Sashe 18
Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Bakon da ake ta shirye-shiryen domin sa bai shigo sassan nasu ba sai bayan sallar la'asar. Tana jin wani irin kirari yana tashi daga bakin bayi (Gyara kimtsi da kyau... Lafiya dan zakin duniya. Lafiya dan malafar duniya. Lafiya dan mai fada da cikawa. Lafiya dan masha-sha. Lafiyar ka dama da hauni mai nasara. Zauna dai-dai dan bawan Allah. Zauna dai-dai dan waliyin Allah. Aminchinka rike linzamin ka dan bawan Allah....zauna dai-dai dan masu Alheri...) daga bisani ta ji muryoyin mutane da alama ba shi kadai bane, mazane sun kai su biyar, bayan Yarima Sageer akwai Awaisun sa, kannen sa maza su hudu tareda Ashgar duk da ba lafiya ce da shi ba hannun sa na cikin na Yarima kamar zai maida shi cikin sa. Tana so ta yi leke tana tsoron Fulani, sai ta zo bakin kofar dakin ta ta kasa kunne ita a dole sai taji me ake yi kuma su wanene? Lol.
"Yarima in a hanya na ganka ai bazan taba gane ka ba, sabida a hoto kawai nake ganin ku wajen Askirama, gara kai kana nan a bakin ka, amma Awaisu ya koma bature sak!" Inji Fulani.
Awaisu yayi murmushi ya ce "duk da haka gara ni ban manta Kanuri ba, amma wannan ko Hausa da kyar yake yin ta, su sanya alkyabba kuwa tuni ya manta yadda ake yin su balle yadda zai wara kafafu ya hau doki". Yarima ya harareshi a lokaci guda yana jijjiga Zarah dake hannun sa, wadda tun ganin sa da ita jiya Allah ya sanya matsananciyar kaunar ta a zuciyar sa musamman da ya ji cewa sikila ce, yayi kissing kumatun ta yace.
"Ranki ya dade da fatan zaki bani Zarah in tafi da ita Amsterdam in kin yaye ta in sa ta a makaranta?" Fulani ta ce "in ka yi aure ba? Kuma matar 'yar gida ka aura wadda bazata ji kyashin rike maka diyar ba" Awaisu ya fashe da dariya da ya tuna wadda Yarima yake shirin aure, dan kuikuiwo ne pet din ta dake biye da ita duk inda zata, ya ga yadda zata rike dan mutum sukutum ko sallah bata yi.
Ta kasan ido Yarima ke kallon sa, shi kadai ya gane me yake nufi da kallon da yayi masan, don haka ya ja bakin sa yayi shiru yana cigaba da dariya. Yarima ya dago manyan idanun sa farare kal, ya sauke su a kan maridin dan uwan sa wato Ashgar, ya ce.
"Ashgar, ina labari?" Murmushi Ashgar din yayi, sannan ya maimaita abinda Yarima ya ce, ba tare da ya san me ya fada ba, Awaisu yace "ya kamata ace Ashgar yana karbar rehabilitation therapy, da an samu cigaba sosai a rayuwar sa, a can kasashen da muka fito ana bawa irin wadannan lalurorin muhimmanci sosai su yi rayuwa mai ma'ana kamar kowa". Suhail dan Ya Kirjinoma yayi tsaki ya ce "da dai Ya Kirjinoma zata yarda cewa ciwo ne daga Allah mai zaman kansa, amma ita kullum zancen ta bakaken aljanu ne aka tura masa" haka hirar ta koma a kan Ashgar, Yarima da Awaisu na fadin ba wani aljanu, in maimartaba zai amince da Ashgar zasu koma Amsterdam su kai shi rehabilitation center na masu lalurar sa. Yarima ya ki ajiye Zarah a tsayin zaman su a falon, tana rungume a hannun sa, baya gajiya da kallon ta yana mata wasa jefi-jefi.
Aka gabatar musu da kabakin da Fulani ta shiryawa Yarima na barka da zuwa, sosai suka ci abincin suna hira a tsakanin su cike da kaunar juna, duk cikin matan maimartaba sai yaji Fulani Bilkisu tafi kowacce samun matsayi a zuciyar sa akan dalilin da bai sani ba. Koda yake a fili yake; Fulani na da matukar kirki sannan tana kaunar 'ya'yan Askirama da zuciya daya kamar yadda yake kaunar ta. Hassada ce kawai da kishi irin na mata zasu sa ka kushe Fulani Bilkisu ko wani hali na ta, domin ita din ta yi ta kowanne bangare.
Basu bar sassan ba sai ana gab da kiran sallahr magriba, shima din sai da Ya Maira ta biyo bayan su don ganin uwar da suke kullawa a unguwar Fulani Bilkisu wajen awanni biyu, tana shigowa ta ce in ya gama yaje Ya Gumsu da bakin ta na jiran sa, dole suka yi haramar tafiyar yana gayawa Fulani gobe in ya dawo daga hawan kilisar da zasu yi zai dawo ya ga Zarah. Tayi murmushi tace "Zarah na murna da dawowar wannan babban Yaya nata, mai ji da ita, bakon Amsterdam!". Yayi murmushin da ya kara masa kyau da ilhama ya sunkuyar da kai sannan ya fita, ya bar kamshin turarensa INVICTUS (by Paco Rabbanne) a sassan Fulani bakidaya.
Zata wuce daki ta hango Sa'ade na leke ta tsakanin kofa, murmushi tayi tace "uwar gulma". Sa'ade bata ankara ba sai ganin Fulani tayi agabanta, sosai ta razana ta ja da baya, Fulani tace "uban me kike lekawa?" Ta zumburi baki. "Ni ba abinda nake lekawa, maganar maza na ji, nikuma na san maza basa shigowa sassan nan". Fulani tace "to ina ruwan ki da ko su waye? Ko maza na soma kawowa? Wallahi ki kiyaye ni bana son gulma, ba ruwan ki da duk abinda bai shafeki ba a gidannan don kuwa ba gidan ubanki bane, kara ki Uban su yayi". Hawaye suka ciko idon Sa'ade, ba yau Fulani ta soma cin mutuncin ta ba akan kankanin abu, amma sai ta ji na yau ya fi na kullum kona mata rai, ta yi alkawarin ta daina mayarwa Fulani magana amma tsabar bacin rai bata san sanda ta ce cikin hawaye.
"Tunda kin ce inada dan uwan uba ki kaini wajen sa mana!"
Fulani tace "an ki a kaiki, anan zaki zauna zaman AGOLANCI. Zaman da ubanki yake guje maki, gashi ya same ki bayan ran sa. Enjoy!".
Ta fice ta rufo mata kofar da karfi.
****