Sashe 4
Hibbatullah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru shiru 'Akhee zai dawo amma babu koda labarinsa,yinin ranar nemarsa take tayi tana kuka agari amma babu wanda yake jin yaren da take balle ya taimaka mata,akarshe awannan karkashin bishiyar ta koma ta shimfida siririn mayafin jallabiyarta anan,raguwar dan ruwan pure water data gani awurin bishiyar ce ta dauka tayi alwala da ita,gashi bata San lokaci ba don haka ta jera sallonlinta duka tayi,dan half sunna hijab ne kanta.haka ta kwana awurin da tsoro,ga yunwar da take ta addabarta,tun safe bata saka komai acikinta ba har dare,kuka take tana ambaton "'Akhee ina ka shige ne?" Allah ne dai kawai ya tsare baiwar Allahn nan daga fadawa hannun yan bata gari da kuma kidnappers har wayewar gari wanda kwana tayi zaune ko runtsawa batayi ba.
****
Washeqari ma haka ta tashi tana kuka tana neman Akhee dinta har bakin titi,shine fa har Allah ya kaddara haduwarta da mai martaba muhammad khamis Bahago.
Mal.Zubair ya karashe zancensa da"Allah ya taimaki mutumin talakawa,Allah yaja da ran sarkin sarakuna,haqiqa kayi tunani mai k'yau daka taimaki wannan baiwar Allahn har ka kawota nan gidan mai martaba sarkin kano,kayi namijin kokari wajen ceton wannan 'yar yarinyar daga fadawa cikin gararin rayuwa da kuma 'yan bata gari,ana yawan fada min cewar kana da taimako amma ban taba yadda ba sai yau,ubangiji Allah ya saka maka da mafificin alherinsa........ "
Gabaki daya kowa ya karba da "Allahumma amin..... "
Babu wanda bai zubdawa Najmiy kwalla ba na tsananin tausayinta.Sarkin kano shine ya sanya Mal.zubair tambayarta ko zata iya bada kwatancen halittar dan'uwan nata,da sauri ta gyad'a musu kai alamun zata iya din.Sarki ya bada umarnin aje anemo kwararran 'sketch artist' yazo ya zana musu fuskar Akhee dinta.
Kafin ah iso dashi,tuni sarkin kano ya sanya aka kawo mata abinci irin wanda aka san zata iya ci,kana ta biya sallar asubahinta don shine kadai ake binta.Bayan mai zanen ya iso,babu b'ata lokaci ya soma zanensa cike da kwarewarsa,tana kwatantawa Mal.Zubair yadda halittarsa take ayayin da shi kuma yake aikin fassarawa mai zanen,sharp sharp kuwa ya gama.
Tsab! Kuwa ya samoshi,tana ganin fuskar Akhee dinta kan farar takadda ta fashe da kuka tana fadin" Akhee kana ina?Don Allah ka dawo kai kadai ne ka rage min.... " da larabci ta fadi hakan.
Mal.Zubair ne ya shiga lallashinta akan cewa za'a ga dan'uwanta nan bada jimawa ba insha Allah.Sarakunan sukayi taking excuse suka fice waje sukayi shawarwari atsakaninsu,can suka dawo suka fadawa kowa shawarar da suka yanke.
Mal.zubair ya dubeta yace"Daya daga yace cikinsu yana son ya rikeki har zuwa lokacin da za'a ga dan'uwan naki,don haka wanne acikinsu kikeson ya rikekin?" ya fadi hakan tare da nuna sarakunan biyu.
Kallonsu ta shiga yi,itafa zuciyarta yafi kwantawa da wanda ya taimaketa afarko wato mai martaba M.k bahago.don haka nunashi tayi tace _*"Hadha*_, ma'ana"wannan "
Kowa yayi hamdala,aka damka amanar baiwar Allah 'Najmiyya Gaddafi' ahannun mai martaba M.K bahago har zuwa lokacin da za'a ga dan'uwan nata.Shima ya qarbi amanar da aka bashi da hannu bibbiyu tare da daukar alkawarin cewar tsakaninsa da Allah zai riketa kamar 'yar cikinsa.Aka rufe taro da addu'a.
Awannan ranar aka fidda wa'enda sune zasu je nemo Aryaan Gaddafi ah cikin garin kano tare da taimakon hoton fuskarsa da aka zana.
Sai goshin magrib Su mai martaba suka iso garin minna.
