← Book details Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 17

Sashe 12

Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ƙuryar ɗaki Ayaman ta sami tsahare ta yi shiru kamar mai tunani, kallonta Ayaman ta yi kana ta girgiza kai hade da murmushi.
Zaunawa kusa da ita ta yi ta fara lallaɓa ta , kamar jira take tsahare ta saki wani kuka mai ban tausayi.
Da ƙyar Ayaman ta rarrashe ta, ta ɗauko ma ta kayan da zata saka, girgiza kai tsahare ta yi sannan ta miƙe ta dauko wata atamfa mai ruwan toka da ja , ta miƙa ma Ayaman guda ɗaya ita kuma ta saka ɗaya.

Riga sa skirt ne wanda ake ya yi tsahare ta ɗinka musu, ga ɗinkin ya yi matuƙar kyau, shiryawa suka yi aikuwa atamfar ta zauna daram a jikin Ayaman abin ka da farar fata.

Fitowa sukai kamar ƴan biyu kowa sai yabawa yake, wata mata ce ta bude baki tace "kai ma sha Allah, Asma'u(babar su tsahare) wannan ƴan biyun naki kamar turawa, kai ma sha Allah, Allah ya nuna mana naki." Ta ƙarasa faɗa tana kallon Ayaman.

Sunkuyar da kai Ayaman ta yi , suka cigaba da gaisawa da ƴan uwa.

Wuraren ƙarfe shida na yamma, motar daukar amarya ta iso, duk da ba wata mai tsada bace amma babu laifi.

Haka aka kwasa aka tafi kai amarya bayan nasihohi masu ratsa zuciya daga iyayenta da danginta.
Ayaman da tsahare sun sha kuka iya kuka, dan da ƙyar aka raba su, ita a ganin tsahare barin Ayaman da zata yi, kamar zai bawa Ladiyo damar cigaba da cisguna ma ta.
Ita kam Ayaman tana tunanin kewar ƙawarta mai ɗebe ma ta kewa a duk lokacin da taji duniyar ta yi ma ta zafi.

An kammala biki lafiya an kai amarya gidan mijinta wanda babu karya Usman ya yi bajinta, dan ɗaki falle ɗaya da madafa sai tsakar gida da banɗaki wanda a wannan kauyen irin wannan ginin sai ƴar gata.

Ga kayan ɗaki da aka ma ta daidai gwargwado anyi ƙoƙari, dan akwai samiru kusan ishirin da sauran kayan amfani na ƴa mace.

********************************

*Bayan wata biyu*

*Ayaman*

Kwana biyun nan ta rasa mai ke damunta, ta yi wani fari na ban mamaki da qiba, ita dai ta alaƙanta hakan da abubuwan da Ladiyo ke bata.
Yanzu ma Ladiyo ce ta shigo ɗakin ɗauke da wani kwanon rubutu a hannunta, miƙa ma Ayaman ta yi "Maza shanye ki bani kwanon."

Karɓar kwanon ta yi , ta sa dai-dai bakinta ta furta Bismillah a hankali, "Dan ubanki ba na hanaki wannan Bismillahn ba? Ko ke daƙiƙiya ce da baki gane hausa?". Ladiyo ta faɗa ta na kwace kwanon.

Matse bakin Ayaman ta yi ta ɗura ma ta rubutun har wani yana zubowa.

********************************

*Farouk*

Farouk kam yanzu kwata kwata ya daina kwana a gidansa, ya tare a gidan Nafee wacce yanzu ita kaɗai yake gani a duniyar shi.

Yanzun ma kuwa shirye-shiryen biki suke yi abinsu.

"Kalli wannan dress ɗin bae." Nafee dake kwance kan cinyarsa ta faɗa tana miƙa ma sa wayar.

Amsa ya yi ya kalla, ya ɗan taɓe baki kaɗan yace "Ta yi." A takaice.

Cigaba da kalle kalle a wayarta ta yi har zuwa wani lokaci ta tashi ta shiga ɗaki.

Sai mun haɗu a next page, more comment more typing ✍️ 💙.

