← Book details Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 17

Sashe 17

Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Ayiririri nanaye." Abinda take ta faman faɗa tana juyi kamar mahaukaciya, "Nabeela? Kinga rabo ko? Hehehe dubu ɗari biyar ba wasa ba." Ta ƙara faɗa tana shinshina kuɗin.
"Wallahi ƙamshi suke, amma wallahi ko zanyi yawo tsirara sai kin aure Alhaji, ga gidan hutu? Ay gwara kawai ko me za'a yi ayi." Ladiyo ta faɗa tana kallon Nabeela.
Nabeela dake zaune tana danna waya ko kallon Ladiyo bata yi ba bare ta amsa mata.
Haka dai Ladiyo ta ƙarasa shirmenta ta kwashe kuɗin ta sa a wata ƙaramar jaka ta rataya a ƙugunta.
Gyale ta saka ta fice daga gidan,
Bata wuce ko ina ba sai kogon bokan kan tudu.
Tana isa ta tarar da Delu na fitowa daga kogon tana saka kayanta, kallon banza suka bi juna da shi kafin ko wacce ta nufi inda zata.
Ladiyo ta cire kayanya ta ajiye a wurin kamar yadda dokar wurin ta tanadar, ita kuma Delu ta nufi hanyar barin dajin.

"Ma gaishe ka ɗan gidan uwar kowa, bokan da babu kamar sa duk faɗin duniya." Ladiyo ta faɗa tana shiga ciki.
"La'ananniyar Allah da Manzonsa , tsinanniya ƴar wuta kuma kafira, me ke tafe da ke." Boka ya faɗa yana wata ƴar ɗariya.

"Boka ƴar wuta kuma, ay baka san tsakanin bawa da ubangijinsa ba."
"Haba Ladiyo, ni da ke fa duk munsan ƴan wuta ne, meye na mai da zance kuma?"

Shiru Ladiyo tayi kafin tace, "Boka ka san me ke tafe da ni ay, babu wata mafita?"
Boka ya yi shiru kafin yace "Kinga Delu da ta fita daga nan? Toh ƙarar ki ta kawo, tana so a lalata auren yarinyar wajenki, a dagargaza miki rayuwa, amma tunda kin zo sai ki fanshi kanki." Ya ƙarasa da wani makirin murmushi.

Shiru Ladiyo tayi ta rasa me zata ce kafin chan kuma sai tayi kamar zata yi magana sai tayi shiru.

"Baza ki fanshi kanki ba? Ni zan fara aikin da aka sa ni tohm."
"Da me zan fashi kan nawa?"

Wata ƙofa ya nuna mata, babu musu ta tashi ta shiga shi kuma ya bi bayanta.

********************************

*Ayaman*

Ayaman kuwa sai ma sha Allahu, dan rayuwa tana tafiyar mata yadda take so, yanzun ma zaune suke su biyu a rumfar inna suna ta hira, dariya take yi sosai dan innar Anas akwai abin dariya ga kuma uwa uba ƙaunar da take nuna mata.
Jikinta yayi luff alamar hutu da kwanciyar hankali sun tabbata, ga wata ƙiba ta ban mamaki da tayi, haske kam ba'a magana dan dama tun chan Ayaman fara ce sai dai Ladiyo da taso ta kawar da farin sakamakon ɓaƙar azabarta.
Sallamar Anas taji, bayan sun gaisa da Inna Ayaman ta gaishe sa, wani kallo ya bita da shi ko ba komai zai samu ladan wannan baiwar Allah r dan ganinta ma kawai na sa shi farin ciki, ledar tsire ya miƙa mata.
Amsa tayi sannan ta miƙa wa Inna, "Ay ni bana cin tsire ko kin manta ciwon sukari da nake da shi." Cewar innar Anas a lokacin da Ayaman ta miƙa mata tsiren.
Innar Anas ce tace "Ku tashi ku bani wuri dare ya yi." Ta faɗi hakan ne ganin yadda Anas ke bin Ayaman da kallo.
Da sauri Anas ya miƙe yana yiwa mahaifiyarsa sallama dan dama ya ƙagu, rufo ƙofar gidan ya yi ya yi mata sallama sannan ya shige sashensu.
Sai da safe Ayaman tayi wa Inna kana ta shiga sashen.
Tana shiga ta ga Anas a bakin ƙofar kamar jiranta yake, ay kuwa ya yi wuff ya chafe ta ta faɗa jikinsa.

