Sashe 4
Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shi ko suna can suna shan hirarsu da Abba, goma dai-dai sun gama kallon labaran ƙasa. Abba ya miƙe tare da bashi hannu gami da cewa friend mu ƙwana lafiya,bari na turo maka A'ishan, wani iri Uncle ya ji, ya ce a'a friend ka barta ta kwana gurin Ummanta, Abba dai bai ce ƙala ba, ya wuce yana shiga ɗakin Umman ya same ta ƙwance, Umma kuma tana ƙoƙarin shiga wanka, ya ce Ummansu ya ya zaki riƙe ƙawallin ta ki ki hana ta zuwa gurin mijinta?" Ta ce,ka ganta nan ba yanda ban yi ba,ta tafi ta ƙi wai zasu yi waya, gashi nan har ta yi bacci, ya ce A'isha! A'isha ta ce,Umm, cikin yanayi na bacci ya ce ke tashi maza mijinki yana kira,ta zuro ƙafafunta ƙasa sannan ta ce wash Allah na, duk gajiyar hanya ta isheni,ta fita ta nufi ɗakin baƙi,shi Jabiru yana can gurin Yaya Abdulrahman, ta ƙwan-ƙwasa ƙofa tuni shi Uncle lokacin ma ya kulle ƙofa yana saka kayan bacci duk jin shi yake a takure shi yasa ya so ya sauka a Hotel amma Abba ya ƙi shi nauyinsu yake ji ya zo ya buɗe ƙofar ya ce a'a Beby ba kiyi bacci ba? Cikin yanayin shagwaɓa ta ce, "To ba kaine kasa Abba ya tasoni ba,?" Ya ce muje in rakaki ki koma, har bakin ƙofar ya rakata. Koda ace yana ƙwana da ita to ai ya haƙura a gidan su komai fitinar shi ya shafi kumatunta sai da safe Bebyna,ta ce to mu ƙwana lafiya.
Ɗakin Ummanta ta shige ta haye gado sai da Umma ta fito bayi ta ganta ƙwance ta ce, a'a dawowa kika kuma yi? A'isha ta ce don Allah Umma ki bar ni Allah kuwa shine ya ce ba kirana yake yi ba,in zo in ƙwanta, Umma ta ce to ai shi kenan.
Su Hajiya Jummai,ƴan Nijar tunda take bata taɓa shan wahala irin ta yau ba. Musamman da yake motar haya suka bi, amma ita wannan baya gabanta,tata damuwar bata wuce su isa yau lardi ba, inda zasu samu bokan da aka yo musu ƙwatance,tata damuwar kenan. Sai guraran goma saura suka shiga ƙauyan. Yanda aka ƙwatanta musu haka suka bi. Sun iso gidan bokan wanda yake gida ne na kara,an sauke su da hura. Bokan Bororo ne, irin masu kitson nan haka ma matarshi sam baya jin Hausa don haka dole su ƙwana a nan kamar yanda ya ƙwatanta musu,in gari ya waye za'a samu wanda zai musu tafin ta,sai dai daga Jumman har Karimar sun ƙwana ne cikin ƙyan-ƙyamin gidan da komai ma,don ma sun riƙe ruwa, can hantsi ya ɗaga me yin tafinta,ya zo nan suka sanar da shi buƙatar su, Jummai ta ce tazo ne saboda tana son a kashe kishiyarta, sannan ta ringa juya mijinta yanda taga dama, sannan tana son in da hali ta haihu, bayan mai tafinta ya sanar da shi komai sai ya tambayi sunan kishiyar da mijin,nan ta sanar da shi, bayan ya zuba tsafin ya kuma zubawa, ya ce kafin wannan ta kashe wasu rayukan ko? Mai tafinta ya tambaye ta, bata ji shakka ba,ta ce ƙwarai,ya girgiza kai sannan ya ce, to aikinta yana da matuƙar wahala,don ita wannan ta sha banban da sauran tana da kariya sosai, sannan yaga wasu abubuwa da take yawan kira tana samun tsaro daga abin bautarta. Sannan koda yarinyar zata mutu to fa ba ƙwana kusa ba,don tana da tsawon rai. Koda aka mata bayanin ta hau zufa ta ce ka gaya masa in ma batun kuɗi ne kada ya damu,in har za'a kashe min ita ko nawa ne zan bada, kace da shi tun daga Katsina fa muke don munji labarin aikinshi yana ci tamkar yankan wuƙa. Kada ya nuna kasawar shi mana, inji Karima. Jin haka sai ya ce shikenan. Nan ya shiga haɗa musu kalolin nashi surkullen, sai da suka sake ƙwana sannan suka kamo hanya.
