← Book details Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 17

Sashe 15

Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaye tayi tana sauraron matar ta window tana faɗin "Ki shiga ki fito da munafuka Nafeesa, kin ci dubu sai ceto mata ƙwalli ɗaya a gidan Farouk Datti, yanzu Farouk zai san ya yi aure wallahi." Matar ta ƙarshe cike da tsiwa da kuma shaƙiyanci.

Haka suka sallame ta da kuɗaɗe kafin aka shigar da amarya sashinta.

Haka ta zauna a ƙasan tiles ta rasa me ke mata daɗi, wani yanzu Farouk zai san ya yi aure, hawayen da bata shiryawa ba ne suka taho ta kuncinta.

Wannan kalaman sun mata zafi, ita kanta ta san ta kamu da son Farouk tunda ba tun yau suke tare ba, bugu da ƙari Farouk mugun ɗan wanka ne wanda a kallo ɗaya zai iya sace zuciyar mace.

Tana nan a zaune a wurin har taji shigowar tawagar ango da abokansa, leƙa wa ta yi ta taga ta hango Farouk sai sheƙi yake cikin dakakkiyar shaddarsa ruwan madara mai kyau da tsada.

Tana tsaye har ta ga fitowar su tare da ƙawayen amarya sun wuce sai Farouk da ya biyo bayansu.
Karaff suka haɗa ido da Farouk, sakin wani makirin murmushi ya yi kana ya mata blowing kiss.

Alwala ta ɗauro ganin zaman bai da wani amfani sannan ta tayar da sallah.
Ita kanta bata san adadin raka'ar da ta yi ba ta fara jin bacci.
Kayan bacci ta sauya sannan ta kashe fitila ta kwanta.

Ihun da Nafee take yi duk ya bi ya takura ta,da take bangon dakinta da na Nafee katanga ɗaya ce dan a manne suke.
Mamaki falll a ranta, "Dama haka amarya take a daren farko?" Tambayar da ta yi ta sako wa kanta kenan babu mai amsa mata.
Gaba ɗaya ta kasa baccin ga Mu'ayyad da ya dame ta da rigima ta rasa ta meye, tashi zaune ta yi duk ta rasa me ke mata daɗi da yaron zata ji ko da wannan mutanen?

********************************

*_Delu_*

Cikin kuka Mariya ta shigo gidan tana bubbuga ƙafa, "Wallahi Inna sai na aure Alhaji Gabatari, taya zai ce ya fasa aure na?" Ta ƙarasa maganar cikin kuka.

"Ya fasa aurenki kamar ya?" Delu ta zabura tana tambayar ta.

"Wallahi cewa ya yi ya fasa aure na wai da Nabila zai yi auren."
"Wace.. Nabeelan...?" Delu ta tambaya a ɗan tsorace.

"Nabeelan Ladiyo mana, wannan munafukar ƙawar taki." Mariya ta faɗa cike da rashin kunya.

"Kam bala'i Ladiyo......." Delu ta saɓi mayafinta ta fice daga gidan.

********************************

*_Ayaman_*

Haka suka kwanta cike da tantama a ranta, amai? Ta ya ya? Sune tambayoyin da take ta yiwa kanta.
Anas kuwa banda lallaɓata ba abinda yake dan har ga Allah ya na matuƙar son Ayaman.

Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️

Khairat ce ✍️🤍

Love you all 💞🥰

😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈

By

Khairat ✍️🤍

https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr
*(Posting room)*

*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇*

https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.

_With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_

BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM

Page 45-46

---------------------------------------------------

Ƙarar bige kwanikan ne ya fito da Ladiyo babu shiri, "Wani ɗan...." Sai kuma tayi shiru sakamakon ganin Delu tana huci kamar zakanya.
"Aw Delu, kece kike wannan ɗayan aikin sai kace taɓabɓiya?"

