Sashe 16
Hibbatullah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
**
Su Hayat kuwa sai wuraren karfe shidda suka samu mai siyar bus dinsu,kuma awulaqance aka siyeta don anga suna tsananin buqatar kudi,90thousand aka siye wannan katuwar bus din kuma dakyar aka siyeta ahakan don bus din tana da dan matsala,tun acan suka ware dubu hamsin wanda zasu baiwa Mal.Rilwan sauran kudin gidan da ake binsu,dubu biyu kuma na Mal.Miskala kudin sigarin da ake binsu kenan.Wuraren shidda da rabi suka shigo cikin unguwar akan dan acab'a wanda sukai two pack,adaidai shagon Mal.Miskala suka sauka suka biyashi kudinsa,kana suka siyi biredi da kosai akusa da shagon,sannan suka nufi gida wanda tuni har an tada kabbarar sallah,akofar gida suka rabe,Shi Hayat ya nufi masallaci da gudu-gudu don kada ya rasa jam'i ayayin da Roughcoin ya shige gidansu Tsoho don siyar musu lemun kwalba gun Anty Ummi kamar yadda ake kiranta.koda ya shiga,ta siyar masa da komai ba tare da ta labarta masa komai ba,don Ummi Aysha macece wacce babu ruwanta da gulmace-gulmace ko kuma shiga sabgar daba tata ba.
Hahaha! acan masallaci kuwa,Hayat adaidai bayan Faruq ya tsaya yayi sallarsa,raka'a daya kawai ya samu,don haka adaidai lokacin daya kai sujjadar karshe,alokacin su Tsoho suka fito daga masallacin suka nufi gida,tsoho sai cewa yake"wai yau Hayatu lafiya bai dawo da wuri ba?basu taba kaiwa warhaka bafa agari?"
Suna isowa kofar gida,tsoho ya haskawa kofar gidansu toci yaga kofar abude take don babu wannan kwadon kuma,da mamaki ya dubisu Faruq wanda suma kallonsu akan kofar take yace"Laaah!kunga ashe sun dawo ina nan inata kumfar baki,amma meya hana Hayatu xuwa masallaci yau?ku jira bari na duboshi.. "
Kafin suyi wata magana tuni ya shige ciki,Roughcoin kadai ya sama acikin dakin ya baje akasa sai cin biredinsa da kosai yake,agefe daya kuma lemun kwalbarsa ce wacce time to time yake dan kurba,ya dume gida da wakar *'Do me Do me'*.
Yana ganin tsoho yayi saurin rage volume don yasan halinsa sarai yanzu zai iya hawansa da fada."Tsoho yane?meh kakeso ne?idan kuma kudinku ne ka biyo toh kasha kuruminka har gida zamu kawo muku shi cikakke anjima... "
Tsoho yace"Dalla rufemin baki mutumin banza kawai,Hayatu nazo nema ina yake?"
"Mosque.... " shine kawai abinda ya iya cewa,shi kuwa Tsoho bai sake cewa komai ba ya fito abinsa,ya gayawa su Faruq din yadda sukai da Roughcoin.
Tsoho yace"Amma abin da mamaki don ko mai kama dashi ban gani ba amasallacin,kodayake ina jin daga baya yazo,kuma nasan sai bayan isha'i zai dawo,Kumu koma masallacin.... "
Suka sake komawa masallacin,koda suka koma sun hangoshi ne can gaba yana karatun Qur'ani cikin zazzakar muryarsa,basu dakatar dashi ba sukayi zamansu awaje,saida aka kira sallar isha'i sannan ya dakata,bayan mutane sun taru aka tada sallar,sai asannan ne su Tsoho suka shige ciki don basu san Hayat yaga Faruq yanzu sai sun kai gida.
Ana idarwa su suka soma fitowa suka nufi gida,daga can wani gefe akusa da gidan suka tsaya,wajen duhu duhu ne,can sai ga Hayat yana tahowa,sai da suka bari ya shige cikin gida kana suka take masa baya.
