← Book details Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 19

Sashe 3

Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sa'ade ta daga kai tana kallon garin Askira, garin da aka ce wai anan ne zata ga mahaifiyar ta, wadda ta haife ta, anan take raye. Babban gari ne wanda ya samu cigaban zamani kala-kala a yankin Borno. Koda aka sauke su a tasha tana ji Baba Saleh na tambayar ta ina zai bi ya je gidan Sarki?
Sa'ade ta tambayi kanta.
Me ya hada mahaifiyar tata da gidan sarki?
Bata samu mai bata amsa ba.
Da tambaya da kwatance aka kawo su har kofar tankareriyar masarautar Askira.
*****

ASKIRA EMIRATE
Gidan sarkin Askira koko in ce masarutar Askira babban gini ne a tsakiyar gari, a unguwar da ake kira "unguwar gabas". Tafkeken gida ne mai ginin sama da kasa. Dogarawa ne tun daga zauren farko har zuwa ciki rukuni-rukuni, wasu a zazzaune wasu a tsaitsaye. Daga soron farko za'a cire takalmi duk mai shiga gidan mace ko namiji, ginin farko dake tsakiyar gidan wani irin gidan sama ne wanda ke dauke da kayataccen falo na sarauta wanda anan sarki ke ganawa da bakin sa na nesa.
Balcony din dake gefen wajen shine wajen zaman sa tare da mahukunta (king-makers) in ana wani muhimmin sha'ani kamar hawan sallah, nadin sarauta, bikin aure da sauran su. Akwai wata doguwar baranda a kasa wadda anan ya kan zauna a kowanne yammaci ya gana da jama'ar gari yayi musu maganin kukan su, alkalanci da zaman fada.
Daga hannun dama na tsakiyar ginin akwai wata babbar kofar katako wadda in ka bi ta zai kai ka barga (ma'ajiyar Dawakai). A kowanne yammaci kyakwawan Dawisu (Peacock) ne a gaban gidan bila-adadin masu ado da ban sha'awa suna baza dogon bindin su cikin nuna baiwar ado da kyau da Allah yayi musu wanda bai yi wa wani tsuntsu ko wata dabba a duniya ba. Akwai fili fetal daga get din farko zuwa ginin farko na shiga ainihin zauren farko na masarautar. Akalla zaka wuce zauruka shida kafin ka tarar da wajen zaman sarki na farko da jama'ar sa na nesa, kafin ka isa wajen zamansa da mahukuntan sa, sannan ka yi tafiya mai tsayi kafin ka shigo ainihin cikin gidan mazaunin iyalin sa.
Tsakanin inda sarki ke zama da 'barga' dakunan samarin gidan ne da yara maza da ake riko a gidan, sannan kayi tafiya mai tsayi wadda zata kawo ka get din cikin gida.

Bangaren sarki zaka fara taddawa wanda ya hadu da get din cikin gida, kuma akwai kofofi da ke hade da bangaren kowacce matar sa ta aure. Daga gaban ginin akwai baranda mai kama da balcony a gaban kayatacciyar shigifar sarki inda anan ne ya ke ganawa da 'ya'yan sa, matan sa da 'yan uwan sa mata. An fi yin wannan ganawa da yamma ko da daddare. A wannan shiyyar babu mutane da yawa, kowa yana bangaren sa, sai bayi mata wadanda suma suke shige da fice babu yawan surutu, kowacce tana bangaren data ke hidima suna kuma shige da fice daga wannan sassa zuwa wancan na matan Sarki.
Sarki kan zauna a kofar shigifar sa da yamma, don gabatar da sallahr la'asar, maza in na jiki ne suna iya shigowa nan, idan 'ya'ya ko jikoki suka shigo a daidai wannan lokacin saidai su rike takalman su a hannu su sunkuyar da kai su wuce in har ba shine ya ce a kira su ba. Amma in a barandar data raba shigifar sa data matan sa yake zaune, da 'ya'yan ko jikokin sun karaso zasu zube gaban shi su kwashi gaisuwa.....
"Alanguburo" (Allah ya kara maka yawan rai) shine abinda ake cewa. Ba'a gaida sarkin Askira da "ina wuni? Ko ina kwana?" Shi kuma ya amsa da "Allah Kawun jo" wato kamar ace (Allah yayi albarka).
Akasari a wannan shiyyyar babu dogarai babu bayi, in ya ga dama ya kan ja 'ya'yansa da jikokin sa da wasa, yayi musu tambayoyi akan rayuwar su a irin wadannan lokutan.
In ka wuce wannan shiyyar ne zaka hadu da bangaren matan gidan. Wato matan Sarki na aure.
Kowacce da bangaren ta wadatacce ginin zamani mai manyan shigifu, wanda aka yiwa ado da royal furnishing, babu abinda babu a ciki na jin dadin rayuwa, domin masarautar a zamanance take sannan ilmi ya wadaci al'ummar masarautar, ba abinda zai hada kowacce da 'yar uwar ta in har ba ita ta neme ta ba. Daga bayan nasu bangaren ne na kwarkwarorin sarki ya ke.

