Sashe 2
Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da suka yi sallah sannan suka ci abincin ita da Hanne a kwano guda, suna ci suna hirar samarin su suna kwasar dariya, Hanne ta roki Innar ta zata raka Sa'ade gida kada Inna Laure ta doke ta.
Har dakin Inna Laure Hanne ta raka Sa'ade, wadda ke rabe-rabe a jikin bango irin na wanda ya san yayi laifi, da Hanne ta fita ji tayi kamar ta bita a guje. Hanne na bada baya Inna Laure ta shaqo Sa'ade ta makure ta a jikin bango ta ce.
"Shine don kar ki kwashe min tuwo kika faki ido na kika tafi gantali ko? To kin yiwa kwanon tuwon ki, ko loma daya bazan baki ba, ki kwana da yunwar ki, 'yar banza mai mugun hali irin na uwar ta".
Sa'ade dai bata tanka ba, don inda sabo ta saba ji a bakin Inna Laure uwartamai mugun hali ce. Kuma dai a koshe take, don haka bata damu ba data ce bazata ci tuwon dare ba.
******
Washegari ma da Inna Laure ta dora mata gasara maimakon tabi gida-gida kamar yadda ta ke yi sai ta karkata hanya ta tafi makarantar su Hanne, yau ma a bakin taga ta tsaya daidai saitin da Hanne ta ke farantin gasarar ta yasar da shi a gefe. Malamin yana cikin bada darasi ya hangota tana leke. Zagayowa yayi ba da sanin ta ba sai ganinsa tayi a bayan ta, ta zabura zata gudu ya tare hanya.
"Shiga aji ki zauna, zan sa Dagaci ya yiwa baban ki magana, kullum ina ganin ki kina leken kawayen ki, wanda ke nuna kina sha'awar karatun da muke yi".
Bakin Sa'ade ya ki rufuwa don dadi, sai dai ta sani Inna Laure bazata taba bari ba, shi kuwa Baba sai abinda tace sabida tsoron masifar ta. Hankalin ta ya dauku ga abinda ake koya musu A BA CA DA Ee FA GA HA.....! Sa'ade ta bude murya tafi kowa yi... abinda ya dauki hankalin malamin a kanta ya gane da gaske take son karatun.
Don haka kamar yadda yayi alkawari har kasuwa ya bi Malam Hashimu bayan sun tashi, cikin nutsuwa ya neme shi ya bar Sa'ade ta dinga zuwa makaranta a daina dora mata talla. Malam Hashimu yayi shiru, daga bisani ya ce a sanyaye,
"uwar rikon ta bata so, kada ka sa ni a tashin hankali ina zama na lafiya".
Sa'ade data zo washegari malam yace tayi zamanta, ana tashi yaje ya gayawa Dagachin Tsanyawa, shi kuma ya tura aka kira masa Malam Hashimu da Laure, a gabanta ya ce yayi umarni ga Malam Hashimu ya saka 'yar sa a makaranta a daina dora mata talla lokacin zuwa makaranta, idan kuma sun ki to su tattara su bar Tsanyawa dama dukkan su ba haifaffun garin bane, gara Laure wadda ta zo da ita Tsanyawa daga kauyen Kiyawa 'yar asalin garin ce. Shi kuwa Malam Hashimu Dagaci ya ce har gobe bai san daga ina ya zo ba.
Mafari kenan da Sa'ade ta samu 'yancin zuwa makarantar boko har da ta allo, wannan bai hana Laure cigaba da dora mata talla ba a duk lokacin da ta dawo. Tana aiki tana mita tana tsinewa Dagacin Tsanyawa. A wannan lokacin ne makerin budurci ya soma kera Sa'ade, ta fara kirgan dangi har da jinin al'ada a shekarun ta goma sha biyu kacal.
Hanne ce ta koya mata kunzugu, da wankan sallah da tuni Innar ta ta koya mata don ta riga Sa'ade farawa.
Manema suka yiwa Sa'ade Caaaa! Manya da yara. Kai ka ce wata budurwar kirki ce, bayan Naziru mai dankali harda dan Dagachi dake karatu a birni, da wani Alhaji Talle mai mata uku amma yana da sukuni sosai. Kyawun fuskar ta shine abinda ya ke fara jan hankalin maza a kanta, wani irin sassanyan kyau ne da ita na mutanen wani yanki daga BORNO da ake yiwa laqabi da shuwa-arab wanda ake rasa gane daga inda ta samo shi don kwata-kwata bata yi kama da mahaifin ta ba, wanda yake baki, tittirna, mai gajeren hanci.
Mutane da yawa a garin na fadin Sa'ade ba 'yar sa bace, tsintota yayi, don babu wanda ya san shi da uwar ta, kawai an wayi gari ne an ganshi a garin tare da yarinyar 'yar shekaru uku yana rainon ta. Daga baya ya nemi auren Laure, ba bata lokaci aka bashi ba tareda binciken asalin sa ba don ta buwayi marikanta kuma ta rasa mijin aure duk fadin kauyen.
A tsakankanin wannan lokacin ciwon da aka rasa gane kansa ya kama Malam Hashimu, tun yana yi a tsaitsaye har ya gagara fita kasuwa, kullum abu kara gaba yake yi, banda jike-jike ba abinda yake sha don Laure ta ce sisin kwabon ta ba zai yi ciwon kai ba wajen kai shi asibiti, ita ba haihuwa ba a barta da asara.
