Sashe 13
Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ango Farouk ya sha shaddarsa ruwan madara wacce ta ji ɗinki na gani na faɗa, mutane da abokan arziki har ma da mutanen banzan da suka halarci taron sun taya sa murna.
Bayan an gama ɗaurin auren a kan sadaki naira dubu ɗari biyu, ango da mutanensa suka wuce five star hotel domin gudanar da reception.
Kalolin abinci da dama sai wanda mutum ya zaɓa ga kuma abubuwan sha kama daga lemuka namu na gargajiya, giya da sauran kayan shaye shaye.
An ci an sha an yi nak kuma an aikata ɓarna a wannan taron.
********************************
*_Amarya Nafee_*
Ta ɓangaren Nafeesa kam, tun daga lokacin da Farouk ya sanar da ita ɗaurin aurensu taji kamar an mallaka ma ta duniya da abinda ke cikinta, dan farin cikin da take ciki ba zai misaltu ba.
Kyaututtukan abubuwa da dama ta rinƙa yi kama daga kuɗi , kayan sawa, turarurruka da sauransu.
Bayan haka ta tara mutane dankam a cikin gidanta ana ta budiri dan har masu kiɗan ƙwarya suka hayo domin a chashe.
____________________________________
*_Ayaman_*
Yau tun da ta tashi da asuba jikinta yake ma ta wani yarrr.
Da ƙyar ta tashi ta ɗauro alwala ta yi sallah a ɗakinta.
Bayan ta idar da sallar ta zauna tana kallon ɗakinta, "Kamar ba gidan biki ba." Ta furta a hankali.
Ita dai a ganinta ba haka gidan biki yake ba, dan da bikin Tsahare tun asuba ake fara hidima.
Shiru ta yi na wani lokaci ki kafin ta buɗe bakinta ta ce "Ko da yake ni ba kamar koya nake ba, bani da gata mahaifiyarta ta rasu ta barni a lokacin da nake tsananin buƙatar ta." Kuka ne ya kufce ma ta, sai da ta yi kuka mai isar ta sannan ta miƙe.
Ta fita tsakar gida , kofar su Ladiyo ta kalla , a kulle alamar su na ciki su na sharbar bacci.
Tsintsiya ta ɗauka ta fara share tsakar gida, bayan ta kammala ta ɗauko kwanuka ta fara wanke wa.
Sallama ta ji ana rapkawa a kofar gida, muryar da baza ta taɓa mantawa ba a rayuwarta.
"Addah Asiya!!!!." Ta furta da ƙarfi tana wani irin tsalle.
Faɗawa jikin ƙanwar mahaifiyar ta ta ta yi tana wani kukan farin ciki.
Addah Suwaiba da su Addah maimuna ƴanuwan mahaifiyarta ne suka ƙarasa shigowa.
Haɗasu Ayaman ta yi ta rungume su kamar za'a kwace ma ta su.
Hawayen farin cikin dake tsere a fuskarta ne Addah Asiya ta goge ma ta da mayafinta.
"Menene na kuka kuma ɗiyar mu?." Addah Asiya ta furta ita ma kamar zata yi kuka.
Tabarmar Ladiyo Ayaman ta ɗauko ta shimfida musu, bayan ta dawo kusa da Addah Maimuna ta kwanta luf a jikinta, ji take kamar a jikin mahaifiyarta ta ke kwance.
Shiru ne ya biyo baya na wani lokaci kafin Addah Asiya ta buɗe baki ta ce "Ina Ladiyo?"
"Tana ɗaki basu tashi ba.". Ayaman ta bata amsa sannan suka ci-gaba da hirar su ta yaushe gamo.
Ayaman ta zauna ta fara basu labaran abubuwan da suka faru tun daga zuwansu na ƙarshe.
Kowannen su ba wanda bai zubar da hawaye ba, a lokacin Adda Asiya ta ke tambayar Ayaman ina kayan ɗakinta.
Shiru ta yi dan ko cokali ba'a kawo ma ta ba.