"Uwarki ce taɓabɓiya Ladiyo, ni za ki yi wa wannan rashin amanar? Ki juyar da hankali Alhaji ya koma kan ƴar ki? Toh wallahi ko sama da ƙasa zata haɗe ba zai yiwu ba."
"Hehehe." Ladiyo ta kece da wata irin dariya kana ta cigaba da faɗin
"Ashe a kan wannan ƴar ƙaramar maganar kika kwaso jiki kika zo min gidan da tsohon daren nan, toh bari kiji gobe in Allah ya kaimu Alhaji Gabatari zai turo a nemar masa auren Nabeela."
In ran Delu ya kai dubu to ya gama ɓaci, ta juya bayanta taga tunkunyar da suke girki ta ɗauko ta tayo kan Ladiyo.
Cike da dabara Ladiyo ta juya bayan Delu ta kwace tukunyar ta rafka mata a kai.
Kafin kace me faɗa ya kaure tsakaninsu, ita Ladiyo ga girman jiki ga ƙarfi, ita kuma Delu ga ƙanƙantar jiki ga kuri.
Mutane ne suka fara shigowa gidan duk da dare ya yi dan ganin mai ke faruwa, Baba Lami ce wata dattijuwa a layinsu ta shigo tana faɗin "Ku rabu da karnuka su cinye kansu, ji kaina wannan munafukan sun addabe ni haka ina ji ina gani suka daƙile auren Binta saboda tsabar munafinci."

Haka kowa ya fara ja da baya yana tofa albarkacin bakinsu, a ƙarshe dai Delu ganin Ladiyo na ƙoƙarin kashe ta ta samu hanyar tsira ta fice tana faɗin "Allah ya isa kuma sai ta rama."
Ladiyo kuwa ranta fess ta doke shegiya haka ta rufo kofarta.

********************************

*_Farouk da Nafee _*

*Bayan wayewar gari*

Taɓa sa da taji yana yi ne ya tasar da shi, "Good morning angona." Nafee ta faɗa tana shirin kai mai kiss.
Saurin tashi ya yi daga gadon ya shige banɗaki ya kullo kofar.
Brush ya fara yi kafin ya yi wanka, sai da ya kammala wankan ya ga babu towel bare wasu kayan, gashi wallahi mugun kunyar Nafeesa yake ji dan jiya ta shayar da shi ruwan mamaki.

Tsayawa ya yi na kusan minti goma sannan ya mayar da kayansa ya fito.
A kan gadon ya tarar da ita tana ƙoƙarin magana ya yi saurin ficewa daga ɗakin.
Direct sashen Ummu Kulsum ya nufa, ƙwanƙwasa ƙofar ya yi dan a kulle take kuma babu mukulli a hannunsa.
Ummu ce ta zo buɗe masa sai Mu'ayyad da ke bayanta yana tafiya a keken koyon tafiya, "Ina kwana." Tayi saurin gaishesa haɗe da russunar da kai.

Bai amsa mata ba ya ɗauki Mu'ayyad suka nufi ɗakinsa.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta kullo ƙofar.
Aikinta ta cigaba da yi a kitchen har ta kammala, shigowarsa kitchen ɗin ta ji shi da yaron a hannunsa ya na ta mai wasa.
Ya sauya kaya ya sa wasu ƙananan kaya na shan iska.
"In kin kammala abincin ki kai ɓangaren Nafeesa muna jiranki." Abinda ya faɗa kenan sannan ya yi ficewarsa daga sashen.
A falo ya tarar da Nafee ta na kallo, kallonsa ta yi kafin tace "Wannan yaron fa?"
"Ai kin san ɗa na ne ko kuwa."

"Ko ma jikanka ne wallahi mayar da shi wurin uwarsa zaka yi, dan baze zo ya ɓata min sababbin kujeru na ba."
Shiru Farouk ya yi, dan Nafee kam tsoro ta fara bashi.
Ƙwanƙwasa ƙofar da ake yi ne ya ja hankalinsu zuwa wurin, "Waye?" Farouk ya tambaya.

"Ni ce." Ummu ta mayar mai cikin sassanyar muryarta.

