← Book details    Hibbatullah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 23

Sashe 6

   Hibbatullah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    "Rufemin dirty mouth dinka anan,idan har da gaske din sonta kake tsakaninka da Allah toh ai kamata yayi ka sami Abba mai martaba wanda shine uban rikonta kace masa _*KA GANI KUMA KANA SO*_,don haka amaka kamun kafanta,amma furta mata kai tsaye da kayi sam bai dace ba,kai look daga yau sai yau,ina son ka fita aharkarta kabar yarinya ta maida hankali kan karatu,karka sake ka raba mata hankali gida biyu........ "

    Azuciye Hayat yace"Ban gane yaren wai in fita harkarta ba,ni da qanwata kuma shine ake kokarin yimin iyaka da ita?"

"Toh ai gani nayi kamar baka dauketa kamar qanwartaka ba,tunda har zaka iya tsayawa ka kalli cikin kwayar idanuwanta sannan ka furta mata kalmar 'so' awannan yan kankantar shekarun nata,In banda girman jiki ma da Najmiy take dashi ai tsarar Hidaya ce,Hidayar ma ai tama dan girmeta,don dai kawai ita bata girma ne shiyasa ake ganin kamar Najmiy ce babba,yanzu idan wani yayiwa Hidaya hakan zakaji dadi?I am very pretty sure dat saika kusan ganin bayansa......... "

     "Yayah Prince kalamanka suna nemar wuce limit dinsu..... "

Da sauri Faruq yace"Amma hannuna yafisu sauri..... "😂 (Hayat kabi ahankali kada Faruq din sahiba ya mazgeka anan😁)

     Murmushi Hayat yayi kana yace"Kada ka kuskura ka kaini bango.... "

"Inma na kaika zaka dawo da baya da kanka ne,na dai gaya maka ka fitar ahanyar Najmiy,karka batawa yarinya rayuwa,Najmiy amanar Allah ce agaremu,karka kuskura ka yaudareta da soyayyar k'aryarka Hayatu,ina baka shawara ne don wallahi hannuna yafi kalamaina saurin aiki,na barka lafiya Yarima karami..... "

   Ya juya ya bude kofa yasa kai ya fice fuuuu! Kamar kububuwa,Hayat kuwa wani dunkulen bakin ciki ne ya tokare masa qahon xuciya,meya shiga cikin kwakwalwar dan'uwan nasa ne da har yake jifarsa da zazzafar kalamai haka?Ayau shi Faruq ke yiwa kallon dan'iska kuma mayaudari?har yake ce masa kada ya kuskura ya b'ata rayuwar yarinya?

Tuni hawayen bakin ciki suka soma shatato masa saman kunci don shi harga Allah ne yake son Najmiyya Gaddafi,sonta har cikin jinin jikinsa yake jinsa,shi kawai yayi saurin fad'a mata ne sabida kada wani can daban ya dauke mata hankali.zubewa yayi saman wata two seater tare da dafe kansa da hannayensa bibbiyu,yama rasa tantance abinda ke masa dadi acikin duniyarsa.

   ****
Faruq kuwa yana fita fadar mai martaba ya nufa zuciyarsa ah dagule,yana shiga kuwa ya tarar babu kowa acikin fadar sai dogarai biyu da kuma mai martaba wanda ke hakimce kan kujerar sarautarsa.

   Samun wuri yayi ya zauna tare da rike Kansa da hannayensa bibbiyu,hankalin mai martaba ne ya daga ganin yanayin dan nasa wanda kana gani kasan yana cikin damuwa ne.
   Ahankali yace"Umari meya faru na ganka cikin damuwa?wani abin aka maka acikin gidan?

Dakyar ya iya cewa"A'ah babu abinda aka min" ya fada ba tare da ya kalli inda mai martaba yake ba.

   Murmushi mai martaba yayi kana yace"A'ah Faruq ba haka yanayin d'an nawa yake ba,duk da cewar kai din miskili ne amma kana da faram-faram da mutane,yanxu Umari ashe har akwai ranar da zatazo da har zaka iya boyemin damuwarka ka barwa cikinka kai daya?iyyeh Umari tambayarka nake?"

