← Book details Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 17

Sashe 1

Mugunta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB
*(Posting room)*

*My WhatsApp group comment section*👇👇👇👇

👇https://chat.whatsapp.com/JL5uulBkRqf3E8JFFxJm8v

MUGUNTA 😈😈😈

by

Khairat 🖤🖤🖤

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Allah ya sa yadda na fara lapiya na gama lapiya.. Allahumma Ameen🙏

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Page 1-2

Dare ne sosai, dan a lokacin kusan karfe biyu na dare, a cikin kungirmin dajin hazdabe da ke garin dan masaki a ƙarƙashin karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano.
Zaune ta ke gaban mutumin dake gaban ta,tsohone mutumin kuma kato, shirgegen ,baƙin mutum.
Jikinsa butubutu wanda idan aka gaya ma bai taɓa wanka ba tsaf zaka yadda saboda baqinsa har sheƙin dauɗa ya ke , ya dago ya kalle ta cike da mamaki yace

"Kin binne layar da na baki?"

Da kai ta amsa mai alamar "Ehh" cike da tsoro da Kuma firgici a tattare da ita, zufa duk ta gama rufe mata fuska,ya kalli wani kwano a gabansa wanda ƙoƙon kan jaki ne,aka ɗinke sa da wani baƙin zare.

Dagowa ya yi ya kalle ta, buɗe bakinsa wanda da alama bai taɓa ganin wani abu wai shi brush ko asuwaki ba.
Ƙyalƙyalewa da dariya ya yi a lokaci ɗaya kuma ya haɗe rai kamar ba shi ya yi dariyar ba.

"BARQAAANNN!!!!!!"

Ya faɗa cikin murya mara daɗin sauraro wadda cikin amo ya yi ta har sai da kogon da suke ciki ya amsa wanda duk cike yake da kayan tsaface - tsaface,kawunan dabbobi da kuma zanen mutane a jikin bangon dutsen.

Wata ƴar tsana ya ɗauko mai kama da mutum sak, "kalli wannan ƴar tsanan ki gani." Ya miƙawa Ladiyo wannan ƴar tsanan.

"Tabbas kamar yadda kike so, Ayaman zata wahala a rayuwa, amma kuma zata yi kyakkyawan ƙarshe." Ya faɗa cikin alamar gargaɗi.

Baki buɗe ta karɓi ƴar tsanan tana kallo, kalmar da boka ya faɗa na cewa zata yi kyakkyawan ƙarshe shi ne ya tsaya ma ta a rai, lallai bata ga ta zama ba........

******************************* "Wasshh Allah na, na gajiii."

Wata kyakkyawar budurwa da aƙalla ba zata wuce shekara 20 ba ta faɗa ta na zama a kan ƙaramar kujerar dake tsakar gidan, karkashin bishiyar mangwaro.

Gida ne mai tsarin ginin bahaushe na asali, tsakar gida mai ɗauke da ɗakuna biyu sai ɗakin soro(wanda yawanci na samari ne).

Sai banɗaki babba na amfanin kowa, da madafa babba , a ƙarƙashin bishiyar mangwaron mai bada wata ni'imatacciyar iska mai dadin gaske, ta zauna.

Duk da gidan talakawa ne amma ko Ina na cikin gidan a sha re yake tsaf.
"Kulululu" cikin wannan budurwar ya yi Kara a lokacin da ta kalli madafar tasu , flask ne a ciki na jollop din shinkafa da taji attaruhu da manja a ciki,sannan kuma ta kalli gefen tulin kayan wankin dake tsakar gidan.
Tuno kalaman inna ladiyo kafin ta fita ta yi, ta ce ko da wasa kar ta taɓa ma ta abinci Kuma ta yi wankin da aka kawo aikatau wanda ko sisi bata samu daga kuɗin aikin .

Taba idonta ta yi taji damshin hawaye,kallon tsakar gidan da ta yi ne ya tuno ma ta da lokacin da aka shimfiɗe gawar innar ta, nann take wani hawaye ya zubo ma ta a idanu .
Mutuwa bata ma ta adalci ba, ta ɗauke ma ta mahaifiya a lokacin da ta ke tsananin buƙatar ta.

