Sashe 11
Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ke ana barci bayan la'asar? Kidahuma kawai". Ta zumburo baki tana mutstsikar ido. "Amma ko sannu da zuwa baki mun ba kin rufe ni da fada, don Allah Fulani me na yi miki ba kya so na?" Ta saki kuka har da na shagwabar ganin uwa, ba wai na zafin fadan da ta yi matan ba. She just felt relaxed by seeing her......after missing her for over ninety days. Fulani ta saki baki tana kallon ta don bata ga abun kuka ba don kawai tace ta daina barci bayan La'asar. Tsaki tayi tace "ba'a son naki, an ki a so ki din, ubanki ya ja miki, banda alfarmar Askirama wallahi bazaki zauna mun a gida ba, Damaturu zan kai ki". Sa'ade ta ida rushewa da kuka, it's painful uwar data haife ka ta bude baki tace bata son ka sabida mahaifin ka komai kazantar laifin uban naka ai mutuwa ma na kunyar idon Da. Balle in ta tuna Uban nata da akewa kiyayyar ba ya duniyar ma. Ita Fulani wace irin zuciya gareta? "Duk talaucin sa dai bazaki kankare cewa shi kika fara aure ba, tun da ga ni.....", sai bayan ta furta kalaman wadanda a zahiri a zuciyar ta tayi niyyar fadar su, ta yi maza ta toshe bakin ta da ta fahimci sun fito fili, amma ina! Already Bilkisu ta ji su. Har ta kai bakin kofa gabadaya ta juyo, ta kankance idanu ta kai mata wani wawan mari, Sa'ade ta kauce amma saida ta samu bayan kunnen ta, dan kunnen ta ya fice ya karce gefen kunnen ta sosai jini ya kwanta a wurin tare da yatsun Fulani Bilkisu. "Wannan ya zamo rana ta karshe da zan kara yin magana ki maida mun, mara kunyar banza! Mai mugun hali irin na uban ta!" Sa'ade na kuka wurjanjan Fulani ta bude kofar dakin ta fice. Tana zuwa falon ta ja ta yi turus! Ganin Askirama a zaune yana jiran fitowar ta. Ya sauke nagartattun idanun sa akanta, ma'abotan kamala da ilhama, a hankali ya ce. "Koma ki kirawo min ita, na jiyo kukan ta". Bata da damar yin musu, haka ta koma jiki a sanyaye tace daga bakin kofa. "Ki zo Askirama na kiran ki". Without giving her a second look ta fice ta bar dakin. Sa'ade saida taje toilet ta wanke idon ta don dai ta boyewa Alanguburo cewa kuka take, amma tana fitowa ta zauna a gaban sa idon sa bai sauka a ko'ina ba sai a bayan kunnen ta. Ya kamo fuskar Sa'ade ya kalli ciwon sosai, yace "Sa'adatu ki yi hakuri kin ji? Ni na gaya miki watarana in wani daban yayi miki haka, sai inda karfin ta ya kare". Sa'ade tayi murmushi duk da idanun ta sun kumbura, a ranta tana tantamar zuwan wannan ranar. Yau ta yarda da gaske Fulani ke kin Baban ta wanda shine mujazar nata kiyayyar. Amma bata ga laifin ta ba, laifin kanta ta gani, da ta ke kasa tankwara zuciyar ta ta mayar mata da magana. Wanda ko kusa bata cancanci hakan daga gareta ba. "Alanguburo ka taya ni bata hakuri don Allah, ni na bata mata rai". Ya yi murmushi ya ce "babu komai ta hakura, amma nan gaba ko me zata yi miki kada ki ji haushin ta, sannan kada ki tanka mata. Uwa ta wuce duk inda kike tsammani. Matsayin ta da darajar ta daban yake dana kowa a wajen ubangiji. Sai da Ya ce abi ta.....a bi ta.....a bita... sau uku kafin ya ce abi Uba. Ina fata kin fahimce ni?" Hawayen nadama na zuba a idanun ta ta gyada masa kai, ta dago ta dubi Fulani da appealing look, amma sai Fulanin ta kauda kai idanun ta jazur, ko kusa bata yi nadamar ciwon data ji mata ba da jinin data fitar mata, ta ma so ya fi haka, tunda ita bata da kunya. Amma can a karkashin zuciyarta ta ji wani sashe daban ya darsa mata tausayin yarinyar. Sanin cewa bata da kowa da zata raba a rayuwar ta sai ita, amma duk kokarin ta ta kasa sanya ta a ranta. Watakila sai ranar da Sa'aden da kanta ta yarda cewa ba laifin ta bane duk abinda take yi mata akan baban nata. Ko kuma ranar da zuciyar ta ta gaji ta russuna ta karbi Sa'aden don kan ta. "Je ki ki huta zan sa a kawo miki magani ki sha". In ji Alanguburo. Har ta mike sai kuma ta dawo gaban sa ta durkusa. "Ka yi hakuri Alan....ban cika alkawarin dana yi maka ba, ban yi kokari a makaranta ba, na yi duk iya kokarin da zan iya amma na kasa kamo kowa....a karshe nice ta biyun karshe". Yana