← Book details    Hibbatullah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 23

Sashe 5

   Hibbatullah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   Toh ayanxu dake bakinta ya soma nuna da hausa,sai ta koma k'iran faruq da 'Yaya prince babba',Hayat kuma tace masa 'Yaya prince karami'.shine su Abida suma suka dauka suke kiransu da hakan.ita kuwa Abida da 'Yaya princess babba' take kiranta,ita kuwa Hidaya 'Yaya princess karama', duk kuwa sunayen yayi musu dadi sosai,shine ita kuma suka sanya mata sunan  _*PRINCESS AUTA*_.

     Kowa na qaunar Najmiy sosai don kallo daya ma zakawa yarinyar kaji kawai ta shiga ranka,yarinyace yar shekaru bakwai kacal amma kallo daya zaka mata ka rantse da cewar tayi sha biyu sabida ba laifi akwai girman jiki da kuma property😀.Malamanta biyu ayanxu,da malamin hausa da turanci,sai kuma malamin koyar da ita karatun boko da Mai martaba m.k ya samo mata wato 'lesson teacher',don anaso ta iya wasu abubuwan dakyau kafin asakata amakaranta.malamin dake koyar da ita hausa da turanci,shi din kuma ke koyar dasu duka karatun arabi harsu Faruq.

    Bayan shekara daya kuwa,tuni hausar Najmiy ke fita dakyau kai kace jakar kano ce😀,turancinta shima ba laifi yana tafiya fluenty duk da cewar ba gama kama bakinta yayi ba,amma still tana kokartawa.Tuni aka sakata ah 'Al-amin International school' wanda makarantar dasu Faruq ke zuwa kenan,bayan an mata wasu gwaje-gwaje aka tabbatar da cewar lallai yarinyar akwai ilimi,shine suka bata Jss1 direct,yan'uwanta sunyi murna sosai,hidaya kuwa kuka ta saka wai ya za'ai princess auta ta wuceta ah aji,dake ita yanzu ne take pri5,toh shine mai martaba ya saka aka mata tsallake zuwa Jss1 din dake itama din akwai kwakwalwar daukar karatu irin _my janaf😉_  amma ya sanya aka raba musu aji don kada su hade suta wasa.Faruq shekarunsa ashirin kuma yana final year,Hayat kuwa shekarunsa 18 ah Ss2, Abida kuwa 13 ah Jss3,hidaya kuwa kamar yadda na fada afarko tsarar Najmiy ce.

Akullum idan ta dawo makaranta sai kaga ta hada kan yan'uwanta kamar yadda Akhee dinta ke musu ita da Yumna ukhti dinta,ta shiga koyar dasu abubuwan da aka koyar da ita aranar,su kuwa sai kaga suyi ta biye mata,hatta larabci tana koyar dasu,kuma ba laifi suna dan daukawa.Bayan ta gama dasu sai taje fada wajen Abba mai martaba,don ita dashi Five & six ne,yana mugun ji da ita haka ma yan fadar suna mugun sonta da kuma son sauraren hirarta da mai martaba.

   Ita da Hayat kuwa wani irin muguwar shaquwace ta shiga tsakaninsu,tasu tazo daya,baya abu idan bata,kai ko abincine zaici tare suke ci ah plate daya,sai kaga yace azuba musu abincin ah plate daya da princess auta,karatu ma tare suke bitarsa,Mai martaba ya lura acikin ya'yansa Hayat da kuma Najmiy sunfi bada himma da kuma jajircewa wajen  karatun boko da kuma arabi,shiyasa sukayi wa sauran fintikau acikin xuciyarsa.

    _*°•вayan ѕнeĸarυ нυdυ•°*_

   Bayan shekaru hudu,tuni Faruq ya kusa kammala karatunsa ah dan fodio University sokoto (Udus),ah inda yake karantar 'Political Science' don burinsa shine ace watarana ya zamo dan siyasa,shi kuwa Hayat yanzu yake level 3 dinsa ah federal university of technology minna,ah inda yake karantar 'Chemical engineering ',sabida Najmiy ne kawai yaki zuwa karatu awani gari.suma matan kowacce has been promoted to the next class.Najmiy da Hidaya an zama yan matan ss1,bama kamar Najmiy wacce tayi saurin girma kamar wacce ake baiwa taki kullum.She has become a woman with the full option😀,ga wani uban kyau data k'ara tatsowa,kai abin dai ba'a magana,sai dai kawai ace 'Tubarkallah masha Allah'

    Watarana Hayat da kuma Najmiy na bitar karatunsu ta makarantar boko acikin filin shaqatawar gidan,bayan sun kammala ta masa sallama,harta juya zata tafi sai kawai taji Hayat ya rike mata gefen hijab.