   Ahankali ya furta"A'ah Abba mai martaba ka gafarceni..... ",Faruq ya dubisu Jabir(dogari)yace"Ku dan bamu wuri jabir zamuyi magana."

Zubewa sukai akasa sukace"Allah ya taimaki Yarima mai jiran gado,agama lafiya..... " suka fice,asannan ne ya juyo ga mahaifin nasa ya kora masa bayani.

Jikin mai martaba ne yayi sanyi qalau,kuma haqiqa zancen yayi mugun girgizashi,duk da cewar shi karan kansa ya dade yana zargin Hayat akan cewar kamar son Najmiy yake sabida irin muguwar sabon da sukayi,amma still bai taba tsammanin cewar irin wannan ranar zata zo ba,shifa tun zuwan Najmiy gidan ya kudurta aransa cewar insha Allahu Faruq zai baiwa aurenta don ya tabbatar da cewar zai rike masa amanarta kuma bazai taba barinta tayi kukan maraici dede da minti daya ba,don Faruq mutum ne mai sanyi hali,haquri da kuma tausayi,uwa-uba kyautatawa,sab'anin Hayat yana da zafi sosai kuma ga saurin fushi,sam bashi da haquri kamar zawo yake,tun yana karaminsa ya taso da wani irin mugun hali,idan har ka masa wani abinda ransa baiso ba toh kuwa saiya rama,haka kuma idan har yana son abu toh kuwa kota halin ƙaƙa ne saiya sameshi,ahalin yanzu kuwa rikici babba ne ke shirin kunno kai cikin royal family din don agaskiya mai martaba baya jin zai iya baiwa Hayat auren Najmiy sabida ko kadan basu dace ba,Najmiy zata cutu sosai idan ta auri Hayat,yana hango mata kukan maraicin da zata sha bayan ta aureshi,shi kuma bazai taba so hakan ta faru ba don Najmiy amanar Allah ce agaresu shiyasa yakeson aurar da ita ga nagartaccen namiji wanda zai kula da ita kamar Faruq.

    Daga murya yayi ya kira sunan Jabir,nan da nan kuwa sai gashi ya iso ya zube akasa"Allah yaja da ran mutumin talakawa gani gareka ya shugabana......  "

      "Maza kuje ku taho min da Yarima Karami,ace masa ina nemansa da gaggawa yanxun nan kuwa..... "

"An gama ranka shi dade...... " ya Mike ya fice don isar da sakon mai martaba.

    _*Tofa my fiful yau ake yinta,wayyo Hayat😭 wallahi harna tausaya maka*_

    *ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕*
      *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*

      {Onward together}
*{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HEART TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINGS 💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔

                      💥

        ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
            *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
              ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️

          *°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*

   *°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαи¢тι¢ ℓσνє💑°*

*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*

        *WATTPAD:HAFNANCY:*

*°ѕα∂αυкαяωα gα Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα*°
____________________________________

                            💥

      *Թɑցҽ 8⃣*

   Najmiy kuwa tana shiga b'angaren Haj.Babba taji wani uban kuka ya taho mata,sam bata lura da Haj.Babba da kuma Haj.karama dake zaune afalo ba,sai kuma ƙuyangun dake durkushe agabansu suna musu hidima,masu firfita sunayi,haka kuma masu tausa nayi.ko lura dasu batayi ba dake makeken falo ne,ta nufi dakin baccinsu da gudu tana 'yar shessheƙa.

   Haj.karama ce ta soma hango bayanta tana wucewa zuwa daki da dan gudu-gudu.Cike da tashin hankali ta dubi Haj.Babba wacce bata masan abinda ke faruwa ba sai aikin baiwa wata ƙuyangi order take dake mata tausa.Tace"Yaya kalli auta can ta shigo da gudu kuma kamar ma kuka take... "
    Agigice Haj.Babba ta dubeta tace"Ina autar take?"

"ta shige daki.. "acewar Haj.Karama

   "maza Maymunerh tashi muje mu dubota nidai Allah yasa lfy dai... " Haj.Babba ta fadi hakan tare da mik'ewa at once,suka sallami kuyangu,kana suka nufi hanyar dakin da Najmiy ta shige da sauri saurinsu.

