← Book details Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 19

Sashe 15

Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sarki Yusufu AbdulHakimu mai Askira, ya dubi uwargidan sa Ya Gumsu da idanun bacin rai kamar koyaushe ta sako zancen YARIMA SAGEER a gaban sa, idan da abunda ya ke bata masa rai a rayuwar sa to al'amarin Yarima Sageer ne, babban Da, kuma zakka a cikin 'ya'ya mazan da Allah ya bashi, yet mafi madaukakiyar soyayya a zuciyar sa.
Dama an ce wai fitinannun 'ya'ya sun fi shiga zuciyar iyaye. Kusan wannan magana haka take. Duk cikin 'ya'yan sa maza da mata ba wanda yake so irin Muhammad Sageer, sai kuma ya zamo mafi munin jarraba da Allah ya taba yi masa. Ubangiji yayi gaskiya da ya ce "ya'ya da dukiya fitina ne......".
"A takaice dai kina rokawa dan ki alfarmar ya dawo cikin gidan nan ya cigaba da turmushe 'ya'yan mutane, ya cigaba da wulakantani tare da tozartani a idanun Bayi na da hadimai na dake tsananin ganin girma na, ta hanyar turmushe musu 'ya'ya dake hidimta masa?".
Fulani ta runtse ido cikin jin zafin kalaman sa, "Alanguburo, wannan abu ne na kuruciya, kai kan ka da ka ga Yarima ka ga nutsuwa da hankali a tattare da shi, abinda yayi yana yaro ba zai taba maimaitashi cikin hankalin sa ba, balle da 'ya'yan bayi makaskanta a gare shi. Wallahi don an ki yarda da nine, amma Yarima makiya ne suke jifan sa a baya, ba yin kansa bane.
Kai shaida ne akan tsantsani da tsafta irin na Yarima, amma a ce ya rasa matan da zai bi sai 'ya'yan bayi, ai daga nan zaka gane akwai lauje cikin nadi a al'amarin sa.
Bayan haka kuma na dukufa da yi masa addu'a tun tafiyar sa, Allah kuma baya juya addu'ar Uwa, inada kyakkyawan yaqinin cewa ya daina, mu taru mu kyautata masa zato, mu bashi dama ya rayu cikin gidan su kamar kowanne Da cikin gidannan, idan aka sake samun sa da wani laifi makamancin wannan, na amince ayi masa duk hukuncin da ya kamata da shi".
Maganganunta ga dukkan alamu sun dan shigi Askirama. Ya dade cikin halin shiru, ya kasa cigaba da cin abincin sa. A karshe yace da Ya Gumsu wadda ke jiran amsar sa kamar ta shiga zuciyarsa taga abinda yake yankewa.
"Zan yi shawara da Waziri".
"Alanguburo (Allah ya kara maka yawan rai nagode matuka, kuma insha Allahu Waziri zai amince da abinda na zo da shi, don shima na tabbata yana son ganin Awaisu)".
"Ina bukatar kadaicewa". Ya ce da ita.
Ta mike cikin azama ta soma tattare akusan abincin dake gaban sa. "In ma kwana zaka yi kai kadai ka yi, ni dai a bar Da na ya dawo gida". Ya Gumsu ta fada cikin ranta, a fili kuwa dukawa ta yi a gaban sa tana fadin.
"Na bar ku lafiya gatan Askira".

Fitar ta ke da wuya ya kishingida ya lula cikin tunani. Tunani mai zurfi na shekarun da suka gabata.
****

SHEKARUN CAN BAYA
(A Masarautar Askira)
Lokacin da Ya Gumsu ta samu cikin babbar 'yar sa 'Yaa Maira' duk burin sa da dokin sa shine a haife masa Da namiji domin ya samu magaji, kamar yadda kowanne sarki ke burin samu. Amma sai aka haifi Ya Maira, ciki na biyu ma yayi ta fata da addu'ar samun da namiji, amma sai ta kara haihuwar diya mace. Dalilin sa kenan na kara auren Ya Kirjinoma a daidai lokacin domin yana ganin 'ya'ya mata kawai Ya Gumsu zata yi ta haifar masa.
Kamar Allah ya san cewa bai yi farin ciki da haihuwar Mairam Lubabatu ba, bata fi shekaru uku ba Allah ya karbi abinsa.
Ya Kirjinoman ma da ta tashi haihuwar ta ta fari, sai ta haifo masa Mairam Murjanatu. Wannan ya kara mayar da shi desperate ga son haihuwar da namiji. Ba ruwan sa da 'ya'yan sa mata, duk kulawar su da hidimar su da tarbiyyar su tana wuyan iyayen su mata. A kullum ya tuna wancan lokacin ya kan ce "wannan shine deadly mistake da ya taba yi a rayuwar sa". Ba shikadai ba, masu sarauta da yawa hakane tunanin su akan haihuwar fari, idanunsu rufewa yake ga son haihuwar da namiji ba tare da baiwa Allah zabi ba.