_*тoн мy ғιғυl ya ĸυĸe ganιn нadυwar prιnce ғarυq da ĸυмa prιnce нayaт zaι ĸaѕance?*_
ĸυ вιyo
*тaĸυ*
*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕*
❄️❄️❄️❄️❄️
*Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/
*°•ѕα∂αυкαяωα gα Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα°•*
*°•ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
__________________________________
💥
_*°•wαnnαn pαgє dín mαllαkínkí nє mч lσvlч ukhtí 'rαmlєrh',ínα ѕσ kí ѕαní cєwα ѕíѕ hαfѕαt dínkí tαnα míkí ѕσ mαrα íчαkα wαndα вαвu αlguѕ αcíkí,uвαngíjí Allαh чαвαr qαunα dα хumuncí mαí dσrєwα,αmєєn°•*_
*Թɑցҽ 1⃣8⃣*
_*°αddu'αr nєmαr tѕαrí dαgα αzzαlumαí kσ kumα mαhαѕѕαdα👇°*_
_*°•Allαhummα rαввαѕ-ѕαmααwααtíѕ-ѕαв'í,wαh rαввαl-αrѕhíl-αzєєm,kun lєє jααrαn mín(ѕαíkα αmвαcí ѕunαnѕα),wα'αhzααвíhí mín khαlαα'íqíkα 'αn чαfrutα 'αlαччα 'αhαdun mínhum 'αw чαtghαα 'αzzα jααrukα,wαjαllα thαnαα'ukα,wα lαα'ílαhα 'íllα αntα•°*_
💥💥
---------Har Hayat ya daga yalalon labulen dakinsu zai shige,sai kuma ya jiyo sallama daga bayansa,muryoyi fiye da biyu ne suka daki dodon kunnuwansa amma yafi saurin shaida muryar Tsoho,don shi da karfinsa ya doka sallamar.Cike da fara'a Hayat ya saki labulen ya juyo yana mai fuskantarsu dakyau,yace"Ayyah baba tsoho abokina kaine tafe?Don Allah kayi haquri yau banzo kiranka muje masallaci ba wallahi yau ban dawo da wuri bane,hasalima yau sallah raka'a daya ce kawai na samu ta magrib,ina can har isha'i amma ko mai kama dakai ban gani ba,nace toh yau Tsoho lafiya kuwa ban gansa amasallaci ba?yanzu haka ma so nake naci abinci sannan na shigo dubiyarka sannan na damkawa Yah Rilwan raguwar kudin gidansa.. "
Shi kwata-kwata hankalinsa ma baya ga mutane biyun dake tsaye agefen tsoho,kuma ko kadan yaki baiwa Tsoho damar magana,yacigaba"Tsoho albishirinka?gobe Zan koma....... "
Wutar da nepa suka kawo ne ya katse masa maganarsa,kuma wutar lantarkin dake can sama ah bangon kofar dakinsu ya matuqar taimaka wajen haskaka masa fuskokin duka halittun dake tsaye agabansa.Ido cikin ido suke kallon juna da prince Faruq.
Akalla sun kwashi kusan daƙiƙu hamsin suna kallo-kallon junansu,Hayat shine wanda ya soma kawar da dogon silent din ta hanyar furta" *'YAYA PRINCE......... '* Ya fadi hakan cikin ƙaryewar murya,sannu ahankali wasu hawaye masu dumi suka soma gangaro masa saman cheeks.Jaa da baya ya soma yi kadan da kadan fuskar nan tasa shimfide take da tsansar mamakin ganin Faruq agarin Lagos kuma wai acikin gidansu,cikin rashin sani yaci karo da wata 'yar karamar kujera dake bayansa,ai kuwa kiris ya rage ya fadi,amma kafin yakai kasa sai yayi saurin sanya hannu ya dafe Bango.
"Hayatu kabi ahankali karka fadi don Allah... " acewar Tsoho.
Tsoho ya maida kallonsa kan Faruq wanda yayi mutuwar tsaye,ruwan hawaye ne kawai keta bulbulowa saman kuncinsa,kuma har yanxu bai dauke kallonsa akan Hayat ba.Duk da cewa dare ne amma wutar lantarki ta taimaka wajen hasko masa yadda kamannin Hayat ya sauya,ya mugun tara sumar kai,haka ma kasumbarsa ta cika fuskarsa,abu dai kamar ba Hayatudden Bahago dan Qayun daya sani ba.
Maganar tsoho ce ta maido da hankalinsa daga duniyar nazarin daya shiga akan Hayat,cewa yayi"Mal.Faruq mu zamu koma gida,zamu baku wuri ku sulhunta,idan har kun daidaita saiku samemu acan... "
"Toh Baba" shine kawai abinda ya iya furtawa cikin dauriya.
"Kai Rilwanu muje.. " acewar Tsoho,har sun juya zasu fice sai kuma Tsoho ya tuna da wani abu,ai kuwa da hanzari ya koma da baya,ya nufi kofar dakinsu Hayat,daga labulen sama yayi,can ya hango Roughcoin raƙube abango,jikin nan nasa sai aikin maƙyarƙyata yake don duk yana ta jin conversation dinsu dake ta wakana atsakar gidan,wato dai *'PRINCE UMAR FARUQ BAHAGO'* is here kenan,lol yasan kashinsa ya bushe shiyasa ya shiga cikin tsantsar tashin hankalin nan.
