← Book details Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 22

Sashe 20

Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kullum sai Ummanta da Abbanta sun kira ta sun tambayi jikin umma ta kan bata shawarwari masu kyau game da rainon ciki. A daddafe cikin ya yi wata biyu, suka yi waya da Samira inda Samira take cewa wannan satin ne za'a koma makaranta, ta ce, ina sane ni da nasha ciwo kamar ba zan tashi ba tun daga wannan dai ciwon? Samira ta ce ayya amma me yasa ba a samun wayarki? Ta ce,ke dai bari,ni da tunanina manta da batun wata waya, sai dai mun haɗu a makaranta. Samira ta ce to shikenan, Allah ya sawwaƙe, A'isha ta ce Amin.

Koda Uncle ya dawo ta ce mishi an koma makaranta, sai ya ce mata wace makaranta? Beby gaskiya ba zaki koma makaranta da ciki ba." Ta dube shi cikin rashin walwala ta ce, Uncle kana nufin ba zan zana (S.S.C.E) ba? Ya ce haba Beby,ke sai ma ance miki,kina ganin yanzun ban bari ki yi nisa da ni? Ta ce, gaskiya ba zan so haka ba, wata uku fa kawai ya rage min in gama duka,don Allah Uncle ka daina wannan maganar." Ya ɗaure fuska wata shekarar kin zana, ganin yanda ya ɗaure fuska, abin da bai taɓa mata ba,sai ta yi shiru ta kifa kanta kan filo, shi kuma ya fita abinshi. Kuka ta ringa yi wiwi,na ta ganin Uncle bai mata adalci ba, ita a nata son ran ta koma makaranta tunda ba wanda ya san tana da ciki, har ta gama.

Da daddare ko da ya shigo ta bashi ruwa, sai dai ba ta cikin walwala,ya amsa yana sha yana kallon fuskarta, wadda ta kumbura ta yi dam. Ya aje kofin da sauri,me ya samu fuskarki Beby? Ta sunkuyar da kai babu komai, ya ce ban yarda ba kin yi kuka ko? Ta ɗago ta ce mishi, a'a sai hawayen da take maƙalewa suka zubo ya kama hannunta suka zauna, yanzu saboda na ce ba ki komawa makaranta ba shi ne ki ke kuka? Beby na fiki son karatun ki domin alƙawari na ɗauka cewa zan tsaya har sai kin ji da kanki cewa kin gaji da karatu, amma yanzu koda ba ciki duka-duka yaushe aka sallamo ki daga asibiti? Ba ki gama murmurewa ba" Ta ce, Uncle ko a makaranta fa zan kula da kaina." Ya yi shiru yana kallonta,sam baya so ko kaɗan ya ga yarinyar cikin damuwa, ya ce to daina kuka za ki koma, amma sai kin ƙara murmurewa, sannan in naga kina cin abinci. Ta ce, to Uncle zan dinga ci. Nan fa A'isha ta dinga ƙarfafa jikinta don kawai ta samu ta koma makaranta, sai dai duk da haka cikin nata mai saka laulayi ne da tsirfar zan ci kaza ba zan ci kaza ba,ga saurin fishi. Wata rana tunda safe ta ce da Uncle idan zai dawo ya zo mata da agwaluma, ya ce ni kam ina zan ga wata agwaluma? Ba na zaton cewa duk Katsina za'a samu agwaluma, amma zan sa a duba. Yinin ranar neman agwaluma gurin mutum huɗu ya baza,neman agwaluma. Ita kuma tana ta yi mishi waya a ƙarshe washegari a Kano aka siyo cikin baƙar leda ya tashi Jabiru ya dawo gida lokacin ƙarfe uku na rana ya same ta tana shan ƙanƙara ta fiya wota, ya ce Beby me yasa kike shan ƙanƙara? Kada in sake gani ta ce, to da ya aje mata ledar agwaluma komawa ya yi gefe yana kallonta, da gudu ta tashi ta ɗauko ruwa a firij ta wanke ta soma sha hannu baka hannu ƙwarya. Tausayinta ya cika shi, ya ce Beby bana son wannan gudun da ki ke yi,kin ga cikin ki bai yi ƙwari ba,ta ce na daina.

Washegari kuma ta ce zogala, gidansu Hajiyarmu ya yi waya aka kawo mata shi da yawa,ta yini ci. Irin waɗannan abubuwan suke sa Uncle tunanin yanda zata zauna a makaranta,ba za'a bari a zo kullum ba,week end ɗin da yake zuwa sun gaya mishi don shi ne, sannan ita abin tattalin shi ce,a yanzun saboda mutane da yawa suna bashi shawara kan cewa ya kula da ita sosai, saboda maƙiya ko ɓarayi masu yin garkuwa da mutum don su amshi kuɗi irin waɗannan abubuwan suna sa shi tunanin barin ta ta koma, amma ya san makarantar su akwai tsaro, sannan albarkacin addu'ar da yake yi ko yaushe Allah zai kare mishi ɗan shi.

