← Book details Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 17

Sashe 4

Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Delu! Delu! Delu! Ke ki tashi mana lokacin sallah ya yi,malam surajo mijin delu ya faɗa yana tashin ta daga bacci.
" Malam ga ruwa a bayi na aje ma fah, da shi kayi wanka dai koh?" Delu ta tambaye shi tana mitsika idanu irin na wanda ya tashi daga bacci.
"Ehh naga da dumi shiyasa nayi amfani dashi, ki tashi fah." ya gama faɗa yana fita daga dakin.
Delu kuwa wani farinciki ne ya cika ta saboda ganin aikin su ya fara aiki dan malam surajo ko da wasa baya shigowa dakinta, wai shi ne yau har da tashin ta daga bacci.

Fita tsakar gidan ta yi ta wanke fuskarta ta dau tsintsiya ta fara shara dan sallar asuba ba wani damun ta tayi ba.

*AYAMAN*

Tun bayan shigar su ɗakin tsahare, ta zauna ta fara maida numfashi sannan ta labarta ma tsahare abinda ya faru.
Tsahare sakin baki tayi tana kallon Ayaman"Toh yanzu yana gidan ne?"
"Eh Yana chan."

"Amma dai Ayaman kinyi min daidai, yanzu Ladiyo ta gane ba tsoro kike ji ba." Tsahare ta faɗa tana jan Ayaman zuwa tsakar gidan.

"Taho muje in karasa aikina, ba kowa a gidan." taja Ayaman suka fita, suka cigaba da girkin wanda tuwo ne na masara da miyar busheshen kuɓewa wanda ta ji daddawa da sauran kayan kanshi.

"Wai gidan ba kowa ne" Ayaman ta tambaya yayin da suke wanke kwanikan da suka yi amfani da shi.
"Ehh duk basa nan, sun tafi biki, ni ce kawai a gidan."

Haka suka cigaba da aikin su har suka kammala gab da lokacin da ake kiran sallar magriba. Sallah suka yi suka ci abincin da suka dafa har suka kammala.

Mahaifiyar tsahare na dawowa , tsahare ta labarta mata abin da ya faru tsakanin Ayaman da Yunusa.
"Kai jama'a, umma ta faɗa (mahaifiyar tsahare) yanzu shi yunusa har lalacewar tasa takai haka?"Gaskiya Allah ya kaimu gobe muje gurin maigari ya dawo da ke hannun mu tunda abu yaqi ci yaqi cinyewa, Ladiyon ba imani ba ga ƴaƴanta marasa ji kuma baza ta tsawatar musu ba."

"Badai a gidana ba." mahaifin tsahare ya faɗa yana ƙarasa shigowa cikin gidan, haka kawai, yarinya ba dangin ku ba kun bi so kuke ku liƙa mana ita, yarinyar da ta qi auruwa? Salan ta zo gidana ta shafama yayana baqin jini, toh wallahi baku Isa ba."
Ya numfasa ya cigaba da cewa "Yau ne kawai zan barta ta kwanan mun a gida amma zuwa gobe zata tafi."

Jiki a sanyaye tsahare ta kalli mahaifin nata tace "Dan Allah baba, wlh Ayaman tana shan wuya gurin Ladiyo kuma naga aure ay lokaci ne in yazo zata yi." Tsahare ta gama faɗa kamar zata yi kuka.

Ɗaki umman su tsahare ta umarce su su shiga, Tsahare ta ja Ayaman suka shige ciki.

Suna shiga dakin, Ayaman tace "Da kin barni na tafi tunda kinga baba baya so."
"A'a Ayaman, gobe kya tafi." tun daga haka suka cigaba da hirar su har dare ya tsala suka kwanta abubuwa da yawa a cikin zuciyar su.

*Bayan wayewar gari*

A bangaren su Ayaman tun da suka tashi ita da tsahare suka yi sallah suka kama aikin gida basu suka kammala ba sai wajen bakwai na safe sannan sukayi karin kumallo suka shirya domin zuwa gurin maigari.

