← Book details Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 17

Sashe 6

Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malam isyaku ne ya shigo da fadawan Maigari aka tattara mutanen aka kai su gaban maigari, bayan bayanai da yawa maigari ya zartar da hukuncin su addah Asiyah ne marasa gaskiya tunda har gida suka je.
Sannan batun Ayaman tana nan gidan ubanta ba inda zata tunda Yana da halin riqe ta, kuma haka addini ya tabbatar.

Bayan an dawo daga wurin maigari ne su addah Asiyah suka kama hanyar gida ba tare da sun kalli ko inda Ayaman take ba, Amma a zuciyoyin su tausayin Ayaman da kuma alhinin rashin ƴar uwar su ne ya dawo musu sabo.

"Ayaman! Ayaman! Ina kike ne?"

Firgigit AYAMAN ta yi daga duniyar tunanin data Lula .

"Na'am "
ta amsa kiran ladiyon tana fitowa daga ɗakin.

"Ungo abincin rana ne Maza ki cinye."
Ladiyo ta fada tana miqa mata kular abinci hade da lemon kwalba.

"Toh, nagode." Ayaman ta fada cike da mamaki qarara a fuskar ta .
Ladiyo ta lura da mamakin nata ne yasa tace "ko baki yafe min bane Ayaman?" Ta ƙarasa fada cike da makirci.
"A'a ba haka bane inna na hakura."

"Yawwa diyar albarka nagode."
Tashi Ayaman ta yi ta shiga dakin ta, yayin da ladiyo ta bita da kallon tsana ta ja tsaki kasa-kasa.

AYAMAN na shiga dakin ta , ta zauna tana ta mamakin halin Ladiyo, dazu fah ta gama hantarar ta ita ce yanzu har da abinci,
"Allah ya kyauta" ta fada tana daɗa jinjina lamarin.

Bude kwanon ta yi taga shinkafa da miya ne har da salak a kai, mayar da murfin ta yi ta ajiye kwanon gefe dan har ga Allah tana tsoron cin abincin nan duba da daga hannun wacce ya fito.

********************************

*DELU*

Ta bangaren delu kam likafa sai cigaba take dan yanzu har ta kai Mariya kullum tana kofar gida da wani saurayin an zo zance.
Haka ma malam surajo ya yi wani kala da shi duk ya firgice, banda umarnin delu ba abinda yake bi, sai hidima yake mata ita da diyar ta.

Yanzun ma zaune suke a tsakar gidan suna shan iska,Dan cikin ya yi zafi da yawa.
Mariya ce ta fito daga daki tana fadin, inna wai Ina abincin ne? Cike da muryar shagwaba.

"Laaa malam, waken tun dazu bai kammala dahuwa bane?" Delu ta fada tana kallon mijin nata.

"Na manta ne, Amma nasan yanzu ya yi kam." malan surajo ya karasa fada cikin sauri dan baya son fadan delu.
"Shi ne kazo nan ka rashe, ka saki baki kana surutu , Amma dai anyi lusari wlh." delu ta karasa fada tana riqe haba.
Ta koma kan Mariya tace "yi hakuri 'yar mama, yanxu abincin zai kammala, kinji."

"Yawwa inna na manta ban gaya miki ba, su ladiyo dazu aka kaisu fadar maigari akan wannan shegiyar Ayaman din."
" Ke habaa! " Delu ta fada tana bude baki kamar taga wani abin mamaki.
"Wlh fah, dazu da iliya yaxo yake fada min."
"Kuma banji maganar ba." delu ta fada, sannan ta cigaba da fadin.
"Wannan iliyan bana son alaqar ki da shi wlh, dan ba wani abin arziki yake tsinana miki ba."

"Toh shikenan." Mariya ta fada.

"Wai inna alhaji gabatari ne? kwana biyu Bai shigo ba.

" Wlh ban San masa ba, Amma qila yau yazo."

