← Book details Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 22

Sashe 2

Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ihu ta saka ita kaɗai,a ruɗe su Suwaiba suka shigo suna cewa, "Lafiya Anty Jummai?" Tana huci ta ce "ku bar ni zanci uban yarinyar can" Sofy ta ce, "Me tayi miki ne Anty? Yanzu mu je muci ubanta? Ta ce a'a ku bari ba yanzun ba,ni zan yi maganinta. (Waya ga sa kai a uku) Yinin ranar Jummai sun ƙule ita da Aminiyarta, suna neman mafita. Ta rantse ta kuma rantsewa cewa maigidan yana kusantar yarinyar gashi an ce zata mutu shiru bata mutu ba,ta dubi Kari,ko dai zan sa mata guba ne? Kari ta ce "a'a komawa zamu yi gurinsu." Ta ce dibi asarar da na yi ta kuɗi, amma ace maganin bai ci ba? Kari ta ce,mu koma musu kawai gobe ke in abin ma ya ƙi wallahi sai mu nufi Nijar,zan binciko miki wani malami ko ince Boka.

Sun bar zancan a kan zasu koma in basu ga dai-dai ba,su nufi jamhuriyar Nijar, Allah ka tsare mu,Amin.

A'isha ko sam bata ma san hidimar da suke yi ba. Ranar ƙuƙewa ta yi tana ta ƙoƙarin yiwa Uncle ɗinta gurasa da miyar taushe. Ta haɗa zoɓonta mai daɗi, Uche ne ya taimaka mata ,Marka mai aiki taje ta sanar da Hajiya Jummai ta same ta suna magana da Karima,don haka ta sanar da su Suby cewa, amarya ta samu sake, tana can kitchen ta girka banza da wofi. Nan ko suka nufi kitchen ɗin suka shiga buɗe mata kuloli, suna cewa, me wannan ƙwamacalar wannan ƙazamiyar ƴar ƙauyen ta ke yi ne haka?" Aisha ko da kallo ta bisu, Sofy ta ce, ashe ma abincinsu ne irin na ƴan ƙauye. Suby ta ce,ke gaja wa kikayi wa wannan ƙwaɗon? Ita dai kallonsu take yi ranta yana zafi,ta ce ina ruwanku da kayana? Duk suka haɗa baki gurin cewa,sai mu zubar dashi,dube ta ƴar matsiyata kawai, A'isha ta ɗauki kulolin ta ta nufi ɗakinta ta dawo ta ƙwashe sauran kayan,su kam sai dariya suke yi mata,suna cewa in dai Alhaji ki kayi ma wannan ƙazantar ba ci zai yi ba ƴar neman gindin zama,zaki gane kuranki. Tagumi ta zuba tana zubar da hawaye,tuni ta kula waɗannan za su takura mata.

Yau tun huɗu Uncle ya dawo, domin tunda ya kira A'isha sau uku bata ɗauka ba,ya soma tunanin ko dai bata da lafiya ne? Ita ko sam bata ma san inda ta jefa wayar ba, kuma damuwar da take ciki bata tuna mata cewa tana da waya ba, domin dawowarta a jiya ne ma ta ɗauki wayar. Amma ba sa zuwa makaranta da waya. Lokacin da ya shigo tana wanka,zama ya yi yaga fitowarta, da ɗaurin ƙirji ta rufa da tawul ta ɗan yi yaƙe tare da kallon agogo tana faɗin, har ka dawo? Shi ko ita yake kallo yana son gano halin da take ciki,jin bai yi magana ba ne yasa ta maida kallonta gareshi ya ce "Beby me yake damunki?" Ta zauna bakin gado cikin irin murmushin takaicin nan,ta ce ba komai. Ya dawo kusa da ita wani guri yana miki ciwo ko? Ta ce "a'a,me ka gani ne Uncle?" Ya ce, "Sau uku ina kiran wayarki ba ki ɗaga ba, sannan yanzun na zo sai na same ki ba yanda ki ke ba.