######
[12/17, 11:31] Ummi Tandama😇: *📗📗Page 15*

Cikin wannan halin wata rana A'isha tana ƙwance da daddare, Uncle yana ɗakinshi,yau Hadiza ce da girki,tasan komai dare zai dawo ɗakinta,don haka ba ta murɗa key ba. Shiru-shiru har ɗaya ta wuce, ita ko bacci na cin ta, don haka ta rufe ƙofarta,ta ƙwanta tana karanta addu'ar bacci ta gama bata gama ba oho bacci ya yi awon gaba da ita. Can cikin baccinta sai wata ƙatuwar mage ta nufo ta, nan suka soma gabza dambe ta nayi tana karanta duk addu'ar da ta zo bakinta,mage ƙoƙari take ta cafko mata cibiya, Allah bai bata Sa'a ba, suka yi wa juna kaca-kaca duk ta yayyaƙushe A'isha, itama ta ji ma magen ciwo. A tsorace ta farka da addu'a, sai me,magen ta gani a kan durowar gefen gadon ta murtukekiya. Ta yi wani tashi ta nufo ta,da matsanancin tsoro ta ƙwala ihu tare da kai ma magen nan duka da filo,ta miƙe tana waige-waige saboda bata san in da magen ta shige ba,ta nufi ƙofa da gudu tana salati, tana buɗe ƙofa Uncle yana fitowa, shima da gudu saboda duk wanda ke gidan ba zai ce bai ji ihunta ba.

Hanyar fita ta nufa ya yi sauri ya riƙo ta, ta sake ƙwala wani ihun tana ƙoƙarin fizgewa. Abinda ya bashi mamaki, wani mugun ƙarfi ya ji ta yi. Ta ƙwace zata fita, ya kuma damƙo ta da ƙyar,ya kai ta ƙasa ya danne ƙafafunta da hannuwanta. Nan ya shiga tofa mata addu'o'i, sai ta yi laƙwas. Ya ɗauke ta zuwa ɗakin yana shiga ta soma ihu da sauri ya fito da ita kan kujera ya ƙwantar da ita yana tofa mata addu'o'i.

Hajiya Jummai tana leƙensu ta window, haka Hadiza daga falonshi ta leƙen su. Hajiya Jummai ta fito da sauri tana cewa, "Lafiya Alhaji?" Ya ce, wallahi nima ihunta na ji. Ta zo ta tsugunna tana cewa, A'isha me ya faru ne? Ina, A'isha sai wani gunjin kuka take yi. Addu'a dai yake ta tofa mata, Hadiza ma ta fito suka zauna cirko-cirko. Jummai tana ɗan mutsu-mutsunta da baki tana tofa mata amma a zukatan su farin ciki suke yi, kowacce tana zaton nata asirin ne ya ci, kafin safe ta yi wani sharaf ta daina gunjin kuma bata ko motsi.

Tun cikin daren ya kira Alhajinmu ya sanar mishi, ya ce mishi ko su wuce asibiti? Alhajinmu ya ce, a'a ya bari sai zuwa da safe. Suna idar da sallar Asubahi sai ga Alhajinmu,ba za ya iya tuna zuwanshi na ƙarshe gidan ba sai ko yau.

Lokacin da ya iso su Uncle ɗin suma fitowar su kenan daga Masallacin. Duk ya yi zuru-zuru yana sanye da farar jallabiya. Alhajinmu ya zuba ma A'isha idanu, inda take ƙwance kaman ruwa. Ya dubi ɗan nashi ya ce, Abubakar wai ya ya abin ya faru ne? Uncle ya ce , nima ban sani ba, ihunta kawai na ji na fito, da na kamata ma zan maida ita cikin ɗakinta sai ta fara ihu.

Hajiya Jummai ta ce,ko mafarki ta yi ne,ni ƴasu?. Uncle ya ce in kaga yanda muka dinga cin dambe da ƙyar na kai ta ƙasa, na soma karanta mata addu'o'i. Alhajinmu ya nufi hanyar fita, Uncle ya bishi.

Bayan sun fito suka tsaya a harabar gidan, ya dube shi.

"A gaskiya Abubakar al'amarin yarinyar nan ba na zaton na asibiti ne, Malamai zamu samu. Uncle ya ce , to yanzu ya ya za'ayi? Alhajinmu ya ce, yanda za'ayi shi ne,a saka ta a mota mu tafi da ita can gidanmu, Allah ya yi mana jagora.

Haka Uncle ya ɗebo ta yaraf,ya ƙwantar bayan mota. Hajiya Jummai ta ce, asibitin za'a ko? Ya ce, a'a bai tsaya wani dogon bayani ba ya wuce ya shiga mota, don hankalinshi ya tashi na ƙarshe. Jummai da Hadiza suka tsaya jikin motar suna to Allah ya sawwaƙa. Alhajinmu ya shiga gaban motar, direba ya ja suna cewa Allah ya sauwaƙe." Alhajinmu ne ya ce,ku koma gida kun ji? Kada ku damu, Allah zai kawo sauƙi.
Chapter 20 · 0% Book details