← Book details Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 19

Sashe 12

Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Har hawaye ta yi na bakin cikin rashin ganin Raheema, ta yarda Raheema mai son ta ce, mai kaunar ta ce. Tunda har ta iya biyo ta tun daga Maiduguri har Askira. A karshe ta dauki shawarwarin Raheema, ta daina kunna talbijin, ta mayar da littafanta da darussanta na baya ababen debe mata kewa kuma abokan hirar ta. Sosai take tsintar abubuwa masu muhimmanci, sannan ta dinga tisa haddar ta, Fanna ta kawo mata 'yar radio tana sauraren karatun Abdurrahman Sudaith a ciki. Cikin haka har Allah yayi wa Fulani da maimartaba dawowa daga aikin hajji ana saura kwana biyu su koma makaranta.
Suna dawowa shirin komawar su aka fara, aka yo musu provision har fiye dana wancan hutun, babu wanda Fulani bata yiwa tsaraba ba cikin unguwarta (sassan ta). Banda Sa'ade. Ko tsinke bata sayo mata ba.
Ita Sa'ade bata san ma an yi rabon tsarabar ba tunda tana cikin daki kullum, ta dai daidaici sanda Fulani take zaman falo ita kadai ta je ta yi mata sannu da zuwa. Tare da tambayar ta "an dawo lafiya?"
"Lafiya kalau, alhamdulillahi"
Kawai ta ce, ba tare da ta tambayeta komai ba, kamar lafiyar ta ko yadda ta sameta, wannan abu ya sosa ran Sa'ade, ta wuce daki tana share hawaye da bayan hannun ta.
Kamar Maimartaba ya san za'ayi haka, da daddare sai ga kyawawan akwatuna manya guda biyu Fanna ta shigo mata dasu, tace tsarabarta ce inji Alanguburo. Ta ce Fanna ta bude mata. Tsala-tsalan dogayen riguna na 'yammatan larabawa ne a ciki kala-kala harda masu ado na sarauta a jikin su, takalma da jakunkuna na yammata masu karshen tsada a daya akwatun kalar kowacce daga cikin dogayen rigunan.
Ta cire biyu a ciki ta bawa Fanna, amma sai Fanna tace bazata karba ba Fulani ta basu irin nasu. Wadannan 'ya'yan gidan kawai suke sanya su. Don haka sai ta dauki guda uku a ciki tasa a kayan ta na tafiya makaranta da zummar zata kaiwa Raheemah a matsayin nata tsaraban.
Tunda suka dawo hutu wajen kwana arba'in bata kara sa gimbiya Humairah a idanun ta ba, sai yau a cikin mota da zasu koma makaranta. Da ta gaisheta ko amsawa bata yi ba don Fulani Hibbani ta kara ja mata kunne akan mu'amala da ita, ta gaya mata duk abinda Alanguburo ya sayo mata a Saudiyyah irin wanda ya saya mata ne ko banbancin kala babu. Wannan ya kara rura wutar kishin Sa'ade a zuciyar Humairah, ta kudiri aniyar kuntata mata wannan zangon fiye da na baya.
****
Da Allah ya tashi taimakon Sa'ade, satin su biyu da komawa aka yiwa dalibai canjin dakunan kwana, inda aka dauke ta daga dakin su Humaira kuma cikin ikon Allah ba'a kaita kowanne hostel ba sai na su Raheema.
Murna wajen su abin ba'a cewa komai, a daren ne ta samu ta baiwa Raheema tsarabar data ajiye mata, ita kuma ta bata labarin zuwan ta Askira, tace ta damu baban ta da labarin ta ne ta yi ta rokon sa kan ya sa a kaita, shi kuma ya amince, amma cikin rashin sa'a sai bata samu ganin ta ba.
Nan aminci ya kara kulluwa, suka hade kai suka zama kamar 'yan biyu, gasu dama tsayin su daya, sai dai Raheema baka ce sosai cikakkiyar Kanuri, yayin da Sa'ade take jajawur kamar Fulani Bilkisu.
Kawancen Sa'ade da Raheema ba karatun Sa'ade kadai ya taimaka ba, ya taimaka mata a sauran fannoni na rayuwar diya mace, tsafta, kwalliya, da iya magana, hatta tafiyar ta Raheema gyara mata take don tace tana tafiya gaba-gadi babu tsanaki. Ta koya mata magana a hankali cikin nutsuwa da yadda zata dinga gyara da kula da sassalkan gashin kanta na Shuwan usli. Rayuwar Sa'ade ta yi ta samun cigaba islamically, educationally, socially and morally a makarantar EL-KANEMI COLLLEGE OF ISLAMIC THEOLOGY.
