← Book details    Hibbatullah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 23

Sashe 19

   Hibbatullah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_*°•ѕσ much lσvє чσu mч dєαr mσmmα hαj.hαdízαtσuh muhαmmαd kαkαkí,mαmmα u gαvє lífє tσ mє,turnєd thє вαвч íntσ α lαdч,mαmmα αll u hαd tσ σffєr wαѕ thє prσmíѕє σf α lífєtímє σf lσvє,thєrє íѕ nσ σthєr lσvє thαn α mσthєr'ѕ lσvє fσr hєr chíld👉---cєlín díσn•°*_

*Թɑցҽ 2⃣0⃣*

     _______jin zancen Mai martaba yayi tamkar saukar aradu,Najmiy dinsa tayi aure sannan wai kuma dan'uwansa Faruq ta aura?yaushe ma akayi auren?acikin shekaru biyun da baya gida?yanxu kuma duk guduwar da yayi agida da nufin idan ya dawo yasan za'a bashi ita don kada ya sake guduwa,yanxu plan dinsa ya tashi abanza kenan?God!!!! shikenan dan'uwansa Faruq yayi masa kwacen *'Adorable'* dinsa kamar yadda yake kiranta kenan.

   Ji yayi kamar ya fasa wani uban ihun da zai iya tada zaune tsaye,ihun da zai iya hargitsa kwakwalwar duk wani halittar daya ji wannan ihun.Baya jin rayuwarsa zata iya cigaba da tafiya normal ba tare da *'Adorable Najmiy'* dinsa ba,sai dai kuma bazai iya raba auranta da dan'uwansa ba amma kuma alqawari ya dauka sai ya sanya Faruq tsiyayar da hawaye akan *'SO'*,sai ya gwada masa yadda akeji idan aka rasa *'Masoyi'*,wannan alqawari ne saiya dauki *'FANSA'* akan *'UMAR FARUQ'*,infact! har ita kanta *'NAJMIY'* din sai ta gane kuranta.

    "Yayah prince ka cuceni,ashe son Najmiy kake shiyasa kasan yadda kayi kabi duk wata hanya ka rabani da ita?toh Ina son ka sani cewa *'KA TAFKA BABBAN KUSKURE'* don ba'a taba *'HAYATUDDEN'* kuma azauna lafiya,wallahi wallahi koda zanyi yawo tsirara ne nayi alqawarin maida rayuwarku abar tausayi daga kai har Najmiy din,sai na firgita rayuwarku fiye da zato da kuma tsammaninku.... " duk acikin xuci yake wannan maganganun.

   Mai martaba ya katse masa zancen xucin da yake tayi ta hanyar fadin "Hayatuna yana ji kayi shiru?kodai shawarace kake da xuciyarka kan matakin da zaka dauka kuma akaro na biyu?"

    Murmushin ƙarfin hali ya saki wanda zamu iya fassarashi da murmushin daya fi wani kukan ciwo,kana yace"A'ah Abba Mai martaba ni tuni ma na dade da cire Najmiy acikin raina kawai lokacin dawowata gida ne beyi ba sai yanzu,dama ina da niyyar dawowa ayau sai kuma naga Yayah prince yazo nemana jiya,wallahi harga Allah nina haqura da Najmiy,ubangiji Allah ya sanyawa auransu albarqa,Allah kuma ya basu zaman lafiya,ni ayanxu fatana shine Allah yasa Hajiyata ta yafeni,kuma Allah ya gafarta min bakanta muku dana yi,kai kuma Abbana kayi haquri ka yafeni sannan kuma Allah ya baka lafiya.... "

    "Allah ya yafemu duka,naji dadi daka hankalta Hayatu,na kuma ji dadi da ayanxu kasan yadda ake daukar *'DANGANA DA KUMA 'HAQURI'*,koda yake ko baka haqura ba dama babu yadda zakayi tunda dai an riga da an daura auran,kai kuma Umaru Allah yayi maka albarqa,hakika ka cika dan'uwa na gari wanda ya fita yaje ya nemo dan'uwansa don kawai ya dawo kan hanya madaidaiciya,ubangiji Allah yasa ka wanye da duniya lafiya Umaru.... "

    "Amin amin Abbana,bara na latso likitanka na kora masa good news... " acewar Faruq kenan,murmusawa akayi gabaki daya har Hayatun.Haj.Babba kuma ta mike tana cewa Hayat yazo yaje yaci abinci,yace mata taje gashi nan tafe,so yake Faruq ya kare wayarsa sannan yayi masa magana.

