← Book details Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 17

Sashe 14

Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A cikin ɗaki kuwa Ayaman ce zaune ita da Tsahare su na hira sama-sama, "Wallahi Ayaman naji miki daɗin auren nan da za kiyi, kinga kema kin huta da uƙubar Ladiyo."
Ayaman bata ce komai ba sai murmushi da ta yi.
Sallamar su Addah Asiya ta jiyo sun dawo daga jere.
Guɗa ake ta saki kamar ba gobe duk gidan ya ɗauka.

Nan dai suka yi zamansu har aka yi kiran magriba, umman su Tsahare ce ta shigo da sauri tana faɗin "Ayaman tashi maza maza ga masu ɗaukan amarya sun zo."
Cikin sanyi jiki Ayaman ta miƙe , wanka ta yi da ruwan da umman su Tsahare ta haɗa , tana wankan tana jin wani irin yanayi da ta rasa na mene ne.

Bayan ta kammala wankan umman su Tsahare ta shafe ta da turarurruka sannan ta saka wata doguwar rigar atamfa sai dogon mayafi da aka naɗe ta da shi.

Ladiyo ce kan gaba wurin tare amarya tana faɗin "Yi nayi bari na bari, kar naji kar na gani." Kamar wata mutuniyar arziki.

Motoci ne guda uku, ɗaya wato ta amarya Toyota ce sai sauran golf .

Ladiyo ce ta yi charaf ta shige gaban mota tana washe baki sai Delu da ta bi bayanta tana ƙoƙarin shiga bayan motar inda aka sa Ayaman, Adda Asiya ta yi saurin janyota.
Watsar da ita gefe ta yi kafin suka yi shigewarsu suka bar Delu da ƙunar rai.........

Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️ 🤍

Love you all 💞 🥰

Khairat ce ✍️ 🤍https://chat.whatsapp.com/KTQQxgEVbju3BpJCQ2YBMu
*(Posting room)*

*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇*
https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈

By

Khairat ✍️🤍

BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM

Page 39-40

__________ Su Ladiyo ne a gaban mota sai washe baki take yi, "Malam direba ka hanzarta mana." Ladiyo ta faɗa tana kallon direban.

Cikin mintinan da basu wuce talatin ba suka ƙarasa gidansu Anas inda Ayaman zata zauna.
Shiga cikin gidan suka yi da sallama , su na shiga suka tarar da innar Anas da wasu aminanta guda biyu dan duk ƴanuwan su Anas ba'a garin suke da zama ba.

Gaisuwa aka shiga yi cikin mutunta juna kafin aka buɗe ɓangaren Ayaman, ɓangaren ciki da rumfa ne ma'ana falo ɗaya sai ɗaki a ciki.
Ta hagu kuma ɗanƙaramin kitchen ɗin ta ne wanda kayan kitchen ɗin da su Addah Asiya suka siya ma ta ne a ciki.

Ta dama kuma ɓanɗaki ne sai ɗan tsakar gida ƙarami.
Shiga cikin ɗakin suka yi da amarya, zo kuga yadda Ladiyo baƙin ciki ya fito ƙarara a fuskarta.
Ƴan kujerun ƙarfe ne a falon masu kalar brown masu kyau duk da ba masu tsada bane.
Sai wasu adon ɗaki da suka sa falon ya haskaka .
Ƙuryar ɗaki aka shigar da amarya aka zaunar da ita a kan gado, shima dai ɗaki ba'a cewa komai dan ya yi kyau kalar dai mai ƙaramin ƙarfi.
Har da wardrobe mai guda uku da mudubi ƙarami.

Ladiyo tsaye ta yi tana kallon dakin bakinta cike fal da tambayoyi.

