← Book details    Hibbatullah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 23

Sashe 7

   Hibbatullah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hayat na kokarin magana tuni mai martaba ya rigashi"Shhhhhhh! yi min shiru anan bana son jin komai daga gareka,ka bude kunnuwanka ka saurareni dakyau,daga yau sai yau bana son ka sake keb'ancewa da ita don Najmiy amanar Allah ce agareni,idan na kuskura nayi sakaci har rayuwarta ya gurbata toh kuwa Allah bazai tab'a yafemin ba,Hayatudden Bahago bazan tab'a baka auren 'yata Najmiyya Gaddafi ba,Najmiy marainiyace don haka yasa nakeson na aurar da ita ga namiji nagartacce wanda nasan zai kula min da ita,wanda kuma nasan bazai taba bari tayi kukan maraici ba dede da minti daya,amma bakai ba Hayat,kaje na yarje maka ka zab'o duk wacce ta maka afadin duniyar nan,muddin dai tana kai kanta k'asa tofa zan aura maka ita,amma ba Najmiy ba,kuma daga yau sai yau na haramta maka k'ebancewa da ita,wannan shaquwar kuma arageta bana so,idan kuma aka kuskura aka sab'a umarnina tofa zanyi hukunci da kuma daukar kwakkwarar mataki,don haka kayi gaggawan yakiceta daga cikin xuciyarka... "

    Gabaki daya network din jikin Hayat ya tsaya cak! ya daina aiki,haka ma dukkan jijiyoyin jikinsa sun tsinke da kalaman mai martaba,gwiwowinsa sun sake,gaba daya kawai yaji duniyar tana juya masa,dakyar ya budi baki yace"Abba mai martaba don Allah karka sa na soma tunanin cewa bakai ne ka haifeni ba,don aganina da kuma iya sanina babu mahaifin da zaiso ganin ya salwantar da farin cikin dansa da gangan,fisabilillahi! Menene aibuna don kawai nace ina son Najmiy?don Allah ba abin farin ciki bane ma don ina son na taimaka mata ita da bata da asali ma?kuma wanene yace ni din bazan iya share mata kukan maraicinta ba?haba Abbana meyasa?

   Fashewa yayi da wani kuka mai tsuma xuciya,da sauri ya isa ga Mai martaba ya zub'e agabansa tare da kamo kafafuwansa,yace"Don Allah Abba mai martaba idan wani laifi na maka wanda ni ban sani ba,toh don Allah ina rokanka daka yafemin dan'adam ajizine,amma pls karka hanamin samin farin cikina,wallahi ina son Najmiy,she really captured my heart starting from day one,kuma itama nasan tana sona,wallahi ku k'irata ku tambayeta nasan zata fad'a muku gaskiya...... "

     "Hey! Young man karkayi tunanin cewar shaquwar dake atsakaninku so ce,sam abin ba haka bane,shaquwa daban haka kuma so daban yake,don haka bana tsammani Najmiy sonka take kamar yadda kai kace kana sonta.... "Faruq ne ya fadi hakan.

Hayat ya dago yana dubansa,cike da tsanarsa yace"Ai dama nasan kaine ka hada komai,ka shimfidawa Abba mai martaba k'arya da kuma gaskiya,waya sani ma ko kaima son Najmiy din kake shiyasa kake son ka hada bomb?"

    "Allah ya kiyaye,tirr da wannan negative thinking din naka,Najmiy kallon qanwar da muka fito ciki daya nake mata,kallon Hidaya da kuma Abida nake mata,kai ko zan nemi budurwa ma ni bazan taba nemar yar kankanuwa kamar Najmiy ba,haba brother wat You are trying to do is simply child abuse.... "

   Haqiqa kalmar 'child abuse' ta daki Xuciyar Hayat don har runtse idanuwansa yayi gam,kuma agaskiya Umar ba wai son Najmiy yake ba,shi kawai gani yake Najmiy bata kai matsayin da har zata soma soyayya ba (waya gaya maka?)

   Mai martaba kuwa saddar dakai yayi kasa yana saurarensu,yama rasa ta cewa,shidai gaskiya acikin 'ya'yansa yafi qaunar Hayat amma bazai iya bashi Najmiy ba don sosai zata cutu da halayyarsa bayan aure,wanda ko kadan bazai taba so hakan ta faru ba.

