← Book details Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 22

Sashe 11

Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aisha ko wayarta ta ciro ta shiga yin game,jin suna ta musu ne ya dakatar dasu da cewa,kai ku min shiru,an ji naki ra'ayin kema anji naki,Beby ke me ki ka ce? Hankalinta ya tafi ba taji ba,ya sake cewa, "Beby." Ta dubeshi "Na'am,Uncle me ka ce?" Haushi ya cika su Hadiza,ya ce ke me kika ce game da kwana? Ta girgiza kai uncle bani da zabi,ya sanyaya murya saboda me? A ranta ta ce ko na zaba me kwana da kai zai kare ni dashi? Amma a fili sai ta ce ,ba komai ni kaga ba zama nake ba,ya ce a a wannan ba dalili ba ne,ta kara sanyaya murya,Uncle Allah na yafe musu,su yi yanda suke yi,ta mike ta tafi. Ya bi ta da kallo sannan ya ce,ba zai yiwu ba. Hadiza ta ce,me zai hanashi yiwuwa darling ba itace ta ce ba. Jummai ta ce kawai ka bar ta tunda ita ce ta yafe ya ce to in ita ta yafe ni ban yafe ba,baku ganin cewa yarinya ce sai mu taru mu cutar da ita? Ya mike ina zuwa, Hadiza ta ce yanzun binta za kayi? Ko sauraronsu baiyi ba,ya tafi.

Hadiza ta miƙe ranta ɓace tana cewa,tabɗi, wallahi ba zan zauna ba ƙaramar yarinya tana juya mu son ranta,ɗazun ya taramu fiye da minti goma muna jiranta yanzun kuma ta tafi ya bita, bayan da ta zo ɗin sai da ta gama yiwa mutane kallon banza," Haka ta wuce tana mita.

Jummai kuwa kasa magana ta yi ita mamakin ta wai ita ce haka, ita ce kuwa? Ita ce Jumman da tasha alwashin kai duk mai ƙararran ƙwanan da ta aurar mata miji lahira? Yau ita ce da kishiyoyi biyu? Ba dan bata da kuɗin da zata biya ayi mata aikin ba,ba don babu malamai ba sai don me? Tana son jin amsar wannan tambayar.

Aisha kuwa tana shiga ɗakinta kan kujera ta faɗa ta ɗauki ƙafarta ɗaya ta ɗora kan gado, tana karkaɗawa, wani irin zugi take ji a cikin ranta. Wai duk yanda take jin Uncle,a ranta waɗannan matan sun fita? In ma Jummai ta furta za ta iya yi mata uzurin daɗewar su tare, amma Hadiza fa da tazo jiya-jiya,ba ta yarda ta fita son Uncle ba,to abinda tafi son sani yanzun ta ji duk suna son Uncle to shi Uncle ɗin wa yafi so?.

Muryarshi ce ta katse ta, inda ya ce, "Beby ban yarda da hukuncin ki ba,ko kina tunanin ba zan miki komai ba, dole ne kema yanzun ki ringa kwana dani. Ya zauna bakin gado ya ɗora hannunshi kan ƙafarta wadda ke kan gadon ta ce "mai yasa ya dace ɗin? Ya ce Beby me yasa kikeson dafa ni cikin ruwan sanyi ne? Ya murza yatsun ƙafarta. Beby kina ji na?" Ta ce "Uncle, Allah ba haka ba ne,kaga ni zan je gida ne ma ko ba zaka kai ni ba?" Ta zuba mishi idanu, ya yi ɗan murmushi ba zan kai ki ba, sai in kin yarda da batun cewa za ki dinga gyara shinfiɗata, duk bayan kwana biyu ko huɗu. Ta ce, to naji na yarda duk ƙwanakin da ka yanke ya yi min. Ya sunkuya ya sumbaci ƙafar dai-dai tafin ƙafarta, wani abu ta ji zir har cikin kanta, har sai da ta yi girgiza tare da yin ajiyar zuciya. Lokaci ɗaya kuma ta sa tafin hannunta ta rufe fuskarta. Ya ce "Beby ina son abubuwa a tare da ke, cikin su har da wannan kunyar ta ki." Ya miƙe yau fa kece da gyara shimfiɗa, don jiya kin ƙi ki buɗe min ƙofa, kuma gobe zan koma in ƙarasa harkokina a can Phoenix,ko zamu je?" Ta ce, a'a ka dai koma da amarya kawai,ya ce Beby kenan ƴar daru, ta ce yanzun har wani daru gareni? Ya ce ai ke darunki daban ne,babu faɗa babu hayaniya cikin ruwan sanyi ne. Ya fita yana cewa, haka ne ko?" Ta ce haka ka ce.