Kuma har yau bata daina mamakin Ladiyo ba , kasancewa Ladiyon aminiyar innar ta ce wadda a lokacin da ta ke da rai ta ga gata da ƙauna a wurin Ladiyo, bayan mutuwar innar ta komi ya chanja.

Tashi tayi ta fara wankin tunda tasan bata da wata mafita da ta wuce wannan ,zafin da ta ji hannunta ya yi shi ya tuno ma ta da ciwon da taji da safe a lokacin da ta ke haɗa wuta.
Durƙushewa tayi ta fara tunani, shikenan ita rayuwar ta a haka zata ƙare, cikin yiwa Ladiyo da ƴaƴanta bauta?
Ganin tunanin ba shi ne mafita ba ya sa ta tashi ta nufi madafar tasu ta buɗe flask din, tuni yawun ta ya tsinke dama rabonta da abinci tun jiya da yamma da tsahare kawarta,ta kawo mata abincin bikin da su kayi har yanzu gurin magriba ake neman kira,wanko hannunta ta yi tazo ta zauna ta fara cin shinkafar nan ko zafi bata ji,

"AYAMAN"

taji an daka ma ta tsawa daga bayanta juyawar da zatai ta hada ido da inna ladiyo tana hura hanci kamar zakanya ......

Masu karatu ya kuke ganin wannan sabon labarin kuwa? Meye ra'ayin ku? Ku ajiye min a comment section. Muje zuwa 🏃🏃🏃🏃🏃

https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB

*(Posting room)*

*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇*

https://chat.whatsapp.com/JL5uulBkRqf3E8JFFxJm8v

😈😈😈MUGUNTA 😈😈😈

by

Khairat 🖤🖤🖤

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM

Page 3-4

AYAMAN!!!! Ta ji an daka ma ta tsawa daga bayanta juyawar da za tai ta hada Ido da inna ladiyo tana hura hanci kamar zakanya

"Uban wa yace ki taɓa min abinci bayan na ce miki kar ki taba?"

Inna Ladiyo ta fada, fuskar nan kamar hadari, kame-kame AYAMAN ta fara yi a kokarin ta na kare kanta amma sai dai jin saukar lafiyayyun maruka ta yi a duka kunchin nata guda biyu ,kuka ta fashe da shi tana ji tana gani inna Ladiyo ke jibgar ta kamar Allah ya Aiko ta .

Dayake inna ladiyo irin matan nan ne jibga-jibga.

Ayaman kuwa tun tana kuka da iya karfin ta har muryar ta ta dashe.
Sai da Ladiyo ta gaji dan kanta sannan ta ƙyale Ayaman, ta tashi ta shige dakin ta, ba jimawa ta fito ,ta shige bandaki ta yi wanka ta fito wanda duk jiqa-jiqa ne ,tana fitowa ta ji sallamar malam isyaku baban Ayaman,kuma mijinta, ya shigo.

Koh kallon inda yake Bata yi ba tai shigewar ta daki,malam isyaku kuwa ya kalli inda Ayaman ta ke kwance duk ta jigata ,kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya shige dakin inna Ladiyo...

********************************
Zaune yake gaban halwar tsafin sa,wadda wata kwarya ce sai farin abu kamar ruwa a cikin ta,can yana cikin tsaface-tsafacen sa, a cikin wannan abun mai kamar ruwa,sai ga wasu dokuna farare biyu sai kuma baqi guda daya sun zagaye sa,ta ke wannan fararen dokunan suka rikide suka koma wata halitta mara kyaun gani.
Tsugunawa wannan halittun sukayi , sukayi sujjada a garesa (wa'iyazubillah) wani yare suka fara ma junansu kafin wannan halittun suka bace baaattt!!! basu ba alamunsu,dariya ya kece da ita yana faɗin "BARQAAANNN kayi kaɗan kayi jayayya da ni kafin kuma ya dakata da dariya sakamakon ganin wani baqin hayaki yana fitowa daga wannan kwaryar.
Sai ga wata mummumar mata ta fito ta cikin qwaryar,kamar ta daya da wannan bokan,"me ya hada ka da BARQAAANNN? Ta fada fuskar nan kamar hadari, hade fuska ya yi ya cigaba da aikin sa,matar kuma buɗe baki ta yi zata tambaye sa sai Kuma ta fasa ta yi wasu irin surqulle ta koma siffar tsaka ta bi bangon kogon ta fice....

