← Book details Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 17

Sashe 7

Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Toh inna." ta amsa ma ta sannan ta bita suka fita tare.
Garin ta fara tankade wa sannan ta daura ruwan a kan murhun.
A ƙasa da awa ɗaya ta kammala girkin kasancewar da iska a garin.
Tana gamawa ta wanke kwanonin ta tattare murhun wuri ɗaya.
Ladiyo ce ta fito daga ɗakin ta, "yawwa, sannu ƴar albarka".

"Yawwa inna".
Kwano ta dauko ta bawa Ayaman din ta zuba nata har da man shanu da yajin daddawa mai matukar kamshi .
A tsakar gidan ta shimfida tabarma ta yi zamanta ga hasken watan da ya haskaka ko ina tarrr kamar rana.
Iskar dake kadawa hade da kamshin abincin, da kuma hasken watan ya bada wani yanayi na daban, tunanin rayuwar su ta baya ta fara.

Kwance ta ke a kan cinyar innar ta tana shafa mata kai, yanayin yayi dai-dai da wanda take ciki yanzu, ta tsuniya ta ke bata a lokacin.
Abban ta ne ya shigo da sallama, sannu da zuwa sukayi mai, bayan ya nitsu innar ta gabatar da abincin dare wanda
tuwon masara ne da miyar kuka.
Tsire da fura abbanta ya fito da, daga jakarsa. Bayan sun kammala cin abincin ne innar ta ta dauko furar tana damawa suna taɓa hira har ta kammala suka cinye kayan su...
Firgigit ta dawo daga tunanin, hawaye taji yana sauka daga idanun ta, kallon tuwon ta yi, ji tayi gaba daya ya fitar mata daga rai.
Rufe abincin ta yi ta kai ɗaki ko dan da safe, alwalar bacci ta ɗauro, kichibis ta yi da Ladiyo tana fitowa daga ɗakinta, sallama ladiyo tayi mata. Ita kam tana ta mamakin ladiyo da dabi'ar ta ta ke.

Daki ta shige ta yi shafa'i da wutiri sannan ta yi addu'arta ta kwanta don bacci......

Ladiyo kam sai da ta raba dare tana tunani da kuma jiran shigowar Nabila.
Sai wurin sha biyu na dare sannan Nabila ta shigo gidan, da gasashiyar kaza, zama sukai suka tadar wa kazar har sai da suka cinye sannan sukai kwanciyar su...

Love you all 😘 ❤️ ❤️

Khairat ✍️✍️✍️🖤https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB
*(Posting room)*

*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇👇*

https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

😈😈😈*MUGUNTA*😈😈😈

By

Khairat ✍️🖤

BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM

Page 19-20

Sai wurin sha biyu na dare Nabila ta shigo gidan,da gasashiyar kaza, zama sukayi ta re da cinye kazar,sannan suka mai da haƙarƙari suka kwanta.

*5 star hotel*

Hausawa suka ce dare mahutar bawa, amma a wannan wurin hakan ya bambanta.
Hotel ne na manyan mutane, iya tsaruwa wurin ya tsaru, amma kash! Ba abinda ake aikatawa a wannan wurin sai alfasha da saɓawa Allah (wa'iyazubillah).
Babban hall ne dake cikin hotel din, fitilu sun haskaka wurin sai ya yi kamar rana ce ba dare ba, cikin hall din kuwa fitilu ne masu mabanbantan kaloli wanda ya haɗa da jar kala, kore, shudi(blue), da sauransu.
Waƙa ce ke tashi a wurin, wanda tun daga harabar hotel din ake jiyo wa, samari da ƴanmata ne chakude a wurin kowa da abinda yake .
Wasu na zaune a kujerun sofa din dake wurin su na shaye-shaye, yayin da wasu ke tsaye suna kwasar rawa, wasu ko na abinda bai kamata ba.
Wani kyakkyawan saurayi ne ke zaune a ɗaya daga kujerun sofar dake cikin hall din, ya sha giya ya yi tatil, ga matan banza zagaye da shi, surutan banza yake ta yi wanda ke nuna a bige yake.

