← Book details Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 22

Sashe 12

Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A'isha ta fito tana kulle ɗakinta a ƙasa kuwa kusa da ita,jakarta ce baƙa da kuma ledarta mai ɗauke da kayan da zata kai ɗinki, Uncle ya fito ya yi ƙyau cikin suit baƙaƙe tamkar matashin saurayi,daga ɗakin Hajiya Jummai ya fito ya kalleta da murmushi,ta sunkuyar da kai shi Uncle ba ya irin kunya ne? Ta raya a zuciyarta,ya shiga gurin Hadiza ya ce mata,ya tafi. Tana ƙwance kan gadonta ko kallonshi batayi ba, ita dole tana fushi an ci amanarta, shi kam bai saurari amsarta ba,ya fita abinshi.

A'isha ta duƙa ta ɗauki jakarta, ya iso shi kuma ya ɗauki ledar tayi saurin dubanshi gami da zaro idanu,ya ce muje,ta ce to kawo ledar. Ya ce zan riƙe miki ne ta girgiza kai,don Allah kawo na riƙe Uncle ba girmanka ba ne. Ya matso kusa da ita saitin kunnanta ya raɗa mata inji wa ya ce ba girmana ba ne? Ko ke kanki ba sai in ɗau abina ba,ta ce haba dai? Ya ce to bari ki gani,ya kai hannu ta ja baya tare da cewa,ana fa kallonka,ya ce na san su Suwaiba a gurin sai naƙi wasa da Bebyna? Ta ce to muje, suka jera yana riƙe da ledar, suna fitowa nan ma'aikatan tun daga kan mai ba fulawa ruwa zuwa direbobin sun zo don su amshi ledar amma duk ya hana su, sai dai jakarshi ta Ofis ce ya ba Jabiru.

A'isha ko hakan ya yi matuƙar bata mamaki, shi da kan shi ya buɗe mata ƙofa ta shiga sannan shi kuma ya koma can gefen inda Jabiru ya buɗe mishi,yana zama cikin hannunshi ya saka nata. Yanayin susar da yake mata a hannu ya sa tajin kasala, har ma bata san lokacin da idanunta suke lumshewa ba,sai da suka hau titi sannan ya ce, "Jabir mu fara zuwa gidan Nafisa mu sauke Beby,ya ce to maigida. Hannu yasa ya kwanto da ita kafaɗarshi,a hankali ya raɗa mata cewa, jikinki yana da laushi Beby, ina son ƙamshinki, ɗan murmushi ta yi tun jiya yake faɗin wannan kalmar.

Wayarshi ce ta shiga ruri,ya ciro ta daga aljihun suit ɗinshi, ya kalli fuskar wayar ya shafa kumatunta tare da cewa, Abbanki. Da sauri ta ɗago daga kafaɗarshi tare da cewa, don Allah? Bai bata amsa ba sai dai taga ya ɗaga wayar yana cewa, "Assalamu alaikum, Friend an tashi lafiya? Bayan sun gaisa ne yake shaida mishi cewa dama batun bikine zai sanar da su na yarinyar ƙanwar Umma da za'ayi ranar juma'a mai zuwa ɗin nan,in sun samu zuwa to,in ma basu zo ba ba matsala.

########
[12/13, 17:32] Ummi Tandama😇: *📗📗 Pages 9*

Aisha duk tana jin su, bata san sanda ta dafa bayan Uncle ɗin ba,tana faɗin "Ɗan bani don Allah Uncle ba ni Abban." Tana magana tana girgiza shi, cikin yanayin irin na shagwaɓaɓɓu, ya ce to gama Beby ɗin,da zumuɗi ta amsa,ta ce Abbana ina ƙwana? Bayan sun gaisa ta ce, bikin Naja ko na Sauda? Ya ce na Naja ne za'ayi ranar juma'a,cike da zumuɗi ta ce zan zo insha Allahu, Abba ya ce a'a in mijinki ya ce a'a ba komai dama dai don ku sani ne,ta ce dama zan zo hutu,ya ce to sai kunzo bawa maigidan naki,ta ce to ka gaida min su Umma." Ta miƙa ma Uncle,suka koma kuma kan batun kasuwancinsu, daga bisani kuma suka yi sallama kan cewa sai sun zo. Suna isowa gidan Nafisa, suka shiga harabar gidan suka sauke ta,ta ce "Uncle ba zaka shiga ba?" Ya ce, nayi latti, idan na dawo ɗaukanki zan shiga, ta ce to. Ya miƙo mata ledar, tare da cewa,sai na dawo,ta ce to ka dawo lafiya,ta nufi hanyar da take zaton nan ne ƙofar falon. Shi kam zamanshi ya gyara tare da yin ajiyar zuciya,sakin fuskar Beby a yau ya samu ƙwanciyar hankali.