Da sauri ta juyo tana dubansa,idanuwansa sun kada sun koma jajawur dasu,cike da tsoro tace"Yayah prince karami lafiya dai ko?ko wani laifin na maka?"

    Dan murmusawa yayi kana yace"Yes Najmiy kin min laifi don zuciyata kika sace,tun farkon zuwanki nan gidan naji kawai ina jin wani abu agame dake amma ban gane cewar sonki nake ba sai da muka soma samun kusanci da juna,Najmiy nasan cewar ke din yarinyace kankanuwa har yanzu,You are juz 12 amma kina da girman jiki kamar yar 16years,naso boye abin acikin zuciyata har sai nan gaba wanda asannan kin kara wayau,amma I can't,ina tsoron kada wani yayi min shigar sauri shiyasa na gaya miki tun yanzu don kisan dani,wallahi tallahi Hayatudden M.K bahago loveѕ you alot,Najmiy ina sonki matuka,don Allah karki so wani bayan Hayat......... "

   Bai gama maganarsa ba kawai ta fizge hannunta tayi cikin gida jikinta na kyarma,shi kuwa blow yakaiwa iska,kana ya lashe lips dinsa na kasa da harshensa,Faruq kuwa daya dawo hutun makaranta,ashe yana can tsaye yana hangosu daga nisa,hijabinta kawai da Hayat ya rike ne kawai ya tabbatar masa da zarginsa akan Hayat din ayau ya zamo gaskiya.

   Azuciye ya soma takawa zuwa inda Hayat yake da sauri-sauri kamar zai tashi sama,duk inda ya gifta zubewa ake ana kwasar gaisuwa "Allah ya taimaki yarima mai jiran gado."

Shi kuwa Hayat ko kadan bai lura da tahowarsa ba don dukar da kai yayi kasa yana tunano abinda ya gudana ayanxu.Ji yayi Kawai an fizgi hannunsa aka mikar dashi ana jansa.

    Idanuwansa ne suka sauka kan gefen fuskar Faruq wanda ko kallonsa baiyi ba sai jansa kawai yake.

      "Yayah prince meye haka?idan wani laifin na maka ai kamata yayi kamin fada anutse bawai ka fizgi hannuna kana ja haka ba kamar wani dabba,haba wannan cin mutuncin da meh yayi Kama?wani irin shit kega agaban bayi ma?pls get ur filthy hands off me Yaya prince....  "

Ko ci kanka Faruq baice masa ba illa cigaba da jansa da yakeyi da karfi,shi kuma Hayat din na biye dashi da sauri-sauri ayayin da yake zuba masa surutu akunne............. 

    _*тoғa нayaтυ ĸa deвo rυwan daғa ĸanĸa😁*_

*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕*
      https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-1194933670662901/

      *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HEART TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINGS 💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔

                       💥

      ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
        *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
             ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️

      *❄️(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)❄️*

  **ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑**

  *MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*

        *WATTPAD:HAFNANCY*

*°ՏɑժɑմƘɑɾաɑ ցɑ Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα°*
__________________________________

    _*°•wannan ѕнaғιn naĸυ ne мoмy zιl,υммυl мeenal da ĸυмa мaмan ĸнaυѕar,ιna ѕo ĸυ ѕanι cewar нaғnan тana мυĸυ ѕo мaι cιĸe da dυмвιn qaυna❤•°*_

             💥

   *Թɑցҽ 7*
Faruq bai saurarawa Hayat ba har saida ya sadasu da dakin baccinsu,suna shiga ya jefar dashi ayayin da shi kuma ya juya ya sanyawa kofar dakin nasu key.shi kuwa Hayat tangal tangal yayi zai fadi,toh dayake shi din jarumin jarumai ne,sai yayi kokari ya rike kansa.

