Sashe 15
Hibbatullah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*°•ѕadaυĸarwa ga Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα•°*
*°•ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍•°*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
____________________________________
💥
_*°•dιz page ιѕ dedιcaтed тo all тнe нaғѕaт's all over тнe gloвe,ιғ υr naмe ιѕ нaғѕaт,нaғѕυ,нanѕaι & waтever den dιz page ιѕ υrх,ιna yιnĸυ мy naмcιeѕ,'тнe вeaυтιғυl вaвy lιoneѕѕ' daтѕ тнe мeanιng oғ oυr naмe•°*_
*Թɑցҽ 1⃣7⃣*
Mal.Sani Falalu wanda akafi sani da 'Baba Tsoho' haifaffen 'Dumawa' ne wanda karamar hukumar 'Minjibir' ne dake jihar Kano.Su biyu ne kawai iyayensu suka haifa,dashi da kuma ƙanwarsa wacce ake ƙira da Inna Ladidi,ya taso yaga mahaifinsa yana noma,wato dai manomi ne,toh dayake shi kadai ne namiji agabansa,sai ya dorashi akan wannan sana'ar,doya ne,masara ne,shinkafa dadai sauransu duk suna nomawa,bayan sun girbe,sai sukai cikin garin kano su siyar,ana haka ne fa har Allah ya habbaka kasuwancinsu suna samun kudi dakyau yadda ya kamata,ita kuwa Ladidi tuni akai mata aure da wani dan makobcinsu wanda ya nuna yana sonta,as time goes on da aka ga kokarinsu na siyar da kayan masarufi,sai gwamnati ta basu wani dan filli akasuwar kano,sai suka kafa rumfa anan,shi Sani aka bari anan ya dunga saidawa,ayayin da mahaifinsa ke kawo kayan ya jibge masa.Ba'a wani jima da dawowarsa garin kanon ba yayi aurensa,ya aure wata 'yar fillo mai kawo musu fura da nono na sayarwa.
Wasa wasa saida suka kwashi kusan shekaru goma kafin Fatoumata matarsa ta haifi danta na farko wanda aka sanya masa suna 'Rilwanu',alokacin kuwa mahaifinsa mal.falalu ya rasu,sai ya zamana shi ke komai na bangaren kasuwancinsa ayanxu,Rilwan kuwa an sakashi amarantar boko har zuwa matakin diploma,ah inda ya karanci electrical engineering,Shima ya soma sana'ar saye da siyarwa ta kayan wuta ta lantarki,abu har lagos yana zuwa sarowa,daga baya kuma yazo ya koma Lagos da sana'arsa dindindin, acan ya amshi hayar shago,ya shaketa da iri irin kayan electronics,sosai arzikinsa ya bunkasa wanda har ginin wani madaidaicin gida yayi inda da zarar yayi aure zasu zauna anan da iyalinsa,ya sake ginin wani dan karamin gida akusa da nashi,gidan zaman mutum daya ne,wato daki daya ne sai kuma kitchen da bayi awaje,bayan ya komo kano yayi auransa kana ya dauki matarsa Ummi Aisha suka koma can garin Lagos.
Wani abin ikon Allah kuma sai alokacin Fatoumata ta sake haihuwa,wanda har sun cire rai da sake haihuwar don daga ita har Mal.Sani sun soma dan manyanta.aka sanyawa yarinya suna *'Maryama'*,maryam ta taso cikin gata ta kowanni bangare,iyayenta da kuma yayanta wanda ahaife ya haifeta duk suna ji da ita,tana ss1 asecondary mahaifiyarta Fatoumota ta rasu bayan tayi yar karamar jinya.
Mutuwarta ta girgiza tsoho sosai don yana bala'in son matarsa sosai,bayan wani dan lokaci da rasuwarta,Rilwan yazo ya dauke tsoho da Maryam ya maidasu Lagos.Yadda akai Sani tsoho ya ijje sana'arsa ta kayan masarufi Kenan. Acikin gidan da Rilwan ke zaune da matarsa,dama akwai extra dakuna biyu,sai aka baiwa tsoho daya,dayan kuma aka baiwa maryam.alokacin tana ss2 dinta ne sanda suka komo Lagos da zama,shine aka samo mata wata makarantar private mai dan saukin kudi aka sakata da kuma islamiyyar da aka samo mata dake kusa da unguwar.