Bayan mahaifin tsahare ya gama shiryawa suka fito daga gidan suka ɗauki hanyar fadar maigari su uku dan umma tana gida bata biyosu ba.

*A bangaren LADIYO*

Bayan ta tashi Bacci taga rana ta taake sosai, tsaki ta yi ta tashi ta fita daga ɗakin. Tana fita tsakar gidan taga yadda rana ta fito sosai kamar ba sanyi ake ba.

Botiki ta dauko zata debi ruwa a randa taga ya qare, tsaki ta kuma yi, ta zauna akan botikin cike da jin haushi ta furta "Zaki dawo ki same ni ne." kafin ta ja kuma jan wai tsakin ta fita da botikin ta ɗebo ruwa ta yi wanka ta dafa taliya.

Ta zauna tana ci kenan bafade ya yi mata sallama, amsawa tayi kaana ta dauki mayafi ta leqa.
" Lapiya malam?" Ladiyo ta tambaya ganin ba fade a qofar gidan Kuma tasan ita ba laifin da tayi.
" Lapiya kalau, maigari ne ya aiko ni ana neman ki a fada." ba faden ya fada yana kokarin tafiya.
"Dan Allah tsaya ta tsayar da shi, me nayi? "

" In kinje fada kya sa ni." wannan ba faden ya fada kamin yayi wucewarsa ya bar Ladiyo tana tunanin me ta aikata har ake neman ta a fada.

Komawa gidan ta yi ta ƙarasa cin taliyar ta sannan ta saka hijabi ta fito ta kama hanyar fada...

*Bangaren delu*

Bayan ta kammala gyaran gidan ta chanchada kwalliya da kayan sallan ta, doya da kwai ta soya wacce tasa malan surajo ya siyo.

Suna zaune a tsakar gidan tana bama mijin nata abinci a baki a lokaci daya kuma wani farinciki ne fal a zuciyarta.

"Gaskiya dole na koma wajen boka na kan tudu domin aikinsa yana yi sosai." Delu ta faɗa a zuciyarta tana kallon yadda malam surajo yake nuna ma ta kulawa, mutumin da bai sakin fuska da murmushi shine yau har da fara'arsa .

"Ahh ah."inna wannan dabgen ake ja a gidan nan." Mariya ta fada tana fitowa daga ɗakin, nima a zuba min nawa." ta faɗa tana miqo kwano.
"Sai yanzu kika tashi mariri yar baba." malan surajo ya fada yana washe baki.
Cike da mamaki Mariya ta amsa da "Eh baba na tashi."

" Toh sannu da tashi, delu a zuba mata abincin mana." malan Surajo ya faɗa yana kallon delu wacce ta ke ta washe baki dan ji ta ke kamar yau sallah a gurin ta.

A haka delu ta yini cikin annashuwa da farinciki Dan Gani take kamar wahalar ta ta yanke.....

Sai mun hadu a next page ... Love you all 😘 ❤️

Khairat 🖤 🖤 🖤 🖊️ 🖊️https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB
*(Posting room)*

*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇*

https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈

Written

By

Khairat 🖤🖤🖤

Dedicated to MUGUNTA hauda novel readers.

BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM

Page 13-14

A haka delu ta yini cikin annashuwa da farinciki Dan Gani take kamar wahalar ta ta yanke....

*LADIYO*

Tana tafiya tana ta faman tunanin me yasa ake neman ta a fadar maigari.

Tana isowa cikin gidan maigari aka yi mata iso zuwa inda maigari yake, zuwan ta wurin ke da wuya ta hango su Ayaman zaune cikin ɗakin.
Wata uwar harara ta aika wa Ayaman wanda yasa cikin Ayaman ya kaɗa.