********************************

*_Amarya Nafee _*

Zaune take a kan gadonta wanda kana gani kasan an narka naira wurin siyansa.
An lulluɓe ta cikin lifaya mai kalar ja da baƙi mai matuƙar tsada da kyau.
Lubna ce ta shigo da gudu ta tarar da Nafee da wata ƙawarsu zee a kan gadon.
"Kuyi sauri ga tawagar ango." Ta faɗa tana miƙar da Nafee.
Turaren da kwallin da boka ya basu suka kuma bulbulawa Nafee.
Sannan suka kimtsa kafin suka bar ango da abokansa shigowa.
Da sallama suka shiga ɗakin, Farouk na shiga yaji dimm zuciyarsa ta buga babu dalili.
Addu'oi da fatan alkhairi ne suka biyo baya kafin abokan ango suka sallami ƙawayen amarya sannan suka wuce.
Fita Farouk ya yi dan ya raka su sannan ya kullo kofar, a kitchen ya tsaya ya taho da plate da cups.
Yana shiga ɗakin ya tarar Nafee har ta miƙe ta cire lifayar, bata ce mai ƙala ba ta shige banɗaki ta yo wanka.
Kayan baccinta ta ɗauko wata yaloluwar riga da ita gwara babu dan duk wani abu na jikinta ya bayyana.
Shima cire rigarsa ya yi ya watsa ruwa sannan ya sa kayan bacci.
Yana fitowa ya tarar Nafee har ta buɗe kazar ta fara ci, sai a sannan suka haɗa ido.
Wallahi tun da yake bai taɓa jin wannan tsoron ba a ransa, sai ya ga Nafee duk ta canza ta zama wata zakanya.
Shiru ya yi dan ji ya yi kamar an kulle mai baki, sannan shima ya zauna .
Kazar ta miƙo mai ya buɗe baki kamar ƙaramin yaro yana ci.
Chan kuma ta ture kazar ta miƙe ta yo brush a ɓanɗaki, ta fito ta tarar baya ɗakin.

Kwanciyar ta ta yi kafin taji shigowar sa ɗakin ya rufe ya kashe fitila.
Yana hawowa kana gadon ta jawoshi jikinta, "Angon Nafeesa."
Ta faɗa cikin wata siririyar murya.
Bata jira ya amsa ma ta ba ta haɗe bakinsa da nata......

More comment more typing ✍️.

Love you all 💞

Khairat ce ✍️ 🤍

https://chat.whatsapp.com/KTQQxgEVbju3BpJCQ2YBMu
*(Posting room)*

*(My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇)*

https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈

By

Khairat ✍️🤍

BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM

Page 41-42

Sai da ta daɗe tana masa wani irin rikitaccen salo kafin ya yi sauri ya ture ta.

"Pls mana my dear." Nafee ta faɗa tana wani kashe murya.
Gaskiya shi gani yake baze iya barin wani abu ya shiga tsakaninsa da Nafee ba, dan Allah na gani yasan Nafee karuwa ce, tun ba yau ba, amma shi kansa ya rasa yadda zai hana aurensa da ita .
Cikin fushi ta kuma jawosa ya kufce, kamar wani yaro ya rasa mai zaiyi ma, tsaki ta yi kafin ta daka masa wata irin tsawa kamar uwarsa.
Haka ya biye mata har ta biya buƙatarta, ko hauka yake yasan Nafee ba budurwa bace amma ya rufe bakinsa tsit!!!

(Su Nafee wannan iko )

********************************

*_Ayaman_*

Bayan wani lokaci Adda Asiya ta kora mutane ganin dare ya yi , sannan aka bar Ayaman ita kaɗai tunda ba wasu ƴanuwa da ƙawaye take da su ba.

Su na tafiya Ayaman taji shigowar su innar Anas, bayan sun gama bata haƙuri duk a ganinsu kukan rashin gida take ita kuwa tasan kukan me take.

Bayan sun fita ta miƙe ta leƙa ta taga, hasken farin wata ne tarr ya fito ya haskaka ilahirin garin.
Ƙarar wutar nefa ce ta bugi kunnenta kafin taji mutanen unguwar sun ɗau kuwwar "Nepa!!!" Da alama sun daɗe basu ga wutar nefa ba.