Love you all 💞

Khairyy ✍️🤍https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB
*(Posting room)*

My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

😈😈😈 MUGUNTA 😈😈 😈

By

Khairat 💞

BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM

Page 33-34

**Ummu Kulsum**

Ta ɓangaren Ummu kuwa, ta mayar da al'amuran ta zuwa ga ubangiji dan ta yi imani shi zai kawo ma ta mafita.

Yanzu ma tana zaune a ɗakinta duk abun duniya ya ishe ta, muryar wata mata ta ji a bayanta,
"Kar ki damu Ummu, damuwar da kike ciki kaɗan ce ga wacce zaki fuskanta nan gaba...."

Saurin juyawa ta yi domin ganin mai magana, sai taga wayam babu kowa.
Saurin tashi ta yi ta fita daga ɗakin, shiru ta yi ta kasa taɓuka komai, ƙwanƙwasa gidan da ake yi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula.
Leƙawa ta yi taga baba maigadi baya nan, slippers ta saka sannan ta fita ta buɗe gidan.

Masu aikin gini ta gani, bayan sun gaisa ne suke sanar da ita cewa maigidan ne ya aiko su.
Shiru ta yi na wani lokaci kafin taji horn ɗin motar Farouk.

Bayan ya shigo gidan ya bawa masu aikin umarnin fara abinda ya kawo su, wurin bayan gidan suka nufa suka fara aiki.
Kangon dake kusa da su aka ruguje katangar aka hade da cikin gidan.
Ummu na gefe tana kallon ikon Allah, dimm zuciyarta ta buga kar dai ace auren Nafee Farouk zai yi, "Innalillahi wa'inna i'laihi raji'un."
Ta faɗa cike da tsoro, bin bayan Farouk ta yi cikin gidan, ɗakinsa ta nufa bakinta da sallama.
Kofar ta ƙwanƙwasa kafin ta tura ta shiga ciki.
A zaune ta tarar da shi a kan gado, "Sannu da zuwa Abban Mu'ayyad."
Ko kallon iskar da ta kwaso ta bai yi ba bare ya amsa.
Shiru ta yi sannan ta cigaba da magana, "Nace wannan masu aikin lafiya dai naga sun fara ruguje katangar gidan nan."
"Tunda ubanki ne ya siyamin filin sai ki hanani kinji." Farouk ya dakatar da ita .
"Kuma ki shirya, nan da sati biyu za'a ɗaura min aure da Nafeesa."

Shiri Ummu ta kasa mayar mai da amsa, wani baƙin ciki ne ya taho ya tare ma ta maƙoshi, kafin ta tashi jiki a saɓule ta fice daga ɗakin.
Tsaki Farouk ya yi kafin ya cigaba da danne danne a wayarsa.....

********************************

*Ayaman(p.o.v)*

Mamakin yadda jikinta ya yi wani sumul ya yi haske take yi, ga wata ƙiba ta ban mamaki da ta yi.

Indai tana lissafi yau saura kwana sha uku bikinta da Anas.

Ladiyo ce ta shigo gidan kamar an hankaɗo ta, Nabeela na biye da ita.
Ɗaki suka shige ko kallon inda Ayaman take basu yi ba, wannan halin Ladiyo na bin bokaye yana matuƙar damun ta , shirka ƙiri ƙiri kuma baka da bakin magana.

Haka dai ta zauna a wurin na wani lokaci kafin nan ta shige ɗaki.

********************************

*Nafee (p.o.v)*

Ta ɓangaren Nafeesa kam sai bankar magungunan mata take yi, duk ta bi ta rikice akan dole sai ta mallake Farouk, ga kuma ƙawayenta da ke gefe suna zuga ta .

Ga shirin biki da take yi babu kama hannun yaro abubuwa dai ba'a cewa komai.

*Bayan sati ɗaya*

*Nafee da Farouk*

Yau take ranar dinner kamar yadda suka tsara , amarya Nafeesa an sha kyau cikin wata bridal gown fara mai duwatsu a jiki, sai ango Farouk cikin shaddar shi fara ƙal wadda taji aikin yan Niger.