Shiko Uncle duk jin shi ya yi takure, shi yasa gari yana wayewa ya ce to fa shi zai yi haramar komawa,in an yi kwanaki zai dawo kafin hutunsu ya ƙare, da ƙyar Abba ya yarda, don cewa ya yi su juya tare ai an gaisa, lokacin da ta je ɗakin don suyi sallama,tuni ya gama shiri,yana shafa turare.
Cike da murna ta shiga tana cewa, Uncle wai zaka tafi? Ya ce "Eh, Beby shi ne ki ke murna? Don zan tafi ko?" Ta ɗan canza fuska zuwa yanayi na tausayi, ta ce "Ayya, Uncle ba wai don zaka tafi ba ne,naga ba mu yi zaka barni ba ne" Ya ce "Naga ya dace ki ɗan yi ƙwana biyu ne,zan yi kewarki da zoɓonki da ruwan da ki ke bani kullum." Ta yi ƴar dariya, "Nima ai zan damu da rashin ganinka." Cikin mamaki ya ce, "Don Allah da gaske ne za ki damu da rashin ganina?" Ta rufe fuska, ya kama hannunta yana murzawa, zan rinƙa kiranki ko yaushe kin ji? Ta ce to Uncle,yasa hannu cikin aljihu ya ciro kuɗi dami ya miƙa mata gashi saboda kashewa. Ta zaro idanu,haba Uncle, sun yi yawa gaskiya ba zan amsa ba,ya ce riƙe in zaki dawo sai ki sayi me kika ce sunan? Corry ɗin nan? Ta ce Amrif an fi samun shi a Kano ne, ya ce to in zamu koma in nazo sai mu tsaya mu siya. Ta ce, "To." Ya ce,in kin dawo ke ce zaki cigaba da min girki, kafin hutunku ya ƙare,ki fa koyo wasu ina son irin su ɗanwake,waina,burabisko,dambu kin dai ga ne,abincinmu na gargajiya ko? Ta ce "Eh,ai dama fa duk fa na iya su, yasa tafukan hannunshi ya riƙe kumatunta,ki kula da kanki,kin ji Bebyna? Ta ce, to sai naji wayar ko? Ya ce, to Bebyna ya shiga ya yi sallama da Umma tana ta godiya, Abba da A'isha zuwa su Abdulrahman da su Jafar sun yi mishi rakiya har mota. Jabir ya ja mota suka yi gaba,ga mamakin A'isha sai ta ji wani irin kewar Uncle cikin zuciyarta, ta ce Allah ya sauke mata da Uncle ɗinta lafiya. Lokacin da Alhaji Saddiƙ ya iso gida yamma ta yi kis,don ma basu tsattsaya a hanya ba, rashin samun Jummai a gidan ya yi mugun ɓata mishi rai,shi dai wannan ɗabi'a me yaƙi da addini,da matan zamanin suka ɗauka tana ɓata mishi rai, ace mace ba zata nemi iznin miji ba,in zata fita saboda rashin sanin hukuncin musulunci,ko a waya ba zata kira ta nemi izini ba,ya samu su Suwaiba sun cika gidan da kiɗa tare da ƙawayansu,sun sha wanduna suna ta rawa ga ƙwalaban totolyn emzolyn nan zube a ƙasa, ranshi ya ƙara ɓaci ya shiga ya tarwatsa su tare da yi musu tatas. Ya ce, ina Jumman da ta ɗaure muku gindi? Cikin maye Sofy ta ce,ta yi tafiya tun jiya, al'ajabi ya cika shi,ya nufi ɗakinshi ranshi yana matuƙar zafi. Ya zauna bakin gado ya soma kiran layin ta, ga mamakin shi tama ƙi tafiya,a ƙarshe ma sai aka ce a kashe layin yake.
