← Book details Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 22

Sashe 17

Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ce, Beby ni dai da mun je, kin gan ki kuwa? Ta ce gobe da jibi ne zamu yi sauran papers ɗin,in ya so sai ka zo ranar Laraba ka musu bayani sai mu tafi. Ya ce,ni barinki cikin wannan halin shi ne matsala ta, ta ce kada ka damu,satina fa biyu cikin wannan halin, to dan ƙwana biyu? Ya yi shiru yana kallonta,can ya ce shi kenan zan zo labarar. Ta yunƙura ta tashi zaune tana ƙarfin hali dan kada ya ƙi yarda. Ta fito ta ce,sai kazo ya ce,to, yabita da kallo shi dai kawai don dai taƙi ne.

Cikin mota suna tafiya tunani yake,ko dai wani ciwon ne ya ɗurawa ƴar mutane? To shi wannan wace irin ƙaddara ce? Allah ka min da sauƙi, cikin ƙwana biyun ta koɗu,ta dai samu ta zana jarabawar, amma fa cikin jin jiki.

Tun misalin baƙwai ya isa makarantar,kai tsaye gurin (P.C) ɗin ya nufa, ya tambaya ko yaran sun gama zana jarabawa? (P.C) ya tabbatar mishi da cewa sun gama. Ya ce, to dama ya zo ne ya tafi da A'isha, saboda ba ta da lafiya, kuma gashi bata son shan magani dole sai an sa idanu kanta (P.C) ya ce,babu matsala,nan ya ce bari ya yi waya da waɗanda suka dace.

Aisha tana ƙwance saƙon ya zo mata, cewa an zo ɗaukar ta, kasa tashi ma ta yi, sai da taimakon su Samira sannan ta tashi ta riƙe ta suka je,ya tare su. Ko lokacin amai take ji, zuciyarta tana tashi ya kamata cikin mota ya saka ta,su Samira ne suka ƙwaso mata kayan,ya yi musu ihsani, suka yi sallama tare da fatan samun lafiya gare ta, sannan ya shiga mota.

Suna cikin tafiya ta kasa jurewa,nan fa amai ya zo mata ta ko dinga sheƙa shi tamkar ranta zai fita, daga nan asibiti suka nufa. Cikin sauri ya shiga ya yi wa Nurse's magana,gadon ɗaukar marasa lafiya suka ɗauketa a kai, har lokacin amai take zabgawa. Uncle ɗin kuwa duk ya gama ruɗewa, ya kira Alhajinshi yana sanar dashi cewa A'isha babu lafiya, kuma babu yanda take ma'ana, jiki ya yi tsanani,ya kira Nafisa da Fatima har da Sadiya, kafin ka ce haka kuwa,tuni Nafisa ta iso,su Fatima suma sun zo, Alhajinmu shima sai gashi ya ce me ya same ta? Uncle ya ce, Likita na tare da ita.

Jim kaɗan Likitan ya fito Nurse's na turo ta a gado. Nan suka bi su zuwa ɗakin da aka ƙwantar da ita, ruwa aka ɗaura mata tare da yin allurori cikin ruwan,nan da nan ta soma bacci. Likitan yana fitowa Alhajinmu ya bishi zuwa Ofis, shi da Uncle ɗin. Likitan ya ce,su ƙwantar da hankalinsu, insha Allah komai zai zo da sauƙi, yanzun dai zasu yi mata gwaje-gwaje daban-daban, tunda bata cikin hayyacinta da zata iya musu bayani, sannan sun ce daga makaranta take. Suka ce to bayan sun fito ne Alhajinmu ya yiwa ɗan nashi nuni da ya ƙwantar da hankalinshi ya san cewa rayuwa da mutuwa duk daga Allah ne.

Itama Hajiyarmu ta damu taga wani daga cikinsu don taji labarin jikin,da ta gaji sai ta kira Nafisa ta ce,wai shin Nafisa ya ya jikin yarinyar nan? Nafisa ta ce, jiki kam tana jin shi Hajiyarmu, yanzun dai ana mata ƙarin ruwa, sannan sun ɗibi jininta za su yi mata gwaji. Ta ce, to Allah ya sawwaƙe

Shi kam Uncle yana nan duk inda Likitan yabi yana biye dashi,don son sanin matsalan A'isha,bai ga wasu cututtuka ba, amma ya fi zaton ciki ne,don haka sai ya shiga wannan gwajin. Sun tafi sallar azahar, Likitan ya shigo yana cewa, ina maigidanta? Fatima ta ce, ya je sallah, ya ce in ya dawo yana neman shi a Ofis, suka ce to.

