← Book details Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 19

Sashe 7

Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wannan lokacin ne Fulani ta yi mata kallo na sosai, tana durkushe gabanta kamar yadda ta ga Fanna na yi, da can a fizge take kallon ta, a 'yan kwanaki hudun kacal data yi cikin gidan har ta fara washewa, kamannin ta da ita sun gigitata, kallo daya zaka yiwa yarinyar ka san ita ta haifi abar ta, kamar ta yi kaki ta tofar. Anya akwai wanda zai yarda in aka ce ba 'yar ta bace? Ko dai ta bari Askirama ya fadi gaskiya ne? Amma in ta tuna gorin da zata sha wajen Ya Gumsu (most senior wife ta sarki) kuma wadda suke buga mugun kishi da ita fiye da sauran matan sarki sabida yadda take jin kanta matsayin uwar manyan 'ya'yan sa, amma ya zo yana fifita Bilkisu akan ta, wanda hakan ya haifar da zazzafan kishi a tsakanin su, sai ta ga gara ta bar ta a 'yar kanwar ta ce, ai is normal dan dan uwanka yayi kama da kai. Ta yi ajiyar zuciya tareda dauke kanta daga kallon yarinyar tana jin kirjin ta na wani irin bugawa, inta kalli yarinyar sai ta tuno sanda Hashimu ya daure ta a jikin karfen gado ya haike mata, ko ta so ta ji tauayin ta abinda take tunawa kenan ta ganta bakikkirin a idanun ta, duk da an ce ya mutu, bata jin nan kusa zata yafe masa, ta hadiye wani kullutu daya tokare ta a kahon zucci, tana mai kautar da kanta ta ce mata. "Kin yi sallahr Isha?" "A'ah Inna, bari nayi sai can dare, an ce sallah cikin dare tafi lada" Ta galla mata harara tace "inji uban wa? Ni kar ki sake ce min Inna". Sa'ade ta yi shiru tana kikkifta ido. Ta nuna mata hanyar toilet da hannun ta "muje ki yi wankan sallah da alwalah akan idona na gani" Sa'ade ta zaro ido. "Kina nufin a gaban ki zan yi timbir?" Ta sake galla mata harara cikin tsawa tace, "Rufe min baki! Ko kin ga ana yi min musu a gidannan? Zaki wuce ko sai na hankada ki?" Sum-sum-sum Sa'ade ta wuce ita kuma ta bi bayanta. Da kyar Sa'ade ta iya cire riga a gaban Fulani, tana yi tana kare kirjin ta, tace tayi wankan tsarki tana gani. Ai yadda ake normal wanka da soso da sabulu haka Sa'ade ta yi, alwala kuwa ba'a zancen ta. Fulani Bilkisu ta ji kwalla ta tarammata, ba na tausayin yarinyar bane na tunanin wai gudan jinin ta a duniya ne wannan ba arabi ba boko. Zama tayi akan masai ta dinga gaya mata yadda zatayi wankan tsarki don ta tambayeta cewa ko ta fara ganin jinin al'ada ta tabbatar mata ta fara, sannan ta koya mata alwala, suka fito ta bata mayafi tace ta tsaya ta lura sosai da yadda take sallah. Sannan tasa ta tayi tana kallo. Akwai improvement sosai duk da haka wani abun sai kyalewa ta yi, ta san a hankali zata kara gyarawa. Sannan ta zaunar da ita a gaban ta ta koyar da ita fatiha, falaki da nasi da ikhlas, cikin 'yan mintuna Sa'ade ta karanta mata su tiryan-tiryan, daga nan ta gane tana da saurin daukar abu muddin zata samu kulawa. Sai karfe goma na dare ta sallameta. Bayan ta gaya mata wannan karatun data koya mata yanzu ta karanta ta tofa a hannayen ta ta shafe jikin