Sashe 2
Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana nan a gurin har aka kira sallar isha sannan ta samu da tashi daga wurin ta rarrafa zuwa akurkin dakinta wanda ko arzikin plaster bai samu ba.
Zama ta yi ta fara kuka me ban tausayi,sai da ta yi me isar ta sannan ta tashi ta dauro alwala,ta dawo dakin ta tayar da sallah,bayan ta idar ne ta daga hannunta sama tana kuka ta fara miqa kukan ta ga Rabbil Arshil Azeem sai da taji zuciyarta ta fara yi ma ta sanyi sannan ta rakuɓa ta kwanta a kasan dakin wanda duk kasa ne,ta lulluba da Wani zaninta.
"Hasbunallahu wani'imal wakeel" Ayaman ta faɗa sakamakon jin saukar wani ruwan sanyi a jikinta,
"Dan ubanki Zaki tashi ko sai na qara zuba miki ruwan?"
Inna Ladiyo ta faɗa tana zaro idanu, rarraba idanu Ayaman ta shiga yi kafin ta bi kofar dakin da kallo wanda Inna Ladiyo Bata Dade da fita ba.
Saukar hawaye taji a fuskarta, ta yi sauri ta goge su tana girgiza kai tana faɗin
"Ba wannan ne lokacin da ya dace nayi kuka ba." tashi ta yi da sauri ta fita daga dakin inda suka yi kichibis da inna ladiyo da bokitin ruwan sanyi zata ta shigo ɗakin saurin tsugunawa kasa ta yi hadi da cewa"Inna ina kwana?'
Harara Ladiyo ta watsa mata mai cike da tsana sannan ta ce "Da ban kwana ba Zaki ganni ne? Munafukar Allah da manzonsa sai wani sim-sim ta ke da kai,ki wuce kije ki ɗebo ruwa Nabila zata yi wanka kuma kinsan ba ruwa a gidan kika kwanta kikai ta sharar bacci."
"Toh inna".
"Keh! Ni fa ba innar ki bace,innar ki ta daɗe da macewa ta bar mana ke annoba kawai."
Ladiyo ta faɗa tana tofar da yawu kamar taga wata ƙazanta a wurin.
Ayaman ta kalli kanta sai asannan taga yadda kayanta suka jiƙe ga sanyin asuba me razana gangar jiki,a sanyaye ta tashi ta nufi gurin randar su ta ruwa,ruwa ta ɗiba ta shiga banɗaki ta fito ta yi alwala ta koma dakinta.
Tsayawa ta yi tana kallon dakin da duk ya jiƙe,rakubawa ta yi a gefe ta buɗe ƙullin kayanta, ta ciro wata doguwar riga ta atampa wacce duk ta koɗe,sakawa tayi sannan ta mayar da hijabin da ke jikin ta,ta tayar da sallah.
********************************
Tafiya take tayi a jikin bango, a siffar tsaka har sai da ta karaso wani gida,madaidaici ne gidan mai shegen kyau duk da kasancewar sa ƙarami.
Shiga ta yi cikin gidan,ta shige har ɗakin matar gidan wacce bata daɗe da haihuwa ba,ɗan jariri ne sabuwar haihuwa a kusa da ita,wannan tsakar ce ta lallaba har sai da ta kusa zuwa kusa da jaririn sai kuma ta koma baya da gudu kamar wacce wani abun ya kawo wa hari.
Ƙara yunƙurin zuwa kusa da yaron ta yi Amma kamar dazu ta kuma yowa baya,sai da ta yi hakan yafi a kirga kafin ta koma gefe ta tsaya tana kallon matar,charaff ! Suka hada Ido, murmushi wannan matar tayi kafin ta dauke yaron ta fita a dakin,tsakar ce ta tsaya tana kallon matar kafin wani lokaci Kuma ta bace baaattt.....
********************************
Tafiya take cikin nutsuwa,hannun ta riqe da bokitin ruwan data debo daga borehole din garin.
