← Book details Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 22

Sashe 14

Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ce, "Haka ne,nima fama nake da su,samarin na su duk ƴan yara babu mai shirin yin aure yanzu,ka yi musu magana da kanka,ni sun riga sun gama raina ni." Ya ce, "Shikenan, zan gan su." Sai suka ci gaba da hira tana gaya mishi cewa kayan shafanta gami da turarukanta sun ƙare, ya ce, to za ya bata ta saya. Da yake ranar ita ce dashi,ta kula da shi yanda ranshi ya gamsu cewa ta gane kurenta, ta yarda da dabarar da zasu sake tunda magani ya ƙi sai a koma kissa, don haka ko gurin ƙwanciya ta yi mishi ba zata, sannan ta sake ba shi haƙuri.

Hadiza tana ƙwance suna waya da Hajiya Lanti mahaifiyarta, tana kuka tana sanar da ita cewa, Saddiƙ ya mata wulaƙanci saboda wannan A'ishar,tun suna can ƙasar da suka tafi ya dawo don kawai ya ɗauko ta daga makaranta, sannan tunda ta dawo sai abinda ta ce.

Haka ya ɗauki ƙwanana ya kai mata, na yi magana ya fi ni fushi, yanzun da haka zancen da nake miki yau ƙwananshi biyu,ya ɗauke ta sun tafi ko'ina ni,ni ban sani ba. Sai yanzun na ganshi suna zaune da waccan tsohuwar Hajiya Jumman,ko tun yaushe ya dawo be neme ni ba? Oho."

Hajiya Lanti ta ce,da Allah ni rufe min bakinki, kin bani kunya, kishiya ki ke wa kuka, sai ka ce ba nonona ki ka sha ba? To bari ki ji in zaki dage ki dage, kuɗi za ki ƙwaƙwalo in bazama kin tsaya yin zuciya,an ce miki fada ko kishi ne silar kawo ki gidan nan? In baki sani ba, bari ki sani, na shiga na fita na kutso ki Wannan gidanne don kawai ki wawuro min dukiyarshi,ke dai dage ki samu ciki kada ki tsaya kishin banza." Hadiza ta ce, "Hajiya ni dai na fi son ki samo min taimakon da hankalinshi zai dawo kaina." Ta ce, kuɗi za ki kawo Hadiza." Ta ce, "zan kawo." Hajiya Lanti ta ce,a to, Hadiza ta ce to dama gobe ni ce da girki,in sauke kenan in daina fushin?.

Lanti ta ja dogon tsaki, "in ba iskanci ba dama ina ke ina fushi? Sauke ki kuma bashi haƙuri yaƙi ɗan zanba ne Hadiza,kin ji ko?" Ta ce, "To Hajiya sai kin zo."

*** **** **** ***

Satin A'isha biyu, Uncle ɗin ta ya yi mata waya cewa, gashi nan zuwa. Ta ce Uncle sauran fa sati ɗaya mu koma makaranta,ka bari mana sai ana sauran ƙwana uku". Ya ce, "Lallai ma Beby,waton ba kiyi missing ɗina ba ko?" Ta ce, "Nayi mana Uncle." Ya ce, "To gaya min da me ki ke tunani?" Ta ce,Da abubuwa da yawa nake tuno ka, ya ce gaya min ɗaya.

Ta yi shiru, ya ce ina jin ki mana." Ta ce, "Ka bari dai ai zan gaya maka in na dawo." Ya ce, "ke ɗin? Kin kasa gaya min yanzun a waya sai a gabana ne za ki iya? To ni bari na faɗa miki ɗaya,kina ji na? Ta ce, Eh." Ya ce, da lallausar fatarki, da kuma zazzaƙan leɓanci..." Da sauri ta kashe wayar tare da rufe fuska sai ka ce a gabanta yake. Shi ko dariya yake mata, ta kunna wayar ta tura mishi saƙon cewa "Uncle kai fa babba ne,ba ka jin kunya?" Ya duba saƙon, sai ya tura mata cewa,a cikin soyayyar ma'aurata Beby ba jin kunya wani abu ma sai in kin dawo." A ranshi ya raya cewa, bari na kashe maganar, sai ya rubuta cewa Beby shin za ki iya gaya min ya ya kike ji a duk lokacin da jikina ya haɗu da naki? Ya tura mata,aiko ya kashe magana don tana karantawa ta kashe wayar gaba ɗaya. Ta ƙwanta tana tunanin shi, Uncle tamkar zuga shi ake yi.