Bayan shigo da amarya da angonta aka fara shagali kamar yadda aka tsara.

Biki ya yi biki dan mutanen banzan da suka halarci bikin sun yi abinda ya kaisu, dan hotel ne guda aka yi renting domin shagalin biki.
An sha giya da sauran kayan shaye shayen da aka gabatar a wurin da kuma sauran saɓon Allah wanda baza su ƙirgu ba.

********************************

*Ummu Kulsum (p.o.v)*

Ita dai tun ranar da Farouk ya sanar da ita ƙarin aurensa bata kuma jin daɗin rayuwarta ba.
Tsaye take a gaban ɗaya daga cikin falon, ƙare wa gidan kallo ta yi, wani ɓangare daban aka gina a gefen ɓangarenta.

Wata aljannar duniya Farouk ya gina a wurin, dan danƙareren apartment ne mai ɗauke da ɗakuna uku kamar nata sai falo babba guda biyu da kuma kitchen babba a takaice dai part din Nafee ya fi na Ummu komai da komai.

Wallahi ta yi dana sanin amincewa sa auren Farouk wanda Ammi ce ta roƙe ta akan ta amince.

Shiru ta yi tana cigaba da tunani kafin taji muryar Maryam tana miƙo ma ta Mu'ayyad.

Amsar yaron ta yi, Maryam ta yi ma ta sallama da niyyar tafiya gida tunda yamma ta yi.

Bayan ta amshi yaron ta goya sannan ta daura abincin dare dan kanta da baba maigadi dan ta manta yaushe rabon da Farouk yaci abincinta.
Ga tarewa da ya yi a gidan Nafee sai yaga dama yake shigowa gidan idan zai ɗauko wani abin.

Ita wannan rayuwar tasu tana bata mamaki .

********************************

*Ayaman (p.o.v)*

Yau dai ya rage kwana uku bikinta da Anas amma duk wani shirye shirye da akr yi wa amarya bata ga anyi ma ta ba.

Ladiyo ce ta shigo gidan kamar an hankaɗo ta, wata baƙar leda ta cillo ma Ayaman kafin ta shige banɗaki da gudu.
Bayan ta fito ta ajiye butar take cewa Ayaman "Gashi nan , mahaifiyar Anas ce ta bayar a baki, kinsan ba shi da wasu yan'uwa bayan mahaifiyarsa."
Ladiyo ta ƙarasa cikin isgili kamar zata yi dariya.

Ledar ta buɗe taga atamfa leda guda biyu, ɗaya riga da skirt sai ɗaya doguwar riga ɗinkin simple ne ba wani ado.
Sai hijab guda ɗaya da takalmi guda ɗaya, sai man shafawa da hoda da kwalli guda ɗaya.
Guɗa Ladiyo ta saki kafin ta kyalkyale da wata dariya , "Yanzu dai a taƙaice wannan ne lefe? Hehehehe lefe iya lefe." Ladiyo ta ƙarasa cikin dariya har da riƙe ciki.
Ɗaki Ladiyo ta shige tana wata dariyar.

Ayaman kam kayan ta ɗauka ta shige ɗaki, gaskiya taji daɗi dan Anas ya yi ƙoƙari, dan rabonta da sabon ɗinki kusan shekara goma kenan a lokacin da mahaifiyarta ke da rai.

Sai mun haɗu a page na gaba, domin jib wannan auren zai yiwu kuwa🤔, .

Khairat ✍️ 🤍

https://chat.whatsapp.com/BozyCwTPDOt1Lh4BxMMKq4

*(Posting room)*

*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇👇*

https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈

By

Khairat ✍️🤍

BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM

Page 35-36

Hausawa suka ce rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya.
Ranar jumm'ah da misalin ƙarfe goma na safe ɗaruruwan mutane suka shaida ɗaurin auren Farouk Aliyu Datti da amaryarsa Nafeesa Ishaq a masallacin markaz imam Sadik dake rijiyar zaki Kano.
Chapter 12 · 0% Book details