"Wallahi ita ce,kin ganta nan duk ta tsufa a gida har yanzu kusan shekarar ta 20 ba mijin aure." wasu mata suka faɗa yayin da suka zo wucewa.
A ranta taji zafin abun sosai,amma in ta tuna aure lokaci ne sai hankalinta ya kwanta.
"Assalamu Alaikum." ta faɗa yayin da ta ke shiga cikin gidan nasu inna Ladiyo da Nabila ta gani a tsakar gidan suna zaune.
Kamar jira Nabila ta ke yi ta hau zaginta, ta uwa ta uba wai tun dazu ɗebo ruwa sai kace an aiki bawa garinsu,ita dai Ayaman bata da tacewa sai dai ta yi kasa da kanta dan tasan koh hauka take baza ta iya faɗa da nabila ba saboda nabilan irin jikin inna Ladiyo gare ta, saboda haka tasan duka zata sha kuma koh bakomi Nabilan ta girme ta.
"Ba zaki wuce ki ƙarasa ɗeban ruwan koh kuwa kin tsaya kina kallon mutane kamar kin ga wasu sabbin halittun?" inna Ladiyo ta fada tana kallon Ayaman, wucewa ta yi ta ɗauki bokiti ta fice daga gida.
Toh fah!!! Lallai inna ladiyo,toh Allah ya kyauta,masu karatu mene ne ra'ayin ku a kan wannan littafin???
More comment more typing......
Khairat 🖤🖤🖤🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ ....
https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB
*(Posting room)*
*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇*
https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8
😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈.
by
Khairat 🖤🖤🖤
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
This page is specially for you zainabu ta 😅❤️
BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM
Page 7-8
Tana tafiya hannunta riqe da bokitin da zata debo ruwan,har ta iso gurin borehole din garin, duk gurin ya cika, saboda manya da yara haka ake diban ruwa tsayawa ta yi tana kallon su yayin da wasunsu ke faɗa akan diban ruwa .
"AYAMAN!!"
Taji muryar tsahare babbar ƙawarta tana Miko ma ta hannu,miƙa ma ta bokitin ta yi ita kuma ta ɗebo ma ta ta bata.
Gaisawa suka yi kafin suka fara tafiya,tsahare babbar ƙawar Ayaman ce duk da Ayaman din ta girme ta dan tsahare bata fi shekara 15 ba.
Amma a haka suke ƙawance da yake tsahare yarinya ce mai hankali da halin manya.
Tafiya suke su na hira sama-sama " Ina ladiyo har yanzu tana nan tana gallaza miki ke kuma kina ƙyale ta koh?" Ay na sani ko baki fada dan ganin ki da sanyin safiyar nan nasan akwai lauje cikin naɗi tsahare ta fada tana kallon Ayaman.
Numfasa wa Ayaman ta yi kafin tace cikin sanyin muryarta " wallahi tsahare abun yana damuna yanzu jiya da naci abincinta baki ga dukan da ta yi min ba, gashi in nayi aikatau ita ta ke karbe kudin ,ga rashin tausayi duk abubuwan sunyi min yawa tsahare yanzu wallahi ba kiji ciki na yadda yake min ciwo ba saboda yunwa." Ayaman ta fada tana zubar da kwallar da ta taru a cikin idonta,haƙuri tsahare ta bata kafin suka yi sallama.
Tun daga kofa take Jin kamshin ƙosai yana tashi,da sauri ta shiga gidan ta tarar da Inna Ladiyo tana suyar kosai a tsakar gidan.
"Assalamu Alaikum. Ayaman tayi sallama tana karasa shigowa cikin gidan,hararar da inna Ladiyo ta aika ma ta ne yasa tai ƙasa da kai ta fara cewa " dama inna layi na tarar a gurin diban ruwan shiyasa... "
"Shiyasa kika yi uwar ki koh ?" Inna Ladiyo ta faɗa tana kallon Ayamam, rasa me zata ce Ayaman ta yi tsuru-tsuru a gurin,can da ta gaji ta shige dakin ta....
