← Book details Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 22

Sashe 13

Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nafisa ta iso da abinci,ya ce wa zai ci? Tayi turus kai mana Bros ya ce ni kam sai kuma nan da tara na dare. Na riga na ci na rana. Yanzun Beby ta fito mu wuce gida. Bayan sun fito, Nafisa ta ce to telan fa bai san measurement ɗin ki ba, A'isha ta ce,zan aika da kayana sai ya yi min girman su, masu ƙyau inji Uncle. Nafisa ta ce kada kaji komai Bros, bayan sun shiga mota ta miƙo ma A'isha tsarabar da ta bata, tare da ki fa yi amfani da shi yanda na miki bayani, A'isha ta ce to na gode,sai mun yi waya.

Bayan Jabir ya ɗauki hanya ne sannan Uncle ke cewa, tsarabar me ki ka samo Beby? Ya kai hannu gurin ledar, kawo in gani. Ta yi saurin ɓoye ledar ba fa wani abu ba ne,ya yi ɗan murmushi tare da cewa, "Mata ba ku rabuwa da tarkace."

Tun fitar su A'isha, Suwaiba da safiya suka shiga gurin Jummai,suna bata labarin abinda A'isha da maigidan sukayi har ma da ƙarin gishiri,wai ya rataya jakarta. Jummai ta ce jaka fa ku ka ce? Suka ce jaka mana, kuma ta ratayawa ko kunya da girmanshi da komai,tsaki ta ja ni ku daina gaya min tunda ku baku da fus cikin gidan,ba ƙwa taimakaman da komai. Safiya ta ce in mun yunƙura zamu daki banza sai ki ce a'a," ta ce Allah wadaran halinku tunda ba ku da wata dabara sai ta duka,ku fitar min daga ɗaki, ance muku yanzu ana ya yin duka ne? Sai dai na ƙarƙashin ƙasa. Suwaiba ta ce to ba sai ki nuna mana yanda zamuyi ba? Ta ce,ai yanzun duk zamanku tare da ni ba ku ɗauki wani darasi ba? Allah wadaran zamanku tare dani, ta miƙe ta nufi toilet tana masifa,shegu kun iya yawon bin ƙana nan yara suna rarake ku, amma baku iya sanin yanda za ku zauna da mutane ba, yanda za ku ƙuntata ma yarinya, ya gagare ku.

Ranar dai haka ta yini cikin ƙuncin zuciya, gefen Hadiza yau kam a cike da A'isha ta yini ga takaicin jiya,nata ganin ya danne mata haƙƙinta, sannan yau ba girkin A'isha ba, amma ya fita da ita don itama tana kallonsu ta window ɗinta, nata ganin ya fi son Aisha. Ƙaramar yarinya tana juya shi son ranta,don haka koda lokacin ƙwanciya ya yi,ya yi sallama da sauran matan nashi ya shige ɗakinshi ba tare da ya shiga gurin Hadiza ba,don ta san ita ce dashi,ƙin zuwa ta yi, dole tana fushi, shima bai neme ta ba, kuma ko washegari bai leƙa inda take ba,hakan ya ƙona zuciyarta.

Ranar Alhamis suka sauka Jigawa,niƙi-niƙi da tsaraba,ga kuma gudunmawa. Aisha ta tattala dubu biyar ɗinta zata bada, sai kuma ta ji Umma da Abba suna mata godiya,wai Uncle ɗin ta ya bada dubu hamsin, talatin nata, ishirin na shi. Tun ranar A'isha suka wuce Gumel, ita da Umma,su Abba sai gobe in sun zo ɗaurin aure. Inna Rabi ta ji daɗi sosai da wannan gudunmawa,nan A'isha ta zama tauraruwa gidan bikin kowa sai birge shi ta ke yi.