_*shigowar Najmiyya Gaddafi 'yar mutan Baghdad cikin wannan royal family din shine mafarin komai,muje zuwa my fiful😉*_
*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕*
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*❄️(Ƙ'վɑմԵɑ ժɑցɑ Aℓℓαн)❄️*
**ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑**
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN*
*WATTPAD:HAFNANCY*
____________________________________
**ՏɑժɑմƘɑɾաɑ ցɑ Dr.մʍɑɾ fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα**
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
{օղաɑɾժ ԵօցҽԵhҽɾ}
*{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HEART TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINGS 💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔
_*°•wannan ѕнaғιn мallaĸιnĸυ ne yaѕeera cool angel,нaғѕaт ĸanтy, мaмan ѕadιq,ғarιda тalвa,мoм ĸadιja, υммυlĸнυrѕooм,ѕιѕтer мaryaм,мy ғυlanι,мy janaғ,мy najaтee da ѕaυran wa'enda вan aмвaтo вa,нaqιqa coммenтѕ dιnĸυ yana ѕυмar danι,ιna мιĸa godιaтa agareĸυ allaн yaвar love da хυмυncι,aмeen•°*_
💥
*Թɑցҽ6⃣*
Koda mai martaba ya labartawa iyalansa labarin Najmiy,suma din sosai suka tausaya mata hadda zubda mata hawaye,ita kuwa sai binsu kawai take da kallo don ko kadan bata tsinci komai da suke fada ba amma dai tasan labarinta ne Mai martaba ya basu.lafiyayyar girki aka taresu dashi kuma ba laifi Najmiy ta cire kunya da bakunta taci sosai.Suna kammala cin abinci aka soma kiraye kirayen sallar magrib.
Kallon mai martaba tayi,akwai magana abakinta amma ta rasa yadda zata fadeshi har su gane abinda take nufi tunda ta lura suma din ba wai jin larabcin suke ba,gwara gwara mai martaba m.k.
Kowa yana lure da ita amma sai aka dake ana sauraron aji abinda zatace,idan ta bude baki zatayi magana sai kuma kaga tayi saurin rufewa,Hayat ne ya sanya hannu ya rufe bakinsa jin wani uban dariya na nemar kufce masa.Haj.Karama ce ta masa ido alamun maza ya kama kansa.
Duk da cewar tasan Najmiy ba lallai ne taji abinda zata fad'a ba,amma sai ta daure tace"Daughter what's wrong?"
Ai kuwa ta gane kalmar 'wrong',don haka da sauri tace"Ummii salat" murmushi sukai gaba dayansu wato dai tana nufin tana son tayi sallah ne,kowa awurin sai yaji kawai ta mugun birgesa,Mai martaba ya dubi su Abida yace"Maza Abida ku tashi kuja yar'uwarku kuje ku gabatar da sallah."
"Toh Abba mai martaba."haka suke kiransa,cike da farin ciki suka ja hannun Najmiy sukayi ciki.Hayat ya saukar da wata ajiyar zuciya wanda hakan ya janyo hankalin kowa zuwa gareshi,saurin saddar dakai kasa yayi yana dan murmusawa ganin an kura masa idanuwa.
Haj.Babba ce kawai ta dan murmusa tace"Kai Hayat akwai shiririta.... " daga haka kowa ya mike don gabatar da sallah.Mai martaba da samarin suka fice zuwa masallacin gidan.kowacce ta koma turakarta don dama ah turakar mai martaba duk suke.Bayan Najmiy tayi sallolinta hadda ta isha'i,su Abida suka bata kayan bacci ta saka tare da bata wata zumbuleliyar hijabi,suka tafi turakar mai martaba suka masa saida safe,shi kuma yayi masu fatar alheri,haka ma sunje sukayiwa haj.k'arama sallama,kana suka komo bangaren haj.babba,itama suka mata saida safe,kana suka wuce dakin baccinsu tare da Najmiy din.Al'adar royal family din kenan,Kafin su kwanta duk sai sun bi iyayen nasu sun masu gaisuwar k'arshe ta wannan ranar.