Wata matashiyar budurwa dake ta tiƙar rawa tun dazu ce ta taho zuwa inda yake, kallon matan da suka zagaye shi tayi sannan ta watsa musu kallon banza.
"Dallah ku tashi ku bani wuri, sai kace mayu kun zo kun sa shi a gaba." ta karashe maganar cikin yatsina fuska gami da kallon banza.
Sumsum suka tashi daga inda yake, dan sunsan halin Nafee.
Amrah ce kaɗai ta zauna saboda sun saba faɗa da Nafee.
"Baki ji me nace ba?" Nafee ta tambayi Amrah hade da ƙare ma ta kallo.
"Ehhh, bazan tashi ba, in ubanki ne wanda bamu san asalin sa ba, ya sayi kujerar sai ki tashe ni." Amrah ta gaya ma ta tana kauda kai gefe.
"Kut....... Nafee ta auno wata uwar ashariya ta danna wa amrah, sannan ta chakumo wuyanta, tai ma ta wata irin shaƙa wanda da ƙyar amrah ke numfashi.
Da yake mutanen banza ne a wurin, ba wanda ya yi yunƙurin raba su faɗan, sai ma waya da suka ciro suna musu video inda wasu ke ihun "ku chasu mata ku chasu." suna faɗin sun samu videon posting a social media dan samun mabiya.
Sai da Nafee ta tabbatar amrah taji jiki a hannunta sannan ta ƙyale ta , sakin ta ta yi kasa, yarap! Kake jin Amrah ta faɗi a kasa.
Duk wannan diramar da ake sha wannan saurayin na nan zaune yana kallon su, tsaki ya yi ya tashi ya fice daga hall ɗin.
Sai da ya kai kofar motar shi ƙirar honda accord 2019, sai ya tsaya, aljihun shi ya duba ya ga ba mukullin motar, "oh shit!" Ya fada yana riƙe kanshi.
Guards ɗin dake tsaye bakin kofar hall ɗin ya yi wa umarnin su ɗauko mai mukullansa da wayoyinsa.
Amsa mai sukayi , ɗaya a cikin su ya tafi dauko mukullan, bayan wasu daƙiƙai ya dawo da mukullan da wayoyin .
Ƙarɓa ya yi ya bude motar ya shiga wurin mazaunin driver, Nafee ce ta bude gidan gaba ta shiga ta zauna, kallon ta ya yi duk ta wani firgice, tsaki ya yi yace "'Fitar min a mota.'" shiru ta yi taƙi fita, "I said get outt!!!" Ya fada cikin karaɗi.
Buɗe murfin motar ta yi ta fita, riƙe murfin ta yi tana kallonsa, jan motarsa ya yi da gudu ya fice daga harabar hotel ɗin.
Tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, bige ta da ya kusan yi ne ya sa matsa da sauri, "Lallai ma Farouk, ita zai ma haka?".
Gajiya ta yi da tsayuwar ta koma cikin hall ɗin, wurin Meenah (ƙawar ta) ta nufa, amsar mukullin motar ta ta yi ta fice , motar ta tada ta fice daga hotel ɗin.