Washegari ana gama ɗaurin aure Uncle ya yi mata waya cewa ta leƙo suyi sallama shi zai wuce, lokacin suna cikin gidan maƙota, tare da su Naja da ƙawayanta. Nan ta fito ta same shi cikin mota,ta shiga ta zauna ya rufe. Sannan ya ce Beby ƙwana nawa za kiyi? Ta ce, duk sanda ka ce Uncle zan shirya in jira ka. Ya ce, to zamu yi waya? Ta ɗaga kai alamar eh,ya sa tafukan hannunshi biyu ya ɗago fuskarta. Kallo ɗaya ta mishi ta lumshe idanunta,tana jin nauyinshi. Cak numfashinta ya tsaya lokacin da taji saukar leɓunanshi kan nata leɓunan ƙamshin turaranshi ne ya doki hancinta.

A hankali ta buɗe idanunta,na shi idanun a lumshe ƙyakƙawar fuskarshi irin ta fulanin Katsina KT cike da annuri. Ba zato shima ya buɗe nashi idanun zata rufe nata, da idanu ya yi mata alamar kada ta rufe. Suka zuba ma juna ido, Kasa jurewa ya yi ya jawo ta zuwa jikinshi, sannan ta yi ajiyar zuciya tare da runtse idanunta sakamakon jinta cikin wani yanayi, muryarshi a sarƙe ya ce Beby yaushe zan zo in tafi da ke zanyi kewarki da yawa. Ta ja numfashi muryarta ƙasa-ƙasa ta ce,nace duk randa ka zo. Ya ɗagota tare da cewa shi kenan sai nazo kanta yana ƙasa don kunya ta ce, to . Ya ɗauki kuɗi daga gaban motar ya ce gashi,ta dube shi ka fa bani kuɗi jiya, ya ce ki ƙara Bebyna, sai mun yi waya? Ta ce,eh ya kuma kama tafin hannunta ya sumbaci tsakiya,tsigar jikinta ta yi yar,ta kalleshi, sannan ta fita daga motar. Ta koma ciki bayan ta ɗaga mishi hannu alamun bye-bye.

Kano ya ƙwana,sannan washegari ya nufo K.T lokacin da ya shigo gidan tsit, wannan lamarin yana taɓa zuciyarshi, kullum ya shigo gida tamkar ya shigo maƙabarta. Ya buɗe ɗakinshi ya shige kan kujera ya zube, sannan ya jingina da bayan kujerar,kai wannan abu yana damun ƙwanyar shi, duk gidan abokanshi in sun shiga,ya kan ji hayaniya sa'an nan ƴaƴan su kan shigo suna oyoyo, saɓanin gidanshi kullum shiru mata biyu a ciki amma ko T.V da wuya, ya shigo ya taras an kunna kowace tana ɗaki tana ƙwance, ya ja tsaki shi yasa in A'isha tana makaranta ko son tuno gida ba ya yi,ita kaɗai ce wadda in ya kalleta ya ke jin annuri.

Ta tare shi da ruwa mai sanyi ko zoɓon nan nata mai daɗi, ya kai hannu kan leɓunanshi yana son tuno yanda ya ji lokacin da leɓunanshi suka mannu da nata,ya sauke ajiyar zuciya, sannan yasa hannu cikin aljihu ya ciro wayarshi. Layin A'isha ya nemo lokacin tana shafa mai,ta fito wanka, tana cikin ɗakin inna Rabi, cikin uwar ɗakanta, da sauri ta ɗaga wayar.

Ta ce, "Assalamu alaikum! Uncle ina ta neman layinka network ya ƙi shiga, ya yi ɗan murmushi gani na sauka gida yanzun nan, ta ce ina ka ƙwana? Ya ce Kano mana,ta ce ka sauka lafiya?" Lafiya lau Bebyna,ki kula min da kanki. Tayi murmushi,nima haka. Ya ce ke ma me?" Ta ce, yanda ka ce,ya yi ƴar dariya, zanyi yanda ki ka ce,kafin ki dawo ki cigaba da kula dani...

