← Book details Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 19

Sashe 10

Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda aka kai Sa'ade da Humairah dormitory dalibai 'yan uwan su ke kallon su, ba don komai ba sai don irin tsadaddun kayan abincin da ake shigo dasu katan-katan ana loda musu a lokokin su, a karshe lokokin nasu ma sun yi kadan su kwashe kayan, sai Humaira ta ce da metron da masu jerawar su je da sauran ta bar musu. Ko kallon Sa'ade bata yi kada a ce tare suke, amma kayan abincin su ba banbanci haka takalmi da jakar makarantar su, wanda ya tabbatarwa 'yan dakin cewa tare suke din. Gadon Humaira na gefen na Sa'ade, don haka ta yi amfani da wannan damar ta maida ita baiwar ta, komai tana daga kwance take sa ta ta yi mata, dauko wannan miko wancan, ko kofi zata yi amfani da shi sai ta sa Sa'ade ta wanke mata shi, kuma da yake Sa'aden ta iya kitso ita ke yi mata duk sati, basa yin wanki iyayensu ke biya a wanke musu shiyasa Sa'ade ta samu sauki, da har wanki da guga ita zata ce ta yi mata. Girman kai irin na Humaira ya hanata alaqa da mutanen dakin, ita kadai take rayuwar ta ko a class don bata ga wanda ya isa tayi mu'amala da shi ba duk da cewa duk 'ya'yan masu kudi ne a makarantar amma a wurin Humaira in ba ka da jinin sarauta cikin jikin ka to baka isa mutum ba. Kuma duk makarantar ita kadai ce 'yar Sarki. Sabanin Sa'ade wadda ta maida kanta abokiyar kowa a dakin nasu, in har bata hidimar Humaira to zaka sameta cikin jama'ar dakin suna hira da harkar arziki, ga ta da kyauta, haka take ta rabar da kayan abincin nata musamman ga wanda ta lura yana da bukata, cakuduwar ta da dalibai 'yan uwan ta wadanda suka fita experience da exposure ya sa ta fara samun wayewar kai. A aji kuwa duk ita ce koma baya a kowane darasi daga na boko har na addini, amma bata barin hakan ya kashe mata gwiwa, ya cire mata hope na cewa da sannu zata iya idan ta sanya jajircewa da bada himma. Haka monitar ajin nasu Raheema Kyari ke yawan gaya mata, wadda tasu ta zo daya, sakamakon yawan tambayar ta abubuwa da Sa'ade ke yi idan bata gane ba ba tareda nuna jin kunya ko girman kai ba. Ba ajin su daya da Humairah ba ita 'yar JSS 3 ce yayin da Sa'ade ke JS 1. Don haka tafi jin dadin rayuwa a class fiye da a dormitory (dakin barcin dalibai) sabida babu Humaira mai takura mata, a nitse take karatun ta tare da likewa monita Raheema tana daukar ilmi daga wajen ta. Malaman ko sun so yin korafi akan rashin kokarin Sa'ade sai su fahimci abin nata daga tushe ne wato bata samu foundation a makaranta mai kyau ba kamar sauran daliban makarantar, don in sun tambayeta wace makaranta tayi tana gaya musu a kauyen Tsanyawa ne, makarantar da maigari yasa aka bude, don a koyawa yara A BA CA DA sai su daga mata kafa musamman in suka lura da yadda take da kishin abun a zuciyarta, in aka koya abu bata gane ba har kuka take yi. Duk kokarin Raheemah na koyar da ita ba komai take ganewa din ba musamman darasin lissafi, da yawa a makarantar sun dauka Sa'ade baiwar Humairah ce, irin 'ya'yan bayi da ake hado 'ya'yan sarakai dasu su zo makaranta tare don su dinga hidimta musu, sabida haka Humairan ke nunawa. Sannu-sannu bata hana zuwa, saidai a dade ba'a je ba, a hankali Kwakwalwar Sa'ade ta soma budewa, musamman a haddar Al'qurani da Ingilishi. Raheema ta taka rawar gani akan hakan don fisabilillah take kaunar Sa'ade sabida saukin kanta, baban Raheema babban dan kasuwa ne a jihar Maiduguri wanda sunan sa yayi fice akan sana'arsa ta fata. Watarana Raheema ta kawo wa Sa'ade ziyara dakin su, sai ta same ta durkushe gaban Humaira ta sunkuyar da kai tana hawaye, Humairan na ta zazzzaga mata fada har tana fadin dama 'yan kalen dangi basu iya cin arziki ba, banda haka tun safe ta sa ta gyaran sittirunta amma tasa kafa ta fice yawon neman suna bata gyara mata ba, su ko Fulani Bilkisu ba wata tsiya bace a wurin su tunda sun san asalin ta balle su ya-ku-bayin data kawo musu gida suna cinye arzikin Babansu. Ba fadan data ke mata ne yasa ta kuka ba, domin in da sabo ta saba, ambaton sunan Fulani data yi ta zaga ne ya tsaya mata a zucci. Ya kona mata zuciya. Fulanin da has never been nice to her in any way amma zuciyar ta na mata wani irin so, da bata taba jin sa akan kowa ba including Baban ta. Rahima ta kama hannun ta ta cira ta tsaye suka bar dakin, Humaira ta sakar musu tsaki tana fadin "ya'yan mutsiyata, gayyar tsiya". Can bayan dormitory suka zaga suka zauna akan duwarwatsun da ke wajen, Raheema ta ce "wai don Allah Humaira ke baiwar ta ce? Ko iyayen ki bayi ne a gidan su?" Bata san me