Sashe 8
Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wannan matar ta ranar nan ce ta kuma zuwar mata, kamar yadda ta saba da gudu ta biyo ta har ta zo kusa da farar matar nan wadda haske ya dabaibaye ta.
Wannan karan, matar nan mai kama da zinariya har jariri ne riƙe da ita tana miƙo ma Ayaman, ita kuma ɗayar matar bata fasa biyo ta ba.
Bayan wani lokaci kuma, wani abu kamar labule ya lulluɓe ta, ta rasa gane hanyar fita daga wannan labule , farar matar nan ce ta miƙo ma ta hannu ɗon ta fito da ita daga wannan labule, sai ɗayar matar ta cillo wani abu mai kama da maciji ya raba tsakanin ta da farar matar.
Firgigit ta farka daga baccin tana kiran sunan Allah, ta daɗe tana tunanin wannan mafarkin nata mai cike da abun mamaki, ba tun yau ta fara wannan mafarkin ba amma na yau ya fi ruɗa ta.
Ɗaga hannun ta sama ta yi ta roƙi Allah ya kawo ma ta ƙarshen wannan mafarkin mai abin mamaki.
Wani abin mamaki shi ne, a kullum in ta yi mafarkin nan a lokaci ɗaya take tashi, shi ne ana kiran sallar asuba, "koma dai mene ne , Allah ya na sane da ni." ta faɗa a ranta.
Tashi ta yi ta ɗauro alwala tazo ta fara gabatar da raka'atanul fajir kafin liman ya tada sallah.
Bayan ta idar da sallah ne ta zauna yin azkar na safiya saboda muhimmancin sa, sannan ta yi addu'ointa har gari ya fara haske .
Fita ta yi tsakar gidan, ta fara sharewa, sannan ta dauki botiki ta fara ɗiban ruwa har ta cika robobin gidan, bayan ta kammala ayyukan ta ne ta yi wanka, ta zauna jiran Ladiyo ta fito.
Yunwar da ke azalzalar cikinta ne ya sa ta tashi ta dauko ragowar tuwon jiya, ta cinye.
Tana nan zaune har rana ta fito tarr, alamar hantsi ya kai bayan ludayi kenan, wurin ƙarfe sha ɗaya kenan.
Ladiyo ce ta fito tana ta rabka uwar hamma, kallon tsakar gidan tayi , sai ta buɗe baki tace " ahh ahh Ayaman ƴar albarka, har kin gama gyaran gidan kenan."
"Ehhh inna, ina kwana?"
"Lafiya ƙalau, kin tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalau. "
"Kin karya kuwa?" Ladiyo ta tambaya cikin kulawar munafirci.
"Ehhh na ci ragowar tuwon jiya."
"Toh ya yi kyau". Ladiyo ta cigaba da faɗin " Ayaman magana nake son muyi."
Ayaman sai taji abin wani ban bara kwai, dan bata saba ba, ita fa wannan sabuwar ɗabi'ar ta Ladiyo ba ƙaramin mamaki take bata ba .
Ta dai daure tace "ina ji" a taƙaice.
"Jiya nayi magana da babanki akan wannan yaron Anas, shin kina sonsa?". Ta karashe tana kallon ta.
Shiru Ayaman ta yi ta kasa furta komai saboda mamakin da Ladiyo ta bata, tuna ranar da Anas yazo gidan Ladiyo ta fito ta ci mai mutunci kuma ta haɗa ta da babanta har ya so hallaka ta da duka.
Ɗaga kai ta yi taga Ladiyo ta tsura ma ta idanunta wanda ke matukar tsorata Ayaman ɗin.
"Zamu yi magana da Anas ɗin.", ta faɗa tana kauda kai gefe.
"Yawwa ko kefa Ayaman? Ai hakan yafi kinga azo ayi abin nan kowa ya huta, muma mu huta da ƙananun maganganu." Ta ƙarasa tana tafiya zuwa banɗaki, sannan ta cigaba da faɗin
"Kinga ƙawarki tsahare, an sa ma ta rana da ɗan uwanta , bikin saura ƴan watanni."
Ita dai Ayaman tana nan zaune bata ce uffan ba sai kallo da take bin Ladiyo da shi.
Nabila ce ta fito daga dakin tana hamma gami da miƙa, "Wai Ladiyo(haka suke kiran uwarsu da shi)naji kina maganar wai Anas ya turo a musu aure da wannan abar?" Ta karashe tana kallon Ayaman a banzance.
"Har kin tashi kenan ƴar albarka" Ladiyo ta faɗa tana washe baki.
"Ni fa ba shi na tambaye ki ba, ki ban amsa." Nabila ta faɗa kamar wadda ke magana da sa'arta ba uwarta ba.
Abin ka da uwar da batasan ciwon kan ta ba sai ta amsa ma ta da "eh, Ayaman da Anas ake so asa ma ranar aure."
Yatsina fuska Nabila ta yi , sannan ta ja tsaki, "kinga Ladiyo ga indomie chan da kwai ki dafa mana." tana gama faɗa ta koma ɗaki.
"Ayyiriri, ɗiyar arziki, Allah ya tsare gabanki da bayanki ya miki albarka." Ladiyo ta ƙarasa faɗa cikin shewa da san abin duniya.
Ayaman dai na zaune karkashin bishiya tana kallon wannan san abin duniya irin na Ladiyo.
Yaro ne ya shigo gidan da kayan wanki a kansa, "wai gashi babar mu tace zamu samu wanki?" Ya faɗa ya na ajiye kayan a ƙasa, a gaban Ayaman.
"Kala nawa ne?" Ladiyo ta yi charaf ta amshe kuɗin wankin,
Aa "Kala ashirin ne." yaron ya faɗa ma ta.