Maryam yarinyace nutsasstsiya,Sam bata da rawar kai kamar na 'yan matanmu na zamanin nan,babu ruwanta da kowa ne idan ba tsoho da wanta Rilwan ba wanda ya zame mata tamkar uba,tsoho kuma ta maidashi kakanta ba uba kuma ba,Akodayaushe idan har zata makarantar islamiya ko kuma idan an aiketa bata taba fita ba tare da dogon hijab da nikabi ba,haka ma idan har zata boko,tofa tun daga gida take sanyawa,da zarar ta kusa da makarantar kuma sai ta cire ta saka cikin School bag dinta,idan an tashi kuma saita mayar,haka dai take gudanar da rayuwarta cikin tsananin kamun kai da kuma nutsuwa,sai dai wani abu ga Maryam shine,ko kadan bata daukar kaniya,Sam batason rainin wayau,keta,cin fuska da kuma wulaqanci.kawarta daya itace 'Hauwa',kuma unguwarsu daya.ѕнeĸarυn Maryam goma sha bakwai,ayanxu haka tana gaba da rubuta Ssce wa'ec dinta ne
Maryam ta tsani mashaya arayuwarta,k'yamarsu take sosai shiyasa su Hayat basu taba burgeta ba dake su Hayatun ne ke haya awannan karamin gidan nasu.Toh dayake Hayat ma baya shiga sabgar mata shiyasa baima san da zamanta ah unguwar ba,shidai barshi da shaye-shayensa amma babu ruwansa da 'yan mata,roughcoin ne dai dan kwashe kwashe.
Akodayaushe idan yamma ta kunno kai,sai kaga Tsoho ya fita kofar gida da kujerarsa ya zauna akarkashin wata bishiyar mangwaro yana dan shan iska,toh wasu lokuttan idan har Hayat na gida tofa yakan fito waje shan iska don sosai wannan bishiyar ke bada wata irin ni'imtacciyar iska,toh sai su hade da tsoho anan,toh har takai sai kaga su zauna suna hira,har Tsoho yayi ta masa fada kan yabar shaye-shaye,idan har ya amsa masa awurin akan cewa ya daina,tofa kuwa yana barin wajen zai cigaba,Tsoho na son Hayat sosai da sosai,don wasu lokuttan ma tare zuwa masallaci kuma su dawo atare,sai dai Hayat bai taba bashi labarin komai agame da kansa ba,haka ma Tsoho bai taba neman jin wani abu agame dashi ba,nashi kawai yana masu fatar shiriyace.
Bayan saida kayan electronics,Mal.Rilwan na kiwon kaji da kuma tantabaru acikin gidansa,matarsa kuma Ummi Aisha sana'arta itace saƙa,agefe daya kuma tana saida su minerals,kunun aya,zobo,pure water da dai saraunsu,kuma alhamdulillah tana samun kasuwa sosai.Ya'yansu uku kuma duk maza ne.
___________________________________
*°•мυ ĸoмo ĸan laвarι•°*
Mal.Rilwan na fita waje ya soma dube dube yana mai son ganin bakon da Maryam tace yana nemansu Hayat,ai kuwa charaf! Idanuwansa suka sauka kan Faruq wanda ke zaune ya saddar dakai kasa yana tunane-tunane.Sannu ahankali ya taka har xuwa inda yake zaune tare da dan taboshi,adan firgice ya dago kai yana dubansa.
"Yi hakuri na baka tsoro ko?" acewar Mal.Rilwan,murmushi kawai Faruq yayi abinsa,sukai musabaha.
Mal.Rilwan yace"Kaine wanda ke tambaya akansu Hayatu samarin dake zaune acikin wannan gidan?" ya fadi hakan tare da nuni da gidansu Hayatun.
Murmushin takaici Faruq ya saki tare da fesar da wani iska daga bakinsa kana yace"Ta fada muku kenan?amma shine ita bata iya tsayawa ta saurareni ba tayi shigewarta ciki,wannan sam ba dabi'a mai kyau bace.... "
Da sauri Mal.Rilwan ya tari numfashinsa"Gaskiya ne bata kyauta ba kuma nayi mata fada akan hakan,amma kasan dai tambayar da tayi maka ko kadan batayi laifi bako?dole ne tasan alakarka dasu sannan abinda ke tafe dakai kafin ta fada maka komai akansu,don haka da fatar zaka mata k'yakkyawar fahimta da kuma yi mata uzuri akan hakan?"
Sai ayanxu Faruq yaga rashin dacewar daukar zafi da yayi,da gaskiyarta kam dole ne tasan alakarta dashi kafin ta gaya masa wani abin kai tsaye,atake anan kawai yaji yarinyar tayi mugun birgeshi.(Kalubale gareku,wen you first meet a stranger,kuma ya tambayeku abu,karku kuskura ku bashi amsa kai tsaye becuz some are evil,Allah yasa mu dace).