Umma da Abba sun yiwa A'isha nasiha a lokacin tahowarsu, Umma ta ce,"Ni dai A'isha ina ƙara yi miki nuni ne da haƙuri, musamman kasancewar ku,ku uku gidan mijinku. Ki kama kanki da bakinki, kada ki yarda ki haɗa kai da wata don kawai ki musguna ma wata,gara ace ke ake cuta ba ke kike Cutar ba. Sannan ki riƙe mijinki."

Abba ya É—ora da cewa,"ki zamo mai yi masa biyayya ki zamar masa wadda zata kai shi gidan Aljanna,ba wuta ba."

A'isha a cikin aurenki ki sa ma ranki cewa, bautar Ubangiji ki ke yi, kada ki kalli ƙyale-ƙyalen duniya da abinda ke cikin ta. Ta ce,"To Abba insha Allahu zan yi yanda ku ka ce."

Jabiru Sarkin tuƙi ya ɗauki hanya da su,yayin da suke zaune a baya suna ƴar hira. Lokacin da suka iso gida ta yi mamakin ganin Hadiza ta zo mata sannu da zuwa, cikin dakewa ta amsa,yau kam Hajiya Jummai tana gida. A'isha taje ta gaisheta, itama cikin sakin fuska ta amsa. A ran A'isha ta ce, ina ma ace har zuciyarsu, saboda gajiya A'isha ko tashi daga kan sallaya bata yi ba, bacci ya yi awon gaba da ita. A haka Uncle ɗinta ya same ta,bai tashe ta ba cak ya ɗauke ta ya ɗorata kan gado.

Hijabin kurum ya zare mata daga ita sai ɗaurin ƙirji, da alama ma wanka ta yi kafin sallar,zama ya yi ya zuba ma fuskarta idanu, komai na yarinyar yana son shi.

A hankali ya runƙufo ya sumbaci leɓunanta, sannan ya miƙe don yin shafa'i da wuturi, sannan ya zauna gaban laptop kafin lokacin da zaya ƙwanta. Ya so ƙwarai ya sami hutu da ƴar Bebynshi, amma ta gaji sai dai ya mannata a jikinshi suka ci gaba da bacci.

Washegari girkin Hadiza, da rana A'isha ta yi zoɓo don ya yi waya za ya aiko a ɗauka, Hadiza tana zaune a babban falo taga Uche ya zo ya amshi ƙwando kamar ta yi magana ta dai share.

Da yamma da ya dawo bayan ya shiga gurin Jummai, ya fito ya shiga gurin Beby, duk da cewa duk inda ya shiga lokacin shigowa gida ko lokacin fita ba ya zama, amma ya kan ɗan yi jum gurin A'isha saboda yana shan ruwa ko zoɓo.

Bayan ya fito ne ya nufi ɗakinshi kamar yadda ya saba, sai mai girki ta bi shi. Wani sabon salo wai sai Hadiza ta shigo wai ta zo (danning) inji darling don su ci abinci, kamar kar taje amma jin cewa Uncle ke kira sai ta fito. Ba shi a gurin sai Hadizan kaɗai, sai ga Hajiya Jummai,jim kaɗan shima ya fito. Ya kallesu, kowacce fuska a ɗaure in ban da A'isha wadda hankalinta ke kan T.V Hadiza ta ce, tana son ya haɗa su su dinga cin abinci tare, sai shima ya ga da hakan zata yiwu,da zai so. Don haɗin kansu yake nema ba rabuwar kansu ba. Ya yi musu sallama su suka amsa. A'isha ta ƙara da cewa sannu da fitowa." Ya ce,"yauwa Beby." Ya dubi Hadiza "Na ji daɗin wannan zaman, Allah yasa ya ɗore" duk suka ce, "Amin." Nan Hadiza aka buɗe abinci, maigidan aka soma zuba mawa, sannan ta tura ma saura plate kowa a gabanta,wai ta zuba abinda ta ke so.