Dariyar mugunta Tsoho yayi kana yace"Shege katon arne ashe dai kaji komai,dan'iska mayaudari kawai,don wallahi ba'a gaya min ba amma nasan dasa hannunka acikin lamarin bawan Allah Hayatu,wallhi karshenka baza tayi k'yau ba,ni wallahi harna hango mazauninka acikin gidan wuta,zaka fito ne ko kuwa saina shigo na sameka anan?" hahah! Tsoho ya sami opportunity don ko dama can shida Roughcoin ko kadan basa shiri,Roughcoin sam baya daraja Tsohon,har ce masa yake Tsohon banza.
"Baba hadda son zuciyar shi Hayatun aciki don haka karka gama dora laifin akan abokinsa.... " haka yaji Faruq ya fada cikin wata kakkausar murya.Jikin Tsoho ne yayi sanyi qalau,ahankali ya juya yaja hannun Rilwan wanda nashi kawai kallo ne yake tayi,har sun kai kofar fita sukaji Faruq yace"Baba ina fatar ba fushi kayi da kalamaina bako?idan kalaman nawa sunyi tsauri ne da yawa toh don Allah ina nemar yafiyarka.. "
Harga Allah ba fushi Tsoho yayi ba,jikinsa ne kawai ya soma tsinkewa da lamarin Hayat,ya tabbata akwai magana akasa sosai akanshi,wai ma don bai san cewa mahaifiyarsa ta rasu akanshi ba kenan.
"Dana wallahi ba fushi nayi ba,nidai idan kun gama ina jiranku agida... " yasa kai ya fice ayayin da Rilwan ya take masa baya.
Roughcoin ne yayi shahada ya fito aguje saura kiris suci karo da Faruq,yayi kofar fita daga gidan ah 180 kai kace ko wani babur ne😂.
Hakan kuwa da yayi ba karamin dariya ya baiwa Faruq ba,harda kwallansa kuwa,ya rakashi da"Bloody monster daka bi ahankali donni bata kai nake ba,infact bani da deal dakai don hadda son xuciyar kanin nawa aciki,kadai je ka gyara rayuwarka if not kana iya karewa agidan wuta,asararre kawai.... "
Yana gama fadar hakan ya dauke dariyarsa,alokaci daya kuma ya juya yana fuskantar Hayat.
Ahankali ya furta"Hayatudden Bahago...... "
Cikin rawar murya yace"Ya... yah princeeeee waya gaya maka inda nake?"
"Ibrahim spanzy.. " Faruq ya bashi amsa atakaice ah sa'ilin daya watsa hannayensa cikin aljihun wandonsa.
Kafin Hayat ya gama shanye mamakinsa kawai yaji Faruq ya cigaba"Spanzy shine wanda ya gayan komai,garin da kake da kuma unguwar da kake zaune,da kuma sana'ar da kake yi,u hav completely turned into an enormous drunker,what an outrageous and shameful thing?the whole prince of sarkin minna has turned his life into a mess!!! Shame on you Hayatudden freaking Muhammad Khamis Bahago.. "
Hayat ya karya gwiwowinsa zuwa kasa tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka tamkar wani karamin yaro,sosai yayi nadamar biyewa zugar aboki kamar Roughcoin.
"Wai duk akan 'ya macece kabar gida?'ya macen ma da bata san kana yi ba?'ya macen da ayanxu hankalinta nacan wani wuri ne daban ba'a kanka ba?macen da take can tana rayuwarta hankalinta kwance kai kuma kana nan kana fuskantar kalubalen rayuwa akanta?bayan bata San kana yi ba?akanka mahaifiyarka ta kamu da congestive heart failure har yayi sanadiyyar barinta duniya,kuma abin mamaki da haushi wai duk kana da information akan hakan amma don toshewar kwakwalwa da kuma rashin imani ka kasa dawowa gida.... "
Matsawa yayi kusa da inda Hayatun ke zaune,shima ya karya gwiwowi zuwa kasa kamar yadda yaga Hayatun yayi,in otherwords,kneels down nake nufi,kana ya cigaba"Hayatu mahaifiyace fa?wacce ta dauki cikinka for good 9months,alokacin da zata haifoka kuwa kafarta daya aduniya dayan kuma alahira ne,alokacin ta fidda rai ne ga rayuwa,tayi nakudarka cikin radadi da kuma azaba,ta raineka cikin tsananin sonka da qaunarka kasancewarka dan data haifa kwara daya tak aduniya,taci kashinka,tasha fistarinka,ta tsotse majinar hancinka don kawai kayi looking good,dede da minti daya bata qaunar taji kukanka,da sauransu dai,shine kai kuma Hayatu ta hanyar da zaka saka mata kenan?ta hanyar kasheta da bakin cikinka?ta hanyar banzantar da mutuwarta?Brother u surely need prayers and deliverance.... "