Ƙare wa ɗakin kallo ta yi , banda "Ma sha Allah." da "Allah ya saka da alkhairi." babu abinda take faɗa.

Ta leƙa kitchen da banɗakin, gaskiya sun mata kyau bata taɓa tsammanin haka su Adda Asiya suka kashe kuɗi ba.
Ta koma ɗakin ita dai komai ya yi mata wallahi, agogon dake jikin bango ta kalla, da yake ba sabawa da agogo tayi ba sai bata gane ƙarfe nawa bane.

Alwala ta ɗauro kafin ta rama sallar isha'i da ake bin ta.
Muryar Anas taji yana gaisawa da mahaifiyarsa kafin ya yi mata sallama .
Ya shigo sashen nasu bayan ya rufo kofa.

Ƙara ɗuƙufar da kanta ta yi jin muryarsa a ɗakin, "Waalaikumus salaam." Ta amsa masa sallamar.

"Amarsu ta ango." Ya faɗa yana ƙara washe baki.
Shiru suka yi na wani lokaci kafin ya tashi ya umarce ta da su gabatar da raka'a biyu dan su godewa Ubangiji ga wannan ni'ima tasa.

Bayan sun idar ya fito da ledar tsirensa wanda sai tashin kamshi yake ga ɗumi alamar bai daɗe ba, sai kuma lemon zaƙi da kuma fanta guda ɗaya.

Buɗe fantar ya yi ya miƙa wa Ayaman, girgiza kai ta yi alamar a'a, takura ta ya yi har ta amsa ta kurɓa ta ajiye.

Tsiren ya ɗauko zai kai bakinta, kamshin turarensa da kuma kamshin tsiren ya haɗe mata sai jin tashin zuciya ta yi kafin kace me ta fara amai.......

********************************

*Ladiyo*

Cike da tunani kala² ta koma gida, kanta duk ya yi zafi, wai taya za'a ce Ayaman ta tafi gidan ni'ima haka?

"Wallahi bazai yiwu ba, ko zan tafi tsirara sai na hana Ayaman zaman lafiya!!"

Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️

Khairat ce ✍️ 🤍

Love you all 💞😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈

By

Khairat ✍️🤍

*(Posting room)*
https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr

*My WhatsApp group comment section 👇👇👇*
https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.

_With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_

BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM

Page 43-44

_____________Haka Ladiyo ta gama surutanta har ta jira shigowar Nabila gidan.
"Toh ni mai kike so nace Ladiyo?" Nabila ta faɗa tana kurɓar yoghurt ɗin hannunta.
"Bangane mai zaki ce ba? Kin manta alwashin da naci a kan Ayaman? Wallahi bazan bar ta ta zauna lafiya ba." Ladiyo ta ƙarashe cike da takaici.

"Ba ma wannan ba, kinsan Alhaji Gabatari yana so ya turo a fara maganar auren mu."

"Ayiririri , lallai ne kice su Nabila sai gidan Alhaji." Ladiyo ta ƙarashe cikin shewa.
Firarsu suka cigaba da yi kafin dare ya tsala suka nufi makwancin su.

********************************

*_Ummu Kulsum _*

Tun da ta zauna a falon bata kuma motsawa ba illa kallon tv da take wanda shima ba ganesa take ba.
Kukan Mu'ayyad ne ya tasar da ita ta nufi ɗaki, dan kwantar da shi.
Ta kwantar da shi a gadonsa kenan tana tofa mai addu'oi sai jin shewa da kuma muryar masu kawo amarya.
Ita a ganinta ana kawo amarya gurin uwargida domin sanin juna amma ko hauka take tasan ba zai yiwu ba.
Chan taji muryar wata mata da alama irin maroƙiya ce sai kirari take yiwa amarya Nafeesa wacce ta laɓe luff a cikin lifayarta purple color.
Chapter 14 · 0% Book details