Bayan ya kare,ya kalleshi yace"Congratulations Yayah prince,ashe an zama babban mutum ban sani ba?anyway ina tayaku murna,Allah ya bada zaman lafiya sannan kuma Allah ya kawo kazantar daki..... "

   Dam!! Faruq yaji gabansa ya yanke ya fadi amma kuma sai ya waske yace "Amin tanks bro,muna ma cikin watanmu na shidda kenan da auran... "

Kan Hayat yayi magana,Faruq yayi saurin kallon mai Martaba yace"Abbana likitanka yace yana nan tafe ya dubaka bayan sallar magrib.... "

    "Toh " shine kawai abinda ya iya furtawa.Hayat kuwa bai sake cewa komai ba ya mike ya fice,Faruq ma ya mike yabi bayanshi,suna fita suka ci karo dasu Abida sunzo ganin Abba mai martaba don tuni Haj.Babba ta karas musu da daddadar labarin.

    "Habib Albi kibi ahankali karki fadi.... " Faruq ya fadiwa Najmiy haka cike da shaukin sonta,sosai abin ya daki xuciyar Hayat,bakin ciki ya turnukeshi,ji yayi kamar ya shako Faruq din ya aika dashi har lahira.

_*"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,  Allahumma ajurni fi musibati wa'akhlifni khairan minha "*_,wannan itace addu'ar daya yita nanatawa acikin xuciyarsa har ya isa b'angaren Haj.Babba.

    *🐾AGURGUJE PLEASE🐾*

  Kan kuce meye wannan tuni gida ya soma rudewa da jama'a 'yan xuwa yin barkar dawowar Hayat dake acikin kankanin lokaci har Faruq ya sanya an baza agidajen radio cewa Yarima karami ya dawo gida,abinka da dan babban mutum kowa so yake ace ai yazo shiyasa akayita tururun xuwa,shi kuwa uban gayyar makalewa yayi adakinsa yaki fitowa don sosai yake jin kunyar hada idanuwa da mutane,tsanar Faruq ya dadu aransa don acewarsa meyasa Faruq din zai bazawa duniya cewa ya dawo?aganinsa wani salon cin fuskar ne ya sake yi masa daga dawowarsa,dangin mahaifiyarsa suma sunzo don su aka ma soma sanarwa kafin kowa,mai martaba yace"Ga dan yar'uwarku nan dan'uwansa Faruq ya fita yaje ya nemosa don haka yau saiku shafa min lafiya,ayau zanyi bacci mai dadi wanda na jima ban sake yin kwatankwacinsa ba..... " suma din dakyar Hayat ya bari suka ganshi.

   Kowa saida yayi mamakin budewar bakin mai martaba wai kuma akan Hayat,nan suka sake tabbatar da tsananin qaunar da yake yiwa Hayatun tunda akansa ya kwanta wannan ciwon sannan kuma akansa bakin nashi ya budu har ya soma magana.

  ___________________
Likitocinsa sunzo sun dubashi kuma sunce da akwai improvement sosai,dama Hayat ne makasudin rashin lafiyar kuma tunda ya dawo insha Allahu zaya mike.

    Awannan ranar Hayat yasha fira da mahaifinsa kamar babu abinda ya faru,fira hadda ƙyaƙyatar dariya,hannayensu sarke cikin na juna har bacci ya kwashesu,Hayat na zaune saman wata kujera wanda ke kusa da gado ayayin da mai martaba kuma ke kwance saman gadon,kafin baccin ya kwashesu sai da suka sake nemar gafarar juna,shi kuwa Faruq nacan kan wata doguwar kujera,shima wani nannauyar bacci yayi awon gaba dashi.

     Can mai martaba ya farka,yana jin wani sabon al'amari ajikinsa,ya kalli Hayat da Faruq wa'enda ke kwasar baccinsu hankali kwance,murmushi yayi ya furta ahankali"Ubangiji Allah ya dada hada min kawunanku,Allah yayi muku albarka,naso ace mun rayu da juna na wani dan tsawan lokaci amma ga dukkan alamu lokacin da aka dibar min ya kare..... "

Yadan ja numfashi,can ya cigaba cikin muryar da bata fita sosai yace"Hayatu komin rintsi koman wuya karka taba juyawa dan'uwanka Faruq baya ko kuma ka zalunceshi don yayi maka gata arayuwa,sannan kuma ku rike min Najmiy amana...... "

    Allahu Akbar!!! his royal highness *'MAI MARTABA MUHAMMAD KHAMIS BAHAGO'*,mutumin talakawa ya cika yana mai dauke da murmushi asaman fuskarsa,ya koma ga mahaliccinsa cikin haske da kuma annuri ah fuska (Allah yasa muyi irin wannan cikawar,amin).

  Sai wuraren biyar saura na asubahi sannan Hayat ya farka,yaji hannun mai martaba dake sarke cikin nashi yayi sanyi qalau,tashiwa yayi ya kunna wutar lanta,kana ya dawo wajensa,fuskarsa dauke da murmushi kamar ka kirashi ya amsa.

    "Abbana kodai jikin ne naji hannunka yayi sanyi da yawa.. " Hayat ya fada tare da dan taboshi,shiru bai amsashi ba,Hayat ya soma tsorata da wannan al'amarin,don haka ya shiga girgizashi continuously yana fadin "Abbana meya faru?don Allah ka tashi mana Hayatunka ne fa"

Faruq ya taso agigice sakamakon muryar Hayat daya tasar dashi.

