yanta uku kacal aduniya, *'UMAR FARUQ'* (present emir) shine danta na fari,sauran biyun kuwa duk mata ne,*'ABIDA'* da kuma *'HIDAYA'*.

     Bangaren ∂ayar matar tasa kuwa,sunanta gimbiya Maymunerh wacce ake kira da Haj.Karama,ita kuwa danta guda daya kacal data haifa adoron kasa,sunansa *HAYATUDDEEN'*,bayan haihuwarsa ko batan wata bata sake yi ba,haihuwar ta tsaya mata cak!,toh dayake ita din macece mai tawakkali da kuma haquri sai ta nuna godiyarta ga Allah madaukakin sarki da guda dayan daya azurtata dashi,wata tana nan mah ko barin wata bata taba yi ba,haihuwa take nema ido arufe amma Allah bai bata ba,toh ita wacece da har zata butulcewa ubangiji bayan mah ya azurtata da guda daya? Haka ta haqura ta rungumi dan tilon danta da kuma 'ya'yan kishiyarta,sosai suke zaman lafiya don itama Haj.Babban macece mai mutunci da kamala da kuma son ganin an zauna lafiya,haka mah 'ya'yansu akwai wata irin muguwar shaquwa ta yan'uwantaka mai karfin gaske atsakaninsu,kawunansu duka ahade yake,kai infact idan ba sanin gaske kayi musu ba,toh kuwa bazaka iya tantance dan dakin nan da dan dakin can ba komin kwakwarka kuwa.Hayatudden mah kwasar duka kayansa yayi ya koma bangaren Haj.Babba ah inda ya saje dasu ya zamana kamar itace ta haifeshi ba Haj.Karama ba.

    Mai martaba M.K Bahago wani irin mutum ne mai saukin kai sosai,shi din mutumin jama'a ne don cewa suke ma yasan darajar mutane,amulkinsa mutane suka san kalmar *'Adalci da kuma kwatar yanci'* suna existing har yanxu azamaninmu,duk wanda ya zalunci waninsa,toh kuwa Mai martaba M.K bazai taba barinsa ya tafi ba har sai yasa an masa hukunci daidai da laifinsa da kuma yadda addininmu ya tsara,atakaice dai Mai martaba yana mugun kyautata mu'amalarsa da jama'a,ga taimakon talakawa da kuma jawosu ajiki,to make it short,kowa na bala'in sonsa kuma akullum fatar alheri suke masa da zuriarsa.

     Mai martaba M.K bahago beyi karatun boko ba seta arabi,yayi karatun allo mai zurfi,duk da cewar beyi karatun boko ba amma yana bala'in sonta shiyasa yaci alwashin 'ya'yansa duka sai sunyi.

        _*°•WASU SHEƙARUN BAYA CAN DA SUKA SHUDE•°*_

    Wata tafiya ce mai martaba M.K bahago ya taba yi zuwa garin kano ta dabo tumbin giwa(sai mu nan munfi kowa😀)sarkin kano ne ya aika masa da katin gayyata ta bikin wata 'yarsa shine yaje,toh akan hanyarsa ta dawowa ne da masu tsaron lafiyarsa (dogarawa) suka gan wata 'yar karamar yarinya wacce bazata wuce sa'ar autarsa Hidaya mai shekaru bakwai aduniya ba tana ta kuka agefen titi,kuma abin mamaki duk cincirindon mutanen dake ta kai komo amma anki samun wanda yayi tunanin tsayawa ya magance mata damuwarta,kowa sabgar gabansa kawai yake.Mai martaba M.k shine ya umarce dogarawansa dasu tsaya yana son jin matsalar yarinyar sannan ya magance mata ita.

   Shida kansa ya fita yaje har inda yarinyar take tsaye ya tsugunna yana tambayarta abinda ke damunta har take kuka,sannan kuma iyayenta suna Ina?

  Ita kuwa yarinyar ko kadan bataji abinda ya fada ba don bata jin Hausa.Fashe masa da kuka tayi tace _*"'ana la'afham ma taqul.... "*_ ma'ana"Ban gane abinda ka fada ba"

     Jikinsa ne yaji yayi sanyi qalau,atake anan ya gano dalilin daya sanya kowa yaki taimakonta,wato ita din balarabiyace don halittarta kadai ma ya nuna hakan,babu meh jin larabcin da take yi shiyasa kowa ya shareta ya cigaba da sabgar gabansa.

  Ya rasa abinda zece mata don shima din ba wani jin arabin yake sosai ba,can ya daure yace _*ayna abuki wa'umki?*_ ma'ana"Ina abbanki da ummanki suke?"
Chapter 2 · 0% Book details