#######
[12/14, 07:15] Ummi Tandama😇: *📗📗 Page 10*

Ta ce na manta kana da wasu masu kula da kai É—in har su biyu, ya ce "ai Beby yanda kowa ke kula dani daban, sannan in muna tare da ke ki ringa ji a zuciyarki ba kowa cikin duniyar nan daga ni sai ke,kin ji ko?" Ta ce to Uncle, ya ce yauwa Bebyna, bari na watsa ruwa, ta ce to. Suka yi sallama.

Ya yi shiru, ya kula A'isha tana matuƙar son shi, kunya ce kurum ke ɗawainiya da ita, shi yasa shima yake jin nauyin yi mata wasu abubuwan, amma yanzu ya san ya ɗauko gangarar cimma burinshi.

Bayan ya yi wanka ya fito zuwa (Dinning table) bayan ya yi wa Uche waya kan cewa ya kawo mishi abinci, ya dubi Uche ba kowa a gidan ne? Uche ya ce Madam ta fita, amma bai ga fitar amarya ba. Zuciyarshi ta tafi ga tunanin yaushe rabon da ya samu kulawa daga Jummai? Ba zai iya tunawa ba, domin tun lokacin da ya zo mata da labarin auranshi da A'isha, ta canza har yau bai gane kanta ba. A fili ya ce, "Allah ka shirya wannan baiwa taka." Yana rufe baki tana shigowa,ta nufo shi "ka dawo ne? Wallahi nima na je gida ne na duba Innarmu." Idanu kurum ya zuba mata.

Ta ja kujera ta zauna,ba ka yarda ba ko? Ta soma magana cikin karya murya, irin ta wanda ke cikin damuwa ɗinnan, ta ce ni yanzun ai ko zan haɗiyi Alƙur'ani ka daina yarda da magana ta, duk abinda na faɗa ƙarya ka ke ɗauka, tun da ka samu yara masu jini a jika, ni ko na tsufa."

Ya ajiye cokalin hannunshi.

"Jummai don Allah ki zauna ki yi tunani, irin yanda ki ke tafiyar da gidan nan matsayinki na uwargida ya dace? Ni kaina yanda ki kayi watsi da duk lamurana,ki ka kama ƙawayan bariki masu kai mutum ga halaka,yawo tamkar an yi miki ƙauri da kan kare. Da na miki magana sai ki kawo duk maganar da ta zo bakinki ki caɓa min." Ya nuna tebur ɗin gabanshi "Look at, yanzu tafiya fa na dawo ku biyu cikin gida amma sai kuku shi ne mai kawo min abinda zan ci, shima ɗin sai da na roƙa. A ce kamar ni bani da wata ƙima cikin gidana?"

Ta ce, "To kai ne ai duk ka canza min, yanzu A'isha ce a gabanka." Ya ce,"Ita ce take ganin girmana, amma fa duk wanda na kawo na ajiye ai so ne ya kawo haka ba wai ƙi ba. Ni dukkanku ina sonku,ki kula da wani abu A'isha, yarinya ce kuma ba mazauniya ba ce,ku ko kullum muna tare da ku, amma duk da haka sai ƙorafinku ya tsaya a kanta? Kun yi mata adalci kenan? Shiru Jummai ta yi, amma a zuciyarta faɗi take yi, adalcin banza,za ku gane kuskuranku. A fili kuwa sai ta ce, to shikenan, kayi haƙuri yanzu me kake so inyi? Cike da jin daɗi ya ce, ina so ne ki canza ki koma Jumman da na sani da, kici gaba da kula da ni tare da yin riƙo da muƙaminki na uwargida sarautar mata, kada ki yarda ki yi watsi da shi, wata ta samu. A'isha ki ɗauke ta ƙanwa, bata da raini zata girmamaki, ta kuma sunkuyar da kai tare da cewa , insha Allahu zan yi yadda ka ce." Ya ce, "To na gode, sai batun yarannan su Suwaiba ya kamata su fito da miji ko ya ya ki ka gani?".
Chapter 13 · 0% Book details