Nafisa ta ce,ni matan Bros suna bani mamaki,dubi har yanzu babu wadda ta leƙo" Fatima ta ce ,ai dama ke kina sa ran zuwansu ne? Gaya min cikinsu wace ce ta kirki? Hadizan Hajiya Lanti ko Hajiya Jummai? Ni dai na ce Allah yasa ba wani ciwon suka sakawa ƴar mutane ba tunda dukkan su ba wadda ta dogara ga Allah."

Sadiya ta ce, "Shi yasa yanda na tsani mutuwa ta haka na tsani auren shi da Hadiza,kina ganin yanda Hajiya Lanti mahaifiyarta ta ke juya Baba Sunusi,sai ka ce remote,shima Bros É—in suna samun guri haka za su maida shi."

Fatima ta ce, "Insha Allahu ba zasu samu haka ba,ta Allah ba tasu ba."

Ya shigo da sallama, ya dubi gadon da A'isha ke ƙwance, sannan ya ce har yanzu bata farka ba? Suka ce eh, Likitan ya ce ma in ka dawo ka je." Ya ce, to kun yi sallah?" Suka ce, yanzun dai zamu yi.

Fuskar Likitan cike fara'a yake kallon Alhaji Saddiƙ, ya miƙa mishi hannu.

"Ina matuƙar taya ka murnar cewa, matarka tana ɗauke da ciki ƙwana goma sha baƙwai."

Idanu Uncle ya tsura ma Likitan, jin zancan ya yi tamkar cikin mafarki. Likitan ya jijjina mishi hannu.

"Ranka ya daÉ—e wannan shi ne sakamakon da muka gani cikin gwaje-gwajen da muka yi."

Cikin wani farin ciki mai tsanani ya rungume Likitan yana cewa, "Na gode, Allah alhamdulillahi" Da sauri ya fita ya nufi ɗakin da A'isha take kwance, har yana cin tuntuɓe. Ya shiga ko ta kan Nafisa bai bi ba ya isa gaban gadon ya tsaya, idanu ya zuba ma A'isha.

Ya kama hannunta ya riƙe gam,a zuciyarshi yana raya dama ɗan shi ne zai fita ranar? Ya gode Allah da bai sa yaba Hadiza ba, ya gode Allah da ya tsareshi bai zama mazinaci ba,bare ya ba wata karuwa. Cikin kiɗima Nafisa ta girgiza shi.

"Brother lafiya ka ke hawaye?"

Sam bai ma san yana hawaye ba.

Fatima ta fito da gudu daga banɗaki, tana cewa "Me ya faru na ji kin ce yana kuka?" Sadiya kam tana sallah, amma duk hankalinta na gurin,sai kawai gani suka yi ya juyo ya rungume Nafisa yana magana cikin rawar murya,tamkar kuka zai ƙwace mishi. Yana cewa, "Sister A'isha tana ɗauke da cikina!!"

Duk su ukun har da mai sallar suka furta cewa ciki? Ya yi ajiyar zuciya, ashe zan ga ɗan kaina? Murna suka shiga yi tare da yi wa Allah godiya. Nan suka shiga kiran iyayansu. Nafisa ce ta yi dacen kiran Hajiyarmu tana ɗagawa Nafisa ta ce Hajiyarmu A'isha na da ciki,Bros zai samu ɗa." Kalmar ta doki zuciyar Hajiyarmu, har ta kasa magana. Nafisa ta ce kin ji me na ce?" Hajiyarmu ta ce, "Allah ya inganta, ya bata lafiya." Ta ce,"Amin" Nafisa tana kashe wayar, Hajiyarmu ta miƙe ta ɗauro alwala ta zo ta soma nuna murnarta gurin Ubangiji, lokacin da take godiya ga Allah har da hawayen ta.

