← Book details Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 22

Sashe 21

Mummunan Zato Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiyarmu tana zaune cike da zullumin wane hali ƴar mutane take ciki? Jiran dawowar maigidanta kawai take yi,ta ji labarin jikin, sai ga su sun yi sallama. Uncle ɗin yana rungume da ita, tamkar babu rai, ta miƙe cike da sallallami, tana cewa,ya ya haka? Uncle ya zube ta kan kujera. Hajiyarmu ta isa gurinta tana tofa mata addu'a, Alhajinmu ya ce ina ganin lamarin kamar na jinnu, shi yasa na ce mu yi nan da ita. Yanzu zan je gurin Malam Yakubu ne yazo ya duba mana ita, suka ce to. Uncle ya zauna yana gaida mahaifiyarshi, Hajiyarmu ta amsa cike da jimami, sannan ta ce ya ya akayi haka? Nan ya shaida mata duk yanda ya sani, ta tausaya sosai. Ta kuma ci gaba da addu'a, Alhajinmu ya shigo shi da malam Yakubu,da kuma wani Malam Sufi,suka zauna suna tofa mata addu'a, tana nan dai yanda take can Malam Sufi ya soma karanto alƙur'ani mai girma cikin Suratul Baƙara,nan ta soma motsi ya matso kusa da ita yana yi cikin ɗaga murya, sai kuma ta soma gunjin kuka cikin wata irin murya. Malam Yakubu shima ya amsa. Ai tuni ta soma fizge-fizge, suka ba da umurnin a riƙe ta, Uncle ya riƙe ta gam,tana fizge-fizge. Suka ce wane ne? Wata ƙatuwar murya ta soma magana,ni ne. Kai ne wa? Ni ne umm! Umm! Suka ce kayi magana kaine wa? Ya ce sunana Sulaiman, suka ce me ya kawo ka jikinta? Ya yi shiru,nan Malam Sufi ya ci gaba da karatu, shi kuma Malam Yakubu yana mishi tambaya,ba za kayi magana ba? Ya ce,kuna ƙona ni fa zan fita, to faɗa mana me kazo yi jikin wannan baiwar Allah? Ya ce turo ni aka yi,an umarce ni ne da inzo in sakar mata jini in fitar da cikin ta. Suka ce kai Musulmi ne? Ya ce eh,ka yarda da Allah da ranar tashin alƙiyama? Ya ce eh, na yarda,to me yasa kazo ka cutar da ita? Ya ce,an sani ne. To wa ya saka? Ya ce Ubangijina,shi Malami ne ni da mahaifana muna ƙarƙashin ikon shi ne. Suka ce to yanzu zaka fita ne ko mu ci gaba da karatu? Ya ce,zan fita. Suka ce to fita ta baki ko ta hanci,sannan ka ji tsoron ranar tsayuwa a gaban Ubangiji ko da ba jinsin ku ɗaya da ita ba, akwai hisabi tsakaninku ko? Ya ce,eh, suka ce to maza ka fita. Nan take ta yi atishawa mai ƙarfi sau biyu. Jim kaɗan ta buɗe idanu, ta tsura ma silin ɗin ba. Uncle ya ce, A'isha? Jin muryar Uncle ɗin ta, sai ta yunƙura,ya riƙe ta ya tada ita zaune ta ringa kallonsu cikin mamaki. Ta dubi Uncle, me ya faru Uncle? Ya ce ba komai,sai sannu suke mata. Alhajinmu mamaki yake tamkar tatsuniya. Hajiyarmu kam har da hawaye don tausayi,nata ganin ba su yi mishi adalci ba,ko waye ya turo su? Yaro shekara da shekaru sai yanzun ya samu rabo amma har ya tsole ma wani idanu, Uncle kam burinshi ta tashi,shi dai lamarin shi ya bar wa Allah, addu'a yake yi kullum Allah ya shige mishi gaba, kuma ya kai ƙararshi gurin Allah duk wanda ya ke son ganin bayan ƙwanshi a duniya.