"Toh shikenan. "

Sai mun hadu a next page, thanks love you all 😘 ❤️......

Khairat 🖤🖤✍️✍️

https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB
*(Posting room)*

*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇*

https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈

By

Khairat 🖤✍️

BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM

Page 17-18

Hira delu da diyarta suka shiga yi,har malam Surajo ya kammala girkin ya miko musu.
Shinkafar da ya dafa ta chabe duk ta yi ruwa ta yi kamar tuwo, fuskarsa cike da tsoro kamar wanda ke gaban Zaki, ya rusuna ya aje shinkafar hade da kallon ladiyo.
" Har ka gam... " Bata karasa maganar ba ta kalli inda shinkafar ta ke.
" La'ilaha illallah, abinda ka girka kenan, lallai ma malan." delu ta numfasa sannan ta cigaba da fadin "haka ma jiya ka yi mana wannan iskancin, wai meye a kanka ne? Tunanin uban me kake?". Ta ƙarasa fada kamar zata kaiwa malam surajo duka.
"Hehehehe" mariya dake zaune ta sheqe da dariya, "wato ada in ni ce nayi wannan girkin ay duka da zagi ba wanda baka min baba, amma yau wai kaine da girki, waii giwa ta fadi, hhhhh." Mariya ta ƙarashe da dariya.
Umarni delu ta yi ma malan Surajo akan ya zubar da shinkafar ya ɗebo wata sabuwa ya dafa.
Ta bangaren malam Surajo kuwa, ya rasa me ke mai daɗi, wani ciwon kai na azaba yake yi, ga shi ya rame ya kanjame tamkar wanda ya yi cuta.
Yana mamakin yadda Mariya ta gayamai magana har ya hakura ya yi shiru, dan ba damar ramawa, koma dai mene ya san duk inda aka je aka dawo dole ya bi umarnin delu.
"Baza ka tashi bane." delu ta faɗa a ɗan tsawace.
Zumbur ya miƙe ya nufi madafar tasu, takaici cike a ransa ya dauko wata shinkafar ya wanke ya dafa.
Yana girkin yana jiyo hayaniyar delu,
"Saura kuma ka kuma lalata shinkafar, wallahi kaji na rantse kayi ta dafa sabuwa kenan." Delu ta fadi cike da daga murya wanda mutumin dake waje zai iya jiyo ta.
Cigaba da girkin sa ya yi har ya kammala, "alhamdulillah ." ya faɗa ganin shinkafar bata chabe ba.

"Assalamu alaikum. "Muryar Ladiyo ta karade gidan .

"Waalaikumus salaam ƙawar arziki, yanzu nake son zuwa gidan naki."

Ladiyo ta watsa ma ta wani kallo, sannan tace "dama kin samu duniya ba dole ki sha re ni ba".

"Wallahi ba haka bane, ƙawas." delun ta faɗa tana wani fari da idanu.

"Waya ga fara, hhhh." ladiyo ta faɗa sannan ta cigaba.
"Ni ba wannan ba ma, kinsan gobe zamu koma wurin bokan....." .
Bata karasa ba delu ta yi azamar rufe ma ta baki, alama ta yi mata da ta yi shiru.
Janta ta yi zuwa dakinta, matsar da tulin kayan dake kan gadon tayi sannan suka zauna.

"Mene? Naga kin jayo ni daki."

"Zaki ɓallo min ruwa, malam fa yana nan."

"Dan malam na nan shi ne kika wani jayo ni, mchteeww." ta karasa da jan wani uban tsaki.

"Ladiyo kar yaji fa aikin ya lalace."
"Yanzu dai ba wannan ba kin shirya koma wa wurin bokan kan tudu?" Ladiyo ta katse maganar.
"Ehhh, ina abubuwan da ya buƙata?" Delu ta tambaya.

"Ni kinsan aiki na daban, dan haka tsakani na da shi ne, sannan kuma wannan yarinyar kin san har gaban maigari ta kaimu Ni da malam?"