Wasa-wasa har wayewar garin ba ta babu labarin ta, kazalika ci gaba da neman layinta ko zai samu,shiru kai daga baya sai ya soma tunanin ko dai ta ɗan fita unguwa ne, ta samu matsala ko mota ta kaɗe ta haka? Yin wannan tunanin ya saka shi kiran danginsu, har da nata wato makusantanta,yana sanar dasu rashin ganinta tun jiya. Ya san ba nisa tayi ba,don ba ta fita da mota ba, kuma bata saba tafiyar ƙwana ba ma in dai ba ƙasar ta bari ba, komai dangatakar ku da ita ba zata taɓa zuwa ta ƙwana don zumunci ba,nata ganin ƙasƙanci ne ta ƙwana gidan da suka fi su kuɗi, amma gata can ai ta ƙwana a bukka,nan fa hankula suka tashi.aka shiga neman asibitoci,ranar basu iso ba sai daf da magriba,kai tsaye gida kowacce ta nufa, lokacin da ta iso gidan yana cike da dangi shi kuma yana daga harabar gidan in da wani ɗan sandan ciki yake neman ƙarin bayani daga bakinshi.
Sai kurum gata ta shigo, ganin maigidan yasa ta ji faÉ—uwar gaba,don sam ba tayi zaton zai riga ta dawowa ba, amma da yake tana zaton yau ya dawo,tun da haka suka yi dashi, sai ta isa gurinshi tana cewa "Sannu da zuwa Alhaji, har ka iso? Na É—an fita ne" bai iya ce mata komai ba, sai dai ya dubi wannan (C.I.D) É—in ya ce shi kenan ma gata nan ta dawo.
Suka yi sallama ya tafi, shi ko ƙin shiga ma gidan ya yi,yana tsaye cike da mamakin baƙin halayen da Jummai ta zo mishi da su yanzun yi,abin har ya kai ta da yin ƙwanaki. To ina taje? Ya na nan har aka kira sallah, ya shige masallaci, ita ko tana shiga cikin gidan ta same shi cike da dangi ana ta jaje. Turus ta ja ta tsaya, tana son sanin wanene ya mutu? Shin ko dai A'isha ce har ta mutu kafin ma ta dawo? Ta yi amfani da maganin? Kai in ko haka ne lallai zata sake komawa ta mishi sabon biya,don ya cancanta,haba shiyasa taga Alhaji a waje babu fara'a,ya ma kasa amsa ta,ta dubi jama'a sannan ta ce, "Haɗarin mota ne?" Nan kuma sai taji sun ɗauki salati, suna tambayarta a ina abin ya faru? Sai kuma ta yi sororo tare da cewa,wai dama me ya tara su haka? Nan suka shaida mata labarin ɓatanta,nan fa ta hau masifar cewa inji uban wa? Ita da taje biki? Shi ne za'a ce wani ta ɓata? Wata Yarsu ta ce, to mu dai maigidan ki ne ya yi waya tun jiya kuma sai nemanki ake yi cigiya gidajen radiyo da na talabijin. Ta ja tsaki, "To ni biki naje, shima bayanan ne kuma na kira shi a waya ban samu ba." Nan dai kowa ya tashi yana Allah to ya kiyaye gaba, gaskiya ta ji haushi don duk tasa ma ranta cewa A'isha ce ta mutu.