Ladiyo ce ta fito a firgice babu salati bare addu'a sai uwar hamma da take zuba wa.
"La'ilaha illah , Asiya! Suwaiba ! Maimuna! Kune a gidan."
Ladiyo ta faɗa tana washe dashashun haƙoranta.
Ta buɗe baki ta cigaba da faɗin, "Sannunku da zouwa."
Ko kallon iskar da ta kwaso Ladiyo basu yi ba, idon Ladiyo ne ya kai kan tabarmar da suke zaune.
"Kam bala'i, uban wa yace ki ɗauko min tabarma ki shimfiɗawa wannan matsiyatan?"
Kalmar matsiyata shine ya daki kunnen Addah Asiya.
Zabura Adda Asiya ta yi zata yi kan Ladiyo Adda Maimuna ta tare ta.
"A'a Asiya kinga dai mai ya faru kwanakin baya."
Tsaki Ladiyo ta saki ta fara zuba waƙar habaici iri iri.
Tashi suka yi Ayaman ta kai su gidan su Tsahare, umman su Tsahare cike da murna da mutunci ta karɓe su hannu bibbiyu.
Sai mun haɗu a next page .
Love you all 💞 🥰
Pls more comment more typing ✍️ 🤍.
Khairat ce ✍️🤍https://chat.whatsapp.com/KTQQxgEVbju3BpJCQ2YBMu
*{Posting room}*
*[ My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇]*
https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈
By
Khairat ✍️🤍
BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM
Page 37-38
Bayan su Addah Asiya sun zauna a kan tabarmar da umman su Tsahare ta shimfiɗa, nan suka fara mai da zance.
Ran Adda Asiya in ya yi dubu toh ya bace, sai a sannan ne Ayaman take jin babanta bai sanar da su Addah Asiya a kan ɗaurin aurenta da za'a yi yau sai wani saurayi da ke zuwa cin kasuwa garin ya sanar da su.
Nan suka fara tunanin haka da za'a kai yarinya babu ko cokali, nan dai suka gama shawara da umman Tsahare a kan zata raka su wurin dillaliya su siya kayan kitchen da sauransu.
Suna isa wurin dillaliya suka fara kwasar kaya dan dama da uwar kuɗinsu a ƙugu.
Duk abubuwan da ƴa mace take buƙata na aikin gida su Adda Asiya sun siya mata shi, kama daga flask din abinci zuwa na shayi da ruwan zafi, cups , cokula, tukwane, ɗan karamin gas , plate da dai sauransu.
Su na gama biyan dillaliya kuɗinta suka bawa yara kayan akai gidan su Tsahare su kuma suka wuce kasuwa.
Gado suka fara taya wa a wurin wani kafinta, gadon ya yi kyau duk da ba wani quality ne da shi ba, sai wata sabuwar katifa mai haɗe da pillow guda biyu.
Ganin lokaci zai ƙure ya sa suka siya gadon da mudubi da wardrobe mai guda uku sai kuma wani set ɗin kujerun ƙarfe kalar brown da suka siya.
Direct suka wuce gidan su Tsahare da kayan, yara da manya kowa ya tsaya yana kallon ikon Allah sai da Addah Asiya ta fara rashin mutunci sannan kowa ya watse.
Shiga cikin gidan suka yi suka tarar da Ayaman an shafa mata kurkur a jiki, Tsahare na gefe tana tsokanar ta,guda Adda Asiya ta saki kafin ta ɗan taka rawa.
Kiran sallar azahar ce ta tasar da su, bayan sun idar da sallah aka shirya amarya Ayaman cikin atamfa doguwar riga.
Tsaff amarya Ayaman ta fito cikin atamfar da tayi matuƙar kama jikinta.
Kafin kace me ƴan gulma da munafirci sun fara shigowa gidan da sunan yinin biki.
Karfe biyu na rana bayan an sakko da masallacin juma'a aka ɗaura auren Fateema Ishaq (Ayaman) da kuma angonta Anas Mustafa a kan sadaki naira dubu talatin.