A'isha baki kai lokacin da zaki haɗiye damuwa ba,sanar dani matsalar ki?" Ta girgiza kai "Yi haƙuri Uncle,ka bar zancan,maganar waya kuwa ni na ma manta ina da waya saboda ka san zaman makaranta yasa na saba da rashin waya." Ya ce, "Ni fa Allah sai kin sanar da ni." Ta ce, "to ni ban san me zan ce maka ba." Ya ce, wani guri ne yake miki ciwo? Ta girgiza kai tare da cewa, a'a.

#######
[12/9, 07:33] Ummi Tandama😇: *📗📗 Page 2*

Ya ce, To mene ne? Hawayen da take maƙalewa suka soma zubowa,ta ce su Suwaiban nan ne, ya ce Suwaiba? Ta ɗaga kai "Me suka yi miki?" Ta ce, Ni dai kawai ka ce musu ba ruwansu da ni in ina abuna, tunda dai ni bana shiga cikin harkarsu, ya ce to kiyi haƙuri zan musu magana." Ta share hawayenta, ta miƙe ta kawo mishi ruwa mai sanyi,yana sha taa ce, "Yau fa na maka abinci,baza ka ci na Uche ba, Allah yasa zaka iya ci?" Ya ce, "Me yasa ki ka ce haka? Ta ce, saboda ban ƙware ba,ni kuma gani da son yin girki." Ya ce,zan ci koma ya ya ne,ai Beby kina da ƙoƙari, na san nan gaba zan huta da cin abincin masu aiki ko?" Ta yi dariya, ya ce, sannan kada ki ce na dawo da hannun agogo baya,shin me ya haɗa ku dasu Safiya? Ta ɗan ɓata rai ganina kawai suka yi ina girki cikin kitchen sai suka hau buɗe min suna zagina wai ƴar ƙauye ina haɗa ƙwamacala,na samu sake.

Suna ta yi min,ni kuwa na fita dan sun ce zasu zubar min." Ya ce, "Ke da wanene cikin kitchen ɗin?" Ta ce,ni da Uche ne,yana taya ni, ya ce to kiyi haƙuri.

Koda ya fita ɗakin Hajiya Jummai ya nufa,tasha adonta tamkar ba ita ce cikin damuwa ba ɗazun, shawarar Karima ta ɗauka wadda ta shawarce ta da cewa ta yi ƙoƙarin ɓoye sirrinta cikin ranta ta daina bari ana gane damuwarta. Ya dube ta "Jummai ina yaran nan ne?" Ta ce, "Sannu da zuwa,ka dawo?" Ya ce, "Eh" ta ce, "Su Suwaiba?" Ya ce "Eh," ta ɗauki waya ta kira Safiya ta ce,su zo ɗakinta yanzun. Koda suka shigo, ganin Uncle sai suka yi tsimi-tsimi ya ce kece ki ka tura su su je suyi wa A'isha rashin mutuncin nasu? Ta dube su,me ku ka je kukayi mata? Suby ce ta soma cewa,nima dai ban sani ba, Allah Anty sharri ne. Sofy ma ta ce, to mu yaushe ma muka ganta ni na ma san ta dawo ne? Bai yi magana ba ya ciro wayar shi ya kira Uche, ya ce ya same shi a ɗakin Hajiya Jummai. Nan a gabansu ya tambaye shi cewa ya gaya mishi gaskiya me ya faru tsakanin A'isha da su Suwaiba. Ya ɗan soma inda-inda, Alhaji ya ce, daina kallonsu,ni ne na ɗauke ka aiki kuma ni ke biyanka don haka bana son kana kallonsu,in zakayi magana." Nan dai Uche ya sanar da su duk yanda aka yi, duk da yana tsoron masifar su. Nan ko Alhaji ya soma faɗa,ya ce maza su fita hanyar matarshi, domin kan A'isha kowaccensu zata iya kama hanyar gidansu,a cewarshi don A'isha ba ta da gidan da yafi wannan, tunda nan ne gidan aurenta.