Ciki na uku da Ya Gumsu ta samu kusan a tare suka sameshi itada Ya Kirjinoma. Ita ta haifi MUHAMMAD SAGHEER, Ya Kirjinoma ta haifi MUHAMMAD ASHGAR tsiran watanni biyu kacal ne a tsakanin su.
Ashgar sai ya zo da rashin lafiya ta Autism wadda aka fi sani da (autism spectrum disorder). Baya magana (in a meaningful way) tun yana karami saidai ya maimaita abinda aka fada masa sannan kamar kwakwalwarsa ba daidai take ba.
Wannan yasa sarki Yusufu ya dauki soyayyar duniya da tattali da kulawa ta duniya bakidaya ya dora akan lafiyayye Yarima Sageer, wanda hakan ya ruruta wutar mummunan kishi tsakanin Ya Kirjinoma da Ya Gumsu, ya kuma sa Ya Gumsu daukar girman kan duniya ta dorawa kanta, da jin tafi kowa, tunda kuwa ita ta haifarwa sarki Yarima. Koma waye zai biyo baya saidai ya zo a matsayin kanin sa ba Yayansa ba.
Soyayyar data sa tun yana yaro daga uwar har uban suka sangarta shi, basa iya kwabar sa, gata na duniya babu irin wanda basa gwada masa. Hakan bai hana shi yiwa Sageer addu'a ba a duk sallahr farillar sa kan Allah ya kare masa shi a duk inda ya shiga. Musamman da ya bayyana ga kowa cewa yaron fitinanne ne na kin karawa.
Ya addabi 'ya'yan jama'ar gari da mugunta da tsokana, baya zama cikin masarauta saidai cikin 'ya'yan talakawan gari, sune abokan sa abokan mu'amalar sa, don Sageer ya tare yaro a lungu ya targadashi ya fasa masa hanci babu gaira babu dalili ba wani abu bane sabo a wajen jama'ar gari, suna dauke ido ne sabida mutuncin mahaifin sa da farin jinin yaron. Yaro ne mai shiga rai matuka, sabida kwarjini da kyawun suffar da Allah ya bashi.
Yana girma fitinar sa na karuwa a ciki da wajen masarauta.
Kullum Sageer ya fita makaranta da yaron da zai targada ko ya fasawa hanci ba'a kuma isa a kawo kara ba sabida tsoron Ya Gumsu, saidai Awaisu ya gani ya zo ya fada a gida. Waziri ya aika a bada hakuri. Don ba'a bari ma Sarki ya ji. (Awaisu dan Waziri ne kuma sa'an Sageer don haka tare aka raine su), har ta kai ga Awaisu ya kwaso kayan sa duka ya dawo dakin Sageer kwatakwata, sai dai hali kowa nasa daban. Don kuwa Awaisu babu ruwan shi yaron kirki ne, amma duk inda Sageer yasa kafa nan zai mayar da tasa.
Darajar Sarki yasa jama'ar gari suka yi ta hakuri da Sageer tun yana yaro har ya shiga sakandire anan Askira. Kafin ya gama sakandire ne kuma yayi dan hankali ya daina taba 'ya'yan kowa, sabida yawan addua'ar Alanguburo akan sa. Har yake dan shigowa fada a zauna zaman fada tare da shi kamar yadda Sarki ke so ya dinga yi kullum amma ya ki. Lokacin da Sageer ya soma balaga, sai abubuwan gabadaya suka canza, 'yar nutsuwar da yake da ita tabi ruwa. Ya koma neman bayin sa mata.
Lokacin da wannan mummunan labari ya kai kunnnen sarki Yusufu mai Askira sai ya kira Wazirin sa cikin sirri.

"Na yanke shawarar in aura masa mata hudu a rana daya, ina ganin hakan ne kawai mafita ga al'amarin sa".
Waziri Ibrahim ya girgiza kai yana kallon maimartaba sarkin Askira cikin tausayi, ganin yadda ya zabge ya birkice a kwanaki uku kacal da samun wannan labari da yayi. Lallai 'ya'ya da dukiya fitina ne. Kamar yadda mulkin kansa fitina ne da rashin kwanciyar hankali ga bawa. Yace.
"Baza'a yi haka ba Askirama. Baza'a yi haka ba gatan Askira, aure ba laifi bane a shekaru goma sha tara amma karatu za'a kai shi, zamani ya canza, auren mata hudu a rana daya ba zai zamo solution ba, don kuwa zai hanashi maida kai ya yi karatu musamman idan ya soma tara iyali. Ka manta da komai ka kwantar da hankalin ka ka barshi yayi karatun da zai amfane shi muma watarana ya amfane mu. Zan hada shi da Awaisu zuwa duk inda zaka kai shi zan kuma san yadda zan yi Awaisu ya zame masa jagora a komai nasa. Mafi a'ala shine mu bisu da addua".
Ya sani duk duniya babu mai kaunarsa cikin 'yan uwan sa na jini irin Waziri Ibrahim, wanda ya kasance Da ga wan mahaifin sa marigayi sarki AbdulHakimu mai Askira. Bai taba bashi shawarar da in ya bi ta baya ganin mafita da yaqini a cikin ta.
Don haka yayi na'am da shawarar Waziri ba tareda shawara da Ya Gumsu ba.
Chapter 15 · 0% Book details