********************************
*_Ummu_*
Ɗaya daga cikin window dake falon ta leƙa, motar baffi furnitures ta gani pake a daidai kofar sabon sashen da Farouk ya gina.
Wata mata ce ta fito daga sashen kanta yaji ƙarin attachment ga hannayenta kamar an yi babbaka alamar ta yi bleaching har ta gaji.
Zuciyar Ummu ce ta buga dimm, yanzu ta ina za ta iya kishi da karuwa?
Tana nan tsaye aka fara shigar da kayan ciki, cikakkun royal bed set da royal chairs ne masu matuƙar ɗaukan hankali.
Gajiya ta yi da tsayuwar ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun.
Ta rasa me ke mata daɗi, sam duniyar ta fita daga ranta, kar dai ta fara son Farouk da har take irin wannan kishin?
Mu'ayyad ne ya taho a irin keken yara wanda suke koyar tafiya ya ƙaraso wurinta, surutansa wanda ta kasa gane mai yake faɗa ya fara yi mata.
Kunna TV ta yi ko takaicin da take ji a zuciyarta zai ragu....
********************************
*_Nafee_*
Sanye take cikin dakkaken lace ɗin ta mai kalar maroon da yaji danƙareren ɗinki na gani na faɗa.
Zaune suke a falonta ita da sauran ƙawayenta su na chapkewa.
Ringtone ɗin wayarta ne ya sa ta ɗauka domin ganin mai kiran, Farouk ne, da sauri ta miƙe ta nufi ɗakinta.
Tana shiga ta tarar da wasu ƴanmata a kwance alamar sunyi shaye-shayen har sun gaji.
Ɗaka musu duka ta yi kafin kowacce ta fice a hankali tana tamɓele irin na masu shaye shaye .
Kiransa ta yi da kiran ya riga ya katse,
"Hello."
Farouk ya faɗa daga ɗayan ɓangaren.
"Hello angon Nafeesa."
"Ya taro moonlight (haka yake kiranta) ?"
"Mun gode Allah.". Nafee ta faɗa tana wani karya murya.
"Good, dama kira nayi na gaya miki na turo motaci za'a zo a ɗauko ki."
Shiru Nafee ta yi na wani lokaci kafin taji ƙittt Farouk ya kashe wayarsa.
Wallahi wannan miskilancin na Farouk yana bata mamaki, duk da cewa aikin boka yana ci amma har yanzu sai yaga dama yake yin abinda take so.
Fita ta yi ta tarar da su Hajiya Turai da muƙarrabanta sun iso.
Da gudu Nafee ta faɗa kan Hajiya Turai tana faɗin "Hajiyata sannu da zuwa."
Hajiya Turai na murmushi ta amsa wa Nafee.
Lubna Nafee ta kira ta sanar da ita Farouk ya aiko da motocin amarya.
Cikin gaggawa suka nufi ɗaki ita da Lubna.
Su na isa ɗakin Lubna ta yi sauri ta tara ruwa a banɗaki ta barbaɗa maganin da boka ya basu.
Bayan Nafee ta yi wanka da ruwan, Lubna ta fito da wani turare kai daga ganinsa kasan ba alkhairi bane ta miƙa wa Nafee.
Shafa turaren ta yi sannan ta yi hayaƙin da boka ya basu hade da shafa kwallin mallaka wanda suka amso a wurin boka.
Tsaff Nafee ta shirya cikin atamfa mai matuƙar tsada da kyau sannan ta lulluɓe cikin lifaya kamar yadda ake yiwa amare.
Sai gidan Farouk..........
(Mu dai namu fatan alkhairi ne, Allah ya bada zaman lafiya)
********************************
*_Amarya Ayaman _*
Gidan su Tsahare ya cika tanƙam da mutane dan sai hidima ake kamar nan ne gidan bikin.
Ladiyo ce a tsaye a kan matan da ke aikin abinci kamar wata isasshiya sai bada unarni take.