← Book details Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 19

Sashe 17

Masarautar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Yau tun safe masarautar Askira ta tashi da bushe-bushen algaita da kalankuwa da goge irin na masarautar, baka jin komai sai tashin kirarin gidan sarautar Askira, maroka da makada daga kowane bangare na garin sun barko sun cika kofar fada, haka tun jiya 'ya'yan sarki maza da mata na nesa dana kusa sun hallara a gida dakunan iyayen su mata ba don komai ba sai don marabtar Yarima Sageer wanda ya kwashe shekaru goma baya cikin masarautar gabadaya. Mairam Murjanatu ce kawai bata samu halarta ba saboda ta yi nisa tana kasar Turkiya.
Naja'atu da Humaira kusan sun fi kowa zaquwa da murnar ganin Yariman domin sune basu san shi ba, suna kanana sosai ya tafi, sai kuma jikokin gidan wato 'ya'yan Ya Maira su wajen takwas. Lokacin da motocin su suka iso fada, sai kade'kaden da bushe-bushen ya karu. Wani abu ne da Sa'ade bata saba ji a cikin masarautar ba in ba wani muhimmin abu ake ba, kamar nadin sarauta ko bikin aure. Duka-duka ma dai tun zuwan ta Askira bai fi sau biyu ta ji irin wannan ba, don haka ta gane akwai muhimmin abin da ke faruwa yau a masarautar.
Tana so ta san me ake yi, amma ta rasa wanda zata tambaya, don Fulani ma tun safe tasa aka shirya Zarah suka wuce babban falon ganawar sarki da iyalin sa, inda sauran iyalin gidan suka hallara, ko ta kanta bata bi ba. Fanna ma dai ta lura yau dukkan su busy suke a cikin gida da girke-girken da iyalin gidan zasu ci da wanda za'a tarbi Yarima Sageer da shi.
Don haka itama tun safe bata sa ta a idanun ta ba.
Sa'ade duk ta zama curious ga son sanin me ake yi haka cikin gidan, a ranta tace yau dai zata yiwa Fulani laifi sau daya, dole taje ta baiwa idon ta abinci, iyakaci Fulani in ta kamata ta murde mata kunne ko ta mare ta.
Da wannan tunanin ta dau mayafin ta, sadaf-sadaf ta fita daga sassansu, a falon daya raba sassan Fulani da inda sauran bayinta ke shige da fice ta ci karo da wasu duk suka zubo mata ido, bata ko kallesu ba ta daga kafa ta fice daga unguwar Fulani Bilkisu.
Mayafin ta ta janyo ta rufe rabin fuskarta, idanun ta kawai ake gani. Ta rasa ina zata dosa? Dan ba sanin kan gidan tayi ba, daga bisani ta lura da inda bayi ke karakaina da manyan farantai, kanta tsaye ta doshi wajen.
Wani babban falo ne ta ga bayin suna shiga da sundukan abinci da katon katon na lemukan gongoni, ta bi bayan su a hankali har zuwa kofar falon, sai ta zagaya ta bayan tangamemeiyar tagar gilashi ta falon ta leka a hankali. Ba zata iya shaida fuskokin data gani ba don tagar ta baya ce duk sun juya bayan su, ta dai hango Alanguburo akan kujerar mulkin sa, zagaye da shi kananan yara maza da mata har da matasan 'yammata kamar ta, a gefensa daura da shi bisa kujerar da bata kai tasa ado ba wani zankadeden matashi ne, duk da bata yi nasarar ganin fuskar sa gabadaya ba ta ga gefen fuskarsa, da dogon karan hancin sa, kalar bakar fatar sa kamar ta mutanen kasar Morocco, hular sa ta nitse a cikin tarin sumar kansa sannan fararen kayan dake jikin sa babu ado irin na sarauta a jikin su. Normal tsadadden yadi ne (filtex London) mai taushi a idon mai kallon sa, sauran mata da mazan dake zagaye dasu duk bata ganin fuskar su, amma ta shaida bayan uwarta Fulani da kalar tufafin dake jikin ta kasancewar ta san ta da kayan. Wata zuciyar ta ce "yi ta kanki Sa'ade, idan Fulani ta kama ki a gaban kowa sai ta yi miki dan banzan duka. Tunda dai kin gani taro ne suke yi nasu su-ya-su (family get together)".
Wata kyakkyawar mata ta juyo tana magana da wata dattijuwa, sai ta gane fuskar ta, tana daga cikin wadanda suka je wa Humaira visiting har suka kira ta (Ya Maira). Salin-alin ta soma ja da baya, sawun ta a likkafa, sannan ta juya da sassarfa akan kafafun ta ta koma inda ta fito. Ko ba komai ta ba idon ta hakkin sa.
Da Fanna ta fara cin karo ta saka bayin dake sassan a gaba tana ta yi musu fada don me suka barta ta fita, sai gata ta shigo kamar an koro ta, da sauri Fanna ta doshe ta tana hamdala. "Daga ina kike Sa'adatu?" "Kai Fanna, sai kace wata karamar yarinya zan bata a cikin gidannan ne da wayo na da idanuna da komai?" "Ba cewa na yi zaki bata ba ranki ya dade, inda Fulani ta shigo ta nemeki bata gan ki ba me kike so mu ce mata?" Sa'ade ta murguda baki tayi shigewar ta ciki tana kunkuni.
"Haka kawai ayi ta kulle mutum a daki sai ka ce wani daddawa, su suna can suna jin dadin su cikin jama'a, bata so a ganni don me ta haifo ni?"
Wunin ranar zungur bata ga Fulani ba, sai washegari da safe ta fito don ta gaisheta kamar yadda ta saba duk safiya in dai tana garin, ta same ta ta hargitsa bayi suna ta gyare-gyare a sassan wai Yarima zai shigo ganin Zarah, yau zai shiga kowanne sassa na gidan. Sama-sama Fulani ta amsa gaisuwar ta sannan ta cigaba da bada umarni, ta juya cikin jin haushi, ta tsani wannan rashin bata muhimmancin da Fulani take yi amma ba yadda zata yi.
Chapter 17 · 0% Book details