********************************

"Ladiyo? Wai Ina ladiyon ne?"

Wata mata wacce baza ta wuce shekara 35-40 ta faɗa tana karasa shigowa dakin,inna Ladiyo ce ta fito daga dakinta tana masifa yayin da malam isyaku ke biye da ita,
"Mallam wallahi yau ba kai ba abincin nan, wannan shegiyar ƴar ta ka ta ci da rabonka."

Inna Ladiyo ta faɗa tana tura daurin kanta gaban goshi irin ba mutuncin nan, Delu ce ta tsaya tana kallon ikon Allah kafin ta kuma rangada sallama,sai a sannan ne Ladiyo ta lura da ita ,

"Ahh deluwa sannu da zuwa."

ta faɗa tana washe dashashun hakoranta ,

"Yawwa Ladiyo ta faɗa tana kallon malam isyaku a wulaqan ce , Ladiyo ce ta jata zuwa dakin ta da sauri suka rufo kofa.
"Ya ake ciki ne kawata?"
Ladiyo ta fada tana zama akan gadonta na ƙarfe, cike da murna da kuma MUGUNTA delu ta ce

"Wallahi yau nake jin an fasa bikin lamin binta,."

" Kai Amma ma sha Allah haka muke so."
Ladiyo ta faɗa fuskar nan kamar anyi ma ta bushara da gidan Aljanna,
"Toh yanzu da usainan za ayi bikin koh kuwa ? " Ladiyo ta tambaya.

"Bamu tabbatar ba gaskiya amma dai ko ma mene ne bokan nan ya iya aiki wlh." Delu ta ƙarasa cikin mamaki.

" Ay aikinsa kamar yankan wuqa haka yake ." ladiyo ta faɗa,ta numfasa sannan tace "Ni yanzu babbar matsala ta wannan yarinyar, Ayaman , kinga duk bayan wahalar da mukasha da zuwa gurin boka aikin nan be yiba,har yanzu samari sai zuwa suke ita kuma Nabila(yar ladiyo) har yanzu shiru sai mazan banza da suke bin ta ga kuma rashin kunya wlh gaba daya ta raina ni a gidan na." Ta ƙarasa cikin yanayin damuwa.

"Toh Ina inusa( ɗan inna ladiyo )yanzu?" Delu ta fada tana kallon ladiyo,
"Hmmm wannan yaron ay sai a hankali,yanzu fa har dai ya shigo garin nan shike nan na shiga uku daga sata,sai dabanci da yake koyawa yaran mutane yanzu dai har mai garin be kyale ba fah."

"Chabb Ladiyo Anya ba uwar yarinyar nan Ayaman ce ta yiwa yaran ki tsafi ba?" Kinga fah duka ƴaƴan ki su ukun ,Nabila yawon banza,Inusa dabanci,ga kuma nafisa da ta shiga yawon duniya,gaskiya ya kamata ki duba lamarin nan Anya ba sa hannu?" Delu ta ƙarasa tana kallon Ladiyo...

Sa hannu Kuma delu? Toh masu karatu ya kuke ganin wannan labarin?

Khairat 🖤 🖤 🖤....🖊️🖊️🖊️

Nagode,love you all 😘❤️

https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB

*(Posting room)*

*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇👇*

https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8

😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈

by

Khairat 🖤🖤🖤

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM.

Page 5-6

_____________"Gaskiya ya kamata ki duba lamarin nan Anya ba sa hannu?"

Inna delu ta fada tana kallon Ladiyo,shiru Ladiyo ta yi sannan tace"Lallai biri ya yi kama da mutum,amma indai haka ne, nasan matakin da zan dauka." Ladiyo ta faɗa sannan suka cigaba da firar su wacce duk yawancin ta munafunci ne da irin sharrin da suke haɗawa a gari..

*AYAMAN (p.o.v)*
Chapter 1 · 0% Book details