← Book details Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 17

Sashe 9

Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙe wa ta yi da ta gaji da zaman, ita kam ta na mamakin halayyar Farouk, kullum da sabuwar ɗabi'ar da zai bijiro da ita, yau kam ko kula ta bai yi ba ya fice.
Ɗaki ta shiga ta kwanta, ta rasa me ke ma ta daɗi, tana kwanciya ta hango wannan tsakar ta ranar nan, babba ce sosai dan zata iya kaiwa girman wani ƙadangaren.
Tsura ma ta ido ta yi ta na kallon ta, idanu taga tsakar ta zaro kamar zata haɗiye ta , ga wani harshe mai lankwasa kamar na maciji.
Addu'oi ta fara karantawa a ranta, ita kam wannan tsakar tun lokacin da aka kawo ta gidan take ganin ta, gashi kullum daɗa zama abin tsoro take yi.
Ta yi shiru tana tunani ta jiyo muryar Saratu dillaliya, fitowa ta yi taga har ta yi ma kanta masauki a ɗaya daga kujerun falon.
Saratu na ganin Ummu Kulsum ta yashe baki ta fara ma ta kirari kamar ƴar maula, gaisawa sukayi da Ummu Kulsum sannan ta fara fito da kayan dake cikin jibgegen buhun ta.
"Ay in gaya miki Hajiya wannan atamfofin ƴan cotouno ne, ga kyau ga sauƙi." Saratu ta ƙarasa maganar tana washe baki.
Duba atamfofin Ummu Kulsum tayi kafin ta zaɓi guda biyu ta chake wa Saratu kuɗinta a hannu.
Bayan sunyi sallama da Saratu ta dauko Mu'ayyad wanda ke gurin mai aikin ta, abincinsa ta ba shi sannan ta kuma miƙa ma ta yaron ita kuma ta koma ɗaki ta kwanta zuciyarta duk ba daɗi.

********************************

*Ayaman(p.o.v.)*

Bayan ta gama kukan nata ta tashi ta kama wankin nan ba ji ba gani, har sai da ta kammala sa cikin mintuna ƙalilan.

Abincin da Inna Ladiyo ta dafa ta bata , ta zauna ta ci ta koshi ta yi wa Allah godiya.

Tana nan zaune har Ladiyo tayi ficewar ta ɗan Nabila na yin wanka ta fice sai ya zamana ita kaɗai ce a gidan.

Tunanin maganar da suka yi da Ladiyo ce ta dawo ma ta, Anas dai mutumin arziki ne ga hankali da nutsuwa, kuma yana da rufin asirinsa daidai gwargwado, dan da shi da mahaifiyarsa ne kaɗai aka sani shiyasa ba wanda ya bashi ƴarsa aure.

Gashi mahaifiyarsa ba lafiya ce ishashiya ce da ita ba, tana buƙatar taimakon wani, gaskiya zata amince ta aure shi ko dan taimakon baiwar Allahn nan .

Da ta gaji da tunanin ta fara karanto ƙur'ani wanda ke kanta dan rabon ta da islamiyya tun mahaifiyarta na da rai, bayan rasuwar ta Ladiyo ta katse islamiyyar.

********************************

*Farouk*

Yana fita daga gidan, gidansu ya nufa, a falo ya tarar da Hajiyarsu ana ma ta tausa, tana kallo tana cin kayan marmari.
Gidan kam dan tsaruwa ya tsaru, dan ya fi gidan Farouk girma da tsaruwa wanda bayan rasuwar mahaifinsu ne aka ƙara tsara gidan, su uku ne a family ɗinsu, babbar mace ce sunan ta Halima tana New York City da zama ita da iyalanta, sai mai bi ma ta , Raihana, tana garin Abuja da zama, sai Farouk ɗan auta, wanda ke zaune a Kano kusa da mahaifiyarsa.

