← Book details Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 19

Sashe 4

Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Baba Sale ya mike yana kakkabe kurar jikin sa Sa'ade ma ta yi firgigit ta farka daga gyangyadinta, sai rarraba ido take gabadaya ta firgice. Cikin raunin murya Baba Saleh ya dubi dogarin ya ce.
"Mu baki ne tun daga Tsanyawa ta jihar Kano, bawan Allah na zo garin nan ne takanas don in ga Sarkin Askira, don Allah don Annabi ka taimaka mana".
Wani wulakantaccen kallo dogarin yayi musu sannan ya ce "ka san wa ka ke nufi kuwa? Tsoho anya lafiya kalau kake?"
Baba Sale yayi murmushi mai ciwo irin wanda dan adam ke yi in yana son boye bacin ran sa, ya ce "bani da alaqa da shi, kuma ban zo neman komai wajen sa ba, sakon dana ke dauke da shi na matar sa ne, kaga kuwa bai yi daidai ba in nemi ganin matar sa ba tare da na fara neman alfarmar sa da yardar sa ba. Ka taimaka mana ko don yarinyar nan da ke jin yunwa, marainiya ce".
Dai-dai lokacin wani gajeren dogarin ya taso don ganin abinda ya tsayar da dan uwansa wajen wadannan mutanen masu kama da korarrun jeji, "Buba me suke nema ne?" A raine ya dube su sannan ya nuna su da bakin sa "wai maimartaba suke son gani" "amma shine zaka bar su a tsaye ko wurin zama bazaka basu ba?"
Ga dukkan alamu shi wannan din mai kirki ne, ya ce da dan uwan sa "maimartaba ya bada damar duk mai son ganin sa ya ganshi cikin kasar sa, cikin aminci da girmamawa, don haka barkan ku da zuwa Masarautar Askira, amma baza ku samu ganin maimartaba ba sai washegarin gobe in Allah ya kaimu idan an fito fada".
Baba Saleh yayi godiya sannan ya ce "don Allah ko zan samawa yarinyar nan wajen kwana? Ba mu san kowa a garin nan ba, ni bani da matsala ko a nan wajen zan iya kwana".
Wanda aka kira da Adamu wato mai kirkin dogarin, ya ce "ta zo muje in kaita wajen matata ta kwana, kai kuma ka biyo ni".
Matar Adamu itama baiwa ce a gidan, bangaren su yana daga can karshen masarautar, unguwa ce guda duk bayi ne da iyalan su, amma yawanci basa wuni anan kowacce tana sassan data ke aiki cikin masarauta, sai dare can suke komawa gidajen su.
Ta zubawa Sa'ade tuwo da miyar yauki ta kawo mata ruwa a kofin silba, Sa'ade ta tasar ma tuwon nan kamar Allah ya aiko ta. Sai da ta ci ta koshi matar ta zuba mata ruwa a buta ta nuna mata bayi, taje ta kama ruwa ta fito tayi alwallah ta shimfida mata tabarma anan dan tsakar gidan ta, ta shiga rama sallolin da ke kanta. Ana idar da sallahr isha kuwa barci ya dauke ta akan tabarmar data yi sallar, matar tayi mata shimfida a dakin ta ta tashe ta ta koma daki, ita kuma ta cigaba da ayyukan ta.
Washegari ta bata koko da kosai ta karya kumallo, ta sa ta tayi wanka ta canza kaya cikin nata dake kulle, Adamu bai shigo ba sai karfe goma na safe ya ce ta biyo shi. Tayi wa matar da ta ji ya kira Kubra godiya sosai, tabi bayansa, anan waje suka hadu da Baba Saleh ya ji dadin ganin ta cikin kyakkyawar kama, ya karbi kullin kayan ta suka bi bayan Dogari Adamu zuwa fadar sarki.
Wuce wannan shigifa, tsallake wannan soro, wuce wannan falo har suka dangana da inda Sarki ke ganawa da jama'ar gari a kowacce rana.
Dogarin ya ce su tsaya daga waje, ya shiga ya fadi yayi gaisuwa, sannan ya fadi sakon Baba Saleh, Wazirin sarkin Askira yayi masa tambayoyi a kan su kafin aka amince masa kan ya shigo da su.