ta da shi. Daga ranar kuma bata kara nemanta ba, sai bayan sati guda, shi din ma kayane akwati uku maimartaba ya aiko mata dasu, atamfofi, lesuka da shaddoji na alfarma, ta sa telar ta tazo har sassan ta ta gwada yarinyar a gabanta, don har zuwa ranar ko kofar falo na biyu bata bari ta fita ba, Allah Allah take ma satin ya zagayo a kaita makarantar kwanan ta huta. Ta manta cewa magana bata buya a gidan sarauta, abinda bata sani ba kuyangi suna magana a junan su cewa yarinyar nan da aka kawo daga kauye tun ranar da ta zo basu kara ganin ko inuwarta ba kuma basu san daga ina aka kawo ta ba ko aikin me ta zo yi. Har tsakanin kuyangin sauran matan sarki suna zancen har zance ya kai kunnen su Ya Gumsu, Ya Kirjinoma da Fulani Hibbani cewa Fulani Bilkisu ta dauko rikon 'ya daga kauye. Ya Gumsu tace "matar so an gaji da zaman kadaici an buge da tsinto 'ya'ya". Ita kuwa Hibbani cikin hila ta tambayi Askirama ko ya san da batun 'yar da Bilkisu ta dauko riko? Ba tareda ya bata hankalin sa ba ya ce 'yar kanwarta ce, kanwar tata ta mutu". Haka ta je ta fesawa Ya Gumsu, ita Ya Kirjinoma dama bata shiga sha'anin su, daga ita sai 'ya'yan ta take harkokin ta, tana da kamun girma sosai. A cikin sati biyun kafin tafiyar Sa'ade makaranta akwai cigaba sosai a tare da ita, sallahrta ta gyaru, ga wanka ya kama jikin ta, Fanna ta koya mata yin Brush sau biyu a rana, safe da dare, ta zama kamar Yayarta. Har hira suke yi sosai in Fulani ta tafi girki Turakar Sarki. Tana kara gyara mata kome ta ga ta yi ba daidai ba, har dige-digen data ke yi a fuskarta da kwalli Fanna ta hana ta. Sannan ta kiyaye umarnin uwargijiyarta da gaskiya na cewa kada ta bari kowacce kuyanga ta zo inda Sa'ade ta ke, bata yarda tayi alaqa da kowa cikin sassan ba bayan ita Fannar. Ana i gobe sati biyun da Sarki yayi alkawari ya sake shigowa sassan nasu, wannan karon da daddare. Ya samu Fulani da kuyanginta kusan su duka goman ana bata labarai tana murmusawa. Yana shigowa duk suka mike, fadi suke in chorused "...zauna daidai mai Askira... takawar ka lafiya Askirama!" Suka fice akan layi, shikuma ya zauna sannan ya soma yiwa Fulani fada. "Haka kawai kin kama yarinya kin kulle a daki don mugunta, kin hanata ko zama cikin kuyangin ki, to wadanda kike gudun su san da zamanta sun riga sun sani, gara ma ki sakarwa yarinya mara ta yi fitsari". Ita dai bata ce komai ba sai "Allah ya huci zuciyar Askirama (mai Askira). Bai amsa ta ba ya ce "kira wo min Sa'adatu". Ta tashi tana tafiyarta cikin yauki na halitta ta nufi dakin Sa'ade. "Ke ki zo ana kiran ki". Ta ce da Sa'ade wadda ke luntsume tsakiyar gado ta kafawa talabijin ido tana kallon diramar larabawa. Irin yadda ta saki baki da hanci tana kallon ba karamin haushi ya baiwa Fulani ba. Kamar tayi fiffike ta shige cikin akwatun talbijin din a yi da ita. Ko maganar Fulani bata ji ba, sai da ta taka ta kashe soket din talbijin din, tayi firgigit tace "haba don Allah Inna ya zaki kashe mini.....?" Sauran maganar ta makale mata a makoshi sabida mugun