Da sallama ya shiga falon, zama ya yi kusa da Ammi , murmushi dattijuwar matar ta yi, sannan ta shafa kanshi,
"Babana (haka take kiransa dan sunan mahaifinta ne da shi)ya aka yi ne?" Matar ta tambaya tana sakin sabon murmushi.

"Ina kwana Ammi" Farouk ya gaishe ta cike da ladabi.

"Lafiya ƙalau babana, ya Iyali?"
"Suna lafiya"

"Masha Allah."

"Bari na tafi office ana jira na"

"Toh babana, Allah ya bada sa'a."

"Ameen, zan dawo zuwa dare"

"Toh, Allah ya kaimu."

"Ameen ya faɗa yana ficewa."

Ammi ce ta ƙura masa ido san da yake fita, sai ya yi ma ta kama da ubansa sak , "Allah ya maka rahama Aliyu" ta faɗa tana tuna lokutan su tare.

Farouk ya na fita bai zame ko ina ba sai gidan Nafee, horn ya yi mai gadi ya buɗe mai, gaisawa suka yi da mai gadin sannan ya nufi cikin gidan.
Ya na shiga falon ya tarar da Nafee zaune ta na breakfast, daga ita sai wata yaloluwar riga a jikinta.
Baba Asabe ce ke ta kai kawo a falon ta na gyaran gidan, ya na shiga falon ya tsaya ya ƙura wa Nafee ido kamar tsohon maye.
Idanunta sun kumbura alamar ta yi kuka har ta gode wa Allah, matsawa kusa da ita ya yi ya rungumo ta jikinshi yana faɗin
"my love fushi kika yi ne naga ko kallo ba ishe ki ba?"
Kawar da kanta gefe ta yi ta na turo baki gaba, murmushin gefen baki ya saki ya na matsawa gefe, ya ce "tunda ba zaki hakura ba bari na je wurin Amrah ita zata lallaɓe ni."
Zumbur ta juyo jin ya yi maganar Amrah, "kar ka sake min maganar wannan ƴar iskar a gida na , kaji na gaya ma." Ta faɗa cike da jan kunne da masifa.

Suna nan wurin ya bata hakuri suka jima suna hira kafin ya tashi ya nufi office ɗinsu.

Nafee kuwa rai ya yi ƙal , dan Farouk ya gaya ma ta yau zasu tattauna da mahaifiyarsa a kan batun auren su, haka nan ta wuni cikin farin ciki.

********************************

*Ladiyo da Delu*

Ladiyo na gama wankan ta shirya ta nufi gidan Delu, a tsakar gida ta tarar da su ita da Mariya sun zube soyayyar kaza wadda aka baɗa ma yajin tafarnuwa a kai.

"Duniyar Allah." Ladiyo ta faɗa ta ƙarasa shiga cikin gidan.
"Ladiyo kece tafe?" Delu ta faɗa ta na yagar cinyar kaza.

"Ni ce fa Delu." Ta amsa ma ta tana ɗaukar naman ta kai baki, "waii wannan daɗi, Allah turo min da naira in more arziki na." Ladiyo ta faɗa kamar ta taka rawa.

Mariya da Delu kam ban da dariya ba abinda suke yi.
Zama Ladiyo ta yi da kyau, sannan suka haɗu su uku suka cinye kazar, bayan sun gama ci Delu ta yi ma malam surajo umarnin miƙo musu da lemu a ɗaki.
Ba musu ya tashi ya nufi ɗakin, duk ya wani susuce , ya rame ya fita hayyacinsa Delu sai abinda taga dama take yi.
Lemu biyu ya miƙo musu, ya na komawa inda ya ke zama, wanda bakin kitchen ne.
"Naga ka miƙo lemu biyu ka aje, da yawa zaka miƙo ay." Delu ta faɗa mai tana kallon sa .

"Ya ƙare ne " malam Surajo ya faɗa kamar zai yi kuka.

"Sai kaje ka siyo." Delu ta faɗa cikin halin ko in kula.