Hajiya Jummai ma dai ta daure ta ce musu su fita harkarta,ta yi musu faɗa a gabanshi, amma yana fita ta ce,lallai yarinyar nan har ta samu guri ta soma kai ƙara? Tabɗi,lallai zata san da wa take yi. Su Suwaiba ma sun sha alwashin cewa sai sun ƙuntata mata.

Ita ko bata san suna yi ba ma,don bai ce mata ƙala ba. Koda ya shigo rashewa ya yi a tsakar ɗaki nan kan sallayarta ta shiga jera mishi kayan gabanshi,ya buɗe babbar kular tare da cewa, tunda kin ƙi gaya min sunan abincin da ki kayi min bara na duba da kaina, ganin gurasa luhu-luhu ya sa shi sakin baki, sannan ya dube ta cike da mamaki, "Allah ke ce ki kayi wannan gurasar Beby? Ta ce,ba tayi ƙyau ba ko? Cikin fargaba take magana,ya ce ina dai mamakin iyawarki. Ya ɗauki ɗaya ya yaga,ya saka cikin bakinshi yana taunawa, ya ce Beby kin yi zaman Kano ne? Tana dariya ta ce, Uncle abinda ya yi Kano ai shi ya yi Jigawa,ya ce haka ne,ba zan ci gurasar nan ni kaɗai ba, bari na kira abokina wanda duk sa'ilin da ya shiga Kano sai ya shigo min da gurasa. Ya ciro wayarshi ya kira Alhaji Salis,ko gaisawa bai bari sun yi ba, ya ce mutumina don Allah ka zo gidana yanzun ka sha mamaki. Alhaji Salis ya ce to bari na ci abinci tukunna, Alhaji Saddiƙ ya ce,in ko kaci abinci za ka sha haushi,ai kurum ka iso da yunwarka."

Ya miƙe, matarshi Rabi'a tana cewa, ina za ka Salis? Ya ce ina zuwa, yanzun zan dawo. Ya fita da sauri.

Shi ko Uncle tuni ya soma ci,miyar ta ji naman rago ga kori tafiyayye tun daga Kano,Curry mai suna Amrif yana gyara girki sosai, Uncle kam babu baka sai kunne. Wayar Alhaji Salis ce ta katse shi,ya miƙe "Bari na shigo da shi,ban so ya katse ni ba."

Sun gaisa da Alhaji Salis, shima ya shiga mamakin ganin gurasa,bai tsinke da lamarin wannan ƴar yarinya ba, sai da ya soma ci. Faɗi yake yi zan turo Rabi'a insha Allahu,ki koya mata har da miyar duk ki nuna mata. Aisha kam sai jin daɗi take yi,ta zuba musu sassanyan zoɓon suka soma sha, Alhaji Salis yana cewa mutumina shi yasa naga ka soma yin tumbi ka ce gara ka ke ɗiba in zan samu wannan me zan yi da lemun kanti, sai dai don ra'ayi, amma ba don daɗi ba. Da suka gama za su fita, Uncle zai mishi rakiya sai da ya yi ma A'isha ƙyautar kuɗi ba tare da ya san ko nawa ba ne, saboda yaba matan da ya yi,suna fita ya dubi Alhaji Saddiƙ ya ce, "Abokina gaskiya Allah ya yi maka baiwa ai macen da ta iya girki baiwa ce, Allah kewa bawansa,gata ɗanya sharaf ko ta ina,kana morewa." Uncle ya ce, kai Salis,kana nan da halinka ko? Ya yi ɗan tsaki, gaskiya nima fa auren nan zan zo in ƙara, Uncle ya ce menene damuwar ka? Rabi'a tana kula da kai, ga kuma ƴan yaranka. Nima matsalar rashin ƴaƴa ne". Salis ya ce, to ai mutum yana son canjin gurin hutun,tunda ai matan sun bambanta." Uncle ya ce "Kai Salis, to ni har yanzun ban taɓa yarinyar nan ba, ina jin tausayinta,ta yi ƙarama."
Chapter 2 · 0% Book details