Gudu ya ke zabgawa akan titin, Allah ma ya sa babu motoci akan titin dan a lokacin wurin ƙarfe uku na dare ne.
Ikon Allah ne kawai yakai shi gidansa dake hotoro tsamiyar boka.
Horn ya shiga danna wa ba ƙaƙƙauta wa, baba Hassan maigadi da ya fara gyangyaɗi ne ya taso da gudu don bude wa ubangidan nasa kofa.
Ko ƙarasa bude get din bai yi ba , Farouk ya danno hancin motarsa cikin gidan, wanda ya kusan bige baba Hassan.
Ko ƙarasa parking ɗin bai yi ba ya fito daga motar, gidan babba ne duk da duplex ne (mara bene) amma ya ƙayatu, flowers kala-kala masu bada kamshi na musamman da niimatacciyar iska.
Kofar parlorn ya nufa wadda ƙatuwa ce mai kauri, bullet proof ce, kalar brown wadda ake ya yi a wannan lokacin.
Buɗe kofar parlorn ya yi, babu haske sai na wasu ƙananan fitilu marasa haske sosai, sai suka bada wani haske mai sanyi a parlorn.
Wucewa ya yi zuwa ɗakinsa, ya kunna fitila.
Babban ɗaki ne mai ɗauke da danƙareren royal Italian bed, gado ne babba sosai wanda mutane biyar za su kwanta har su wataya.
Ajiye wayarshi ya yi sannan ya fara rage kayan jikinsa, banɗakin ya buɗe, ba wani babba bane sosai,ya wuce wurin shower ya sakar wa kansa ruwa, "oh God!" Ya fada yana ɗaga kansa sama.
Sai da ya kammala wankansa sannan ya fito daga banɗakin, gaban madubi ya tsaya ya shafa mayukan shafawa sannan ya saka kayan bacci ya nufi ƙofar fita.
Kashe fitilar ɗakin ya yi, sannan ya fice daga ɗakin. Ɗakin Ummu Kulsum (matarsa) ya nufa, buɗe kofar ya yi, har zai shiga sai kuma ya tsaya a bakin kofar kusan minti goma yana nan tsaye yana kallon ta, kwance take cikin kayan baccinta sai jaririn da ke gefen ta tana shayar da shi.
Shiga ya yi ya rufo kofar.

Nima kuma na rufe page ɗin😅 kuyi hakuri da small page ɗin ...

Love you all 😘 ❤️

Khairat ✍️https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB
*(Posting room)*

*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇*

https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

😈😈😈 *MUGUNTA *😈😈😈

By

Khairat ✍️🖤💙

BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM

Page 21-22

Shiga ya yi ya rufo kofar ɗakin. gaban gaɗon ya tsaya, suffar nasa sak sai dai kalar da ta bam banta su, nata fari ne ƙal, ya yin da na shi ya ke golden color.
Kwance take ta lulluɓa da bargo sai jaririn da ke kusa da ita tana shayar da shi, da alamu rigimar dare ya yi ma ta har ta farka yanzu kam ta fara gyan gyaɗi bata sa ni ba.

A hankali ya zare yaron daga jikinta, ɗan riƙe shi ta yi cikin magagin bacci, "ubansa ne." ya raɗa ma ta a kunne.
Sakin yaron ta yi sannan ta kuma jan bargon mai tsananin laushi.
Yaron ya riƙe a hannunsa, ya tsaya yana ƙare ma sa kallo , mamakin tsananin kamar da suke yi shi da yaron ya ke, kama sosai kamar an tsaga kara.
Ba wani fari ne shi ba amma za'a iya kiran sa ruwan tarwaɗa, kalar fatar yan yanƙin Senegal,Egypt da maka mantan su, hakan ya samo asali ne daga kasancewar mahaifiyarsa ƴar Morocco ce, sa shin baƙaƙen larabawa kenan, inda mahaifinsa buzu ne dan asalin ƙasar Niger.
Hanci kuwa, gadon sa ya yi daga mahaifiyarsa , dan ta kasance mace kyakkyawa me kyakkyawar zuciya .
Cigaba da tsurawa yaron ido ya yi kafin ya ajiye shi a gadon shi na yara mai net.
Kan gadon ya koma kusa da matarsa, ya matso da ita kusa da shi, ɗan hura ma ta iska ya yi sannan ya raɗa ma ta a kunne, "momyn Mu'ayyad, ga dadyn Mu'ayyad ." Sannan ya yi murmushi kamar tana ganin sa.

********************************

*AYAMAN (P.O.V)*

*Mafarki*
Chapter 7 · 0% Book details