← Book details Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 22

Sashe 6

Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nuna musu yake yi ba shi da ra'ayin sake aure,don haka su yi haƙuri.

Yau bayan tashinsa daga Office,gidan Hajiyarmu ya nufa, ya samu Alhaji Sunusi wan mahaifinshi,amma ƴaƴa maza suke. Alhajinmu yana jin maganar Alhaji Sanusi sosai, domin yanzu ku san shi kaɗai ne ya rage mishi a maza, cikin dangi. Alhaji Saddiƙ ya zauna suka gaisa,ya juya ya gaida Hajiyarmu, Alhaji Sunusi ya ce wannan zuwan naka ne fa Abubakar, Uncle ya dube shi tare da gyara zama sannan ya ce, to ina jin ka Baba. Alhaji Sunusi ya yi gyaran murya sannan ya ce, maganar Hadiza ce ta kawo ni, Uncle ya dube shi wace Hadiza fa? Alhaji Sunusi ya ce,ai ba ka ma san ta ba? To Hadiza ta gidana, tun lokutan baya na sani kaima ka sani tsayawa ta yi tsayin daka kan cewa kai take so, amma a lokacin kowa yaƙi saboda kai ba a son ra'ayinka ba,to sakamakon haka har izuwa yanzun taƙi kowa ta ce ita dai sai kai, gashi an tashi bikin ƙannanta su Hussaina shi ne muka yanke shawarar aura maka ita kawai.

Uncle ya dubi gefen da Hajiyarmu take zaune,tana ta nazarin littafin ƙawa'idi, ya sani tana jin su sai dai ba zata taɓa magana ba. Sannan duk ƙwaƙwarka ba zaka iya gane me ke fuskarta ba, ma'ana zancan ya yi mata daɗi ko ko akasin hakan, sannan ya dawo da dubansa ga Alhaji Sunusi wanda ya san yanzun nan zasu hau sama su faɗo in dai ya bashi amsar da ke bakinsa, ya ce Alhaji ai ko lokutan baya na san anƙi in auri Hadiza ne saboda matsalar da ke tare dani, ta mutuwar matana, yanzun kuma an yarda ne saboda an ga nayi aure matar bata mutu ba,don haka ni dai a bawa Hadiza haƙuri, ta nemi mijinta kawai."

Alhaji Sunusi ya ce, inji wa ya ce maka don wannan matsalar ne? Mu dai burinmu mu ga Æ´aÆ´anka."

Alhaji Saddiƙ ya ce, "Gaskiya ba ni da ra'ayin mace fiye da biyu, kuyi haƙuri."

Ran Alhaji Sunusi ya soma ɓaci, don haka cikin fusata ya ce, "Abubakar ba wai na zo neman izininka ba ne, umarni na zo baka domin ko mahaifinka ne na bashi umarni baya tsallakewa,in ma mahaifiyarka ce zata zuga ka to ku sani daga kai har ita aure babu fashi."

Uncle ya ce, "Allah ya huci zuciyarka,ba ruwan Hajiyarmu cikin wannan zancan, Hajiya da ke jin su ta rufe littafin hannunta, sannan ta dubi wan mijin nata ta ce, Yaya Allah yasa alkhairi, kuma yasa muna da rai za'ayi." Jin haka yasa gaban Alhaji Saddiƙ ya faɗi, ya sani zancan ya tabbata tunda Hajiyarmu ta amince, Alhaji Sunusi ya miƙe yana cewa, "Duk yanda muka yi zaku ji gurin Alhajin gidan nan." Ya tafi.

Shiru Alhaji Saddiƙ ya yi,yana kallon ƙasa,shi da yake tunanin lokaci ya kusa da zai daidaita tsakanin shi da A'isha,don yin zaman aure cikakke, sannan sai kuma a kawo mishi batun wani auran? Shi fa ya sani ya so ya auri Hadiza a lokacin yana cikin tsananin son haihuwa, amma yanzun sam babu Hadiza a ranshi, duk da ko can da ɗin ma ba itace ta ƙi shi ba, dangin mahaifinshi ne suka ƙi, musamman Hajiya Lanti da Alhaji Sunusi mahaifanta yanzun kuwa ya sani ganin daɗewar A'isha a gidanshi ne yasa su amincewa.