Sun bada magunguna irin su habbatus sauda, zaitun, sai garin itacen magarya,sun ce ta ringa yin azkar safe da yamma, sannan ta zama mai yawan jin alƙur'ani.

Alhajinmu da Uncle sun musu rakiya tare da godiya gami kuma da yi musu alkhairi mai yawa. Hajiyarmu ta matso kusa da A'isha wadda ta jingina da kujera duk gaɓoɓin jikinta ciwo suke mata,ta so ta san yaushe ta zo gidan su Hajiyarmu? Ta ce,ƴan nan sannu kin ji, A'isha ta ɗago kai ta ce ko zaki yi wanka ne? A'isha ta girgiza kai alamun a'a, sannan ta ce bacci nake ji,ta ce to yi ƙwanciyarki nan bari in ɗauko miki filo. Luba mai aiki ta shigo tana cewa Hajiya an gama a kawo?, Hajiyarmu ta ce, a'a bari su Alhajin su shigo,je ki kawo mata filo, kafin ka ce haka tuni bacci ya yi gaba da ita. Uncle sai da Hajiyarmu ta matsa mishi sannan ya tafi gida.

Su Jummai rai fal murna, addu'a take Allah yasa rai ya yi halinsa,lallai zata koma gurin wannan makamin don za'a dashi,tashin farko aiki ya soma ƙyau? Hadiza ma tana baje kan gado suna waya da Hajiya Lanti tana cewa,ai gaskiya malamin nan ya yi ne, ina ga aljannu ma ya haɗa ta da su,fatana dai Allah yasa cikin ya zube,tunda kinga damben da suka sha da maigidan? Yanzun dai ya fita da ita. Hajiya Lanti ta ce, Allah yasa asibiti suka je,kin san Aljani yana son a yi gabas shi yana yamma, ana maganin asibiti shi yana nan yana ɓanna. Suka sheƙe da dariya. WANDA YA YI NISA BA YA JIN KIRA.

Lokacin da Alhaji Saddiƙ ya shigo gidanshi, abinda bai taɓa gani ba wai yau Jummai da Hadiza ne zaune suke hira. Hakan ya yi mishi daɗi,ga nashi zaton jikin A'isha ne ya sa su zubar da komai, domin ya lura sun tausaya ma A'isha.tare suka miƙe suka nufo shi, suna cewa ya ya me jikin? Ya ce,jiki da sauƙi, Hadiza ta ce, wane asibiti aka kaita? Ya ce, tana gidan Hajiyarmu, ta dawo cikin hankalinta ma, yanzun na barta tana bacci. Jummai ta ce Alhamdulillah, amma Alhaji babu abinda ya samu cikin ko? Ya ce bana zaton ya samu matsala, ta ce amma mun gode Allah,ni dama damuwata kenan. Hadiza ta ƙara da cewa mun yi arziƙi, Allah dai ya kar lafiya,ya nufi ɗakinshi su kuma kowacce ta shige ɗakinta ba haka suka so ba,jikin A'isha yana yin sauƙi sosai ɗakin Hajiyarmu take ƙwana,zuciyar A'isha na matuƙar son Hajiyarmu,duk sanda ta farka kan sallaya take ganin wannan baiwar Allah, gashi suna jin nauyin juna balle ta tambaye ta cewa tana bacci kuwa? Sai dai duk lokacin da ta farka ta ga Hajiyarmu tana ibada, itama sai ta tashi ta hau yi. Wannan abin yasa itama Hajiyarmu jin A'isha a ranta. Ta yarda yanzun wannan yaron ya samu mata, irin matar da ta ringa mishi addu'a tun yana yaro.