murmushi ya ce "to ai babu komai tunda kin kada mutum daya, a ta gaba na tabbata goma zaki kayar, a ta can gaba ashirin, a ta gabanta talatin, daga haka har ya zamo kece a saman kowa. Kada hakan ya karya miki gwiwa kin ji? Ba wanda aka haifa da iyawa, kowa a hankali yake zama gwani, je ki kwanta ki huta sosai kafin a kawo maganin, ko talbijin ban yarda ki kunna ba sai gobe". Cikin jin dadi ta amsa tareda yi masa godiya, ta saci kallon Fulani ta ga harara kawai take zabga mata, ta wuce su zuwa daki kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki. Barcin da ya ce ta yi, ta so ta yi amma ta kasa, duk tunanin ta na yadda zata dinga yiwa Fulani biyayya ne, insha Allahu daga yau bazata sake bata mata rai da gangan ba. ***** "Me ya kai ki? Me ya kai ki dora hannu a jikin marainiyar Allah Bilkisu? In da ya zo da tsautsayi kin kurunta ta fa? Wallahi bar ganin ke kika haife ta, akwai hisabi tsakanin 'ya'ya da iyayen su". "Ku yi hakuri Askirama!". Abinda ta iya furtawa kawai kenan, ya mike cikin bacin rai mai tsanani ya ce "ni kam ba abinda kika yimin sai kyautatawa, balle ki bani hakuri, tunatarwa ce kawai nake miki domin tana amfanar da muminai. Amma tunatarwar da kullum sai an maimaita maka ita, ban ga amfanin ta ba. Daga yau bazan kara yi miki magana akan 'yar ki ba, na tabbata kin fi ni son ta. Saidai bana bayan zulunci, ni shugaba ne mai adalci wanda Allah ya damkawa amanar duk wani talaka da ke cikin garin Askira babba da yaro, balle wanda ke cikin gida na karkashin iyali na don haka bazan lamunci duka ba, in kin so ko dakin ta ki daina shiga wannan ya rage naki, amma duk ranar da kika sake kai hannu a jikin ta zaki ga bacin rai na Bilkisu". Ta tabbatar yau ta kure hakurin mai Askira, dole ta kwantar da kai tayi ta bada hakuri. Tsakanin mace da miji sai Allah balle Bilkisu da Sarki Yusufu mai Askira. Soyayyar su wata ajiya ce daga Allah. Wadda babu irin ta a wannan zamanin, soyayyar mazan jiya masu dattako da sanin yakamata. Fanna ta kawo mata magani ta sha, arashin sanin ta har da maganin barci a ciki. Haka tayi ta barci kuma Fanna bata tashe ta ba saida lokacin sallah yayi. **** Kwanansu bakwai da dawowa hutu, Sarki Yusufu da Fulani Bilkisu da Fulani Hibbani suka tashi zuwa kasa mai tsarki domin gabatar da aikin Hajji na wannan shekarar kamar yadda suka saba duk shekara, yana daukan mata biyu ne cikin matan sa su tafi da kwarkwarori biyu. Harkokin gidan suka cigaba da gudana kamar yadda suke gudana in sarki baya gari karkashin kulawar Wazirin gari Ibrahim. Kadaici ya kara yi wa Sa'ade sallama, bata ganin kowa sai Fanna, bata zuwa koina daga dakin ta sai falon Fulani na karshe wanda babu mai shigar shi in ka dauke Fanna. Ta kagu a koma makaranta ko ta hadu da Raheemar ta su yi ta karatun su ya fiye mata wannan jin dadin mara 'yanci. Domin kafin Fulani ta tafi ta ja kunnen ta sosai akan kowa na gidan koda kuwa bayi ne, bata yarda ko magana ta hada ta da kowa ba sannan bata yarda ko kofar unguwar ta ta fita ba. Ko me take so ta gayawa Fanna zata yi mata. Satin su Fulani biyu a kasa mai tsarki, rannan da Fanna ta kawo mata abincin rana ta hado mata da wata wasika da aka rubuta da fensir, tace "sakon ki ne daga kawar ki". Tun kafin ta bude takardar ta gane rubutun Raheema wadda ta rubuta sunanta a bayan takardar. Raheema Kyari. Jikin ta har rawa yake wajen warware takardar. Ga abinda Rahima ta rubuta. "Hi Sa'adatu, Ni ce Raheema, na zo tun daga Maiduguri as i promised to surprised you, an hana ni ganin ki, don an ce ba'a bada umarnin ki ga kowa ba, sannan Fulani bata gari balle a nemi izninta. Ina fatan ba za kiyi ta kallon talbijin ba, zaki yi ta bitar littatafanki ne kina koyar da kanki kafin mu koma hutu, na so in kwana uku tare da ke don muyi karatu sosai in koya miki mathematics, Allah bai yi ba, musamman Abba ya bada mota aka kawo ni, dana gaya masa masarautar Askira ne bai hana ba. Na so mu hadu, na so in ga Fulani, na so in gan ki, but some other time insha Allah. Mama da Sarina suna gaishe ki. Yours sincerily, Raheemah Kyari.