Saƙonni suka fara aika wa junansu kafin suka rufo kofa.

********************************

_*Nafee*_

Ita kuwa Nafee sai san barka dan rayuwa tayi dai-dai, sai fachaka take yi a dukiyar Farouk a gefe ɗaya kuma tana tunanin raba Farouk da Ummu.

Yanzu ma shirin tafiyarsu yawon cin amarci suke inda zasu ziyarci ƙasar Dubai daga nan su wuce Spain.

A ɗayan ɓangaren kuma ta kama duk wata ragamar gidan a hannunta, babu mai yin wani abu sai da izininta, ta kori ƴan aiki ta mai da Ummu a matsayinsu, yayin da ta shanye Farouk bashi da bakin magana ko mai tayi dai-dai ne.

_*Ummu Kulsum*_

Baiwar Allah, tana kitchen sai aiki take ga Mu'ayyad a bayanta sai rigima yake dole yasa sai da ta goya sa.
"Ummu" ta jiyo muryar Nafee.
Amsa wa tayi sannan ta fita zuwa wurin ta, tana falo duk ta birkita wurin kamar ba yanzu ta gama gyarawa ba.
"Ina fruit salad ɗin?"
Kame-kame ta fara yi kafin tace "Baba mai gadi bai kawo ba."

Cillo mata ɗari biyar Nafee tayi kafin tace "Ki je ki siyo." Sannan ta cigaba da abinda take.
Ɗaukar kuɗin tayi ta zira takalminta ta fice.

Tsuru tayi a ƙofar get ta ma rasa ta ina zata fara neman fruit, kallon jikinta tayi , jaga-jaga kamar ƴar aiki, ko da yake ƴar aikin ce.

Hawayen da bata so fitowarsu bane suka fara zirya a lallausan kumatunta, ta gaji har ga Allah ta gaji, gani take dama kar ta koma cikin gidan wace irin rayuwa ce wannan? Haka ta cigaba da yiwa kanta tambayoyi kafin ta fita bakin titi dan bata san inda zata nufa ba.
Ƙiiiiiiiiiiiiiiiii ƙarar mota ta bigi kunnena a lokacin da na juya zan bar wurin.

*Ladiyo*
Sai wurin tara na dare suka fito daga wannan ɗakin, tafiyar talala ta ke yi yayin da boka ke ƙyalƙyala dariya.
Wani farin haske ne ya fito daga bangon kogon na dama, neman mafaka Ladiyo ta shiga yi dan jikinta ko ƙyalle babu.
Wannan hasken wurin boka ya nufa , kafin kace me babu boka babu alamarsa a wannan kogon.
Duhu mai tsanani ne ya baibaye wurin wanda ko tafin hannunka baza ka iya gani ba.
Wata uwar ƙara Ladiyo ta saki kafin kuma diff kamar anyi ruwa an ɗauke, kogon ya yi shiru kamar babu wani ɗan Adam da ya taɓa rayuwa a wurin.

_*Delu*_

Tana dawowa daga wurin boka ta shigo gidan da aka fara gyara musu amma ba'a kammala ba, duk da haka suke zaune sai ɗan zani da aka yafa a ƙofar gidan.

Da masifa da banbami ta shigo gidan babu ko sallama, ta ajiye mayafinta ta shiga ɓanɗaki.
Sai da ta fito sannan ta lura da fuskarta da ta gani a cikin ruwan.
" Wayyo!" Ta saki wata uwar ƙara tana taɓa wurin, fuskar ta kumbura kamar fanke sai idanunta da suka yi jaa alamar taruwar jini.

Ɗakin Mariya ta nufa da gudu dan ɗauko mudubi ta kuma tabbatar wa fuskar tace ba ta aljana ba.
Abinda ta gani ne ya tsayar da ita chakk, "Mariya?" Ta faɗa cike da mamaki, waje tayo da gudu tana salati da sallalami.

Alhamdulillah a nan muka kawo ƙarshen book one, book two zai fara zuwa gobe in Allah ya kaimu domin jin wannan chakwakiya, shin waye ya ɗauke boka? Me yasa Ladiyo tayi ƙara? Me Delu ta gani har ta firgice? Sannan wannan zaman lafiya na Ayaman zai daure? Kar ku manta da alwashin da Ladiyo ta ci a kan Ayaman, na gode da gudunmawar da kuke bani a ko yaushe Allah ya saka da alkhairi.

Khairat ce ✍️ 🤍

Love you all 💞 🥰
Chapter 17 · 0% Book details