Ta ƙwankasa ƙofar ana ukun ne Nafisa ta iso,ta leƙo sannan ta buɗe cike da zumuɗi,tana cewa Bebyn bros ce? A'isha ta shiga tana cewa,amare, Nafisa ta amshi ledar tana cewa, kawo in taimake ki. A'isha ta ringa juyi cikin ƙaton falon mai shegen tsari tana cewa, wow Anty Nafisa falonki ya tsaru,gaskiya maigidanki ya iya zaɓen guri.

Nafisa ta ce, maigidana ko maigidanki? Ai da gidan da abin da ke ciki har shirya gidan duk Uncle ɗinki ne. A'isha ta sake kallon falon "kai gaskiya Uncle ya San tasta, mutumin nan ya haɗu da yawa fa, shiyasa kome ya zaɓa zaka ganshi ya haɗu. Nafisa ta zuba mata idanu tana dariya cikin mamaki ta ce, A'isha yaushe ki kayi baki haka? Wasa mijinki ki ke yi, ta ce Allah Anty Nafisa kinsan gaskiya na faɗa, domin Uncle ko kaya ya saka sai kiga tamkar don shi aka ƙera su. Nafisa ta riƙe haɓa tana cewa, lallai A'isha kin shigo gari yarinyar,ta ja hannunta,to zo mu shiga cikin ɗaki. A ɗakin ma haka A'isha ta yi ta santin gadon da sauran kayan tare kuma da koɗa Uncle ɗin nata,ta zube kan gado tana kallon Nafisa tana cewa "Anty Nafisa ga shi kema kin yi ƙyau, Nafisa ta zauna tare da dafa A'isha wai yaushe ki ka zama haka ne? A'isha tana dariya ta ce,me nayi wai? Sannan suka gaisa ta ce, ina Bros? Aisha ta ce, tare muke, ya yi latti ne shiyasa ya wuce, amma in ya dawo za ya shigo. Ya ya maigidanki?" Nafisa ta ce, yanzun za ki ganshi yau yana gidan uwargida ne.

A'isha ta taɓa baki gami da cewa, don ma ku biyu ne, da ace kamar mu ne daga can gidan sai ya wuce wani gidan,don ma Allah yasa gida ɗaya muke. To yanzun kuma ke kaɗai kike kuma Anty Nafisa? Ta ce "eh mana, sai dai ƴan aiki na" Nafisa ta dafa A'isha tare da cewa,sai kurum ki kaji auren Uncle ɗinki? A'isha ta gyara zama tare da cewa,hum ai na ji mamakin auren Uncle,in kin ji takaicin da nayi sai da na kai zuciyata nesa, sannan fa na iya zana jarabawa.

Nafisa ta miƙe,bari inje in kawo miki abinci, A'isha ta riƙe ta,ban daɗe da karyawa ba,bari sai anjima. Nan fa zan yini sai naci abinda nake so " Nafisa ta zauna tana cewa, "ai dukkanmu babu wanda ya so auren bros,ke shi kanshi ma fa ba wai yana son auren ba ne, don dai babu yanda zai yi ne."

A'isha ta ce,ni barni. Yana sonta har fita ya yi da ita waje."