   *
Acan daki kuwa,su gimbiyoyin ne suka tasa Najmiy agaba akan tayi musu bayanin abinda ya sakata kuka,dakyar ta hadiye kukanta kana tace"Wai ya za'ayi ace Yaya Prince karami ya kalli cikin k'wayar idanuwana yace yana sona?shin ya manta cewar ni din k'anwarsa ce?ko kuwa haka kukeyi anan?ko kuma nace shin haka kukeyi ah al'adarku wa yace yana son k'anwarsa da soyayya?"

  Jikin Haj.karama ne yayi sanyi qalau da jin wannan zance na Najmiy,ita kuwa Haj.Babba sosai abin yayi mata dadi na ganin za'ayi 'yar gida gida ne,haka ma su Abida abin yayi musu siga sosai.

      "Abinda ya sakaki zubda hawaye kenan?" haka haj.karama ta furta sam babu ko digon annuri akan fuskarta,kai kawai Najmiy ta daga mata alamun eh. "Toh share hawayenki yarinya don nima ko kadan bana qaunar wannan hadin.... "

Cike da mamaki Haj.Babba tace"Haba Maymunerh lafiyarki kuwa?wannan wani irin zancen banza kenan?Najmiy ce fa?shine kike ambaton cewar bakya qaunar hadin nan?toh gaskia ki sake tunani Maymunerh don nidai banga dalilin dazai saka kiyi irin wannan furucin ba.... "

    "Yaya akwai dalili... "acewarta

Haj.babba tace"Wani dalili kenan?"

    "ki bari anjima zamuyi magana... "

Ta maida kallonta ga Najmiy tace"Ke ina Hayatun yake?"

    Da rawar murya Najmiy tace"Na barosa ah inda muka saba bitar karatunmu..... "

    Fuuu! ta mike tayi hanyar kofa,Haj.Babba na mata magana ko waigowa batayi ba balle asa ran zata tankata,da hanzari Najmiy tabi bayanta tasha gabanta,kamo hannayenta tayi tace cikin muryar kuka"Ummi khuddha basat (take it easy),don Allah na rokeki karki masa fada,kedai ki sake tunatar dashi cewar Najmiy qanwarsa ce,don haka bai kamata ace ya furta Kalmar so agareta ba...... " kala bata ce mata ba ta rab'a ta gefenta ta wuce.

    Haj.Babba wacce fitowarta daga daki kenan tace"Ke kuwa Najmiy in banda abinki ai akwai aure atsakaninki da Hayat,Hayat ba shaqiqinki bane,ba ciki daya kuka fito dashi ba,don haka akwai aure tsakaninku..... " she was suprised sabida ita bata taba sanin cewa ana iya auran gida gida bama,kuma ita ta dauki su faruq kamar 'Akhee dinta ne wanda suka fito ciki daya.

   Haj.karama ta janyo hannunta suka zauna saman kujera,kana ta shiga warware mata komai dalla dalla harta fahimta,sai dai har yanzu mamakin bai bar fuskarta ba.

      _*Toh yanzu bari mu koma fada mu dubo wainar da ake toyawa,sannan kuma meh Gimbiya Maymunerh take nufi ne?kuma meh take shirin aikatawa?ku biyoni*_

    *ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕*

      ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
        *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
           ❄️❄️❄️❄️❄️❄️

        *°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*

      *°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*

     *MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*

      *WATPADD:HAFNANCY*

*•ѕadaυĸarwa ga Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα•*

  *°•ιnтellιgenт wrιтerѕ aѕѕo🖊•°*
___________________________________

                           💥

       *Թɑցҽ 9⃣*

Acan fada kuwa,rigima ce ko kuwa nace cin musu ce ta kaure sosai tsakanin Faruq da Hayat,shi Hayat cewa yayi sai Faruq din ya gaya masa hadisi ko kuma ya kawo masa ayar da akace nemar mace kamar Najmiy child abuse ne,shi kuwa Faruq ya kuke sai masa bayani yake akan tsarin bayahude.

     Mai martaba wanda keta sauraransu tun dazu ne ya doka musu wani uban tsawa,yace"Ku min shiru mutanen banza da wofi,kunbi kun cika min kunne da shashancinku na banza.... "

Ya dubi Hayat yace"Kai kuma Hayat ko kadan banji dadin furucinka dakace wai Najmiy bata da asali ba,haqiqa kayi daƙiƙanci anan,toh ina son ka sani cewar ni awurina kallon 'yar cikina nake mata,Najmiy tana da cikakkiyar asali,kuma zan tsaya kan tsayin daka koda kuwa kowa ya gujeta ne,toh ni zanyi kokari naga na zame mata gatanta wanda zatayi alfahari dashi fid-dunya-walakhira,kuma koda wasa ka sake ka sake maimaita wannan kalmar,toh wallahi sai nayi mugun sassab'a maka,da fatar kaji abinda na fada?"