Zubewa ta yi ta kwashi gaisuwa kamar ba abinda ta gani wurin maigari, bayan an amsa gaisuwarta ne, maigari ya nemi sanin ko wacece ita a wajen Ayaman.
Bayani ta yi akan cewa ita ce abokiyar zaman maman ta tun kafin ta rasu.
"Ina mahaifin ta?" Maigari ya kuma tambaya.
"Ranka ya daɗe, mahaifinta yana wajen zaman banzan da ya saba, ba aikin fari bare baƙi." ladiyo ta fada tana qara russunar da kai.
Maigari ne ya yi umarni da a je a kira mahaifin.
Bayan malam isyaku ya iso ya miqa gaisuwa wurin maigari sannan ya yi bayanin matsayin sa a wajen Ayaman.

Ayaman aka bukaci tayi bayani akan me yasa batason zaman ta tare da su Ladiyo, ta fara bayani kamar haka:
"Allah ya baka yawan rai, inna Ladiyo ta kasance kishiyar uwa mai mara tausayi da imani a gareni, tun bayan rasuwar mahaifiyata wacce aminiyar inna ladiyo ce." Ta numfasa kafin cigaba kamar haka.
"Inna ladiyo da ƴaƴanta sun daɗe suna cizguna min a rayuwa kuma na dade Ina jurewa, ina neman alfarmar a nema min wani gurin zama ba wai gidan mu ba." Ayaman ta karasa fada cikin muryar kuka.

Maigari ya numfasa kafin ya kalli Ayaman da take ta sheƙar kuka tsahare na rarrashin ta.
Maigari ya kuma kallon Ladiyo da malam Isyaku da suka yi tsuru-tsuru a gurin, sannan yace" malam isyaku kaji abinda ta fada ko"? .

"Naji ranka ya dade, muna neman afuwa kuma zamu gyara insha Allah ."

Maigari ya koma kan Ladiyo yace "ke baki ce komai ba."

"Ranka ya dade ay malam ya gama magana, muna neman afuwa kuma baza mu ƙara ba." ta karasa fade tana russunar da kai.

"Ayaman, kinji me iyayen naki suka fada, zaki haƙura ki koma gidan da zama ko koh, ki bi ra'ayin ki."

"Na hakura ranka ya dade" AYAMAN ta fada tana ƙara matsar kwalla.

"To Masha Allahu, dama maslaha muke nema Kuma tunda kin ce kin yafe Kinga shikenan komai yayi daidai" maigari ya fada yana washe baki.

Anan wurin su AYAMAN suka kammala sulhu suka koma gida, a hanya ne tsahare ta fadawa AYAMAN abinda tayi bata kyauta masu ba, kamata ya yi taqi hakura har sai an hukunta su ladiyo.

AYAMAN dai shiru tayi tana kallon tsahare na masifa dan ta rasa abin fada, dama chan bata so aka kai su Ladiyo gaban Mai gari ba.

Haka suka karasa kan hanya inda tsahare da baban ta suka kama hanyar gidan su, ita ma Ayaman suka shige gida...

*DARE*

Tun komawar su AYAMAN gida ladiyo ke ta nan nan da ita tana lallaba ta har dare ya yi suka kwanta.

(An ya kuwa ladiyo)

*DELU*

A bangaren delu kuwa sai mulki ake zubawa a gidan, dan yanzu malam surajo ya zama tamkar bawan ta (wa'iyazubillah Allah ya cigaba da tsare mu).

A yanzu ma kuwa zaune ta ke kan tabarma da nama gashashshe a gaban ta tana ta cillawa baki, hade da lemo na kwalba da ta ke kurba a hankali, yayin da malam surajo ke zaune gaban ta Yana mata firfita.

Yaro ne ya shigo gida ya gaishe su kafin ya ce ana sallama da Mariya, baki delu ta washe kafin ta ce " wane yake sallamar da ita? "Alhaji gabatari ne."

Fara'ar ta ce ta qaru, kafin tace " je ka ce tana zuwa."
"Toh" yaron ya fada yana fita.

"Mariya! Mariya! Ina kike be yar baba?" Delu ta daga murya tana Kiran Mariya.

"Gani inna."

"yawwa maza je ki shirya alhaji Gabatari ne ya zo."
Chapter 4 · 0% Book details