    "Hayat meke faruwa ne?" ya nufo wurinsu.

"Yayah prince nima wlhy ban sani ba,inata kiran sunansa amma yaki tankani,don Allah kazo ka duba mana shi karya mutum ya barmu.... " ya fada already in tears..........

   _*wayyo Allaн мaι мarтaвa ya rιgaмυ gιdan gaѕĸιa,wa'adι ya cιĸa,wanι aвιn вιrgewa da ĸυмa ғarιn cιĸι ѕнιne an ѕaмυ ya yaғewa нayaт ѕannan ĸυмa aнannυn нayaтυn ya raѕυ,нaĸan yayι*_

_*тoғa!wнaт ιѕ нayaт υpтo?мeн yaĸe ѕнιrιn aιĸaтawa ĸan ғarυq da ĸυмa najмιy?ĸυ вιyo*_

_*αlвíѕhírínku?fαtαlwαr míjínα nαnαn tαfє muku gσвє ínѕhα Allαh*_

    *TAKU*

*mσm híввαh💕*
          ❄️❄️❄️❄️❄️
            *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
              ❄️❄️❄️❄️❄️

          *°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*

    *°•ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑•°*

   *MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*

      *WATTPAD:HAFNANCY*

https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/

*°•ѕα∂αυкαяωα gα Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα•°*

         *°•ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍•°*

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
__________________________________
                      💥

*NOT EDITED*

*Թɑցҽ 21*

       Faruq shima karan kansa bai gane komai agame da mai martaba ba,don haka arude ya kira likitansa,dakyar aka samu ya daga wayar sabida baccin dake idonsa,jin abinda Faruq ke gaya masa ya saka baccin wartsekewa daga idanuwansa,at once ya tashi,ya shirya agurguje ya kamo hanyar gidan mai martaba.

   Babu b'ata lokaci Faruq ya latso Haj.Babba ya kora mata bayani,hankali tashe ta taso su Najmiy suka nufi turakar mai martaba.Tunda Haj.Babba ta sauke idanuwanta kan mai martaba ta gane cewa inaaa! rai yayi halinsa,kota fadawa su Faruq ba yadda zasuyi ba don haka zata barsu suji hakan daga bakin likita.Fita waje tayi ta sami wani gu ta zauna,ta hau cizgar kuka ahankali yana furta"O'ooh mai martaba ashe korarmu kake tayi adaren jiya?kana ta cewa mu tafi mu kwanta ashe dai bakaso ka cika ne agabanmu?Allah sarki my dearest husband Allah yayi maka aikin gafara,Allah yasa kaje asa'a don wallahi kayi mugun kyautata mu'amalarka da mutane,don haka bani da fargabar komai akanka,Allah ya jikanka Muhammadu... " kuka yaci karfinta,su dogarawa da ƙuyangi suka cika kofar turakarsa cike da jimami,kowa jira yake yaji sakamakon likita wanda xuwansa kenan.

    Can suka jiyo ihun Faruq yana fadin"Noooooo!!!! Not again!!!! Hayat ka sake kashe min wani nawa,kayi sanadin barin someone so dear to me,my hero,my everything,tsakanina dakai babu yafiya,kotun Allah ce kawai zata rabani dakai...... " sam baya ma cikin hayyacinsa yake fadin wa'ennan maganganun.Haj.Babba tayi wani irin zabura ta shige ciki tana mai rushewa da wani sabon kukan,ƙuyangi kuka,dogarawa kuka,kowa da kowa kuka yake,babu zancen jarumtaka acikin wannan al'amarin mai tab'a xuciya wato mutuwar mutumin talakawa.

    Dakyar Haj.Babba ta iya b'anbare hannun Faruq daga makurar daya yiwa Hayat,cikin muryar kuka tace"Haba Faruq menene kakeyi haka kamar wani jahili?ko kuwa ka manta cewa rayukanmu duka ahannun Allah yake?ka sani fa wani baya iya kashe wani sai dai ace ta sanadin mutum wannan din yabar duniya,kuma ni inason ku dauka cewa wa'adin mai martaba ne kawai ya cika,kuyi masa addu'ar samun rahamar ubangiji,maza ku hanzarta ah shiryashi don mamaci baya son jinkiri....... "

   Kuka yaci karfinta ta juya ta fice da gudu,acan waje taga kowa sai kuka yake,wani murmushin karfin hali ne ya sub'uce mata tace"Allahu Akbar!! Muhammdu mutumin mutane,sarkin sarakuna,kabar mutanenka da kewarka da kuma kewar kirkinka agaresu,ubangiji Allah yayi maka aikin gafara,don Allah kubar yi masa kuka babu kyau,gatar da yake nema agareku itace addu'a...... "
Chapter 19 · 0% Book details