Baba Sale ya shigo rike da hannun Sa'ade, ya fadi yayi gaisuwa yadda ya ga ana yi, dogarawa suka ce "Sarki ya gaishe ka, ka yi gaggawar fadin abinda ke tafe da kai".
Baba Sale ya muskuta sannan ya soma koro bayanin sa cikin nutsuwa, wasiyyar da abokin sa marigayi Malam Hashimu ya bashi a lokacin da yake cikin tsananin ciwo akan gargarar mutuwa, na cewa ya kawo yarinya Sa'ade hannun BILKISU a masarautar Askira idan ta Allah ta kasance da shi. Ya gaya mata cewa diyar ta ce da ta haifa tare da shi a garin Tsanyawa.
Sarki Yusufu Bin AbdulHakimu (mai Askira), ya dan zamo daga cikin kujerar mulkin sa ya tsurawa yarinyar ido, wadda ke sanye cikin ragga, 'yar kauye futuk, ya shiga tunanin ta inda ta fito daga jikin matar sa mafi soyuwa a gare shi, ya san ta taba aure kafin ya aureta, amma bai taba sanin tana da 'ya ba, bata taba gaya masa ba.... Sai dai ido, hanci da baki kadai sun nuna zahirin kamannin Fulani Bilkisu a tare da yarinyar. Jini baya taba buya. Har lange-langen jikin. Musamman data dago manyan idanunta tana kallon sarkin, sai ya ga kamar Bilkisun ce ke duban sa da manyan fararen idanun ta.
Magana yayi kadan da Wazirinsa, shi kuma ya yiwa bafaden dake gefensa magana, sai bafaden yace da Baba Saleh su biyo shi.
Wani hamshakin falo ya kai su can hanyar shiga cikin gidan, falon bai cika girma ba, amma ya sha adon kayan fata na sarauta dasu tum-tum, dogarin ya ce su zauna anan, su jira rabin awa.
Daga Sa'ade har Baba Sale ba mai magana, sai kalle - kalle suke mai nuna kauyancin su tifikal, zuwa can Baba Sale ya nisa ya ce.
"Sa'ade! Ko me kika ga ya faru da bawa haka Allah ya ga damar ya kasance a gare shi, idan mahaifiyar ki ta karbe ki shikenan, idan bata karbe ki ba, ni zan rike ki tare da Hanne a cikin iyali na har iyakar nawa numfashin".
Daga yadda yake magana zaka gane ya karaya, bai san girman masarautar da kasaitar ta ya kai haka ba! Bai san sarautar babba ce irin wannan ba! Ya dauka normal sarkin kauye ne irin wanda ya sani. Masarautar Askira kuwa tana cikin manyan masarutun jihar Borno masu tsohon tarihi da yalwar arziki wadanda ke sahu na biyu a jihar ta Borno bakidaya.
Sa'ade cikin rawar murya ta ce "Baba Sale ni dai mu koma Tsanyawa.... ko ta karbe ni bazan iya zama a gidan nan ba tsoro nake ji....wallahi bazan zauna ba". Baba Sale cikin lallashi ya ce "ki kwantar da hankalin ki Sa'ade, idan ta karbe kin shine babban gatan ki, kin ga ni na tsufa, ko zan rike ki na dan lokaci ne nima wa'adina zai cika, baki da kowa a Tsanyawa bayan ni da Innar Hanne, aure zai yi miki wuya don kuwa babu wanda ya san asalin iyayen ki".
Yana rufe baki suka ji ana "gyara kimtsi mai Askira......taka lafiya Giwan Askira.....". Sarki ya shigo falon shi kadai, dogarawan suka tsaya daga waje. Kujerar sa wadda ita kadai ce kujera a falon ya je ya zauna. Baba Sale ya fadi kamar zai yi sujjadah yadda ya ga ana yi ya kara gaida sarki, sarki yai masa murmushi ya amsa da wata irin hamshakiyar kamilalliyar murya. Ya mika hannu ya yafito Sa'ade,
"zo nan kusa gare ni diya ta".