Zan cigaba in Allah ya kaimu gobe... Nagode
BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM
Continued to page 7-8
Tana shiga dakin nata taji muryar inna ladiyo cikin masifa tana fadin " Dan ubanki da kika shiga dakin waye zai karasa miki aikin?
Sauri tayi ta fito ta dauki tsintsiya ta share tsakar gidan tass, ta janyo ruwa a rijiya ta fara wanke kwanikan da ba da ita aka ci abincin ba, bayan ta gama ne ta tafi wurin dabbobin inna ladiyo ta share wurin su,tana cikin Sharan ne yaro yayi sallama ya kawo aikatau na surfe kwano 3,inna ladiyo ta amsa ta amshi kudin.
Tana fitowa daga wurin dabbobin inna ladiyo ta kalle ta sama da kasa sannan tace "ga surfe nan kwano 3 kiyi sauri kiyi musu zasu dawo yau su amsa". Da "toh" AYAMAN ta amsa mata kafin ta kalli gefen kwanon kosan dake ajiye har ya fara bushewa,inna ladiyo tace "wannan kosan sai kin gama surfen dawar nan sannan Zaki ci" kin jima na gaya miki.
Daukar surfen tayi zata fara har ta fara debo ruwa daga cikin randar su taji inna ladiyo na cewa"wannan ruwan bana surfe bane na amfanin gida ne Dan haka kije ki debo Wani"
"Toh" AYAMAN ta fada tana daukar bokitin ta fita daga gidan,"saura ki tsaya yawon iskancin ki kar kiyi sauri ki debo ruwan".
AYAMAN dai fita tayi ta kama hanyar da zata sada ta da borehole din garin,ta tarar da borehole din ba mutane Dan haka tayi sauri ta dibi ruwan ta kama hanyar gidan,tana cikin tafiya taji muryar Anas,
Anas wani saurayi ne da yake tausayin AYAMAN matuka,saboda irin halin da take ciki, "ahh yau ko nema na ba kiyi ba AYAMAN? Idrees ya fada yana murmushi.
Murmushi AYAMAN tayi Mai kafin tace "Ina wuni". "lapiya kalau AYAMAN" ya gida? Idrees ya amsa mata gaisuwar tata, "lapiya kalau alhamdlh" AYAMAN ta fada tana kokarin wucewa kar inna ladiyo ta ga ta Dade, Anas ne yace "AYAMAN ya maganar mu ta ranar nan? Kina so na?
Rasa me AYAMAN zata fada tayi kawai tayi sauri ta wuce tana murmushi,shima murmushin yayi kafin ya wuce.
Inta ce Bata son idrees toh wallahi tayi Karya,Dan Anas ya cika namiji,ka hankali da nutsuwa ga Kuma neman na kanshi,a haka tayi ta tunanin Anas har ta qarasa gida.
"Assalamualaikum "AYAMAN tayi sallama,shiga cikin gidan tayi Amma Bata tarar da kowa ba a tsakar gidan ajiye ruwan tayi sannan ta leka dakin inna ladiyo ta tarar ba kowa Dan haka tayi sauri ta debi ruwa tayi wanka da tokar da ta Tara ta shiga dakin ta shirya sannan ta fara surfen Wanda sai da ya dauke ta awa 4 ba tsayawa sannan ta kammala.
Ruwa ta Sha, sannan tayi alwala tayi sallah, karar da cikin ta yake mata ne yasa tai saurin fita zuwa tsakar gidan ta dauko busheshen kosan ta zauna ta fara ci, ta cinye Ta sha ruwa ta gode wa Allah,ta zauna tana tunanin rayuwar ta....
Love you all 😘 ❤️
Khairat 🖤 🖤 🖊️ 🖊️ 🖊️https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈
Written
By
Khairat 🖤🖤🖤
Na sadaukar da wannan shafin zuwa ga babbar yayata, happy birthday my dearest sister ❤️ ❤️ 😘
BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM
Page 9-10