yasa ta yarda da Raheema ba, tun sanda ta fahimci Raheemar na tausaya mata tsakani da Allah. Ta girgiza kai tare da share hawayen idon ta "ni ba baiwar ta bace, ana riko na ne a gidan su, kishiyar mamanta ce yar mahaifiyata a hannun ta nake". Raheema tace "tabdi! Amma shine kike mata bauta tana miki wannan wulakancin? Ke ba baiwar ta ba iyayenki ba bayin su ba? To wallahi ki kama kan ki, ki nuna mata zaman kan ki ke yi ba zaman ta ba in ba haka ba watarana sai ta kai ga taba lafiyar jikin ki" da sauri Sa'ade ta girgiza kai. "Zan yi mata komai saboda Baban ta!". Raheema ta rasa abinda zata ce, sabida a amon muryar ta kadai ta fahimci akwai wani girmamawa da kauna na musamman data ke yi wa Baban Humaira, abinda ta fada har zuciyar ta ya ke. Wannan ya tabbatar mata Sa'adatu irin mutanen nan ne da basa manta alkhairin da wani yayi musu komai kankantar sa. **** An yi jarrabawar karshen zango, as expected Sa'ade ta dauko na biyun karshe, ta yi kuka har ta gode Allah, amma a islamiyya ta yi dan kokari ba laifi musamman a hadda. Damuwar ta yadda zata dauki wannan mummunan sakamako ta kaiwa Alanguburo, bayan ta yi masa alkawarin yin kokari iyakar iyawar ta. Raheema ta ce ta bata lambar wayar wani a gidan su zata kira ta in ta koma gida, Sa'ade tace banda Fulani babu mai waya a sassan su, ita kuma bata san lambar ta ba, ko ta sani bazata yi karambanin bayarwa ba Fulani ta tsinke mata kunne haka kawai. A daren ta hada musu kayan su da zasu tafi dasu gida a kananan trollies din su, sauran kayan abincin da suka rage Humaira tace ta fitar duka ta kaiwa metrons. Ta yi sallama da 'yan dakin su cike da kewa suna fadi a ransu ai gara ta je gida ta huta da wannan bautar data sha ta gimbiya Humaira, wasu kuma suka ce a ran su watakila har a gidan ma irin bautar data ke mata kenan. Kusan su ne na farko da aka zo dauka a washegari. Suna tsaye ita da Raheema a jikin bishiya suna hira, Humaira na daga zaune a gefe akan jijiyar bishiya tana ta harare-harare irin wanda ta saba da kallon kowa a wulakance. Zungureriyar mota kirar 4matic baka wuluk ta yi parking a gefe, da rubutu baro-baro cikin ruwan gwal "ASKIRA EMIRATE". "Ma'assalam Raheema, an zo daukar mu" Ta fada tana jan trollies din biyu dake gaban ta, nata da na Humairah, Raheemah ta daga ido tana kallon inda ta nufa, tun kafin ta karasa dogarawa biyu suka yi wuf suka fito daga motar suka karbi kayan hannun ta. Ta karanta rubutun ta sake karantawa "ASKIRA EMIRATE" Ashe daga masarautar Askira suke, no wonder Humairah take mulkin data ga dama. Baban ta ya sha basu labarin masarautar Askira da irin dimbin arzikin ta da shaharar ta a yankin Borno. Ta karasa da gudu ta cimma Sa'ade, ta rike hanayen ta, tana murmushi ta ce "ki gaida mun Fulani, i will give you a giant surprise insha Allah" Sa'ade ta yi dariya ta ce "Fulani zata ji, ki gaida Mama dasu Sarina (kannen ta)". Raheema na juyawa ta kusa karo da Humairah, da sauri ta bata hanya sabida mugun kallon data sakar mata. Ta shiga gefen dama data saba zama dogarin ya rufe kofar. Ya zaga mazaunin sa ya zauna suka ja motar zuwa get, inda suka cike takardun daukar dalibai sannan aka basu dama suka wuce daga get din makarantar. Tun daga kofar gida kuyangin Humaira na tsaye suna jiran isowar ta. Cikin rakiyar su suka wuce cikin gida kowacce ta doshi bangaren su. Fanna ta fara cin karo da a bakin kofar shiga unguwar Fulani Bilkisu da alama jiran karasowar ta take, tana mata murmushi tace "sannu da zuwa 'yar gida na, yaya hanya kuma yaya karatu?" Tare da karbar jakar kayan ta wadda Humaira ta hana kuyangin ta su daukar mata. Suka wuce zuwa ciki, tsakanin ta da sauran bayin Fulani sai ido, don ba'a basu damar alaqa da juna ba, only Fanna. Ta kaita har dakin ta, ta hada mata ruwan wanka a bathtube sannan ta fita don ta kawo mata abinci. Sa'ade tayi wanka ta ji dadin jikin ta, ta sauya kayan makaranta zuwa doguwar rigar atamfa exclusive mai hasken sararin samaniya, sosai tayi kyau, farar fatar ta ta yi tas, wanka da tsafta sun kama jikin ta, ita kanta data tsaya a jikin mudubin dogon yaro ta kalli kanta sai da ta razana, don gani tayi kuruciya kadai ce zai sa ta kasa cewa Fulani Bilkisu ce a cikin mudubin. Ta ga ta kara tsayi, hancin ta da idon ta sun kara fitowa dara-dara, tsarki ya tabbata ga Ubangijin halitta. Sai data ci abinci ta koshi tayi sallar data kufce mata sannan ta hau gado sai barci. Cikin barcin ta ji an dala mata duka a cinya, ta zabura ta mike zaune, Fulani ce tsaye a kanta ta ci gayu kamar mai shirin gasar sarauniyar kyau. "Wa ya ce da
Chapter 10 · 0% Book details