"Kuɗinku ya kama naira ɗari biyar kenan", Ladiyo ta ƙarasa faɗa tana amshe ɗari biyun dake hannun yaron sannan tace "wannan kuɗin sabulu da ruwa ne ko?"
"Eh" yaron ya amsa ma ta.
"Toh ka dawo bayan magriba ka amsa.", Ladiyo ta faɗa mai.
"Toh", yaron ya faɗa a takaice.
Duk wannan abin Ayaman na gefe tana kallon Ladiyo, a mamakinta sai taga Ladiyo ta miƙo ma ta kuɗin, sannan tace "gashi Ayaman ki siyo sabulun kiyi wankin in su zo amsar wankin sai ki amshi kudin".
Karɓar kudin ta yi sannan ta tashi ta saka hijabinta ta fita.
Shagon shafi'u ta nufa, tana zuwa taji wurin anyi tsit alhalin tun daga kan layin ake jiyo hayaniyar samarin unguwar masu zama a shagon nashi.
Sallama ta yi , ta shiga cikin shagon suka gaisa da shafi'u sannan ta karɓi sabulun ta fita.
Tana fita daga shagon taji samarin sun kwashe da dariya, juyowa ta yi ta kallesu, har wa yau kuwa kallon ta suke suna ɓaɓɓaka dariyar su.
Kwalla ce ta zubo ma ta daga idanunta, saurin tare ta ta yi har ta isa gida.
Ruwan da ta ji yana kwarara a banɗakin ne ya tabbatar ma ta da Ladiyo na sheƙa wankan ta.
Ɗakinta ta wuce ta yi zaman ta a kan zanin tana sha re kwalla....
********************************
*Nafee*
Tun da ta amshi mukullin ta fice daga harabar hotel ɗin bata zarce ko'ina ba sai gidanta dake Nassarawa GRA a Kano, maigadinta ne ya bude ma ta ƙofa ta shiga da motar harabar gidan.
Kofar parlorn ta fara budewa ta shiga ciki, a wurin shoe rack ta ajiye takalminta, mai aikinta asabe ta tarar a parlorn har ta fara baccin ta, tashin ta ta yi ɗan tafi ɗaki tunda ta dawo.
"Hajiya sannu da zuwa, an dawo lafiya?" Asabe ta gaida uwar ɗakinta.
"Lafiya kalau." Nafee ta amsa a takaice tana wani yatsina.
Ɗaki ta wuce ta kullo kofarta ba tare da ta tsaya amsa sai da safen da Asabe ke yi ma ta ba.
Cire top ɗin jikinta ta yi, ta ƴar a ƙasan ɗakin, sauran kayan jikinta ta cire duk ta zubar da su a ƙasa kamar asabe bata gyara ba.
Watsa ruwa ta yi ko ta ji sanyi a ranta na wannan wulaƙancin da Farouk ya yi ma ta. Bayan ta kammala wankan ta shafa kayan skin care ɗinta sannan ta sa kayan bacci ta yi kwanciyar ta ba tare da tunanin sallah ko addu'ar bacci ba.
********************************
*Farouk*
Sai wurin sallar asuba tukunnan ya sauko daga kan gadon, kallon Ummu Kulsum ya yi , samun kanshi ya yi da sakar ma ta murmushi, ita ma ta mayar mai da murmushin.
"Tashi muyi wanka." ya raɗa ma ta a kunne.
Tashi sukayi, banɗaki suka nufa, tare sukayi wankan sannan kowa ya yi na tsarki suka fito daga banɗakin.
Jallabiya ya dauko ya sa sannan ya dauki sallaya ya shimfiɗa musu su biyu, raka'atanul fajir ya fara gabatarwa kafin aka kira sallah ya ja su tare, bayan sun idar ne ya yi azkar ɗin sa , sannan yadauko ƙur'ani ya fara karantawa, kamar wasa ya ji wani bacci mai nauyi ya yi awon gaba da shi.
Ummu Kulsum na ganin haka ta gyara mai kwanciyar sa akan sallayar sannan ta ɗauki mu'ayyad ta fara shayar da shi saboda rigimar da ya ishe ta da shi.
Tana kammala ciyar da yaron ta mayar da shi keken su irin na yara wanda ke taimaka musu wurin koyar tafiya.
Kitchen ta nufa ta kunna fitilu yayin da Mu'ayyad ke biye da ita akan keken shi yana ta wasan shi.
Dankalin turawa ta ɗebo ta fara ferewa, tana yi tana lura da yaron, bayan ta gama fere dankalin ta yi mai yankan farfesu.
Cikin ƙasa da awa ɗaya ta kammala girkin wanda faten dankalin turawa ne wanda yaji kayan lambu da kifi.
Baba maigadi ta miƙa wa nashi sannan ta koma ɗakin ta kunna heater har ta tafasa ta juye ta fara yiwa yaron wanka, tana kammala mai wankan ta yi nata wankan , tana gama shirya yaron ya yi baccinsa , ita kuma ta fita falo ta kunna tv tana breakfast.
Tana nan zaune ƴar aikinta Maryam ta shigo, gaisawa sukayi sannan ta fara aikinta.
Tana nan zaune har Farouk ya tashi bacci ya fito ya same ta a falon, gaishe shi ta yi ya amsa ciki-ciki, dinning ya nufa ya fara breakfast ɗinshi kafin ya yi wanka ya fice daga gidan....
Ya kuke ganin labarin du Farouk?
Love you all 😘 ❤️
Khairat ✍️💙🖤
https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB
*(Posting room)*
*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇👇*
https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈
By
Khairat ✍️💙
BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM
Page 23-24