← Book details Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 19

Sashe 14

Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yarinyar dake tsaye yau a gaban ta wata siririyar budurwa ce, cikin shekaru na tashen balagar diya mace. In bata manta ba tana kamar girman ta aka yi mata auren fari, auren dolen da ya zamo silar zuwan ta duniya.
Tana tsaye daga bakin kofa sanye cikin uniform din ta na makarantar sakandire, kyakkyawar fuskar ta kunshe da sassanyan murmushi, wanda kai tsaye ta fassara shi da murmushin farin cikin abinda yarinyar ta shigo ta tarar tana yi (breastfeeding her baby).
Ta tako a hankali cikin tafiyar data banbanta da ta SA'ADEN da ta sani watannin baya, mai tafiya tana hada hanya, wannan Sa'adatun a nitse take tafiya. Her gait, her serene smiles duka suna kara tabbatar mata da cewa, ta fito ne daga cikin mahaifar ta kwatankwacin diyar dake rungume a hannun ta a yanzu, wato Zarah.
Banbancin dake a tsakani shine; wannan soyayyah ce ta kaita ga haifar ta, yayin da waccan kiyayya ce silar nata zuwan duniya.
Ta yi nisa a wannan tunanin har bata san lokacin da Sa'ade ta karaso gareta ba, kokari take ta karbi 'yar daga hannun ta wadda ta saki nono tana kallon Sa'aden da kyawawan idanun ta. Sa'ade blushing ta ke from ear to ear, ta dauka Fulani zata hana ta daukar diyar ta, amma ga madaukakin mamakin ta sai ta ga ta sakar mata.
Ta dauki kanwar tata tana ta murmushi. "Beautiful!" Ta fada cike da kauna. Fulani ta cigaba da bin ta da kallo ba tare da ta sani ba, duk wani kankanin canji dake tare da Sa'aden a watannin data kwashe bata ganta ba saida ta zaqulo shi cikin idanun ta.
"Ashe kilewar diya mace ba wuya muddin zata je makaranta!" Fulani Bilkisu ta fada a zuciyar ta. Tana son comparing soyayyar data ke ji akan Sa'ade da Zarah. Sai ta ga cewa ratar dake a tsakani mai tsananin fadi da girma ce, ta haifi Sa'ade ne kawai amma babu ko digon soyayyar ta a zuciyar ta, sai tausayi da kyautayi irin na zuciyar musulunci.
Yanzu ne ta san kaunar uwa akan dan ta, da ta haifi 'ya da wanda take so. Can wani lungu na zuciyarta kuwa kururuwa yake yana objecting: idan soyayyar Sa'ade da ta Zarah, bata zo daidai da juna ba, sai dai ace ta Zarah ta rinjayi ta Sa'ade, amma ba wai ace babu burbushin ta ko kankani a zuciyar ta ba.
Bata ankara ba sai ganin 'yar ta tayi a bayan Sa'ade, tasa tawul din da aka nannade ta a ciki tagoye ta tsam ajikin ta, ta soma dan jijjigata sabida dan rikici data ke yi irin na jarirai. Sai tasamu kanta da kasa cewa ta sauko mata 'yar ta, ta mike ta shige turakarta ba tare da ta ce da ita komai ba. Dama kuma tana so ta huta din, gashi ta sallami kowa tace bata son ganin kowacce baiwa a bangaren ta sai gobe da safe in Allah ya kai mu. Sai ganin tsayuwar Sa'ade ta yi a gaban ta ba zaton ta ba tsammani.
Sa'ade saboda jin dadin Fulani ta bar mata Zarah sai ta nufi dakin ta goye da ita, roba ta samu ta hada ruwan dumi ta saukota ta soma yi mata wanka, ta gama ta nade ta cikin shawul ta fito kan gadon ta ta dauki basilin din ta tana shafa mata.
A lokacin Fulani ta shigo, ta bude baki da zummar yin fadan don me ta yi mata wanka bayan ba'a jima da yi mata wanka ba? Amma sai ta ga yarinyar na ta bangala dariya Sa'ade kuma ta himmatu wajen yi mata wasa a cute kumatunta. Sai suka bata sha'awa, ta juya silently ta fita. Ta dauko set din kayan baby na sanyi ta dawo ta watsawa Sa'aden ta sake juyawa ta koma.
Shikenan daga wannan ranar Sa'ade ta kwace rainon Zarah daga hannun Fulani da masu rainon ta, kayan yarinyar ma saida ta san yadda tayi suka dawo dakin ta. Tsakanin ta da Fulani shine kawai idan ta bukaci nono.