Sa'ade ta rarrafa ta isa gaban shi, ya dora hannu a kanta ya ce "yaya sunanki?" Murya na rawa ta ce "Sa'ade!" Yayi murmushi ya ce "Sa'adatu dai ko? Sannu da zuwa Askira kin ji Sa'adatu?".
Sannan ya maida hankalin sa ga Baba Saleh yace ya bashi labarin rayuwar Sa'ade a hannun mahaifin ta tun daga sanda mahaifiyarta ta bar ta. Baba Sale ya gaya masa duk irin abinda ya sani cikin nutsuwa akan Sa'ade da Baban ta, da irin yadda yadda ya raine ta cikin tsananin kulawa, ya gaya masa malam Hashimu ya gaya masa ba don rayuwa da yake zaton ta kare masa ba bazai taba baiwa Bilkisu 'yar sa ba, sabida bai taba jin dadin zama da ita ba har auren shekara biyu ya shiga tsakanin su ya kare a shekaru biyu kacal.
Ya gaya masa wahalar da yarinyar ta sha a hannun matar uban ta, da yadda ta kare rayuwar ta a talle. Sarki Yusufu ya kara jan Sa'ade jikin sa yana tunani cikin ransa "anya Bilkisu ce da ya sani? Zata haifi Da ta tafi ba waiwaye shekaru goma sha biyu? Kuma bata taba gaya masa ba daidai da kuskure, ya san dai a bazawara ya aureta amma bai san komai ba bayan wannan akan auren nata na baya. Bata son zancen ko kadan. Shi kuma nan duniya sai ya samu zuciyar sa da matsananciyar kaunar Sa'ade, wadda tausayi da soyayyar uwar ta shine sila.
Ya tambayi Baba Sale asalin malam Hashimu, Baba Sale yace "kowa ya san Malam Hashimu bakon haure ne a Tsanyawa babu wanda ya san asalin sa, amma a sanda yake bashi wasiyyar kawo Sa'ade wajen Innar ta ya gaya masa shi dan asalin garin Damaturu ne.
Daidai lokacin da aka daga labulen falon, ta shigo cikin taku na kasaita, sanye cikin farar alkyabba da hular alkyabbar a kan ta. A kasan alkyabbar wani kasurgumin bakin leshi ne mai matukar nauyi. Doguwa sambaleliya, fara sol, kamar da ka taba ta jini zai yi tsartuwa. Fatar jikin ta a murje, ga tsayi ga zati, sannan ga kira ta matan Shuwa-Arab tattare da ita. Akwai barima ta danyen gold makale a gefen hancin ta. Manyan fararen idanun ta sun sha 'kohl' sai walainiya suke suna fidda wani sheki na musamman.
A hankali take taku har ta isa gefen mijin ta ta zauna. Kuyangin ta suka tsaya daga waje. Ta bi mutanen dake sunkuye a gabansa da kallon mamaki, don sun fi kama da normal talakawan gari, amma a falon ganawar sarki da iyalin sa? Kuma saboda su ne aka kirawo ta?
Idanunta suka kai ga birkitacciyar bakauyiyar yarinyar dake zaune gefen sarki, ya rike ta cikin jikin sa. Ta tsurawa yarinyar manyan idanun ta tana kallon ta, idanunta a hankali suke kara girma suna fidda mamaki da al'ajabi. Da gaske ne da aka ce duk inda uwa ta ga dan da ta haifa cikin kowanne hali sai jikin ta ya bata.
Babu wanda ya ce mata uffan tsakanin sarki da Baba Saleh, har saida ta dauke idon ta daga kan yarinyar ta sunkuyar. Wani abu yammmm! Na bin jikin ta. Tsigar jikin ta na tashi. Ta kifa fuskar ta cikin tafukanta, cikin zuciyar ta take fadin......
"dama na san ko bajima ko ba dade zata zo ne da kafafun ta, muddin ni na haife ta. Amma ban zaci a wadannan kananan shekarun ba, na dauka dai sai ta mallaki hankalin kanta zata kawo kanta".
Chapter 4 · 0% Book details