Bayanin kanshi yayi masa azuwan ai shi din dan'uwa ne ga Hayat,kuma yazo ne don tafiya dashi gida,Cike da farin ciki Mal.Rilwan yace"Allahu Akbar! yau Allah ya karbi adduarmu nida tsoho,akullum bakunanmu basa gajiya da rokarwa 'ya'yan nan addu'ar shiriya da kuma komawa gaban wani nasu,musamman ma Hayatu wanda ga dukkan alamu ya nuna rinjayarsa akayi xuwa cikin wannan kazamar rayuwar,bismillah Mal.Faruq shigo muje ciki tsoho ya ganka."
"Assalamu alaykum ya jama'atul muminin.... " Shine abinda Faruq ya furta ah sa'ilin da suka kutsa kai cikin gidan sosai,tsoho ne ya amsa masa don shi kadai ne ke zaune atsakar gida,yau bai fita shan iska ba.Tabarma Mal.Rilwan ya karbo wajen uwargidansa ya shimfida akusa da Tsoho,yace"Bismillah! Mal.Faruq zauna... "
Ya amsa tayinsa ya zauna,suka shiga gaisawa da kyau sosai,shi kuwa Mal.Rilwan yaje ya karbo lemun da Ummi Aysha ke saidawa da kuma ruwa asaman tray ya kawo ma Faruq.Ruwan kawai Faruq ya iya dan tabawa,Mal.Rilwan yayiwa Tsoho bayanin Faruq din da kuma abinda ke tafe dashi.
Shima tsoho kabbara yayi kamar yadda Rilwan yayi,cike da farin ciki Tsoho yace"Alhamdulillah!Alhamdulillah!! Haqiqa bazan iya misalta maka tsananin farin cikin dana shiga ba ayau,wato yau watarana ce da bazan iya mantata ba harna kare rayuwata adoron kasa,Hayatu mutumi na ne sosai,kai na daukeshi ne tamkar dan cikina,tarayyarsa da wannan katon arnen yana min ciwo sosai donna tabbata shine ya rudeshi suka bar gida,sai dai kuma bayan shaye-shaye sam bashi da wani mugun hali don ko budurwa ma ni ban taba ganinsa da ita ba,sallar nan kuwa bata taba wuceshi,wasu lokuttan ma tare muke jerawa muje masallaci,kuma duk inda yake muddin yamma ta kawo kai,ma'ana ana gab da kiran sallar magrib tofa zaka ganshi ah unguwa ya dawo,har gida zai shigo idan bai ganni awaje ba yace tsoho na dawo taso muje masallaci,bayan mun idar kuma kafin ayi kiran sallar isha'i zaka ga ya hau karatun Qur'ani,bazai dakata ba har sai anyi kiran isha'in.Ayau Ina mai Farin ciki da har wani nashi ya nemi inda yake ya kuma taso har yazo nan don tafiya dashi,ubangiji Allah yayi maka albarqa Umaru,Allah yasa ka wanye da duniya lfy.. "
Cikin muryar kuka Faruq yace"Amin amin baba,kuma dalilin barinsa gida shine..... "
Da hanzari Tsoho ya katseshi yace"Kai Umaru kul bana son jin komai,banda tonon silili ka koyi boye sirrin gida,kai bama gida kadai ba,ka koyi boye sirrin wani,Sam babu kyau tone-tone... ". Sai kuma Faruq yaji haushin kansa da abinda yayi niyyar fada ada,subutar baki ce.
Tsoho ya umarci Rilwan daya kirawo masa Maryam tazo ta baiwa Faruq haquri,dakyar ta fito sanye da dogon hijabinta da kuma nikab,ta tsugunna tana baiwa Faruq haquri,acikin nikab dinta kuwa murguda masa baki take tayi,shi kuwa bawan Allah ahankali yace"Tashi kije komai ya wuce,nima don Allah ki yafemin... "
"Bakomai nima komai ya wuce" ta fada tare da mikewa at once tayi gaba.
Adaidai lokacin kuma aka soma kiraye-kirayen sallah,tsoho ya dubi Rilwan yace"Maza Rilwanu tashi ka debo mana ruwa abutoci mu daura alwala kila ma mu hade dashi acan masallaci donna tabbata sun dawo.. "
Da sauri sauri Mal.Rilwan yaje ya debo musu ruwa abutoci ya kawo musu,duk suka daura alwala,jakar Faruq kuwa Mal.Rilwan ne ya karba yakai dakinsa,kana suka fito suka nufi masallaci wanda bashi da wani nesa da gidan.