Ana kiran bangaren kowacce matar sarki da sunanta.....Unguwar Ya Gumsu (Fulani Babba), Unguwar Ya Kirjinoma (Fulani Halima), Unguwar Fulani Hibbani (matar sarki ta uku) sai unguwar Fulani BILKISU (amaryar sarki).
'Ya'yan gidan duk sun girma, mazan na wajen ayyukan su da masu karatu a garuruwa daban daban, matan duk an yi musu aure a masarautu daban daban na jihar Borno, 'ya'yan Hibbani ne kawai 'yan kasa da shekaru sha takwas. 'Yammata ne guda biyu: Naja'atu, da Humaira. Sune kuma kadai ba'a yiwa aure ba a 'ya'ya mata.
Kowacce cikin matan sarki tana da manyan 'ya'ya maza da mata, in ka dauke amarya Fulani Bilkisu, wadda har yau take haihuwa suna mutuwa tun suna jarirai wato (wabi).
Wannan a takaice shine description na gidan sarkin Askira mai ci a yanzu, da bayanin tsarin masarautar gabadaya. Masarauta ce mai farin jini da tarin arziki wadda aka yiwa shaidar adalci da kyautayi ga talakawanta. Daidai gwargwado 'ya'yan sarki maza da mata sun wadatu da ingantacciyar tarbiyya da ilmin addini da na zamani, duk da ba'a rasa masu fitina ba musamman samarin maza. Kishin da ke tsakanin iyayensu mata bai hana su hadin kai a junan su ba, suna matukar kaunar junan su. Sarki na da 'ya 'ya goma sha biyar, maza da mata da jikoki sama da goma.
****
Baba Saleh ya koma gefe ya daga kai yana kallon wannan babbar masarauta da bai taba mafarkin gani a zahiri ba, tun suna yara ya ke jin labarin masarautar Askira, irin tarin arzikin ta da karfin mulkin ta, hannun sa cikin na Sa'ade, sun yi zuru-zuru sabida yunwa da gajiya. Tunanin sa shine wa zai dosa ya ce yana son ganin BILKISU? Wadda marigayi Malam Hashimu ya ce tana daga cikin matan gidan???
Bar ta wadannan dogayen dogaran dake shige da fice suna muzurai kamar sa ci babu, wasu a tsaye kyam kamar an kafe su. Kai sai ka dauka babu bargo a cikin jikin su. Babban abinda ya fi razana shi shine shirgegiyar kofar masarautar, irin kofar nan ce ta jan karfe da ake kira mahdi-ka-ture.
Ya ajiye kunshin kayan Sa'ade dake hannun sa a kasa yace da Sa'ade ta hau kai ta zauna, shikuma ya zare sidadden silifan sa ya zauna akai ya kurawa kofar shiga masarautar ido yana tunanin ta inda zai bullo.
Kafin ya farga sai ya ga Sa'ade na gyangyadi akan kunshin kayan ta sabida wahala da gajiya.
Sai ji yayi wani Dogari ya buga musu gigitacciyar tsawa, "Kai tsoho! Me kuke nema anan?"
****
Chapter 3 · 0% Book details