kallon da Fulani ta jefe ta da shi. "Na ce ki zo, ko ke kurma ce ne?" Sa'ade ta sauko daga gadon ta bi bayan ta don tuni har ta fice, tana shigowa falon ta yi arba da Sarki, ai tuni ta washe ta daina fushin kashe mata talbijin da Fulani ta yi ta nufi wajen sa cikin tsananin murna. "Alan....ina wuni?" Yayi murmushi ya yafito ta da hannun sa. "Zo nan kusa gare ni Sa'adatu" ta rarrafa gabansa ta zauna ya ce "Ah! Masha Allah, da alama Fulani tana kula da ke, gashinan kin yi haske kin yi kumatu" ta saci kallon Fulanin, hararar data ke mata yasa ta kasa fada masa abinda ta yi niyya, cewa ita bata wani kula da ita, Fanna ce take kula da ita, ita sai tayi kwanaki bata ko ga inuwar ta ba. Aka soma shigo da kwalaye da katon katon na kayan masarufi ana jibgewa a gefe. Daga ita har Fulani Bilkisu bin kayan suka yi da kallo don basu san ko na menene ba. "An samo makarantar Sa'adatu, an gama komai, gobe za'a kaita, ita da zuwa gida sai karshen kowanne zangon karatu, sai kuyi sallama yau, don gobe da sassafe za'a kai su ita da Humaira". Fuskar Fulani ta tattare cikin rashin jin dadi, bata son a alaqanta komai na Sa'ade da 'ya'yan gidannan, ba don komai ba sai don gudarwa kanta gori. Balle 'ya'yan Hibbani sarakan surutu, ita kuma Hibbanin uwar tsugudidi, in taji abu to tabbata Ya Gumsu ta ji ta gama. Amma ai da kunya tace masa bata so ya hada 'yar ta da 'yar sa, shi da yayi wannan kara ta mutuntawa in ba'a gode masa ba akalla baza'a kalubalance shi ba. "Allah ya kaimu" Kawai ta ce. Sa'ade ta dago cikin farin ciki ta ce "Alan....amma inna tafi sai bayan shekara zan dawo ko?" Cikin mamaki yace "ba kya marmarin ganin Innar ki zaki yiwa kanki fatan yin shekara a makaranta?" Ta sunkuyar da kai a ranta tana so ta gaya masa ita Innar ce bata son gani kusa da ita da wadannan muzuran idanun nata masu karkada mata 'ya'yan hanji, sannan kadaici yana damun ta, banda yanzu da aka jona mata talbiin take debe mata kewa. "Wata uku zaku yi ku dawo hutu, na hada ki da 'yar uwarki Humairah don ki ji dadin zama kina ganin na gida a kusa da ke. Ki maida hankali kiyi karatu, ki kawo min sakamakon da zan yi alfahari da ke, kin ji Sa'adatu?" Ta gyada masa kai "insha Allah zan yi kokari Alan....guburo, nagode, Allah yayi maka fin abinda kayi min". Shi da Fulanin duka suka kalle ta jin abinda ta ce, don basu yi zaton tana da hankalin sanin an yi mata alkhairi ta bi da kyakkayawar addua irin haka ba. Cikin daren Fulani ta kasa barci, ba kewar Sa'ade ta ke ba, damuwar ta na hada Humaira da Sa'ade da za'ayi ne waje daya, ta san Humaira da shegen kinibibi kamar na uwar ta zata iya jan Sa'ade a jiki ta ji sirrin su ta fesawa uwarta. Don haka ta mike daga kwanciyar ta ta sanya hijab kan rigar barcin ta ta nufi dakin Sa'ade. Ta yi dai-dai sai sharar barci take abinta, santala-santalan fararen cinyoyin ta a waje, rigar barcin ta yaye can sama, gashin kanta da Fanna ta wanke mata dazu da shampoo sai sheki yake ga santsi, sai ta ganta exactly like herself
Chapter 7 · 0% Book details