A'isha na da kunya da son addini, tana jin nauyin surukanta, sai dai hakan ba ya hana ta zo ta zauna kusa da Hajiyarmun,in ko Uncle ɗin ta yazo ba ta iya yi mishi magana gaban Hajiyarmu, kuma takan miƙe da kanta ta shiga kitchen ta kawo mishi ruwa mai sanyi,ta bashi cikin girmamawa. In ko ya ce Beby ban ci abinci ba yau ta kan je ta kawo mishi ba tasa me aiki hakan yana yi wa Hajiyarmu daɗi, ba kamar Jummai ba duk da tana ƴar uwarta, ko ruwan gidan su bata sha, sannan gabansu zata yi ta yiwa mijinta yatsine-yatsine,bata la'akari da cewa su iyayan shi ne.

Uncle in zai je Ofis zaya biyo haka in ya dawo, waya kuwa sai ya kira ta fiye da sau goma a rana. Ita dai kullum zancan ta ya barta gidan Hajiyarmu,ta fi jin daɗi. Shi kuma sai ya ce a'a,ko hirarta ba ya samu sosai, ballantana ya ɗan shasshafa jikinta ya ji daɗi, sai ta ce duk me ya ke so zai mata ai gidansu Hajiyarmu ma gida ne, ya ce abinda in nazo sai ki zauna kusa da Hajiyarmu,ko magana da ƙyar ki ke amsa min, ta ce to in ban da abinka Uncle,da so ka ke inyi ya ya? Ya ce ka ji Beby da wani zance,ke baki da irin wayon nan ne naku na mata? Sai ki shige ɗaki ki zauna ni kuma na biyo ki, ta ce kai. Cikin mamaki ni dai ina jin nauyi, ya ce to ko irin rakiya ɗin nan cikin mota? Ta t, Uncle kenan,ni dai ina jin kunya, ya ce to ba zan iya barinki ba kenan ki zauna,nan da ƴan ƙwanaki zamu koma gida." Cikin shagwaɓa ta ce, kai don Allah Uncle ɗina. Ya ce Allah Bebyna. Ta ce, to in ka zo in baka ganni a falo ba ba sai ka shigo ɗakin ba. Ya ce,kin ga ina shigar ma Hajiyarmu ɗaki ne,bare ma in miki wani abu ciki? Ta ce to to ai dai haka kakeyi ba? Ya ce,in ba mutane ba, amma in da mutane sai ta ce min in fito mata daga ɗakinta tun ina ƙarami fa. Ina ga Hajiyarmu ba ta sona shi yasa nake tausayin kaina, gashi ban dace da matar da zata rungume ni ba.

A'isha ta tausaya mishi, sannan ta ce haba Uncle, ya ya zaka ce haka bayan ga ka da mata uku? Ya ce, duk ba ku damu da ni ba. Hajiya Jummai bata ma zauna ba, ballantana ta san matsalolina. Hadiza ko son abin duniyarta yasa na kasa sakin jiki da ita,ke ko Beby kunyarki ta yi yawa, ta ce to zan rage yace to na gode.

Satinta biyu gidan Uncle ya ce ma Alhajinmu tunda ta samu sauƙi yana so ta koma. Ranar da A'isha zata tafi har da kukanta,wai ita tafi son gidan Hajiyarmu, Hajiyarmu ɗin ce ta bata baki kan cewa ta ɗaure ta koma ɗakinta. Ta yi mata nasiha kan cewa ta ƙara dagewa gurin addu'a.

Su Jummai sun zo duba ta sau ɗaya, ganinta cikin hayyacinta yasa su cikin baƙin ciki, duk da suna ɓoyewa junansu mugun halinsu, ma'ana babu wadda ta nuna ma ƴar uwarta cewa tana shiga gurin bokaye, sai dai duk suna zargin junansu. Daga nan ko basu ƙara zuwa ba har kau da ta dawo gida. Sun dai shigo ɗakin sun yi mata Sannu, A'isha ta amsa tare da yi musu godiya.

*📗📗Page 16*
Chapter 21 · 0% Book details