    Ya juya yana duban wan nasa xuciyarsa na tafarfasa kamar danyar ganda,yace"Wai Yayah prince meye hakan?what's the meaning of all diz bullshits?wani laifi nayi da har yakai girman wannan cin fuskar daka min?iyyeh tambayarka nake...... "

Ji kake tassss! Faruq ya kwasheshi da wani wawan mari wanda har saida yaga wasu shining stars⭐ na blinking.

      "Kayi gaggawan kiyaye harshenka da irin kalaman rainin da kake jifana dasu,that slap was simply a reminder to tell you dat am ur elder one and not ur junior neither ur mate...... "

Murmushi Hayat yayi tare da shafa fuskarsa inda aka watsa masa marin,yace"Wow rana ta farko da Yayah prince ya taba daga hannu ya mari k'aninsa wanda yafi so duk duniya,ban san dalilin wannan rashin mutuncin da kake shirga min ba amma kuma bai kamata hakan takai ga mari ba,anyway am grateful buh seriously the slap was kinda hot Prince Faruq Bahago...... "

   Ya sakar masa wani killer smile amma axuciyarsa shi kadai yasan irin takaicin dake cinsa.Shi kuwa Faruq jikinsa ne yayi sanyi qalau,meyasa yayi hakan?meyasa zai daga hannu ya mari dan'uwansa akan abinda bai tabbatar ba?

Kallon kwayar idanuwan Hayat yayi daya tsura masa ido yana jifarsa da kallo mai cike da ma'anoni iri iri.Duk da hakan kuma yana iya hango true 'love & affection' kwance cikin k'wayar idanuwan Hayatun wanda babu tantama it's for Najmiy Gaddafi.

      "Meye dalilinka na rik'ewa Najmiy hijab dazu sannan kuma meye ka fada mata wanda har ya sanya ta fincike hijabinta tayi cikin gida da gudu?"

Wani irin malalacin dariya ya fashe dashi wanda yafi kuka ciwo,yama maida Faruq wawa wanda hakan ya sake fusata Faruq din.
    "stop laughing like a mad man and answer my question....... "

Wayyo!haqiqa kalmar 'mad man' yayi nasarar soya xuciyar Hayat,amma baice komai ba illa tamke fuska da yayi kamar ba wanda shine ya gama k'yak'yatar dariyar ban haushi ba.

     Yace"Ohh! now I see,was dat the reason why you treated me like a coward in the presence of those servants out there?well na fada tarkon so ne,prince Hayatudden freaking m.k Bahago is inlove with Princess auta Najmiyya Gaddafi.... "
Ya fadi hakan ne with full confidence babu alamun tsoro atattare dashi.

    "Shut the hell up! Hayatudden Bahago,ain't you ashame of urself?kai baka ji kunya ba?yarinya kankanuwa kamar Najmiy wacce ko gama sanin kanta batayi ba itace kake furtawa kalmar so?ta gane meh acikin soyayyar?look,tun ba yau ba na dade da gano take-takenka akanta ta hanyar shisshige mata da kake yawan yi which is earnestly out of bound,amma naki amincewa da zargin da xuciyata take akanka agame da hakan,nace kila kawai ba sonta kake ba,shaquwace kawai ta yan'uwantaka,amma ayau zargina akanka ya tabbata gaskiya,ni ban hanaka sonta ba amma meyasa baka bari harsai ta dan kara girma da wayau ba kafin ka furta mata wannan kalmar?kai infact! Kai dinma har guda nawa kake da harka soma tunanin soyayya in banda iskanci irinta 'ya'yan zamani?You are juz 22 fa Hayat?ko ni da nake da shekaru 24 wallahi yan mata ma basa gabana for now,burina ayanzu na samu na kammala karatuna lafiya qalau,naje service dina,na kuma samu aikin yi kafin na nemi matar aure,donni wlhy babu ruwana da wata yarinya ayanzu tazo ta yaudareni ko ni kuma na yaudareta,arabu ana dibar albarkar juna.......... "

      Hayat ya tari numfashinsa"Wannan kuma kai kakesowa kanka wannan tsarin,da kake jifana da maganganu,toh ni din ba dan'iska bane da nake shirin lalatata ba,nadai furta mata ne don tasan da zamana amatsayin mai sonta kafin wani yayi min shigar sauri harya sami wani gurbi acikin xuciyarta............... "
Chapter 5 · 0% Book details