Tana kishingiɗe tana kallon (Zee Aflam) fim ɗin soyayya suke yi,in tana kallon finafinan soyayya sai ta rinƙa jin yana taɓa zuciyarta, ta sani tana son Uncle ta girma ne cikin son shi,ba wani namiji dake birge ta in bashi ba. Amma shi tana shakkar son da yake mata,ta san dai so ƙwaya ɗaya ne tak, kuma nata shi take yi ma wa,to shi fa wa yake mawa cikinsu? Matarshi da suka yi auren saurayi da budurwa, kuma zamanin ƙuruciya? Ko ita da ya aura tana yarinya ya kuma kasa haɗa shimfiɗa da ita? Ko amaryarshi da ya ke shanawa da ita? Saboda son ta fa wata ƙasar zai je sai da ya tafi da ita, ita ko ko nan da can bata taɓa zuwa ba, daga gida sai makaranta, sai ko garin su in taje hutu. Unguwar ta kuwa ba ya wuce gidan Hajiyarmu,Anty Sadiya ko Anty Fatima. Gidan Nafisa ma ba taje ba, tunda tana makaranta aka yi bikin yanzu dai take son zuwa kafin ta tafi hutu Jigawa. Jin da tayi an dafa mata cinya shi ne ya dawo da ita daga tunanin da take yi, da sauri ta dubi ko wane ne don ta ɗan razana, ganin Uncle ta yi cikin kayan bacci ya zauna kusa da ita, gabanta ne ya sake faɗuwa, amma da ta tuna cewa tana al'ada sai kurum ta ƙwantar da hankalinta, ta ce sannu da shigowa Uncle,ta miƙe ta kawo mishi zoɓo cikin zumuɗi ya amsa tare da cewa, Beby ƴar albarka, har kin min zoɓon? Ya cika kofi ya soma sha idanu lumshe sai da ya sha yafi rabi sannan ya dube ta, nayi missing ɗin zoɓonki sosai Beby, ta ce, to yanzun zaka sha har ka gaji.

Ya kalli wuyanta kullum yana sha'awar shafa wuyan nata,leɓunanshi suna ƙwadayin sumbatar wuyan ya ce, Beby yau dai za ki yi gyaran shimfiɗa ko? Ta kasa kallonshi, amma ta ce to, ya miƙe da jug ɗin zoɓon a hannunshi ina jiran ki,ta ce to.

Tana son kallon fim ɗin nan amma haka ta haƙura ta miƙe ta ƙara fesa ɗan turare ta nufi ɗakinshi. Tana kama ƙofar, Hadiza na fitowa daga ɗakinta. Ta yi saurin zuwa gurin ƙofar tana ke! Ke!! Tsaya ina za ki shiga? Aisha ta dube ta sannan ta shige, itama Hadizan ta shigo,ban gane ba, tunda ka yarda cewa ƙwana ɗai-ɗai ne to ai yau ni ce da ƙwana." Ya dube ta wa ya ce miki ta ƙwana nan jiya? Hadiza ta ce, to an hana ta ne? A'isha ta yi sororo tana kallonsu,bata da lokacin hayaniya, don haka sai ta nufi bedroom ɗin shi da niyyar ta yi abinda ya kawo ta,ta fita watan gyaran shimfiɗa.