*****
Washeqari Mai martaba ya tara duka iyalansa da kuma bayinsa,ya sake bada labarin 'Najmiyya Gaddafi' tare da nuna musu cewar ita din amana ce agareshi,don haka ya gaya musu cewar duk wanda ya bakanta mata toh kuwa kamar ya bakanta masa ne,don haka kowa ya kiyaye.kowa ya daukar masa alqawarin cewar insha Allah ze kiyaye kuma Allah ya bayyana dan'uwanta.Ita kuwa Najmiy sai bin mutane take da kallo don ta kasa gane wainar da ake toyawa,shi kuwa Hayat duk abinnan da akeyi hankalinsa baya garesu,gabaki daya hankalin nasa ya tafi ne ga Najmiy,sosai yarinyar ke birgeshi,ya rasa meyasa yanayin tsoronta da kuma yanayinta cikin danuwa yake bashi sha'awa.(Anya Hayat?I think you are alrdy inlove with balarabiya😀).
For the very first time,idanuwanta da nasa suka sarke cikin na juna,irin kallon da yake jifarta dashi yasa tayi saurin dauke kallonta daga gareshi,can kuma ta sake maida kallon nata gareshi,taga still ita din dai yake kallo hadda wani kashe masa ido daya.Tuni ta saddar da kanta kasa.
"Allah yaja da ran yarima karami,muje kayi shirin makaranta.... " haka yaji wani dogari ya fada,sai asannan ne ya lura ashe har an watse har Najmiy din,shi kadai ne ya rage acikin fadar sai kuma mai martaba da wasu dogarawan fada da kuma mai kula ko kuma nace mai hidima dashi Hayat din.
"Ai daka bari ya gama tunane-tunanen banzansa har yayi latti yaje yasha bugun tsiya amakaranta.... " mai martaba ne ya fadi hakan awasance.
Hayat yace"Tabdi! Abba mai martaba yanzu sai adoki the whole prince of sarkin minna?remember am Hayatudden freaking M.k bahago...... "
"Dallah can rufewa mutane baki anan,don kana d'an sarki shine zai hana ah hukuntaka?".....
Aka fashe da dariya,so yake yayi magana sai kuma wannan dogarin nasa ya sake magana"Allah ya taimaki Yarima karami,lokaci na kurewa kuma ina jiye maka fadar malaman makaranta..... "
Wani kallo ya watsa masa don shi sam arayuwarsa ya tsani ata nanata masa magana dai daya.bai sake cewa komai ba ya russuna ya sallami mahaifinsa,kana ya wuce ciki don yin breakfast cuz already yana saye cikin uniform dinsa ne.
Awannan ranar Mai martaba M.k ya sanya aka samo masa wani malamin larabci wanda kuma ya goge ab'angaren harshen hausa da kuma turanci,zai dunga zuwa ne akullum yana koyar da Najmiy hausa da turanci har zuwa sanda zata kware,sannan kuma idan tana da wata damuwa sai ya dunga fassara musu.Babu ranar da Najmiy baza tayi kukan rashin iyayenta da dan'uwanta ba,su mai martaba kuwa sai kaga suna rarrashinta,zuwa yanzu tasan meh kalmar 'haquri' yake nufi don malaminta ya fassara mata shi da larabci,yace 'asifa' yana nufin 'Haquri' ayaren Hausa.Toh idan taji ana cewa yi hakuri ko kuma sorry tasan lallashinta akeyi.
Aryaan Gaddafi kuwa babu labarinsa,duk wani lungu da sako na garin kano babu inda ba'aje ba amma ko mai Kama dashi ba'a gani ba,har gidajen radio aka bada cigiyarsa,infact harda gidajen radio na wasu garuruwa amma shiru kakeji babu labarinsa,Aryaan Gaddafi dan mutan Baghdad has gone,gone and gone forever😭.(Allah sarki Najmiy harna tausaya miki wallahi.)
Haka dai Najmiy ta haqura ta rungumi iyayen rikonta,amma akullum cikin addu'ar Allah ya bayyana mata Akhee dinta take da kuma yiwa iyayenta da kuma Ukhti dinta addu'ar samun rahamar ubangiji.
_*°•AFTER FIVE MONTHS•°*_
Acikin watanni biyar kacal Najmiy harta soma kwarewa da harshen Hausa da turanci,dake malamin jajirtacce ne kuma gwanin iya koyarwa,sosai mai martaba M.K ke yabawa da aikinsa,don zuwa yanzu Najmiy ta saki jikinta har tana zama tana hira dasu.Afari da 'Big Akhee' take kiran prince Faruq,wato 'Babban yaya',hayat kuma 'Small Akhee',Abida kuma 'big ukhti' wato 'babbar sister' sai kuma Hidaya 'small Ukhti',watanni biyar ne kacal ke tsakaninsu da Hidaya,don haka ita Najmiy dinne ta zama autar gida.