"Hmmm", delu ta ja numfashi sannan ta cigaba da fadin "ay dazu mariya ke gaya min, amma kwa in haka ne Ayaman ta fara sanin kanta".

"Ke dai bari delu, yanzu jiran lokaci nake ƙanƙani, na fara musguna ma ta wanda ya fi na da .
"Haka nake so muniya ta. " hannu suka tafawa sukayi sannan suka cigaba da hirar har malam surajo ya kammala girkin ya kawo musu.
Ladiyo dai tayi dariyar ta har ta gode Allah, sannan ta chachakali abincin.

Sai wurin magriba ta fito daga gidan delu, akan alƙawarin gobe zasu koma kogon boka.

*Ayaman*

A bangaren Ayaman kam tun lokacin da Ladiyo ta kawo ma ta abincin nan ta kasa ci, sai tunani da ta ke ta fama da, da kuncin rai.

Da ta gaji da tunanin, ta miƙe ta fita zuwa gidan su tsahare, ta yi rashin sa'a tsaharen bata nan, dan an sa ranar auren ta da Umar dan ƙanin baban ta, dan haka ta koma gidan babbar yayar ta domin horon aure.
Abinci babar su tsahare ta zuba ma ta, godiya ta yi,ta hau cin abincin su na ɗan taɓa hira.

Bayan wani lokaci ta tashi ta nufi gidan, Anas ta tarar yana kofar gidan da niyyar aika yaro yayi kiran ta.

"Assalamu alaikum." ta faɗa cikin sassanyar muryarta.
"Waalaikumus salaam ." Anas ya amsa ma ta cikin murmushi.
"Ya gidan?, naji abinda ya faru,me yasa kika kai su baba gaban maigari?"

"Lpy kalau, wallahi yaya(dama haka ta ke kiran Anas), ni ma ban so ba , tsahare ce ta bani shawarar hakan, duba da yanda inna ke azabtar da ni".

Ta ƙarasa maganar kamar za ta yi kuka.

"Toh meye kuma na kuka, shikenan na bar maganar. "

Shiru ta yi bata amsa masa ba.

"Amma ba'a son kai iyaye kara, saboda darajar da Allah ya yi musu, ko ba komai inna Ladiyo ay ta haife ki, dan Allah kar na ƙara ji". Ya karasa da alamar jan kunne.

"In sha Allah, yaya" ta amsa mai.
Hirar su suka cigaba da yi irin ta masoya har ladiyo ta ƙaraso, sakin baki tayi tana kallon su, ko me yazo mata a rai kuma ta saki wani murmushi.
"Ahh ah , su Ayaman ne anan, sannun ku toh." ta faɗa tana washe baki hade da russunar da kai kamar mutuniyar arziki.
"Inna Ina wuni." Anas ya gaishe ta cike da ladabi.
"Lafiya kalau ɗan albarka, ya mutanen gidan?"
"Alhamdulillah inna ya gida ya yau?"
"Wallahi qalau."

"Toh Ma sha Allah."

"A gaida mutanen gidan. " Ladiyo ta faɗa tana wucewa.
Har ta je bakin kofa kuma, "Ayaman ki shigo da shi ciki mana."
Ayaman dake tsaye tana kallon dramar ladiyo, ta amsa ma ta da "toh".

Kallon Anas ta yi ta kalli kofar da Ladiyo ta shige ciki, tace "tabb".

Sallama sukayi, Anas ya wuce ita kuma ta shige gida.

Tana shiga ta ɗauki buta ta shige banɗaki, tana fitowa ta daura alwala, ta nufi daki dan gabatar da sallar magriba.
Ladiyo ce ta shigo dakin ta tarar da Ayaman kan zanin da ta ke sallah.
"In kin idar da sallah ga garin tuwo nan ki tuƙa mana da miyar kuka."
Chapter 6 · 0% Book details