    Cike da nadama Hayat yace"Eh duk naji abinda ka fada Abba mai martaba,don Allah ka gafarceni subutar baki ne... "

**
Haj.Karama kuwa tana fitowa ta aiki wani dogari da yaje ya k'irawo mata Hayat ah inda Najmiy tace yake,da sauri dogarin ya zub'e agabanta yace"Ranki shi dade,Yarima Karami yana fada.... "

    Bata bari ta k'arashe jin zancensa ba ta nufi hanyar fadar,har ƙuyangu sun soma take mata baya sai kuma tayi saurin dakatar dasu.Tana shiga cikin fadar kuwa ta hango Hayat durƙushe gaban mai martaba yana kara rokansa akan yayi haquri ya bashi auran Najmiy,shima Faruq din ya saka baki don bai tab'a tunanin hakan ne zai kasance ba da kuwa bai kawo kararsa ba,shi kansa bai san dalilin daya sanya mahaifin nasu yace bazai baiwa Hayat auren Najmiy ba,shifa kawai yazo ne yace masa ya kirawo Hayat ya masa fada kan ya fita hanyar Najmiy don bata kai matsayin da har zata tsaya tayi soyayya ba ayanxu,ya bari sai ta dan kara wayau da kuma girma,sai kuma gashi mahaifinsu yace kwata kwata ma wai bazai bashi auranta ba. 

Babu b'ata lokaci ta isa ga Hayat fuskarta babu ko digon annuri akansa,dagoshi tayi ta mikar dashi tsaye,shi kuwa mutumin naku yana hada idanuwa da ita,ya soma sakin murmushin jindadi,don atunaninsa itama zancen ya isketa ne shine tazo ta tayashi roƙan mai martaba akan yayi haquri ya bashi Najmiy.

    Babu zato babu tsammani kawai Hayat yaji saukar wani lafiyayyan mari saman kuncinsa,bai gama shanye mamakinsa ba kuma yaji saukar wani adayan gefen kuncinsa,har ta daga hannu zata k'ara masa wani,sai kawai taji an rike mata hannun,Faruq ne,Yace"Haba Haj.karama meh kuma yayi zafi haka da har yakai ga mari?"

    "Cikan hannu... " shine kawai abinda ta iya furtawa da k'arfi,da sauri Faruq yayi kamar yadda ta bukata tare da jaa da baya da sauri sabida irin tsantsar bala'in daya hango shimfid'e acikin ƙwayar idanuwanta.Juyawa tayi ga Hayat wanda tsananin mamakinta ma ya hanashi furta komai,nunashi tayi da 'yar yatsa tace"Don qaniyarka ni Maymunerh ni zaka janyowa abin ƙunya da kuma abin fada agari?ka rasa wacce zakace kanaso sai wacce ba'a san asalinta ba?toh wallahi da sakel,bada yawuna ba kuma ba'a cikin wannan masarautar ba,don haka maza ka gaggauta binne wannan zancen nadai gaya maka tun wuri don kada matakin da zan dauka agareka yazo bai maka dadi ba.... "

    Har ta juya zata wuce,da sauri mai martaba yace"Maymunatu maza dawo nan.... " cak! ta tsaya ah inda take,sai data kwashi kusan daƙiƙu goma kafin ta juyo ta soma dawowa da baya zuwa gareshi.Rissinawa tayi har k'asa tace"Gani ranka ya dade... "

  Zuba mata idanuwa mai martaba yayi ba tare da ya furta komai ba,sai girgiza kansa yake cike da tsananin mamakin jin furucin daya fito daga bakinta,gani yake kamar ba maymunarsa bace mace mai tsananin son mutane da daukar kowa nata ne,koda yake ai ba abin mamaki bane don dama can ance mutum tara yake bai gama cika goma ba,dama duk ƙyawun halayyarka tofa dole za'a samu wani b'angare naga mai muni.Toh ayau kuwa other side dinta Gimbiya Maymunerh ta gwada masa.

    Gyaran muryarsa yayi daidai da shigowar Haj.Babba cikin fadar,shiru shiru taga haj.karama bata dawo ba shiyasa ta biyo sahunta.samun wuri tayi ta zauna ganin kamar magana muhimmiyace akeyi acikin fadar.
Chapter 7 · 0% Book details