Buɗe ƙofar ya yi ya bara damar shigowa falon, "Ina kwana?" Ummu ta gaisar da Nafee.
Ko kallo bata ishe ta ba ta cigaba da kallonta.
"A ina zan ajiye abincin?" Ummu ta kuma tambaya.
"A kan uwarki, baki ga dining ba?" Nafee ta bata amsa a zafafe.
A hankali Ummu ta tashi daga tsugunon ta nufi dining ta ajiye abincin.
Har ta yi hanyar fita ta ji muryar Farouk "Zo ki ɗauke yaron."
Ɗaukar Mu'ayyad ta yi suka fice daga sashen.

Tana shiga sashenta ta zauna tana tunani, yanzu da wannan mutanen zata zauna?

********************************

*Ayaman*

Da asuba ta farka, alwala ta ɗauro kafin tazo ta tashi Anas, ya shirya ya fice zuwa masallaci, ita kuma ta tayar da sallah.
Ta na cikin azkar taji shigowar Anas, "Ina kwana?"
"Lafiya ƙalau Ayaman, ya kwanan sabon wuri?"

"Alhamdulillah."
Komawa ɗaki ya yi ya kwanta, ita kuwa Ayaman ta yi tsuru dan ba saba baccin safe ta yi ba.
Kan kujera ta koma ta kwanta ta na tunanin wai ita ce a kujera yau, tunda take a rayuwa bata taɓa ganin kujeru na falo a gidansu ba sai dai wani gidan amma yau ita ce a nata kujerun.
Ikon Allah kenan kowacce irin ƙaddara Allah ya baka akwai sakayya in dai kayi haƙu.
Bacci ne sama² ya fara ɗaukarta, ta gyara kwanciyarta ta fara bacci.

Taɓa ta da taji ana yi ne ya yi saurin tayar da ita, Anas ne ya na sakin wani lallausan murmushi a fuskarsa.
Tabbas Anas kyakkyawa ne mai kyakkyawar zuciya, "Ayaman!" Taji ya ambaci sunanta.

"Na'am."

Kallon kallo suka tsaya yi kafin ta yi saurin janye idonta ta miƙe, wani uban jiri ne ya kwasheta yarap ta faɗi a kan kujera.

Anas ne ya bita da sannu kafin ya ɗebo mata ruwa a zatonsa ko rashin ruwa ne.
Muryar mahaifiyarsa taji ta na ƙwallamai kira, ya na isa ta miƙa mai flask ɗin ruwan zafi da na abinci.
Ɗauka ya yi ya na godiya, buɗe kular ya yi a gaban Ayaman tuni yawunta ya tsinke kafin kace me ta fara jin soyayyar doya da ƙwan ko jiran tayi brush balle shan tea ko cikinta ya warware ba.

Tsayawa Anas ya yi ya na kallonta, shi duk a tunaninsa yunwa ce take kuwa yaji wani tausayinta ya ratsa shi.
Ruwan lipton ɗin ya ɗebar mata a kofi ya sa sugar, sannan ya miƙa mata.
Sai da ta tayar da doyar tass sannan ta juya ta ga yadda Anas ke kallonta.
"Sannu." Ya faɗa cikin tausashiyar murya.
Ƙasa ta yi da kai dan sai yanzu ta ga aika²r da ta yi, flask ɗin wayam babu komai ita kanta tayi mamakin yadda ta iya cinye wannan uban abincin.
Kitchen ɗin ya shiga yaga babu komai na gara da aka kawo wa Ayaman, shiru ya yi dan ya san ba zai iya komawa yace wa mahaifiyarsa babu abinci ba.

Wurin idi mai shayi ya nufa, "Ahh ahh ango? Kaine da safiyar nan ina amaryar?" Idi mai shayi ya tambaya cike da munafinci.

"Bacci take bata tashi ba." Anas ya basa amsa.
"Ah ya kamata ta huta kam da wannan gajiyar ay sai da hutu." Idi mai shayi ya ƙarasa ya na wata shaƙiyiyar dariya.

Ayaman kuwa wanka ta yi ta saka wata sabuwar atamfa duk da leda ce amma kuma ta yi kyau, fita ɓangaren mahaifiyar Anas tayi suka gaisa cikin mutunta juna.
Chapter 15 · 0% Book details