    ***
Bawan Allah kuwa Hayat yana nan zaune dai inda Faruq ya barshi,zuwa yanzu hawayen ya daina zubo masa,sai saukar da numfashin da yake tayi da karfi,acikin wannan halin ne su Jabir suka shigo suka riskesa,acikinsu babu wanda ma ya lura da yanayin da yake ciki don suna shigowa ko hada idanuwa dashi basuyi ba suka zube ak'asa,kafin Jabir yakai ga magana tuni yaji Hayat yayi saurin katse masa hanxari"Jabir wai sau nawa ne zan gaya muku cewar ku dena zub'e min ak'asa?karfa ku manta dani daku duk daya muke awajen Allah,wanda kawai yafi wani matsayi awajensa shine wanda yafi tsoronsa,kuma ko ba komai ai ni din k'anin bayanka ne na nesa ba kusa bama,don Allah ku daina bana so,pls get up immediately.... "

    Allah sarki!ta inda kuma suke son Hayat kenan,sam bashi da ganin kansa azuwan shi din wani ne,infact yama daukesu kamar yan'uwansa ne.

Jabir yace"Allah ya taimaki jarumin jarumai,amatsayinka na dan sarki ya zama dole kaima mu girmamaka,don haka kayi haquri bazamu iya dainawa ba...... "

   Bai tankashi ba,ya dauki ruwan faron dake gabansa,ya balle marfinta,sai daya furta"Meke tafe daku yakai amintaccen Abba mai martaba?" kafin yakai bottle din bakinsa.

   Jabir yace"Allah yaja da ran Yarima Karami,ga sako zuwa gareka daga mai martaba,yace yana nemarka da gaggawa..... "

     Da sauri ya cire bottle din daga bakinsa,ruwan kuwa ya kwareshi sosai wanda ya janyo masa wani mugun tari har idanuwansa sukai jajawur,duk kuma adalilin tashin hankalin daya shiga ne,hakan na nufin Faruq yakai kararsa ne koko menene?don fitarsa kenan baa wani jima ba sai ga dogarai wai mai martaba na nemarsa da gaggawa kuma yanxun nan.

    Dogarawan kuwa sai sannu suke ta masa ayayin da yake ta aikin gyad'a musu kai alamun amsawarsa kenan.Can ya dubesu cike da faduwar gaba bayan tarin ya sakeshi yace"Jabir kuje gani nan tahowa... "

   "A'ah Yarima karami mai martaba yace kafarmu kafarka. " Gabansa ne ya tsananta faduwa jin furucin Jabir,atake anan ya sake tabbatarwa kansa da cewar lallai kararsa Faruq yakai.

    Mik'ewa yayi ya shige gaba yace"ku muje... " suka take masa baya da sauri sauri.

**
Gabansa ne ya karashe tsinkewa ah sa'ilin da sukayi ido hudu da mai martaba wanda se faman jifarsa yake da wani irin mugun kallo,kana iya cewa ma kashe masa wani Hayatun yayi.Shi kuwa Faruq kansa ya saddar kasa alokacin daya jiyo takun tafiyar Hayat,ko kadan baya son su hada idanuwa.

     "Barka da warhaka Abba mai martaba,sakonka ya riskeni don haka gani gareka Allah dai yasa lafiya.... "

"Ba lafiya ba..... "acewar mai martaba cikin hargowa.Hayat baiyi mamakin jin furucinsa ba don dama can jikinsa ya bashi cewar Faruq ne ya kawo kararsa,watakil k'arya da gaskiya ne ya fad'a masa.

         Mai martaba ya sake cewa"kana jina ko?nace ba lafiya ba,meh ka gayawa Najmiy dazun?"

Murmushin takaici Hayat yayi kana yace"Abba mai martaba cewa nayi ina sonta ko kuwa yanzu ya zama laifi ne mutum yace yana son wani?"

   "Rufemin baki anan mutumin banza da wofi,ita ya kamata ka gayawa hakan ko ni?meyasa baka sameni ka nemi izinin tunkarenta ba ko kuwa zamanka take agidan ne?"
Chapter 6 · 0% Book details