Uncle shi ne ya sanar da Alhajinmu wanda shima ya katse duk harkokin da yake yi a wannan lokacin ya sake nufo asibiti. Lokacin da ya iso, Uncle ya koma masallaci, inda ya zube cikin sujjada yana yi wa Allah godiya. Lokacin da ya dawo ɗakin su Alhajinmu, suna cikin ɗakin har da Likitan. Alhajinmu nan take ya yi wa Likitan ƙyautar mota, ya ce yaje gidan motocinsa da ke kan titin Isa Kaita ya zaɓi duk wadda yake ganin ta mishi. Kai yau kam duk wanda ke da dangantaka da su, sai da ya san A'isha na da ciki.

"Kai Nafisa, har da ƙawayanta ta ringa kira tana shaida musu, cikin ne da ita. Amma yanda suke murnar na A'isha abin da mamaki...

######
[12/15, 19:45] Ummi Tandama😇: *📗📗 Page 13*

Lokacin da Alhajinmu ya iso gida har lokacin Hajiyarmu tana zaune kan sallaya amma yanzun tana jan carbi ne, cikin tsokana ya ce ke ban ganki a asibiti ba, tunda na san dai kin samu labarin matar É—an naki tana da ciki."

Ta sunkuyar da kai, "Me zan je in musu? Na san duk Æ´an'uwanshi suna can." Ya zauna, "Naga fuskarki, ta nuna murnarki, tayi É—an murmushi kana son jin ta bakina ne kawai,to na ce Allah ya inganta mishi, shikenan? Ya yi dariya na sani duk cikin Æ´aÆ´aki kin fi son Abubakar,don haka yau babu wanda ya kai ki murna. Ta yi É—an murmushi.

"Gaskiya ka faɗa." Ya sheƙe da dariya," Ashe dai kina son shi ki ke share shi? To yau zan gaya mishi ya daina min mita kan cewa shi baki son shi,shiru ta yi mishi.

Ku tambaye ni lokacin da ake wannan murnar ina su Hajiya Jummai da Hadiza suke? To sai in ce muku suna gida, labarin ya ishe Hadiza ne ta bakin mahaifiyarta wadda Alhaji Sunusi maigidanta wanda Alhajinmu ya yi mishi waya ya sanar dashi, cikin murna ya zo gidanshi ya sanar. Nan fa Hajiya Lanti ta ji tamkar labari mutuwarta ya zo mata dashi. Nan ta kira Æ´arta tana son jin gaskiyar lamarin.

Haƙiƙa Hadiza ta ruɗe da jin wannan labarin, sai dai ta ce wa Hajiya Lantin tana shakka domin a saninta dai A'isha tana makaranta. Hajiya Lanti ta ce,an ce tana asibiti. Hadiza ta ce, zan dai bincika,nan take ta ɗauki waya ta kira maigidan.

"Assalamu alaikum,darling kana ina ne?" Ta tambaye shi.

Cikin murna ya ce, "muna asibiti da A'isha,na manta ban sanar da ku ba, A'isha tana nan asibiti."

"Me ya same ta?"

"Ciki ne." Ya bata amsa a taƙaice.

Ya kira layin Jummai lokacin tana lissafa kuɗin da zata kai ma wasu malamai guda biyu, ɗayan yana mata aiki kan Hadiza, ɗaya kuma kan A'isha. Ta ɗaga wayar cikin raha ta ce, "Maigidana na kaina." Ya ce, "Jummai yau dai Allah ya amshi addu'armu." Ta ce, "Ta me fa?" Ya ce,"A'isha tana da ciki." Da sauri ta miƙe tsaye, "Ci me?" Ya ce,"Ciki." Ta yi ƙoƙari ta saisaita numfashinta,"kai Allah mun gode maka,kuna asibitin ne? Ya ce eh,ta ce gani nan zuwa,ya ce dama na sani Jummai za ki yi murna,ta ce ai faɗa ma ɓata baki. Ya kashe wayar.

Jikinta har rawa yake wajen neman number Hajiya Karima,daƙyer ta samu taga number saboda fita hayyacinta da ta yi,tana ɗauka ta fashe mata da kuka "Na shiga uku!, Shikenan tawa ta same ni,ni nasan tawa ta ƙare."
Chapter 17 · 0% Book details