Sa'ade ko makaranta daina zuwa tayi sabida jinyar baban ta, kullum ce mata yake ciwon sa ba na tashi bane, bai damu ba don ya mutu a wannan lokacin, ita Sa'ade ce damuwar sa. Wa zai rike masa ita? Ina za ta je idan bai tashi ba? Ya sani Laure ko a kafa aka daura mata Sa'ade sai ta kwance ta yar. Sabida tsanar data yi mata. Damuwa ta karu akan ciwon Malam Hashimu ta yi sanadin da ko idonsa baya iya budewa.
Sa'ade na ji Laure na gayawa mutanen da ke zuwa duba shi wai ciwon daji ke damun sa.
Baban Hanne shine ya tausayawa Sa'ade ganin halin da take ciki na fita hayyaci sabida ciwon Baban ta, duk da shima ba wani karfi gareshi ba haka ya kukkuta ya samo motar akori -kura ya tafi dashi asibiti a cikin Kano. Ba yadda Sa'ade bata yi ba zata bisu amma Malam Sale yace ta zauna a ranar zasu dawo.
Har kwana uku basu dawo ba, a kwanakin nan uku Sa'ade ta gama karewa a tsaye, bata ci bata sha. A rana ta hudu kuwa tana gindin murhu tana hurawa Laure wutar tuwo taji ana fadin.
"Ku shigo da shi daga ciki, a kawo tabarmi.......". Sai ihu da kururuwar Laure. Tana fadin "Malam ashe sa'i ya yi? Ashe rabuwar kenan?"
Fitowar Sa'ade a guje daga madafi yayi dadidai da shimfide gawar da aka yi a tsakar gidan su. Da gudu ta karasa ta bude fuskar ta tabbatar Baban ta ne..... Ya rasu! Tafiya ta har abada wadda babu dawowa........ Ji kake yiff! Ta fada kan gawar a sume bata kara sanin inda kanta yake ba.
*****
Ta farfado ne ta ganta a gidan su Hanne, Hanne na kuka Innarta na mata firfita. A lokacin ne abinda ya faru ya dawo cikin kwanyar ta. Ta rushe da kuka tana fadin "Hanne da gaske ne Babana ya rasu?" Innar Hanne ta rungumota jikin ta tana ta lallashinta tare da bata kalamai masu dadi. Sai da aka kwana bakwai Sa'ade bata daina kuka ba, kulawa da kauna ta duniya babu wadda iyayen Hanne basu gwada mata ba don dai su samu ta kwantar da hankalin ta ta karbi reality na rasuwar Malam Hashimu.
Washegarin sadakar bakwai malam Saleh Baban Hanne ya kirata dakin sa, ya ce ta je ta kwaso kayanta gabadaya, ta kuma yi sallama da Laure ta dawo. Zai cika wasiyyar da marigayi ya bar masa suna hanyar zuwa asibiti. Zai dangana ta da mahaifiyar ta hannu da hannu....
A razane Sa'ade ta dago ta dube shi manyan idanun ta kamar sa fado kasa. Ya gyada mata kai da murmushi a fatar bakin sa ya ce "maza je ki ki dawo, daga yau zuwa gobe, zan sadaki da Innar ki da ta haife ki".
****
Tunda suka iso tasha Sa'ade ke rarraba idanu, wannan ne karo na farko da zata fita daga garin Tsanyawa tun tasowar ta. Ita da Hanne rabuwar su mai taba zuciya ce. Tunda suka taso basu taba rabuwa na kwana biyu ba, kullum suna tare dare da rana, yau an ce Jihar Kano zata bari bakidaya ba garin Tsanyawa kadai ba. Zuwa inda bata sani ba, bata taba mafarki ba. Zuwa wajen uwar da bata sani ba, bata taba gani ba.
Ko mahaifiyar tata ya zata karbe ta? Ko zata bata matsayin 'ya? Duba da cewa bata taba sanin ta ba? Sai yau a dalilin mutuwa.... mai tonon asiri!
Tunaninnikan da Sa'ade ke ta yi kenan a lokacin da suka bar garin Tsanyawa cikin motar Rake Akori-Kura, suka hau titi dodar! Wanda zai sada su da birnin Kano. Hanyar garin ba kwalta a wancan lokacin don haka kura ta turnike idanun su a bayan akori-kurar, sai rufe fuskokin su suka yi da mayafan su.
A tashar unguwa uku aka sauke su, inda direbobin suka ce yamma ta yi, zasu yi dare, su nemi waje su kwana in ya so washegari su yi asubanci su samu motar farko.
A rumfar wata mai tuwo malam Saleh ya roka mata ta kwana, shi kuma ya kwana a masallacin tashar. Da asubah suna idar da sallah sune pasinjan farko a fasinjojin da zasu tafi garin MAIDUGURI....
*****
"Tafiya yankin azaba".
Sa'ade ta fada a zuciyar ta. Sabida yadda ta wahala a motar. Kafin su isa Maiduguri sai yamma lis, duk sun yi wujiga-wujiga daga ita har Baba Saleh. Sau biyu yana saya mata gurasar masu balangu da pure water tana ci a hanya. Shi kam bawan Allah bata tunanin ko loma daya ya saka a bakin sa.
Aka sauke su a tashar BAMA, anan ma a tashar suka kwana, da Asuba suka bi mass transiet wadda zata tafi kai tsaye zuwa garin ASKIRA.
Sa'ade ba zata manta da garuruwan da suka wuce ba, saboda akwai wani mutum mai yawan surutu a motar tasu, duk garin da aka zo sai ya fadi sunan sa, sun wuce Damboa, sannan suka bulla ta Chibok, sannan Uba, a karshe sai garin da ta ji an kira ASKIRA.
(A wancan lokacin ba insurgency, garuruwan Borno lafiya kalau suke).