Hajiyarmu ta katse shi da cewa,ka ci gaba da addu'a,zamu taya ka. Ka zama mai biyayya sannan ka shiga shirin bikin,to kurum ita ce kalmar da ta fito bakinshi, ya miƙe tare da cewa,ni zan ƙarasa gida. Duk ƴan ƙwanakin yana cikin damuwa.

A'isha tana school, Hajiya Jummai kuwa damuwarta ta sha ƙarfin tashi,don haka ita bata ma kula da me yake ciki ba, ganin haka yasa yau ya shiga har cikin ɗakinta tana ta waya ne da Hajiya Kari,kan cinikin wani gidan ta wanda shi ne kurum ya rage mata. Saboda tsabar ba ta cikin natsuwa sam bata ma san ya shigo ba, sai da suka gama sannan ta gan shi ta ɗan razana don ta san yaji me suke zantawa.

Ya zauna kusa da ita, ya maida hankalinshi kanta cikin sanyin murya, ya ce "Jummai wai menene matsalarki? Me ke damun ƙwaƙwalwarki? Ta dube shi da idanunta da suka yi jajir duk kwanakin nan haka yake ganinsu, ta ce ba komai me ka gani? Ya ce,haba Jummai, duk wanda ke gidan nan ya san kina cikin matsala, ta ce ni dai bana cikin wata matsala, ya ce to shikenan, yanzun menene dalilin ki na saida gida? Ta ce, matsala gare ni, kuma na san in na ce ka bani ba bani zakayi ba,don haka gara na saida ƙadarata, ya ce wacce irin matsala ce? Ta yi shiru tana son ta tuno me zata ce?.

Ya sake tambayarta, ta ce,zan je ne in dama dai wani likita zan gani a Indiya, saboda matsalar haihuwata,don naga wata mai irin matsalata kuma ta haihu,na gane in na ce zan tambaye ka ba yarda zaka yi ba cewa zaka yi ina ne ba mu je ba ance ba zan haihu ba."

Ya dube ta cike da zargi, sannan ya ce, "Ki bari zan shirya muje tare." Ta ɗan zaro idanu,ni dai ka bar shi kawai inje ni kaɗai, tunda kaga kai baka da wata matsala." Ya miƙe yana cewa, "Jummai waɗannan sabbin halayen da ki ka ɗauka sam ba zan ɗauke su ba, tunda ki ka bar gidan nan har ƙwana biyu ba ki gidan danginki ba ki gidan nawa, zuciyata ta soma zargin kin canza layi.....

#####
[12/11, 17:18] Ummi Tandama😇: *📗📗Page 5*

Sakamakon yawo da kawayan banza,to ba za kije ba,kuma kada inji kin saida wannan gidan,ta ce ai ba gidanka ba ne,ya ce to shikenan. Amma ki sani halayanki sun gundure ni,baki zaman gida ke ba ma'aikaciyar gwamnati ba,kullum sai shegen yawo,ni kaina yaushe rabon da ki shigo dakina? Koda kin zo baki iya tsinana min komai,sai dai ki min jungum kina tunani,don haka ni ba karfe ba ne ina da bukatar kulawa. Aisha tana makaranta,ke kuma baki da lokacina."

Ta dube shi a hasale,to ka dauki mataki mana." Ya fita yana fadin "shikenan."

Gidan su Hadiza ya nufa yau,saboda yana son bin umarni,sannan Hajiya Jummai ta bashi haushi. Daga waje ya tsaya ya aika kiranta. Hajiya Lanti ta ce,maza a bude mishi kofar falo ya shiga. Hadiza kuwa murna tamkar me,don tana bala'in son shi,ba wata hira sukayi ba. Bayan gaisuwa ya ce,mata shi fa yazo ba ta hakuri ne,da zata daure ta nemi miji. Nan ta soma kuka tare da rokonshi,ya ce mata shi kenan sai dai fa ta san yana da mata har biyu,kuma suna zaman lafiya don haka kada ta yi kokarin rusa mishi tsarin gida. Ta ce,in Allah ya so ba wannan. Nan dai suka yi sallama ya tafi.