Aiko sai Hadiza ta yi caraf ta cafke mata hannu cikin ɗaga murya take cewa, Malama kada ki shigar min ɗakin miji,don yau nawa ne,ran A'isha ya ɓaci, ta tsani ayi mata ihu,don haka sai ta fisge hannunta ta juya tana jin lokacin da Uncle ya ce wa Hadiza dama haka halinki ya ke? Beby zo nan." Ya miƙe yana kiranta,ai wannan tuni ta kai ɗakinta, ta zauna kan gado ta riƙe kai ta tsani ayi mata ihu a kai. Ita ba ta iya masifa ba,bata saba ba, amma duk ba wannan ya fi bata takaici ba irin yadda Hadiza take nuna mata kan Uncle ba zata barta taji da kishin dake cin zuciyarta ba.

Shi kuma Uncle saboda yafi son Hadizan ya kasa hanata. Ya tura ƙofar ya shigo, ya tsaya a gabanta ya maida hannuwanshi baya,ya ce "Beby tashi kizo mu je." Ranta ya kuma ɓaci,tamkar ta dubeshi ta ce ba zan je ba. Amma kimar shi ta wuce haka,koda ba zataje ɗin ba ba zata iya yi mishi rashin kunya ba,don haka sai ta girgiza kai "kayi haƙuri Uncle, ba zani kuma shiga ɗakinka ba, cikin sanyin murya ta ke magana.

Ya jawo kujerar madubi zuwa gabanta, ya zauna,ya kira sunanta cikin tattausar murya, ya ce A'isha sai yaushe zamu yi zaman aure? Da farko na barki ne saboda kasancewar ki ƙaramar yarinya, yanzu kuma kin girma ya kamata mu canza,shiru tayi mishi, ya ce kin ji ni? Ta sunkuyar da kai,ni dai kurum kai min alfarmar cire ni cikin masu zuwa ɗakinka." Ya taso ya dawo kusa da ita ya zauna, amma Beby ni kin amince in dinga zuwa naki ɗakin ko?kai kurum ta ɗaga mishi ya ce shikenan zan ƙwana nan kenan ko?" Ta ce "In kana ra'ayi."

Duk da cewa bai so ba lokacin da ya ce tazo su yi sallah don yiwa Allah godiyar zuwan wannan rana sai ta sanar da shi cewa tana fashin sallah, amma ya ji daÉ—in yanda suka yi bacci tana lafe a jikinshi. Sannan ya yi wasanni da ita,ita kanta irin yanda yake mata É—in yasa ta jin daÉ—in cewa itama mace ce.

Sai dai washegari ta kasa kallonshi,in ta tuna jiya duk ya kalle mata jiki, musamman ƙirjinta da take jin kunyar ko a riga taga mutum na kallon mata su, shi kam farin ciki ya farka da shi tamkar ya biya buƙatarshi da ita. Tana gama abinda zatayi ta ce tana son zuwa gidan su Anty Nafisa, ya saka Jabiru ya zo ya kaita mana? Sai cewa ya yi ni zan kai ki Bebyna, tana wanka ta dinga kallon guraren da Uncle ya yi ta mata wasanni da su, ta yi murmushi in tana tuna yanda taga Uncle ya fita cikin hayyacinshi sai taji wani alfahari, ashe itama mace ce.

Riga da siket ne a jikinta na pink ɗin atamfa ƴar Holand,ta ɗora baƙar after dress mai shara-shara, ta saka baƙin takalmi, fuskarta tasha fenti. Ta kalli madubi cikin zuciyarta ta ce, wasa-wasa fa nima nayi. Ina da ɗan kyauna dai dai gwargwado. Ta saka turare mai sauƙin ƙamshi, saboda ta san tare da Uncle zasu fita, kuma gidan Nafisa zata je da ba za ta saka turare ba, saboda bin umarnin da Manzonmu ya yi mana kan cewar bai halatta ba ga mace ta saka turare in zata fita. A wata ruwayar ma an ce in har ta saka to in ta dawo tayi wankan janaba.
Chapter 11 · 0% Book details