Sashe 8
Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
when she was twelve years of age, a perfect replica of Bilkisu! Bata taba yi mata cikakken kallo irin na yau ba, kauyancin duk ya fara barin jikin ta, a maganarta kawai zaka ji shi. Ta daddage ta daka mata duka a cinya, Sa'ade ta zabura ta tashi tana sosa wajen tana mutstsikar ido. "Haka kike kwana tsakiyar kwan lantarki sabida baki da hankali ko? Me yasa baki kashe ba?" Sa'ade ta zumburo baki "ni ban san ana kashewa ba" "daga yau duk sanda zaki kwanta ki kashe fitila mai haske ki bar dim, na ga alama ke kidahuma ce" Sa'ade ta kumburo kumatu bata amsa ba. Ta dora kafarta daya bisa gadon ta tsaya akan daya, sannan ta kama kunnenta na dama da kyau ta murde, Sa'ade ta saki tsuwwa don zafi, Fulani tace "idan kika gayawa wani a makarantar ku ko wadda zaku tafi tare ke 'ya ta ce sai na kabari ya fi ki jin dadi a gidannan, kowa ya tambayeki wacece ni a wurin ki ki ce ke 'yar kanwata ce, babar ki ta mutu, kin ji ni ko baki ji ni ba?" Hawaye na fitowa daga idon Sa'ade ta ce "na ji!". Fulani ta sakar mata kunnen, ta juya zata bar dakin. Sai ta tsinkayo muryar Sa'ade cikin rishin kuka. "Amma me yasa kika tsaneni haka? Da har ba kya so a ce ni 'yar ki ce? Kawai saboda ni Babana talakane ba sarki bane?" Wuta ta daukewa Fulani Bilkisu, ta kasa gaba, ta kasa baya. Bata taba zaton yarinyar zata iya yi mata wannan tambayar ba. Sa'ade tayi murmushi mai ciwo ta share hawayen ta da bayan hannun ta..... "Ki nemo min dan uwan mahaifina na Damaturu, tunda kinsan inda ya ke, insha Allahu zan nesanta kaina dake kamar yadda kike so, zan koma wajen sa". Bata bata amsa ba ta fita daga dakin, jikin ta yai matukar sanyi, bata zaci yarinyar nada hankalin gane abubuwa har haka ba, a shekarun ta goma sha biyu, ko ta yi mata bayani bazata gane ba, bata kin mahaifin ta don talaucinsa sai don rashin SO da zafin AUREN DOLE. Tunda itama 'yar talakawa ce futuk! Gaba da baya, inda halacci ashe kuwa bazata manta talauci sabida arzikin gidan aure ba. Da maganganun da Sa'ade ta gasa mata ta kwana a ranar suna gasa mata zuciya. Shi yasa da safe ta ki fitowa balle ta ga tafiyar ta, bata so ta karasa karya mata zuciya, bata shirya karbar ta matsayin 'ya anan kusa ba kuma har abada bata jin zata iya idan ta tuna Hashimu ne Baban ta. Fanna ce ta zo ta tashi Sa'ade ta taimaka mata tayi wanka, ta bata kayan makarantarta ta sanya, tuni an fidda kayan ta zuwa mota. Tun shigar ta gidan kwana ashirin da daya sai yau ta fito ta shaqi fresh air, daga iskar fanka sai ta A/C. Ta na ta wurga ido ko zata ga Fulani, amma ko motsin ta bata ji ba, ta san kuma bata isa ta shigar mata daki ba bisa umarni ba. Duk ta ji ba dadi da abinda bacin rai ya kwashe ta ta gaya mata jiya. Ta san a matsayin ta na uwa, ko me zata yi mata bata cancanci wadannan kalaman daga gare ta ba. Kawai sai ta kama kuka. Jikin ta a sanyaye ta bi bayan Fanna suka fita daga shiyyar Fulani, kuyangin Fulani na ta kallon ta don su har sun manta tana cikin gidan. Da yake safiya ce basu hadu da mutane sosai a hanya ba sai bayi jefi-jefi amma matan gidan da 'ya'yan su ko jikokin su babu ko daya, kowa yana sashen sa. Har suka shiga dalleliyar motar da direba da dogarai biyu ke ciki, daya na tuki, daya na gefen sa. Sa'ade bata bar kuka ba. A jikin motar an rubuta da ruwan gwal "ASKIRA EMIRATE". Gefen hagu dogarawa suka bude mata ta shiga, kafin su rufe kofar ta kamo hannun Fanna, idanunta narai-narai da hawaye tace. "ki ce ma Fulani don Allah don Annabi ta yi hakuri". Fanna bata san akan me ake aiken ta bada hakurin ba, ta dai lura akwai wani babban al'amari tsakanin uwargijiyarta da wannan bakauyiyar yarinyar. An raineta ne kawai a bisa bin umarni, babu tambaya, don haka tace "insha Allahu zan gayawa Fulani sakon ki". Fanna na barin wajen ba da jimawa ba Sa'ade ta hango wata kyakkyawar budurwa na tahowa karkashin rakiyar bayi 'yammata tsararrakin ta, tafiyar ta kawai data banbanta da tasu ya sa ta gane itace Humaira da Alanguburo yace zasu tafi tare wato 'yar autar sarki. Duk da kayan makaranta ne a jikin ta irin wadanda ke jikin ta amma an dora farar alkyabba wadda ta sha aiki da zare ruwan gold mai matukar walwali akai. Tun kafin ta karaso dogarawan nan suka bude kofar da azama suna yi mata kirari irin wanda 'ya'yan gidan kawai ake yi wa. Ta shiga barin dama, yayin da Sa'ade ke barin hagu. Da ta zo bakin motar sai kuyangar dake bayanta ta zare mata alkyabbar ta shiga daga ita sai kayan makaranta. Daga haka aka ja sullubebiyar motar a hankali suka soma tafiya, kuyangin nata basu bar wajen ba har motar su Sa'ade ta hau kwalta. Tunda suka mika hanya sosai yarinyar take ma Sa'ade kallo na kurilla, ita kuwa tun gaisuwar farko data yi mata bata kara ce mata komai ba. Ta maida hankalin ta ga kallon hanya suna wuce bishiyu da dazuzzuka kamar walkiya. Sanda suka cimma garin Chibok ta ce da Sa'ade cikin ginshira. "Me ye hadin ki da Fulani?" Sa'ade ta tuna gargadin Fulani don haka nan da nan tace "ni 'yar kanwar ta ce, mahaifiyata ta mutu". Gimbiya Humaira ta yi mata kallon shakka don ita dai bata taba ganin irin wannan kamar ta kwabo da kwabo ba irin wadda ke tsakanin Fulani Bilkisu da yarinyar da ke gefen ta. Kamar kamannin sun zarta na matsayin data ambata din na kasancewar ta 'yar kanwa a gareta. To amma wace hujja gareta na karyatawa? Tunda ta san bata haifi 'yar a gidan su ba? Sai ta dauke kai itama ta koma kallon gefen titi. A ranta tana fadin ita sam bazata yi mu'amala da 'yar kalen dangi ba mai maganar kauyawa. ****