Balle yanzun da bata da tension din Humairah, kowa son ta yake a dakin su, kowa so yake ace shi abokin ta ne. Ga hannun ta a bude, kyauta gare ta kamar 'yar siyasa. Kwakwalwar ta ta bude a lokaci daya kamar kiftawar ido, take grasping ilmi na kowanne bangare wanda nan da nan ya kara canza ta.
Dama Alanguburo ya ce mata tunda ta kayar da mutum daya, to nan gaba zata kayar da goma ne, to ba goman kadai ta kayar ba talatin ta kayar, ita ce ta dauki na goma a ajin su, Raheema ta dauki na farko.
Don haka da karfin gwiwarta ta dawo gida wannan hutun. Amma har ta kwana ta wuni, bata ga Fulani ba haka bata ji shigowar Alanguburo sassan su ba. Ta gaji da kallon kofar dakin Fulani ta tambayi Fanna, sai Fanna tayi murmushi ta ce.
"Fulani ta tafi kasar India zata haihu".
Ta rasa a wane yanayi ta karbi zancen, haihuwa? Daman ciki gare ta? Tana farin ciki da jin zata samu karin mutum a kusa da ita, amma wani gefen na zuciyarta yana kishi. Idan ta tuno dama fa Fulani ba wai tana son ta bane, inaga ta samu dan kanta da ta haifa a gidan sarauta? Ai wulakanci gareta zai koma mode activated.
Ta kyabe baki tareda cewa "Allah ya sauke ta lafiya".
Hutun nasu dama ba mai yawa bane, na sati biyu ne, har sati biyun ta cika Fulani bata sauka ba balle ta dawo, suka koma makaranta zuciyar ta cike da kewar ta, bata san tana son ta har haka ba, sai yau da ta nemi ganin ko inuwar ta cikin gidan ta rasa. Shima Alanguburo Fanna tace yayi tafiya zuwa kasar Amsterdam (Neitherlands) shi da Ya Gumsu kaiwa babban dan Ya Gumsu dake karatu a can ziyara.
Rayuwa ta mikawa Sa'adatu Hashim a makarantar EL-KANEMI da budi da nasara da cigaba ta kowanne bangare. Wani sihirtaccen kyau ke bayyanarwa Sa'adatu wadda zuwa yanzu Sa'ade ya bace bat da taimakon Raheema, dama itace in an tambayeta sunanta sai ta ce Sa'ade Hashimu, bayan ba haka yake a rubuce a rijista ba. Raheema ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da ta mantar da ita rayuwar ta ta kauye, ta yi adopting rayuwa mai cike da cigaba, wayewa da aji daidai na shekarun su, kaunar su da juna abin akwai sha'awa da burgewa a ciki.
Ranar wani visiting ne Raheema ta kira ta don ta gaisa da 'yan gidan su, fuska fal far'a take gaida Abban Raheema da mamanta, Bakin Babarbare mai zanen bare-bari akan fuskar shi ya sha manyan kaya na kamala, bayan sun gaisa ya sa musu albarka sai ya kasa dauke ido akan Sa'ade yana tunanin inda ya san wannan fuskar. Tabbas ya san fuskar amma ya rasa ta inda ya santan. Yana ta kokari ya tuna amma ya kasa. Har Sa'ade ta yi musu sallama ta koma cikin dalibai 'yan uwan ta.
Su dama ba'a zuwa musu visiting daga ita har Humairah, aiken kayan abinci kawai ake musu daga gida a kowanne visiting. Amma yau tana tsaye cikin daliban da ba'a zo musu ba ta hango shigowar motar data bata mamaki, bakar 'Land Cruiser' ce mai tsayi dauke da rubutun 'Biu Emirate'. Ba ta tafi wajen motar ba ta tsaya a inda take tana kallon su, don ta san ba wajen ta aka zo ba sai dai ko Humairah.
Wasu hamshaqan 'young ladies' ke fitowa daga motar tare da kyawawan 'ya'yan su kanana maza da mata, matan su hudu ne, daga inda take tsaye ta hango Humaira ta nufo su, duk jan ajin ta yau sai da ta hada da gudu-gudu ta rungume babbar cikin su.

"Yaa Maira! Ashe da gaske zaku zo?"
Chapter 12 · 0% Book details