Hausawa suka ce wai "Mai Da wawa ne", wannan kyautatawa da kauna ta Sa'ade ga Zarah a hankali yake hakurkurtar da zuciyar Fulani Bilkisu, daga mummunan kullacin Mal. Hashimu dake cikin ta, wanda ya hanata ganin farin Sa'ade har ta kaunace ta matsayin 'ya 100%.
A hankali ta soma rage fada, da tsawa da hantarar da take yawan yi mata, ta soma yi mata magana jefe-jefi cikin sanyin rai.
Satin ta uku a gida sai ga Raheema Kyari, wannan karon ba'a hanata shigowa ba, Kuyangar data rako ta sai ta hada ta da Fanna, ita kuma Fanna tace ta jira daga waje, ta nemo izni tukunna.
"Kawa kuma daga Maiduguri?"
Fulani ta fada cikin mamaki.
"Haka ne ranki ya dade, sannan ta tabbatar min ita aminiya ce ga Sa'adatu sannan ta san da zuwan ta".
Fulani ta hadiye fushin ta wanda tayi aniyar saukewa akan Sa'ade bayan tafiyar bakuwar, ta ce Fanna ta shigo mata da yarinyar.
Cikin sallama da shiga ta mutunci da kamala Raheemah ta shigo, tunda ta shigo Fulani ta kura mata ido. She looks so much like her father wanda ta yi wa farin sani. Mikewa tsaye tayi ba tareda ta san lokacin da ta yi hakan ba, hatta tsagin fuskarsa biyu-biyu dogaye gasu nan kwance a fuskar Raheema.
Da ta gaisheta da kyar tayi controlling razanar ta ta amsa,
"yaya sunanki?"
"Raheema Kyari Babagana"
"Kyari?!"
Ta fada da amon muryar da ya baiwa Raheema mamaki, "eh, sunan Babana kenan" "daga wane gari kike?" "Daga Maiduguri na zo, acan muke zaune, amma mu 'yan asalin Damaturu ne".
"Shikenan dangin ubanta sun biyo ta, a lokacin da na fara sanyata a raina".
Fulani ta ayyana a zuciyar ta, ta kuma kudiri aniyar kin gayawa Sa'ade kowacece Raheema a gareta.
"Shiga nan dakin, tana ciki"
Ta fada tare da nuna mata dakin, ta kuma tashi ta bar musu area din gabadaya zuwa turakar ta.
Sa'ade sai ganin Raheema ta yi ta shigo da sallama, zo ki ga gudu da murna wajen Sa'ade, saura kadan ta kada Raheema. Ita kuwa sai dariya take. Ta dauki Zarah dake tsakiyar gadon ta tana fadin "masha Allah, beautiful baby". Hira kamar ta kashe su. Fanna ta shigo wa da Raheema abinci na musamman suka ci tare cike da farin ciki.
Can da yamma Raheema ta ce "Sa'adatu ki zagaya da ni mana in ga masarautar taku in samu abun baiwa su Sarina labari". Sa'ade tayi dan jimm! Kafin tace "ni bana zuwa ko'ina, daga daki sai daki, Fulani bata bari na". "Amma meyasa?" Inji Raheema. Ta dan kyabe baki "i don't know. May be sabida kishiyoyin ta". Daga haka suka bar hirar.
Washegari Fulani ta sa aka yiwa Raheema sallama ta girma, aka maida ita har Maiduguri.
****
Ya Gumsu ta shiga turakar mai Askira cikin kwalliya ta kasaita a matsayin ta na mai girki ranar, abinci yake ci tana gefen sa tana masa firfita, cikin hila irin ta matan da suka san kan mazan su ta yi durkuso a gaban sarki, ta ce "Alanguburo (Allah ya kara yawan rai) Yarima na rokon alfarmar a bar shi ya zo gida, ko da na sati daya ne, shekaru goma kenan rabon sa da gida, yayi digiri yayi masta ya jima yana aiki har ya fara digiri na uku, yana cikin damuwar rashin sanin halin da 'yan uwan sa ke ciki, yayi alkawarin baza'a sake samun sa da laifi makamancin na baya ba".
Nan da nan wani kwantaccen bacin rai ya bayyana a fuskar sarki, ya dago idanun sa da suka kada ya dube ta, sai da hantar cikin ta ta kada. Ta yi azamar sunkuyar da kai amma a ranta zata jure komai in har zai bar dan ta ya zo gare ta, haka kawai ai ba shikadai ne fitinannen Da ba, fitinannun nawa ya haifa? Amma bai daukewa Ya Kirjinoma nata ba sai shi kadai bayan ba fin su fitinar yayi ba. Yana kusa da su ma suna masa fada ai zai fi gyarawa fiye da hannun aminin nasa.
Chapter 14 · 0% Book details