"Wai dan Allah Delu ta kike so na yi ne, duk kuɗin dake wuri na sai da na kashe su a kan ki da wannan yarinyar, sannan kin hanani fita in samo, sai bauta da na zauna nake miki a gida, hatta gonar gadon mu da aka raba kuɗin na hannunki kin hanani, ya kike so na yi ne?." Malam Surajo ya ƙarasa faɗa cikin kuka wanda duk wani mai imani zai taya sa , dan a halin da ya ke ciki ya gwammace mutuwa a kan rayuwar da ya ke.

"Wannan kuma matsalar kace ba tawa ba, matsala ta ita ce ka nemo min lemu na sha." Delu ta faɗa cikin halin ko in kula.

Ladiyo da ke zaune kam , lemun ta dauka tana shan kayanta, dan duk wannan batun ba damunta ya yi ba.

More comment more typing.......

A taya mu sharing please.

Khairat ✍️

https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB
*(Posting room)*

*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇👇*

https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

😈😈😈* MUGUNTA* 😈😈😈

By

~Khairat~🖤💙

BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM

Page ~25-26~

Sai da ta dire kwalbar lemun sannan ta kalli inda Delu take tace "ke kam ki kyale shi haka mana, da wanne zai ji, habaa deluwa."

"Kin ga fa Ladiyo babu ruwanki a harka ta, wannan matsalata ce da mijina dan haka ba ruwanki."

Iya ƙuluwa Ladiyo ta ƙulu, ranta ke tafarfasa wai ita Delu ke gaya ma haka.
Mariya da ta gaji da diramar ta tashi ta shige ɗakinta tana mitar wannan lamarin.
Su Ladiyo kuwa saboda rashin zuciya, zama ta yi ta cigaba da cin kazar har sai da ta koshi, sannan suka ɗau hira ita da Delu.
Malam Surajo na gefe yana kallon su, gaba ɗaya ya rasa me ke mai daɗi duk ya susuce ya fita hayyacinsa.

Hira tai hira har suka kai wurin la'asar suna hira dan dama sallah ba damun su ta yi ba.
Abinci suka nema suka, bayan sun ci suka dasa hirar tasu hade da fatan yau da dare zasu kai wa a bokan kan tudu ziyara.

*Ayaman(p.o.v)*

A bangaren Ayaman kuwa zamanta ta yi tana harsaso irin rayuwar da zasu yi ita da Anas, tabbas in tace bata san Anas ta yi ƙarya, rayuwarsu mai cike da nishaɗi da kaunar juna take harsashe.
Kwatsam tunanin mafarkinta ya dawo ma ta a rai a lokacin da ta yi ido biyu da wata murtukekiyar tsaka mai girman ƙadangare ta ƙwalalo ma ta idanu.
"A'uzu bi kalmatil lahi tammat min sharri ma kalaq." Ta faɗi a ranta saboda ba ƙaramin razana ta yi da ganin wannan halittar ba.
Tsoro ne ya kamata sosai ganin tsakar bata daina kallonta ba.

Hijabinta ta dauko a ɗaki ta saka ta fice daga gidan. Tana fita bata zarce ko'ina ba sai gidan su tsahare, da sallama ta shiga gidan, Innar su tsaharen ce ta fito daga banɗakin tana amsa sallamar.
Dire butar hannunta ta yi tana faɗin, "Ayaman kece tafe, sannu da zuwa."
"Ni ce inna, ina wuni?"
"Lafiya ƙalau ya mutanen gidan?"
"Su na lafiya."
"Toh ma sha Allah."

Zama ta yi a tabarmar dake tsakar gidan su na taɓa hira da Inna, "Inna yaushe tsahare zata dawo?" Ayaman ta tambaya ta na tsince shinkafar da Inna ta auno.
"Ta kusa dawo wa Ayaman, nan kusa." Inna ta bata amsa.
"Toh Allah ya kaimu."
"Amin."
Chapter 9 · 0% Book details