A'isha ba gwanar cin abinci ba ce,don haka kawai sai ta ɗan zuba romon farfesun kazar dake gurin tasa cokali tana sha. Ya dubi plate ɗin beby wannan ne abincin? Gira ta ɗaga tare da yin murmushi, Hadiza ta ce, shi yasa baki yin ƙiba ko? Kullum kamar a hure ki ki faɗi, tana magana tana dariya, A'isha ta fahimci magana ta gaya mata da wasa,don haka ba tare da ta dube ta ba tace, "ai ƙiba ciwo ne,ke baki sani ba ne." Hajiya Jummai dai tana ji ba ta ce ƙala ba, kuma abincin da tasa sai juya cokalin take yi tana mamakin,yau ita ce zaune da kishiyoyi biyu? Abin tamkar cikin mafarki.

Shi ko sam bai ma fahimci suna jefa ma juna magana ba ne, musamman da yaga Hadiza tana fara'a ta yi maganar. Sannan A'isha bata nuna wani fushi ba. Hadiza ta ji haushin kalmar A'isha, amma bata da ta cewa, A'isha ba ta jima ba ta miƙe, Uncle ya ce, har kin ƙoshi? Ta ce, na ƙoshi Uncle." Ta dube su sai da safenku, dukkansu sun amsa ne a maƙoshi,ko mene ne yasa dukkansu suke jin zafin ta? Ta tafi ya bita da kallo, komai na Beby yana birge shi, musamman tafiyarta cikin natsuwa, tamkar mai tausayin ƙasa, wani sa'in shi kanshi sai ya dinga ganin tamkar yanga take yi. Hadiza ce ta buga cokali akan plate ya yi ƙara, sannan ya dawo daga tunanin da ya tafi, cikin ɓacin rai ta ce "ko yaushe in A'isha na guri kowa banza ne?" Ya ce "haka ki ke gani?" Ta ce, "Eh mana." Ya ce, shikenan. Ranta ya sake ɓaci, ta ce "sai ka ce wata ƴar gwal?" Bai kula ta ba, shima ya miƙe ya nufi ɗakinshi suma suka watse kowace zuciya na raɗaɗi. Washegari ma A'isha ta wuce makaranta, ta bar su suka ci gaba da neme-nemensu.

Wannan karon A'isha sun buÉ—e wuta,don daga wannan hutun sai na fita.

Hadiza dai kowane wata ana jiran a ji ciki shiga, amma shiru. Zaman su da Hajiya Jummai zama ne na ba ruwan wani da wani, sai dai ana gumawa juna ta ƙarƙashin ƙasa. Cikin haka wata ranar Lahadi maigidan nasu ya tashi da matsuwa ta buƙata, Jummai ke dashi to amma jiyan tana fashin sallah,yau kam Hadiza ce a daddafe ya kai magriba, inda so samu ne ma tunda rana ya biya buƙatarshi, ana idar da sallah ya shiga gida,kai tsaye ɗakinshi ya shiga,ya ɗauki waya ya kira layin Hadiza,sai da ta ɓata lokaci sannan ta shigo.

Ya nufe ya dafa ta, sannan ya cire ɗanƙwalin da ke kanta na shaddar da ke jikinta, doguwar riga. Abubuwan da ya soma yi mata su ne suka fahimtar da ita abinda ya ke so. Nan take mulkinta ya tashi ta ƙwace daga rungumar da ya yi mata.

"Ba ka sanin darajata sai in kana buƙata,to gaskiya nima yanzu lokacina ne, kuma ba zan yi abinda ka ke so yanzun ba." Idanunshi da suka yi jajir, ya dube ta, "Don Allah Hadiza ki bani haƙƙina, wallahi na matsu da yawa,ki min taimako.

#####
[12/14, 18:12] Ummi Tandama😇: *📗📗Page 11*
Chapter 14 · 0% Book details