Nafisa ta ce,"Amma dai kin san yafi son ki ko gaban waye yana faɗa." A'isha ta ce, "Gaskiya ni ban gaskata ba." Nafisa ta ce, "saboda me?" Aisha ta ce don yana musu abinda ba ya min." Nafisa ta gyara zama "me kenan? A'isha ta taɓa baki, duk garin nan Anty Nafisa ke kaɗai ce nake gaya miki matsalolina,ni ko ba wai na matsu ba ne,kuma ba jaraba ba ce,hasali ma matsayina na budurwa kuma yarinya na san bai dace in yi wannan zancan ba. Amma zan gaya miki ne ba wai don ki faɗa ma Uncle ba,sai don ki yarda cewa Uncle yafi son matanshi fiye da ni,kin san cewa Uncle bai taɓa taɓa ni ba?."

Nafisa ta zaro idanu,"kai haba?" A'isha ta ce wallahi, amma amaryarshi har da fita ƙasar waje da ita." Nafisa ta ce,wai har yanzun? A'isha ta ce, Allah kuwa,ba wasa nake ba, da yana cewa ban isa ba, yanzun fa? A'isha ta ce God forbid,ai sai ya zata na matsu ne, Nafisa ta ce amma ai addini bai hana ba, kuma in da baki damu ba yanzun ai kin kai ki damu ɗin, tunda ba dutse bace ke, A'isha ta ce koda zamu tabbata a haka ba zan taɓa ce mishi ƙala ba, tayi ƴar dariya tare da cewa kuma shikenan sai ince Uncle me yasa baka ƙwana da ni? Suka yi dariya tare, A'isha ta ce Allah ko ke ce Anty Nafisa na san ba zaki ce ba. Nafisa ta ce bazan ce ba, amma zancan zan maka fuska. A'isha ta ce, "Ni fa ban damu ba,ni da ina makaranta ma,in ya saba min naje makaranta na damu fa? Haka dai suke ta hira har suka zo kan batun su Hadiza nan Nafisa ta shiga ba A'isha labarin wacece Hadiza,ta ce daga Hadiza har Jummai sun auri Bros ne, saboda kuɗi,kuma dukkansu babu wadda bata buga duniya ba. Kuma shi Bros da Hajiyarmu sun ƙi yarda cewa Jummai tana da hannu a cikin mutuwar kishiyoyinta, A'isha ta ce nima haka kawai sai inji zuciyata tana zarginta musamman da wannan ƙawar tata Hajiya Kari.

Nafisa ta ce, kamar kin sani ke dage da yin addu'a, amma batunki da Bros zamu ga yanda zamu yi yanzun dai ki barshi ya gama amarcin da Hadiza, yanda in ya juya kanki zai san kuna da banbanci. Haka ta yini suna hira suka shiga kitchen.

Biyu dai-dai mijinta, Alhaji Bello ya shigo. Nan A'isha ta saki baki tana kallon yanda Nafisa ta ruga da gudu ta rungume mijinta,ta ma manta da wata A'isha a gidan, sai da ya tafi sannan Nafisa ta samu natsuwa. A'isha ta ce tabɗi,Anty Nafisa kina sha'aninki, ina ma zan iya na dinga yiwa Uncle ɗina haka? Ta ce kin ko san da kin ƙara haskawa cikin zuciyarshi. Hadiza zata iya shi yasa ki kaga tana ɗan jan hankalinshi. A'isha ta yi ɗan tagumi ta tsurawa mirrow ido tana tunanin shin zata iya? Ta dubi Nafisa ta yi ɗan tsaki ina jin nauyin Uncle shi ne matsalar amma ina son in burge shi. Nafisa ta ringa yi mata dariya.

Biyar dai-dai Uncle ya kira Nafisa,wai ga shi a ƙofar falonta, suka fito suka buɗe mishi ya shiga. Nafisa ta yi kicin, A'isha kuwa kamar yanda ta saba, ruwa ta kawo mishi ya amsa yana kallon fuskarta, sannan ya ce A'isha Allah ya shayar da ke ruwan Alkausara, yanda ki ke gusar min da ƙishina, shiyasa ko bana ƙasar nan duk lokacin da naji ƙishi,sai kin zo raina kuma sai na miki addu'a. Daɗi ta ji sosai sannan ta ce, "Allah yasa in sha tare da kai Uncle." Ya ce, "Amin Bebyna."
Chapter 12 · 0% Book details