Tun daga ranar bai sake zuwa ba,sai dai ya kan kira ta a waya. Kafin wani lokaci labari ya watsu cikin dangi,Nafisa da bata so ba,don gaskiya tana ganin za'a kwari Aisha ne,tunda duk cikinsu ita ce karamar yarinya,haka ma su Aunty Fatima suke cewa.

Shi ko da ya tuno cewa bai sanar da iyalanshi ba,duk sai ya damu,musamman Hajiya Jummai,yanda ta daga hankalinta lokacin auren shi da Aisha,amma don Aisha yasan ba zata damu ba,tunda ita yarinya ce sannan ba ya tunanin ta ma san mene ne ma auren,don haka bai damu ba. Sai dai yana tunanin ya ya zai tunkari iyayanta da batun auren shi? Ko me Friend zai kawo a ranshi in ya ji batun auran? Kullum ya kan yiwa kanshi wannan tambayar.

Hajiya Kari ce ta jiyo zancan auran a gari,jin wannan labarin daga gidan mitin din su na gungun mata aiko gidanta ba taje ba,gurin Hajiya Jummai ta nufo,ta same ta zaune tana aikin gyaran kumbunanta. Hajiya Kari ta ce,ke Aminiya,dama wata ta taso shine baki sanar da ni ba?" Hajiya Jummai ta ce "Um zo zauna dama ina nemanki." Kari ta ce, kice muna kukan targade sai kuma ga karaya ta samu? Hajiya jummai ba tare da damuwa ba a zatonta fa zancan hana zuwa Indiya ne sai ta ce ai kan batun nike neman ki wai ni zan yi mishi dabara,sai kuma na rufta.Ya hana tafiya yanzun ya ya ki ke ganin zamu yi? Hajiya Kari ta ce,ke da Allah can,ba wannan zancan nake miki ba, ina miki zancan auren shi, ashe aure zai ƙara? Hajiya Jummai ta yi mutuwar tsohuwa a zaune, kusan minti biyar Hajiya Kari ta girgiza ta sannan ta ce, "Aminiyata me ki ke tunani ne haka?" Hajiya Jummai ta ma rasa ta cewa, zufa ce kurum take keto mata, duk kuwa da (AC) da ke ɗakin.

Can ta ce, "ko dai ba kiji dai-dai ba Karima?" Hajiya Kari ta ce, "Ki dai bincika." Ta suri jakarta tare da cewa, sai naji wayarki,don jin gaskiyar lamarin." Ta fita ta bar Aminiyarta cikin hawan jini.

Inda Hajiya Karima ta bar Hajiya Jummai,tana nan a gurin, har ƙarfe tara na dare. Ta rasa wane irin tunani ma zata yi? Wayarta ce ta shiga ruri, ashe maigidan ne cikin ƙarfin hali ta miƙe. Ta same shi da laptop yana harkokinshi,ta shigo ta zauna, jikinta ba laka, ya dube ta.

"Jummai ba ki jin daÉ—i ne?"

Ta ce, "shi ne dalilin kirana don ka san ko ina jin daÉ—i ko bana ji?"

Ya ce, "A'a." Ta ce "To yi maganar ka." Ya ce, "To dama kan batun aure ne da aka bani, cikin cijewa ya yi maganar, ya ci gaba su Baba Alhaji Sunusi ne suka ba ni mata," zaraf ta miƙe kana nufin Hadiza? Ya ce, ita, tayi wani guntun murmushi, sannan ta ce, "Allah ya bada Sa'a." Ta fita ya bita da kallo ya san gatse ta yi da ta ce Allah ya bada Sa'a.

Ya lumshe idanu, ya gama da nan sauran A'isha, duk da ba ya jin ta yasan ita ba zata ce komai ba.
Chapter 6 · 0% Book details